Skip to content
Part 13 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Na yunƙura kenan da nufin juyawa sai mamana ta dafa ni tana mai cewa,

“Ina tare da kai Haidar, ko me zai faru ina tare da kai.”

“Ni kuma ina tare da Allah.”

Na bata amsa fuskata cike da murmushi. Sa’annan na miƙe tare da juyawa na fuskanci sauran mutanen da ke zaune zagaye da wannan wuta da ke faman ci. Ko da juyowa ta sai na yi arba da waɗansu tsofaffin mutane su uku. Dukkansu za su kai kimanin shekara tamanin-tamanin a duniya. Domin har gashin kansu ya canza launi daga baƙi ya koma fari fat saboda furfura. Wanda ke tsakiya shi ne a miƙe, kuma ko ba a faɗa min ba na san cewa shi ne ya yi wannan maganar. Don haka sai na nufe shi kai tsaye ba tare da wata fargaba ba. Ko da na iso gare shi, sai na tsaya sa’annan na dube shi cikin girmamawa na ce,

“Gani gareka ya kai wannan dattijo, shin ko zan iya sanin ku su waye da kuma dalilin da ya sa kuka kira ni?” 

Ko da jin haka sai na ga yayi murmushi sannan ya ce,

“Ga jiji da kai kuma ga girmama na sama da kai, babu shakka kai jinin Hammadi ne.” har na buɗe baki da nufin in tambaye shi abinda yake nufi da wannan magana sai ya katse ni da cewa,

“Ni sunana Fafale, wannan da ke dama da ni kuwa sunan shi Bafale, wannan da ke dama da ni kuma sunan shi Bankami. Mu ne jagororin wannan ƙabila ta maƙera a ƙarƙashin shugabar mu Shamadara. Ba komai ne yasa muka kira ka ba face a bisa al’adar mutanen wannan ƙabila tamu ta maƙera, muna yi wa mutum gwajin abubuwa guda huɗu domin tabbatar da shi a matsayin ɗaya daga cikinmu yayin da ya kai wasu shekaru ƙayyadaddu. Waɗannan abubuwan kuwa su ne waƙa, jarumta, ‘yan uwantaka da kuma ƙira. Ka sani cewa, muna yin jarabawa akan waƙa ne domin ita ɗin abar ɗebe kewa ce tare da isar da saƙo cikin sauƙi. Sannan muna yin gwaji akan jarumta ne domin ita ce ibadar mutanen wannan birnin tun kafin zuwan sauran addininai cikinsa, domin kuwa jaruman cikinmu ne suka ƙwato wa kansu da sauran mutanen birnin ‘yancin da suka rasa na tsawon lokaci. Abinda ya sa muke yin jarabawa akan ‘yan uwantaka kuwa shi ne, saboda mu a al’darmu duk abinda ya taɓa ɗayanmu to kamar ya taɓa mu ne gaba ɗaya. Abu na huɗu kuma na ƙarshe shi ne ƙira. Kamar yadda ka sani mu maƙera ne, kuma muna alfahari da sana’ar mu ta ƙira fiye da yadda kowa ke tsammani. Ko da yake ba ma gudun wani namu wanda bashi da baiwar ƙira, an fi ganin wanda ke da ita da daraja fiye da wanda bai da ita. Ya kai wannan ɓaƙo, ka yi sani cewa tuni ka cinye ɗaya daga cikin waɗannan jarabawa da za mu yi maka a lokacin da ka tunkari waɗannan tsuntsaye masu aman wuta har ka tseratar da shugabar mu. Kuma da muka yi mata magani irin namu ya kasa tasiri sai gashi kai ka yi mata naka kuma har ya yi tasiri. Sannan yanzun nan duk mun ga yadda hankalin ka ya tashi sakamakon ganin rauni a fuskar wacce duka ba ku wuce awanni bakwai da haɗuwa ba. Lallai ka sani cewa, ba don taimakonka ba da mutanenmu da yawa sun halaka a sakamakon wannan hari da tsuntsayen suka kawo mana. Kuma wannan nagarta da soyayyar ‘yan uwa da ka nuna mana ta sa tuni ka samu matsuguni a cikinmu. Amma duk da haka, za mu yi maka sauran jarabawar guda uku in har ka amince.”

