Skip to content
Part 14 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Tsit wurin yayi kamar mutuwa ta gifta, aka rasa wanda zai ce ƙala. Ni kuwa a wannan lokaci sai ajiyar zuciya nake yi tare da haki kamar wanda yayi awa biyu yana gudu. Tsoho Fafale ne ya fara yi min tafi, kafin daga baya gaba ɗaya sauran jama’ar da ke wurin suka fara yi min tafin su ma. Nan fa wurin ya kaure da sowar jama’a, ya zamana hatta su Imran da Sadiya tafin suke yi. Ita kuwa Shamadara murmushi kawai take yi tana kallona cike da alfahari. Daga can sai tsoho Fafale ya ɗaga wa mutanen da ke wurin hannu suka yi shiru. Bayan kowa ya nutsu kuma an kawar da waɗannan jarumai da na yi wa dukan tsiya. Sai tsoho Fafale ya fara magana da cewa,

“Haƙiƙa wannan baƙo ka nuna bajinta irin wacce ta dace da jinin Hammadi, kuma ka tabbatar da cewa lallai kai jarumi ne na a zo a gani. Ina mai jinjina a gareka tare da taya ka farincikin cinye nasarar jarabawa ta biyu da ta uku. Yanzu kuma za mu yi maka jarabawa ta huɗu kuma ta ƙarshe wadda ita ce ƙira. Yanzu zan sa a gabato maka da kayan ƙira iri daban-daban domin mu ga irin basirar da kake da ita a wannan fannin.”

Ko da gama wannan jawabi nasa sai yayi tafi, nan take aka fara fito da kayan ƙira iri-iri. Su madashi ne, matsoni, gizago, kurfi, tama, kasko, awartaki, masaɓa, zugazugi, guduma da dai sauransu. Wasu ma ban taɓa ko ganin su ba balle in san sunan su. Kafin ka ce kwabo sun tayar da wata ‘yar ƙaramar maƙera a daidai inda wutar nan take. Da suka gama sai suka koma gefe kawai suka zuba min ido. Nan fa wurin ya sake yin tsit kamar an ɗauke ruwa da tsakar dare. Zuwa na yi na zauna akan wata ƙaramar kujera da aka ajiye a wurin ina tunanin abinda ya kamata in yi. Sai a sannan ne na fara tunanin to ni wane irin abu ma ya kamata in gwada ƙerawa?

Su dai maƙera sun kasu kashi biyu ne bisa irin abubuwan da suke ƙerawa. Akwai ƙirar fari, akwai kuma ƙirar baƙi. Ƙirar fari ita ce ƙirar kayan alatu da na ƙawa da kuma kayan aikace-aikacen gida. Abubuwan da suke ƙerawa su ne irin su ɗan-kunne, askar wanzamai, sarƙa, abun hannu, kumbo, da kuma kayan adon dawaki da dai sauran su. Irin waɗannan maƙeran su ake yi wa laƙabi da maƙeran farfaru a wasu wuraren.

Su kuwa maƙeran baƙi su ke ƙera kayan yaƙi da na amfanin gona irin su fartanya, garma, takobi, sulke, majaujawa, mashi da dai sauransu. Su kuma irin waɗannan maƙera su ake yi wa laƙabi da maƙeran babbaƙu a wasu wuraren.

Ruɗewa na yi gaba ɗaya na rasa me ma zan yi, kuma a cikin waɗannan maƙera guda biyu wane ɓangare zan zaɓa, kuma me zan gwada ƙerawa?

