Skip to content
Part 11 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Daga nan Sanafaratu bata ƙara cewa komai ba, ni kuwa da Imran muna zaune tare da Sadiya muna kallon juna yayin da muka gaza cewa juna komai. A wannan lokaci babu irin tunanin da bai shigo cikin ƙwaƙwalwata ba, amma tambayoyi guda biyu su suka fi tsaya min a rai. Tambaya ta farko dai ita ce, ‘idan har dokar birnin Sahara bata amince da mace ta yi mulki ba ta yaya aka yi har Nadiya to ta hau kan mulki? Me suka shirya mata? Shin wace hanya ce zan bi domim ganin na shawo kan matar mahaifinmu? Lallai ya kamata in san dubara tun kafin lokaci ya ƙure min. Yayin da na zo nan a tunani na, sai na lura da Sadiya kamar tana son yin magana amma ta kasa . Don haka sai na kalle ta na ce,

“Sadiya me kike son cewa ne, na ga kamar kina son yin magana ko?”

Yayin da Sadiya ta ji wannan tambaya tawa, sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce,

‘Yaya Haidar wani abu ne yake damuna tun shekaran jiya na kasa fahimtarsa kuma na rasa yadda zan yi da shi a raina.”

Ko da na ji haka sai na matso kusa da ita na ce,

 “Kin san dai za ki iya faɗa min ko me ke damun ki ko?”

Ta jinjina kai sannan ta sauke numfashi. Bayan ta sake yin ajiyar zuciya a karo na biyu sai ta ce dani,

“Yaya Haidar tun shekaran jiya nake jin kaina kamar ba ni ba, wani lokaci sai in dinga jin jikina kamar ba nawa ba, gashi dai jikina ne amma kamar ba ni ke sarrafa jikin ba, wasu abubuwa da na faɗa ko na aikata sai daga baya nake jin kamar ba ni na aikata ba kuma ni na aikata.”

Ko da na ji wannan bayani nata, sai nan da nan na ji kaina ya buga dimm! Kuma take wani mummunan tunani ya fara taruwa a cikin ƙwaƙwalwata. Amma sai na danne na ce mata,

“Kada ki damu, dukkan mu muna cikin tashin hankali ne shi yasa, amma kin yi sallah kuwa tun shekaran jiyan?”

Sai ta ce min a’a saboda a ɗaure ta kwana. Daga nan muka yanke shawarar cewa muna sauka zata samu waje mai tsafta domin ta rama sallolin da ake binta.

A dai-dai wannan lokaci ne kuma muka ji keken dokin da muke ciki ya fara rage gudu a hankali. Wannan dalili ne yasa na leƙo da kaina waje domin ganin me ke faruwa. Ai nan take na hangame baki ina kallon wani sabon abin al’ajabi kuma na daban.

Ba komai ne yasa ni hangame baki ba face wata irin danƙareriyar katanga da na gani wacce aka sana’antata da zallan baƙin ƙarfe kuma aka yi masa shafe da ruwan gwal. A tsakiyar katangar, wata wangamemiyar ƙofa ce wacce ita ma da zallan baƙin ƙarfe aka yi ta. A saman wannan ƙofa kuwa, gumaka ne guda uku waɗanda aka ƙera su da turɓaya. Gumakan suna zaune ne, amma hakan bai sa na kasa fahimtar biyu daga cikin su ba. Na farko daga hannun dama dai ba kowa ba ne face kungin Ptah.

Na san mai karatu zai yi mamakin yadda na gane hoton wannan gunki nan da nan, amma kada ka yi mamaki. Domin na tabbatar da cewa ko da kai ne aka tilasta maka karanta littatafai irin yadda aka min, to ba zan yi mamaki ba don ka san wannan gunkin. A taƙaice dai Ptah shi ne abin bautar maƙera, kafintoci, magina da duk wasu masu ƙere-ƙere a birnin Misra tun gabanin zuwan sarki Fir’auna, kuma har izuwa yanzu akwai wasu mutane da suke bauta mishi a wasu sassa na duniya. Don haka banyi mamakin ganin shi a nan ba.