Ko da na ji wannan jawabi daga bakin tsoho Fafale sai nai ajiyar zuciya sannan na dube shi da kyau na ce,

“Ya kai wannan dattijo mai karamci, ina godiya sosai a gareka bisa karramani da kuka yi. Kuma na amince da wannan jarawaba da za ku yi min, amma ku sani cewa, tun da nake sau ɗaya na taɓa shiga maƙera kuma ban taɓa koyon ƙira ba, don haka ba lallai ba ne in yi abin da kuke tsammani ba, iya abinda zan iya yi shi zan yi, babu ragi kuma babu ƙari. sai dai kuma ba uzuri nake bayarwa don a sassauta min wani abu daga cikin jarabawar ba. Sannan karamcin da kai min ne nake ƙoƙarin maido maka da shi.”

Ko da tsoho Fafale ya ji jawabina sai ya yi murmushi sannan ya dubi Bafale dake dama da shi ya jinjina mishi kai sannan ya dubi Bankami da ke hagu da shi wanda shi ma ya jinjina mishi nashi kan sannan ya kalle ni ya ce, 

“Babu shakka kai jinin Hammadi ne, saboda da duk wani abu da kake aikatawa ko furtawa kake ƙara tabbatar mana da hakan. Ka sani cewa har mahaifinka ya bar garin nan irin tsarin da yake kai kenan, don haka mun ji jawabinka kuma mun amince da shi. Yanzu sai ka rero mana waƙa mu ji irin fasahar da kake da ita a wannan fannin.”

Ko da gama faɗin haka sai tsoho Fafale ya koma mazauninsa ya zauna sannan ya harɗe ƙafa wuri guda. Nan fa wurin ya yi tsit kamar mutuwa ta gifta, ya zamana ba a jin ƙarar komai face wutar da ke ta faman ci a tsakiyar wannan fili. Ni kuwa babu abinda nake yi face tunanin wacce irin waƙa zan yi wa mutanen nan wadda ta dace da su. Nan fa na fara saƙe-saƙe a raina ina tunanin abinda ya kamata in yi. Na kai dubana inda mamana take tare da su Sanafaratu da Fa’iza na ga duk sai murmushi suke yi min. Na sake maida dubana inda Sadiya da Imran suke tsaye, su ma dai murmushin suke yi min. Nan fa na fara addu’a a raina ina fatan samun waƙar da zan yi wadda zata dace da mutanen nan domin bana so in basu kunya. Can kamar an ce in ƙara kallon inda Sadiya take, ai kuwa sai na kai dubana gareta, hakan ya yi daidai da lokacin da wata iska mai ɗumi ta kaɗa har sai da ta jawo mayafin da ta lulluɓa da shi ta rufe mata fuska. Sadiya ta kai hannu domin ta yaye wannan mayafi, aikuwa sai hannunta ya bayyana a fili wanda har yanzu akwai shaidar ɗaurin da Dargazu ya sa akai mata da sarƙa a hannunta. Ko da ganin wannan shaida sai labarin da Sanafaratu ta bani na yadda aka yi har birnin Sahara ya kafu ya dawo min. Babu wani abu da za a faɗa ko a yi waƙa akan shi wanda zai taɓa zukatan mutanen birnin Sahara gaba ɗaya fiye da abinda ya shafi bauta da cinikin bayi. Saboda birnin ya kafu ne daga jinin bayin da suka gudu domin neman ‘yancin kansu. 

Nanfa na fara tunanin waƙar da zan tsara domin ta dace da wannan batu amma babu lokaci, don haka sai na fara laluben waƙoƙin da na sani a kaina wanda za su iya dacewa da yanayin da nake ciki. Caraf kuwa, sai ƙwaƙwalwata ta cafko min wata waƙa wanda wani shahararren mawaƙin zamani mai suna Aminu Ala da Hausawa ke ji da shi a ko’ina ya yi, aka kuma yi sa’a na riƙe waƙar tsaf a kaina. Don haka kawai sai na yi gyaran murya na fara da cewa, 

Rayuwar Afirkawa 

Lokacin siyan bayi 

Lokacin zuwan turawan mallaka ƙasar Hausa. 