Da dai na ga wannan tunanin da nake yi ba zai fisshe ni ba sai na yi watsi da shi sa’annan na dauƙi wani dogon ƙarfe me matsakaicin kauri domin na saka shi a wuta ya yi ja, in ya so kafin nan na san abin yi. Ko da ɗaukar wannan ƙarfe sai na ji wani irin kusanci na ban mamaki ya shiga tsakanina da shi tamkar dama can na saba taɓa wannan ƙarfe ne. Kusanci ne irin wanda ma’aikaci ke ji da kayan aikin da ya saba aiki da su tsawon rayuwar shi. Cikin tsananin mamaki na saka shi a cikin wutar sannan na fara hura wutar da zugazugin da ke wurin. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ƙarfen ya yi ja. Ko da na ga yayi ja sai na sa awartaki na ciro shi daga wutar na ɗora shi akan maƙerar sannan na jawo wata guduma na fara dukan ƙarfen da ita. Ai nan kuma wani sabon abin mamakin ya sake faruwa, domin ji na yi kamar dama can na saba aikin ƙira ne tsawon rayuwata. Ji na yi kawai ina fahimtar irin dukan da ya kamata in yi wa ƙarfen da kuma inda ya kamata in doka. Nan fa na cika da tsananin mamaki fiye da da, domin bani da wani bayani da zan yi wa kaina dangane da faruwar wannan al’amari. Don haka kawai sai na ci gaba da aikin bugun wannan ƙarfe ba tare da ni kaina na san abinda nake shirin ƙerawa ba. Bayan na bubbuga ƙarfen yadda nake buƙata, sai na mayar da shi cikin wutar na ci gaba da hura ta da zugazugin. Ko da na ga ya fara yin ja a karo na biyu sai na ɗauko wasu madaidaitan ƙarafan su ma na saka su a wutar sannan na ci gaba da hurawa. Bayan na ɗauki tsawon lokaci a haka sai na fara zaro su kawai ina sake bugun su da wannan guduma. Shi wancan babban ƙarfen da na fara ɗauka sai na sai na rage mishi kauri sannan na miƙar da ƙarshen shi na kuma raba shi gida biyu har sai da na ga kowane ɓangare ya miƙe sosai, sannan na yi rami a ɗaya ƙarshen yadda zai zama kamar mariƙi, sannan na fara amfani da sauran kayan aikin ina yin huji da wasu zane-zane a jikin ƙananan ƙarafan da ke wurin. Zane-zanen abubuwa ne da ni kaina ban san ko menene ba a wannan lokacin. Haka na ci gaba da yi, in ƙarfen yayi sanyi sai in maida shi wuta ya ƙara gasuwa, in kuma yayi zafi sosai fiye da yadda nake buƙa sai in ɗan hutar da shi a cikin wani kasko da ke gefena sannan in ci gaba da aiki. Ko da na gama, sai na ajiye shi gefe sannan na ɗauko wata ƙaramar tukunya da ke gefe na ɗorata akan wutar sannan na fara zaɓo madaidaitan ƙarafa har sai da na zaɓo guda shida sannan na zuba su duka a cikin wannan tukunya na ci gaba da hurawa babu ƙaƙƙautawa. Su kuma waɗancan ƙananun ƙarafan sai na fara sana’anta wasu ƙananan abubuwa da su waɗanda su ma bansan ko menene ba. Bayan na ɗauki tsawon lokaci ina wannan aiki, sai na duba wannan tukunya mai ɗauke da waɗannan ƙarafa da na sa a wuta, ai kuwa sai na ga har sun narke, don haka sai na yi maza na sauke tukunyar daga kan wuta, maimakon in ajiyeta a ƙasa sai na zuba narkakken ruwan ƙarfen a ɗaya daga cikin waɗancan ƙarafa da na fara aiki akansu da fari, ai kuwa sai na ga ruwan ya zauna a cikin ramin da na yi a jikin ƙarfen daidai wa daida. Ban yi wata-wata ba na ɗauko ɗan uwansa na rufe. Bayan wani ɗan lokaci kuma sai na buɗe shi sannan na zuba mishi wani mai da na gani a wurin sannan na fito da shi na fara sabon aiki. In taƙaice muku zance dai haka nai ta yin abubuwa cikin ƙwarewa kamar dama can na yi shekaru ne ina aikata su. Sai a wannan lokaci ne na fahimci haƙiƙanin maganar da Sadiya tai min na cewa tana jin tana yin wasu abubuwa kamar ba ita take yi ba alhalin kuma ita ce take yi. Ba zan iya cewa ga tsawon lokacin da na ɗauka ina wannan aiki ba, abinda kawai na sani shi ne hankalina gaba ɗaya yana kan wannan aikin ta yadda bansan ma halin da mutanen wurin su ke ciki ba. Su kuwa ido kawai sauka zuba min suna kallon abinda nake yi. Bayan na ɗauki tsawon lokaci ina wannan aiki, sai siffar abinda nake ƙerawa ya fara bayyana a gabana, takobi ce mai baki biyu.