Gunki na biyu kuma shi ne gunkin Geb. Shi kuma Geb shi ne abin bautar ƙasa a cikin addinin mutanen birnin Misra tun gabanin zuwan sarki Fir’auna. Gunki na uku kam ban gane ko wanene ba, amma nayi mamakin ganin waɗannan gumaka a birnin Sahara. Kasancewar addinin bautar gumaka da sauran alloli ya riga ya shuɗe tun zamanin jahiliyya, duk da cewa labari yana ta yawo cewa har yanzu akwai ire-iren waɗannan addinai suna ci gaba da wanzuwa a doron ƙasa, ban yi tsammanin zan ci karo da su ido-da-ido ba. Sai a wannan lokaci ne na fahimci inda Sanafaratu ta dosa da ta ce min ubangiji Khonsu ne ya albarkace ta da ilimin mafarki. A taƙaice dai in na canka daidai, mutanen Birnin Sahara cikakkun baƙaƙen arna ne waɗanda suka ɗauki addinin maguzawan jahiliyya kuma suke ci gaba da aiwatar da shi. Har da zan takali Sanafaratu da maganar amma sai na fasa, a ƙarshe dai sai na tambaye ta da cewa,

“Ina ne nan, kuma wannan gunki na uku gunkin wanene?”

A nan ne ta ke bayyana min cewa,

“Nan ita ce ƙofar shiga yankin ƙabilar Maƙera na Birnin Sahara, kuma wannan gunki na uku da na ke gani ba na kowa bane face gunkin abin bautar rumawa, watau Vulcan. A cikin Addinin rumawa sun yarda da cewa Vulcan shi ne ubangijin wuta, Maƙera da sauran masu zane-zane. Sannan Vulcan shi ɗa ne a wajen Jupiter da Juno, sannan kuma shi ne miji a wajen Venus.”

Ko da naji wannan bayani sai nan da nan na fahimci wani abu. Girkawa suna da ababen bauta masu tarin yawa a addinin su na jahiliyya, da Rumawa suka zo sai suka ɗauki waɗannan ababen bauta suka ci gaba da bauta musu, amma sai suka canja musu zubi da tsari, sannan kuma suka ƙara tare da rage wasu ababen bautar yadda zai dace da tsarin su. A addinin girkawa, shi wannan Vulcan ɗin shi suke kira da Hephaestus, Jupiter kuma shi ne Zeus, Juno kuma ita ce Hera yayin da Venus kuma ita ce Aprodhite. Hmmmmmm lallai ana fama! Na ayyana a raina ba tare da na sake cewa komai ba. Abinda kawai na tattara wuri guda shi ne, mutanen Birnin Sahara suna bautawa kowane irin abin bautar da suka ga ya dace da wata buƙata tasu.

Ko da muka iso bakin wannan ƙofa, sai mai ja mana akalar keken dokin ya ja akalar suka tsaya. Ba mu daɗe a cikin wannan hali ba sai muka ga ƙofar ta buɗe, daga nan muka shiga cikin wannan yanki ba tare da fargabar komai ba. Haƙiƙa wannan wuri ya ƙawatu matuƙa, domin duk yadda zan misalta muku shi dole sai na rage. Amma a taƙaice dai, wannan ba yanki ya kamata a kira shi ba, wani birnin ya kamata a kira shi da shi. Dogayen gine-gine, manya-manyan shaguna,unguwanni daban-daban tarin jama’a da sauran abubuwan da idanuwana ba za su iya kaiwa gare su ba face sai na zauna an yi min bayanin su. Tun da muka shiga wannan yanki na maƙera na ga mutane suna ta tuttuɗowa daga ko ina, saman gidaje ne, shaguna ne ta ko ina dai. Kowa ya zuba mana ido, ko in ce kowa ya zuba min ido sai kallona ake yi kamar talabijin.

Babu wanda ya ce da mu ƙala, ammafa kowa ya zuba mana ido, yayin da muke ci gaba da tafiya kuma sai na lura da cewa ashe bin mu kuma suke yi a baya. In taƙaice muku zance, kafin mu kai zuwa inda muka nufa, rabin mutanen yankin suna biye da mu a baya. Muna cikin tafiya, sai na fara hango hasumiyar wani tafkeken gini, tun daga nesa na fahimci cewa wannan gidan muka nufa, domin na hango mutane a tsaitasaye sunyi cirko-cirko alamar jiran mu ake yi. Yayin da muka muka ƙara kusantar wannan gini, sai na ga ashe fada ce mai girman gaske, ga mutane nan birjik sun tsaitsaya a ƙofar fadar. A tsakiyar waɗannan mutane kuwa, wata kyakkyawar mace ce tsaye cikin wasu baƙaƙen kaya masu matuƙar kyau. Matar zata kai kimanin shekaru arba’in da ɗoriya, amma ga dukkan alamu girma bai fara zuwa mata cikin wahala ba. Duk da cewa baƙa ce, fatarta tana da haske kaɗan fiye da na mafi yawancin mutanen da ke tare da ita. Fuskarta a murtuke take, amma hakan bai ɓoye kyawunta ba. Doguwa ce mai matsakaicin jiki, sannan da ka ganta ka ga irin matan nan ne masu ji da kansu.