Haka dai nai ta rera wannan waƙa har na kai zuwa ƙarshe. A wannan lokaci tuni tsofaffin da ke wannan wuri sun yi nisa da fara kuka. Masu dauriya daga cikinsu ne ke zubar da hawaye kawai, wasu kuwa har da birgima da iface-iface. Ba sai an faɗa min ba, na san cewa wannan waƙar ce ta sa su yin wannan kuka, domin an taɓo musu inda yake musu ƙaiƙayi ne. Hatta su Fafale, Bafale, Bankami da su mamana Shamadara duk kukan su ma na ga suna yi. Ko da ganin haka, sai na yi maza na fara yin wata sabuwar waƙar kamar haka:

Awara da yaji 

Da ɗumi-ɗuminta

Na ci a layi ina jin yunwa 

Ta shaƙe ni ina yin ƙwalla 

Ke mai zoɓo, yaki ki bani… 

Na ci gaba da rera wannan waƙa ina mai dafe ciki ko riƙe wuyata a wuraren da suka dace domin fito da ma’anar abinda nake nufi a fili. Nan fa aka bushe da dariya, mutanen da ko minti ɗaya ba su gama yi suna kuka ba sai gashi sun komo suna dariya. Ai ko da ganin haka, sai na yi maza na ɗauko wani ɗan faranti da na gani akan wani teburin ƙarfe na fara bugawa tare da yin sabuwar waƙa ina cewa;

Masu kuka suna dariya 

A basu sadakar daddawa 

Su ci su ƙoshi su bi da ruwa 

Gan-gan-gan-gan. 

Habawa! Ai sai suka ƙara ɓarkewa da sowa, ni kaina a wannan lokaci dariyar nake yi, domin yadda suka zage suna ta tiƙar rawa ya tabbatar min da cewa mutanen nan akwai ƙawance mai ƙarfi a tsakaninsu da bidi’a. Ana cikin haka ne ban yi aune ba sai gani na yi wasu zaratan samari masu ƙirar ƙarfi su uku sun nufo inda nake a guje. Ko da ganin haka sai na ji wurin ya yi tsit aka zuba mana ido a ga yadda za ta kaya a tsakaninmu. Ni kuwa sai na ja tunga na yi tsayuwa irin ta jaruman da suka yarda da kansu. Ko da ya rage bai fi saura taku biyu su iso wurin da nake tsaye ba sai duk suka kawo min naushi da hamɓari a lokaci guda. Cikin wani irin zafin nama da shammace na yi tsalle sama tare wuntsulawa baya. Hakan yasa duk suka naushi iska tare da zamewa suka faɗi ƙasa. Jama’ar da ke wurin suka rafka tafi da ganin irin wannan bajinta da na nuna. Su kuwa waɗannan jaruman samari sai suka miƙe a fusace suka sake tunkaro ni. Nan fa muka kacame da sabon faɗa. Ya zamana sun rufar mini su uku basa komai sai kawo min duka, naushi da hamɓari. Ni kuwa na wanzu ina mai karewa tare da maida martani. Bayan mun ɗauki kimanin mintuna biyar a haka muna wannan fafatawa ne sai kuma na ga wasu jarumai mata su uku sun nufo inda muke a guje sun shigar wa waɗannan samarin suka taru min su shida ni kaɗai. Ji kake tim, titim, tim ta ko’ina kawo min bugu suke yi. Nan fa na zage damtse ya zamana kare kaina kawai nake iya yi ba tare da na iya mayar da martani ba. Ko da muka yi kimanin wasu mintinan biyar a haka sai na ji na fara gajiya, amma duk da haka ban sare ba. Babu zato balle tsammani sai na ga dukkansu su shidan sun je sun ɗauko sanduna sun sake nufo inda nake. Maimakon su dawo su kaɗai, sai na ga wasu matan su shida sun ƙaru wato sun koma su goma sha biyu kenan. Bisa mamakina, sai na ga matan duk sun tuɓe kayan jikinsu ya zamana sun wanzu a gabana kamar yadda aka haife su. Nan take maganar da mahaifina ya taɓa yi min watarana da faɗo min a cikin kaina. 

‘A wasu lokutan idan akai yaƙi aka kasa cin galaba akan maƙiya, sai a tura mata a gaba su yi tsirara su tunkare su ko da makami ko babu. Wani lokaci asiri ake yi kuma ba zai yi tasiri ba har sai matan sun yi haka. Wani lokaci kuma akan yi hakan ne domin a ja hankalin mayaƙan su ɓige da kallon matan wanda kafin su ankara tuni an hallaka da yawa daga cikin su. Babu yadda za a yi mutum ya san ga abinda suke nufi, kuma a wannan lokacin tausayi da tunanin cewa su ɗin mata ne ba zai yi tasiri ba. Ya kai ɗana, a duk lokacin da ka tsinci kanka a irin wannan hali, ka rufe idanuwanka da baƙin ƙyalle mai shara-shara, hakan zai baka damar ganin su ba tare da tsiraicinsu ya ja hankalinka ba, domin idan na masu asirin ne, to babu makawa sai ka kalle su, kuma kana kallonsu shikenan sun yi galaba akanka.’