Nan take murmushi mai sauti ya ya ƙwace min. Babban dalilin yin wannan murmushin nawa kuwa shi ne tunawa da na yi da maganar da mahaifina ya taɓa faɗa min kusan shekaru goma da suka gabata.

*****

A wani dare ne da aka wuni ana tsuga ruwan sama har kusan goman dare ba a daina ba. A wannan lokaci mahaifiyata tuni ta yi bacci sakamakon maganin mura da ta sha. Muna zaune tare da mahaifina muna hira sai yake bani tarihin Sayyidna Aliyu Bn Abi Talib da irin jarumta da rashin tsoronsa. A nan ne yake faɗa min cewa babban dalilin da yasa ya saka min suna Haidar shi ne saboda yana fata zan gaji mai sunan. A cikin tarihin ne yake min bayani akan shahararriyar takobin Sayyidna Aliyu mai baki biyu wadda ake kira da Zulfiƙar. Ban manta ba, saboda tsananin burge ni da labarin ya yi har cewa mahaifina na yi ya siyo min irinta nima. A nan ne yake bayyana min cewa ai ba a siyar da ita, amma wataƙila watarana zan ganta da idanuwana, wa ya sani ma ko ni zan ƙera tawa ma da kaina. Cike da mamaki na tambaye shi da gaske zan iya ƙera tawa? Sai ya ba ni amsa da cewa,

“Me zai hana? Ai duniya faɗi gareta, kuma babu wanda ya san abinda zai faru gobe.”

Tun daga wannan lokacin na ƙwallafa raina akan Zulfiƙar, lokacin da aka siya min waya kuwa kusan kullum sai na yi bincike a yanar gizo na ga hotuna da bayanai akan takobin.

*****

Ko da na tuno da wannan magana, ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba, a lokaci guda kuma dariya ta kubce min ba tare da na shirya ba. Lallai mahaifina yayi gaskiya, duniya da faɗi take, kuma abin da ke cikinta tarin yawa gareshi. Sannan babu wanda yasan abinda zai faru gobe sai Allah. Ko kaɗan ban yi mamakin ganin cewa kwafin Zulfiƙar nake ƙerawa ba, mamakin da nake yi kawai shi ne irin yadda nake aikin kamar dama can asalina maƙeri ne tun ina ƙarami.

Bayan na kammala aikin sai na bar wannan takobi a cikin ruwa domin ta huce, sannan na ci gaba da aikin waɗannan ƙananan ƙarafan da su ma sai da na kusa gamawa tukunna na fahimci ashe abin wuya ne nake ƙerawa na baƙin ƙarfe mai siffar waɗannan tsuntsaye da muka fafata yaƙi da su ɗazu. Bayan na gama, sai na samu wuri na ajiye su sannan na koma kan takobin na shafeta da wani mai da ke nan kusa da ni. Bayan na gama shafeta da man sai kuma na koma kan wannan abin wuya da nake haɗawa. Haka dai nai ta yi kai ka ce dama can na saba aikin ne. Domin ji kawai nake yi zuciyata na riya min cewa yi kaza, ni kuma kawai sai in yi.