Ko da na ganta sai naji gabana ya faɗi, domin nan take na ji ta tuna min da mahaifina, zan yi magana kenan sai Sanafaratu ta matso kusa da ni ta yi min raɗa a kunne ta ce,

“Waccan matar da kake gani, ita ce mahaifiyata, idan ka samu amincewar ta ka tsira in kuwa ba haka ba za ka halaka. Fatan nasara.”

Daga nan sai ta Sauka daga keken dawakin kawai ta kama gabanta. Mata kenan, ta ceto ni daga can ta zo da ni nan kuma tana cewa zan iya rasa raina. Da kyau. Ko da muka matsa inda waɗannan dandazon mutane suke kaɗan, sai na na ce wa Sadiya da Imran,

“Komai rintsi da tsanani kada ku sake ku fito har sai na ba ku umurnin hakan.”

Sannan na cewa da bawan da ke jan akalar keken dawakin da ya tsaya.

Dama duk ya ƙosa, domin na lura tun da muka matso kusa da wannan mata jikin shi ya kama karkarwa . Ko da ya tsaya sai na sauka sannan na nufi inda wannan matar take tsaye tare da jama’ar ta. Bisa mamaki, sai na ga ita ma ta baro jama’ar nata ta nufo inda nake. Nan fa sai na buɗe hannaye tare da sakin murmushi ina mai cewa,

“Oyoyo mama!”

Na san za ku iya cewa ‘kai amma Haidar baka da hankali, matar da aka gaya maka za ta kashe ka kuma ita kake yi wa Oyoyo?’ Amma ina sane da me nake yi. Mutane kowa yana da lago, bisa labarin da Sanafaratu ta bani, matar mahaifina tana cikin baƙin ciki ne da kaɗaici. Musamman bisa irin halin da ta tsinci kanta a ciki na rashin miji da kuma kafaɗar da za ta jingina a jikinta. Wannan shi ne lagonta, don haka da shi zanyi amfani wajen samun nasara akanta, amma wannan tarar aradu da ka ne wanda Haidar ne kawai zai iya.

Ko da mutanen da ke kewaye da mu suka ga wannan abu da na aikata sai na ji wajen yayi tsit kamar mutuwa ta gifta. Amma ni ko a jikina kawai ci gaba na yi da tunkarar ta hannaye na kuma a buɗe. Ko da muka ƙara kusatar juna, kawai sai gani nayi wani abu na tunkaro ni da wani irin azababben gudu a cikin iska. Cikin matsanancin zafin nama nayi sauri na Cafke abin. Sai da na kai dubana kan abinda hannu na ya kama ne sannan na fahimci cewa ashe ƙaramar wuƙa ce irin ta sojojin nan. Wannan shi ne karon farko da na fara riƙe wuƙa a hannuna. Cikin alamun mamaki na dubi inda wuƙar ta fito, sai a sannan ne na fahimci cewa ita dai wannan matar ce ta jefo ni da wuƙar. Nayi mamakin irin zafin naman ta da har ta iya jefo wuƙar daidai wa daida daga waje mai nisa haka, domin ba ƙaramin ƙwararre bane zai iya yin hakan.

Maimakon in razana sai na ɗaga kai na kalle ta cikin yanayin mamaki na ce,

“A’aha wannan kuma wani sabon salon gaisuwa ne kuma mama?” Maimakon ta bani amsa, sai kawai ta ƙara jefo min wasu wuƙaƙen guda biyu cikin zafin nama. Nan take na cafe su ba tare da ko ɗaya ta same ni ba. Wannan bajinta da na nuna ce fa ta sa mutanen da ke tare da ita yin shewa tare da yi min tafi. Bisa yadda na lura da yanayinsu, da alama bata taɓa kuskuren abinda ta jefa da wuƙaƙen ta ba sai yau. Ita kuma hakan ba ƙaramin fusatata yayi ba, don haka sai ta zare takobin ta sannan ta nuna ni da tsinin takobin, wannan alamar muƙabalantar abokin karawa ne ga waɗanda basu sani ba. Maimakon in nuna fargaba kawai sai na ɗaga murya da ƙarfi na ce,

“Nagode Mama! Waɗannan ukun sun ishe ne ba sai kin ƙara min wasu makaman ba!”