Ko da na zo nan a tunanina sai na yi sauri na yago wani sashe na hannun rigar da ke jikina. Ko da yake mai ruwan ƙasa ce, idan na ninka shi gida biyu na tabbatar zai bani abinda nake so. Ina cikin wannan yanayi ne na ji muryar Sanafaratu na ƙwala min kira. Ko da na ɗago kaina, sai na ga ta cillo min sandata. Nan take na caɓe ta tare da ɗaura wannan ƙyalle da na yago daga hannun rigata ya zamana na rufe idanuwana ruf da shi. Bisa mamaki sai na ga ina iya ganin giftawar mutum dishi-dishi amma bana iya fahimtar mace ce ko namiji. Bansan lokacin da wani murmushi ya ƙwace min ba. Nan fa na sake gyara tsayuwata da kyau da nufin in tunkare su a ci gaba da wannan fafatawa. Su kuwa duk sai suka taso min a lokaci guda suka rufe ni da duka kamar za su cinye ni ɗanye. Nan fa suka wanzu suna masu kai min duka ta ko’ina, ni kuwa bana ko iya maida martani face kare kaina kawai. A hakan ma ba kowanne nake iya karewa ba. Domin kafin a cika minti biyu da fara wannan sabon faɗa namu har sun yi nasarar dukana sau goma a sassan jikina mabanbanta. Ana cikin haka ne na ji an yi min wani wawan duka da sanda a ƙirjina, ƙarfin dukan ya sa har sai da na faɗi ƙasa ina haki, numfashina na shirin sarƙewa sakamakon iska da na ji ta daina shiga jikina yadda ya kamata. A wannan lokaci ne na ji mutanen wurin sun fara yi musu tafi da jinjina. Cikin takaici na girgiza kai ina tunanin anya mutanen nan basu yi hauka ba kuwa? Ace mutane goma sha biyu sun tarar wa mutum ɗaya kuma wai har tafa musu ake yi don sun yi nasara akan shi? 

A dai dai wannan lokacin ne kuma na sake jin wasu kalaman na mahaifina suna juyawa a cikin kaina. ‘kada ka taɓa haɗa kanka da kowa, domin kai ba irin kowa ba ne. Kai na musamman ne, saboda kai ne Haidar, kuma kai ɗana ne. Sannan ina son ka kamar yadda kowane uba ke son ɗansa.’

Nan take na kauda wannan tunanin gefe sannan na fara karanta Ayatul Kursiyyu a cikin zuciyata. Ba tare da na daina karanta ta ba na dage na miƙe tsaye. Ko da ganin na miƙe, sai waɗannan jarumai suka sake nufo ni a guje da nufin su yi mini rubdugu su gama aikin da suka fara. Ni kuwa a daidai wannan lokacin karatun da nake yi ya samar min da wata nutsuwa ta ban mamaki. Sannan duk hayaniyar da mutanen ke yi sai na ji bana jinta, abinda kawai nake iya ji shi ne bugun zuciyoyin waɗannan jarumai da muke fafatawa da su. Cikin tsananin zafin nama na kamo hannun wani da ke kusa da ni, daga jin yanayin jikin na fahimci cewa mace ce, don haka sai na daki maƙoshinta sannan na hamɓareta da ƙafa a ciki, nan take ta faɗi ƙasa tana mai dafe maƙoshinta. Ba tare da na juya ba na sa sandata na kare dukan da wani ya kawo min sannan na goce wa wani dukan wanda kai tsaye ya samu goshin wanda ya kawo min duka na kare, kafin wanda yayi dukan ya kawo min wani tuni na daki ƙeyar shi sun yi ƙasa a tare. Nan fa muka ci gaba da wannan fafatawa, ya zamana ina yi musu dabara ta hanyar matar inda suke, idan wani ya kawo min duka sai in goce ya samu ɗan uwansa, kafin ya ankara ni kuma na make shi. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na yi laga-laga da su ya zamana sun kasa ko da ɗaga hannu balle su miƙe tsaye. A wannan lokaci ne na kwance ɗaurin da ke fuskata ina mai kallon inda tsoho Fafale yake zaune tare da sauke wani numfashi mai nauyin gaske wanda bansan ina riƙe da shi ba. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.1 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Birnin Sahara 12Birnin Sahara 14 >>

10 thoughts on “Birnin Sahara 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×