Bayan na sake shafe wasu tsawon lokuta sai na miƙe hannuna na riƙe da takobin kwafin Zulfiƙar da na ƙera da kuma wannan abin wuya mai siffar tsuntsaye masu kama da macizai. Na tunkari inda tsoho Fafale yake kai tsaye ba tare da wata fargaba ba. Ko da zuwana inda yake, sai na yi mishi irin gaisuwar da na ga suna yi ta hanyar sa gwiwa ɗaya a ƙasa sannan na miƙa masa abubuwan guda biyu. Cikin sanyin jiki da almun mamaki tsoho Fafale ya amshi takobin yana duddubata da kyau tare da kai wa iska sara da ita, kafin daga bisani ya miƙa wa Bafale shima yana duddubawa. Daga nan kuma sai tsoho Fafale ya karɓi wannan abin wuya shi ma ya duba shi da kyau sannan ya miƙa wa Bankami shi ma domin ya duba. Ni kuwa sai na miƙe na koma gefe inda Imran da Sadiya suke na tsaya. Kowa da ke wurin ya yi tsit kawai ana kallon su tsoho Fafale waɗanda a wannan lokaci tuni sun yi nisa cikin tattaunawa da junansu game da waɗannan abubuwa da na ƙera.

Bayan sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawar ne, sai tsoho Fafale ya sake miƙewa tsaye ya yi gyaran murya sannan ya fara magana da cewa,

“Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa mun ga abubuwan da ka ƙera kuma mun tattauna akansu. Amma za mu so jin ƙarin bayani game da su daga bakin ka kafin mu yanke hukuncin da ya dace.”

Ko da na ji haka, sai na sake gabatowa zuwa gaban tsoho Fafale sannan na karɓi wannan abin wuya na ɗaga shi sama yadda kowa zai iya gani sannan na ce,

“Wannan abin wuya ne, ko in ce sarƙa ce da na ƙera domin tunawa da gwagwarmayar da muka sha ni da mamana Shamadara da waɗannan tsuntsaye masu siffar macizai. Na sana’antata ne domin ta zamo kyauta kuma abin tunawa ga mamana tare da sauran jama’ar wannan ƙabila. Ko da yake ban daɗe a cikin ku ba, na san cewa ba kullum ba ne irin hakan ke faruwa a cikin wannan yanki naku don haka lallai wannan wani abu ne da zai shiga kundin tarihin wannan ƙabila har zuwa tsawon zamunna, hakan ya sa na ƙera wannan sarƙa domin ta zamo wasa farin girki a cikin abubuwan da za a ƙera domin tunawa da wannan rana.”

Ko da jin haka sai mutanen wurin suka fara jinjina kai alamar yarda da abinda na faɗa, yayin da wasu kuma suka dinga yi min tafi. Ni kuwa kai tsaye kawai sai na je inda Shamadara take na sa mata wannan sarƙa a wuyanta. Nan fa aka sake ɓarkewa da sowa. Na koma inda tsoho Fafale yake tsaye na karɓi takobin daga hannun shi sannan na fara wasa da ita. Ya zamana ina kai wa iska sara da suka da ita. Wannan shi ne karo na farko da na fara riƙe takobin ƙarfe a hannuna, kuma shi ne karo na biyu da na fara riƙe makamin ƙarfe. Amma da yake mun sha fafatawa da takobin katako ni da mahaifina, na riga na san yadda ake sarrafata, kuma bambancin ba wani mai yawa ba ne. Matsalar kawai ita ce, bata yi min daidai a hannuna kamar yadda sandar nan ta yi min ba, to amma wannan ba abin damuwa ba ne saboda dama ba kaina na yi wa ba. Bayan na gama wasa da ita, sai na ɗaga ta sama sannan na ce,

“Wannan kuma takobi ce wanda na ƙera ta a zubi da tsarin asalin takobin Sayyidna Aliyu Allah ya ƙara yarda da shi wanda na ci sunan shi. Shi ɗin jarumi ne na gaban kwatance kuma a bin koyi ga dukkan jaruman duniya. Ya kai tsoho Fafale, na san cewa ba za ka rasa yara matasa sa’o’ina ba, don haka wannan takobi na yi ta ne domin ta zama makullin karamci a tsakaninmu. Na san cewa ba lallai ta yi daidai ba, ba kuma lallai ta burge ba, amma a matsayinka na mutum na farko da ya fara bani damar jarraba baiwata a fannin ƙira, na yi imani cewa ka cancanci ace kai zan fara ba wa abinda na fara ƙerawa. Ina mai roƙonka, ko da ba za ka yi amfani da ita ba, zan so ka ba wa ɗaya daga cikin yaran ka yayi amfani da ita, lallai zan yi alfahari da hakan sosai da sosai.”