Ai kuwa sai jama’ar wajen suka sake ɓarkewa da sowa. Maimakon ta bani amsa, kawai sai ta nufo ni da wani irin azababben gudu wanda ko namiji mai shekarunta bana tunanin zai iya. Dama na san za a rina, don haka kawai sai na zaro wannan sanda dana ɗauka tun a fada, na tare ta muka fara fafatawa. A karon farko da ta kawo min wani wawan sara na kare da sandar ƙarfen da ke hannuna, sai wata ƙara kake ji ƙal! Yayin da tartsatsin wuta ya tashi a inda makaman namu suka haɗu. Hakan yasa muka ja da baya muna kallon kallo, madadin in yi shiru sai na ci gaba da cewa,

“Lallai yanzu na fahimci dalilin da yasa mahaifinmu ya so ki sosai har soyayyar ta kai ga aure, kyakkyawar mace mai tsayi tare da jarumta irin taki ba kasafai aka cika samun ta ba!”

Ai kafin in rufe baki sai ji nayi ta mangare ni da hannunta na hagu. ƙarfin dukan yasa sai da na faɗi ƙasa yayinda leɓe na ya tsage jini ya fara tsartuwa.

Ko da na taɓa leɓena na ga jini, sai nayi murmushi sannan na miƙe tsaye ina mai cewa,

“Haka kuma dai na ƙara fahimtar dalilin da yasa ya iya barin ki ya shiga uwa duniya, saboda ke mace ce mai son kanta da yawa wacce bata iya ganin surar hoto matuƙar babba ne, amma in ƙarami ne, nan da nan sai ki gane, saboda ƙwaƙwalwarki ƙarama ce…!”

Ban gama rufe baki ba nan ma sai na ji wani naushin a kumatu na wanda shi ma sai da ya sani na faɗi ƙasa. Take kumatu na ya kumbure. Amma sai na sake miƙewa na tsaya da ƙafafuna. Na sake dubanta na yi murmushi sannan na ce,

“Ba lallai bane ki karɓe ni a matsayin ɗa amma ni na ɗauke ki tamkar mahaifiyata ce, duk da yake dai zan yi matukar mamaki idan na yi tsawon rai yayin da nake tare da ke a matsayin uwa a gareni…!

Tasss!!!

Naji saukar mari a fuskata wanda shi ma sai da ya sani na yi taga-taga kamar zan faɗi amma sai na turje. Na sake ɗago kai na kalleta sannan na ƙyalƙyale da dariya. Bayan na gama dariyar sai na sake kallon ta na ci gaba da cewa,

“Ki aikata duk abinda kike so a gare ni wannan ba matsala ta ba ce, amma ki yi tunani, yau inda mahaifina yana da rai da wane ido za ki iya kallon shi yayinda ki ka lahanta masa ɗa? Sannan wacce irin fahimta mabiyanki za su yi miki a matsayin ki na jagorar su?”

Wannan karon bata duke ni ba, sai ta yi wani irin ƙaraji mai ban tsoro sannan ta fara magana cikin ɓacin rai da kausasa murya tana mai cewa,

“Kada ka sake ka ce zaka zarge ni! Ko me na aikata mahaifinka shi ne sanadi! Da ace bai tafi ya barni ba da yanzu muna tare cikin zaman lafiya, amma saboda taurin kai irin wanda ka gada daga gare shi, ya tafi ya barmu ni da ‘ya’yana cikin ƙunci da rashin jagora!”

 A daidai wannan lokaci ne ta fara kuka mai cike da baƙin ciki da damuwa, sannan ta ci gaba da cewa,

” Mahaifinka ya tafi ya barni da ɗawainiyar da babu wata mace da zata iya jurewa, amma saboda tsabar rashin kunya kai har kana da zarrar da zaka iya zargina? Ka bani amsa na ce kana da ita?!

Yayin da na ji wannan tambaya daga bakinta, sai na sunkuyar da kaina ƙasa ina mai yin shiru cikin alamun rashin gaskiya. Wasa na yana tafiya daidai, sauran na kan hanya. Bayan wani ɗan lokaci sai na ɗago da kaina na dube ta da kyau yayinda ƙwalla ta fara fitowa daga idanuwana. A lokaci guda kuma sai na fara tafiya a hankali na nufi inda take sannan na fara magana da cewa,

“Tabbas ba a yi miki adalci ba mama, ba a kuma kyauta miki ba kuma ban goyi bayan hakan ba! Amma ki sani cewa komai yana faruwa ne bisa yadda ubangiji ya ƙaddara zai faru, kuma babu wanda ya isa ya kaucewa ƙaddararsa. Wannan ƙaddara ce ta jawo mahaifina ya tafi ya barki, kuma ita ce yau ta zamo silar zuwa na nan yayin da shi kuma baya doron ƙasar balle ku gana. Haƙiƙa na fahimci irin baƙin cikin da kike ciki, kuma ina mai nemarwa mahaifina gafara a gareki, sannan na yi miki alƙawarin cewa daga yau zan zamo mai ɗebe miki kewar mahaifina, domin na amintu da cewa ƙaddara ce ta kawo ni gareki don in aiwatar da hakan, ya ke mamana ina mai roƙon ki da ki ɗauke ni a matsayin ɗan da kika haifa. Kuma ki sani cewa kashe ni ko lahanta ni ba zai samar miki da nutsuwa ba a zuciyar ki domin wuta bata kashe wuta, wannan aikin ruwa ne.”

 A daidai lokacin da na zo nan a zance na, hakan kuma ya zo daidai da ƙarasowa da na yi dab da ita, don haka nan take na aikata wasana na ƙarshe wanda zai iya gyara komai ko kuma ya ɓata komai. Ba komai na yi ba a wannan lokacin face rungume ta da na yi kai tsaye.

Tsananin mamaki ya sa ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta iya aikata komai ba. Ganin haka ni kuma sai na kwantar da kaina a kafaɗarta sannan na ce,

“Na san abin da ciwo mama, amma ki yi haƙuri ki yafe mana, tabbas babu wanda zai yi haƙuri face sai ya cimma nasara a rayuwar shi, domin ana gwada mutanen kirki a ma’aunin haƙuri ne ba fushi da ɗaukar fansa ba.”

Ko da na zo daidai nan a zance na, sai naji ta ƙanƙame ni a jikinta yayinda ta narke da wani sabon kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Can bayan wani lokaci kuma sai ta ɗago kai ta sumbace ni a goshi tana mai yin murmushi a gare ni, ba zato kuma ba tsammani sai naji ta ɗaga hannuna sama kamar yadda Sarauniya Nadiya ta yi a fada. Ai kuwa nan take mutanen da suka halarci wajen suka ɓarke da gagarumar sowa. Masu fito na yi, masu kiɗa na yi, masu waƙa na yi.

Can kuma kamar a fim, sai muka ji waɗannan kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe sun koma iface-iface yayin da mutane suka fara darewa kowa na neman matsera. Cikin firgici ni da mamana muka juya don ganin abinda ya sa waɗannan mutane suke gudu. Aikuwa nan take na ji ƙwaƙwalwata ta fara juyi sakamakon abinda idanuwana suka hango min.

Wasu jajayen tsuntsaye ne na gani masu jikin macizai, a’a kai macizai ne dai masu fukafukan tsuntsaye. A ƙalla kowane guda ɗaya zai yi girman ɗan kwikwiyo, jikin su jawur kamar an daka toshshi. Kowane maciji guda ɗaya yana da fukafukai guda biyu manya waɗanda suka ba shi damar tashi sama. Sannan bayan kowace daƙiƙa biyar macizan suna furzar da dafi daga bakin su. Shi kuwa wannan dafi yana zuwa ne a cikin siffar wuta wacce take narkar da duk abinda ta sauka a kanshi. A ƙalla macizan za su kai su talatin a ƙiyasce. Mamakin abinda na gani ma sam ya hanani cewa uffan, kafin in ce wani abu sai na ji mamana ta ce,

“Yi maza ka gudu ka ɓuya, ni suka kawo wa hari babu abinda za su yi maka.”

Ko da na ji wannan batu ya fito daga bakinta, sai na kalle ta cikin mamaki na ce,

‘Ke kuwa ya akayi kika san cewa wajen ki suka zo, kuma me yasa za su kawo miki hari?”