Ko da na zo nan a zance na sai na miƙa wa tsoho Fafale wannan takobi a karo na biyu cike da girmamawa. Cikin sanyin jiki da rawar hannu tsoho Fafale ya karɓi wannan takobi yana mai kallonta tare da shafa ta. Ba zato ba tsammani kuma sai na ga hawaye sun fara zubowa daga idanuwansa. Ko da ganin haka, sai na yi tunanin ko na yi mishi wani laifin ne, wataƙila a al’adarsu ba a yin haka nan ni kuma gashi na yi. Don haka sai na matsa kusa da shi na dafa shi sannan na ce,

‘Ya kai tsoho Fafale, ka yi haƙuri idan na yi maka wani abu wanda ba daidai ba, kuma ka sani cewa ba da niyya na yi hakan ba, kuskure aka samu.”

Ko da tsoho Fafale ya ji wannan batu nawa sai ya share hawayen da ke fuskar shi, sannan muryar shi a can ƙasa ya fara magana da cewa,

“Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa baka yi min laifin komai ba. Kuma ba komai ba ne ya sani kuka ba face kasancewarka mutum na farko da ya fara bani kyauta irin wannan. Na gode sosai da karamcinka a gare ni. Amma ka sani cewa ba zan iya karɓar wannan kyauta taka ba, ba don na raina ba, kuma ba don wulaƙanci ba, sai don ni yanzu na tsufa ba zan iya amfani da ita ba, kuma ‘ya’yana gaba ɗaya basa raye balle in ba wa wani daga cikinsu. Na gode sosai, kuma ina fatan watarana za ka zo koyon ƙira a wajena, domin alamu sun nuna idan ka samu horo mai kyau za ka iya zama fitaccen maƙerin da babu kamarsa a duk cikin wannan ƙabila tamu.”

Ko da gama faɗin hakan, bai jira na faɗi komai ba sai yai maza ya ɗaga hannuna na dama sama tare da cewa,

“Ya ku ƙabilar maƙera! Ina muku albishir da samun magajin Hammadi domin wannan baƙo ya nuna mana cewa a kowane ɓangare na al’adunmu da rayuwar mu yana da jiɓi, kuma yayi nasara a dukkan jarabawar da muka yi mishi. Ko da yake abubuwan da ya ƙera guda biyu sun nuna cewa yana da baiwar zama a cikin maƙeran fari da na baƙi gaba ɗaya. Ba mu da tantama akan cewa fasahar shi ta fi ƙarfi ta fagen maƙeran baƙi. A bisa wannan dalili, tare da amincewa da na samu daga Bafale ɗan Ci-wake da Bankami ɗan Adahama tare da sauran jama’ar wannan ƙabila ta maƙera, ni Fafale ɗan Falalu nake gabatar muku da Haidar ɗan Hammadi ɗan Hantsi a matsayin ɗan wannan ƙabila ta maƙera.”

Ko da gama wannan jawabi sai ya ɗebo wani abu mai ruwa-ruwa da ban san ko menene ba ya watsa min a jiki. Nan take aka ɓarke da sowa tare da tafi. Daga nan kuma sai kowa da ke wurin ya fara jefo min irin wannan abu da tsoho Fafale ya watsa min. Kafin wani lokaci jikina ya jiƙe sharkaf da ruwan wannan abu. Daga nan sai mamana Shamadara ta jawo ni ta wuce da ni wani wuri da ban san ko ina ba ne. Su Sadiya da Imran da Fa’iza da Sanafaratu duk suna tare da mu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 11

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Birnin Sahara 13Birnin Sahara 15 >>

9 thoughts on “Birnin Sahara 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×