Yayinda taji wannan tambaya tawa sai ta yi murmushin ƙarfin hali sannan ta ce,

“Kai dai ka tafi kawai, in na rayu daga baya ma yi magana…”

“To in kuma baki rayu ba fa?”

Na aika mata da tambaya tun kafin ta gama rufe baki.

“Shikenan sai mun haɗu a lahira.”

Ta bani amsa cikin rashin nuna alamar damuwa. Ko da naji haka sai na ɗauko sanda ta na gyara tsayuwa sannan na ce,

“Ni ba soko bane, don haka in dai za ki tsaya anan ki fafata da su, to ni ma zan tsaya in kuma gudu zaki yi kina iya gudu, amma ni ina nan sai na ga abinda zai ture wa buzu naɗi!”

Ko da gama wannan jawabi nawa sai na ga ta tsaya ta zuba min ido ƙuriiii… Bayan wani lokaci kuma sai tayi murmushi sannan da dafa kafaɗata tare da cewa,

“Haƙiƙa kai ɗan Hammadi ne.”

ko da gama faɗin haka sai ta karanta wasu ɗalasiman tsafi, nan take wasu zabga-zabgan takubba guda biyu suka wanzu a hannayen ta. Kafin kace kwabo tuni ta tunkari macizan waɗanda tuni har sun kusa ƙarasowa inda muke tsaye. Da naga haka nima sai na bi ta muka fara fafatawa da waɗannan macizai.

Cikin zafin nama na ga ta kai wa wasu macizai biyu da ke gabanta sara, nan take ta fille musu kai suka zuɓe ƙasa matattu. Nan take suka fara narkewa tare da narka hatta ƙasar da ke wajen saboda masifa. Bata ko koma ta kansu ba kawai sai ta ci gaba da ratsawa ta cikin su tana saran su ba ji-ba gani. Duk inda suka faɗi sai ka ga wajen yayi baƙi yana huci kamar an zuba tafasashiyar dalma. Ni ma sai na tare su da sanda ta ya zamana ina dukan su da dukkanin ƙarfina. Duk wanda na wa duka ɗaya da ƙyar yake iya miƙewa, idan kuwa nayi sa’a ya faɗa cikin ‘yan uwanshi da suka faɗi a ƙasa, to nan take zai narke kamar an saka gishiri a ruwa.

Haka muka wanzu muna yaƙi da waɗannan macizai har sai da ya rage saura guda uku kacal a filin wajen. Su ma sun yi nisan kwana ne sakamakon wayo da kuma mugun zafin nama da suke da shi. Ba sa yarda su sauko ƙasa yadda za mu iya samun su da sara ko duka. Sannan sukan kawo mana sara ko mangari da bindin su sannan kuma su sake tashi a guje su ƙara yin sama. A ƙarshe dai dole mu ka sake salon faɗa inda muka zo muka haɗe waje guda muka jingina bayan mu waje ɗaya ta yadda duk abin da ya zo ta ɗaya ɓangaren zamu iya tare shi. Ai kuwa wannan dabara ba ƙaramin aiki ta yi ba domin muna yin hakan sai su ukun duk suka yo kanmu a lokaci guda. Cikin zafin nama muka goce tare da kaiwa na gefe-da-gefe duka da sara, hakan yasa na tsakiyan ya caki rairayi maimakon ɗayan mu, kafin ya ankara ko yai wani motsi tuni mun kai masa duka da sara a lokaci guda. Nan take su ukun duka suka zube ƙasa matattu.

Nan fa muka yi cirko-cirko muna kallon wannan abin al’ajabi da ɗaure kai ba tare da ɗayan mu yayi magana da ɗayan ba. Sai a sannan ne na lura da cewa mamana layi take yi kamar wacce ta sha kayan maye. Nan da nan na je gare ta ina tambayar me ya faru, ai ban ma gama tambayar ta ba sai kawai naga ta yi ƙasa zata faɗi. Cikin hanzari na taro ta tare da saɓa ta a wuya na nufi inda naga mutanen nan sun nufa sa’ilin da suka ga waɗannan macizai. Har na ɗan yi nisa sai kuma na tuna da cewa na bar fa Sadiya da Imran a cikin keken dokin da muka zo. Don haka sai na koma da baya na kira same su na saka mamana a cikin wannan keken doki muka ci gaba da tafiya tare muka nufi inda wannan fada take.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Birnin Sahara 10Birnin Sahara 12 >>

11 thoughts on “Birnin Sahara 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×