{"id":1002,"date":"2021-11-26T15:26:48","date_gmt":"2021-11-26T15:26:48","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=1002"},"modified":"2022-07-13T01:36:00","modified_gmt":"2022-07-13T01:36:00","slug":"yadda-ake-sanya-tsakure-taba-ka-lashe-da-somin-tabi-a-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-sanya-tsakure-taba-ka-lashe-da-somin-tabi-a-labari\/","title":{"rendered":"Yadda ake sanya tsakure, taba ka lashe da somin tabi a labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alar da ta gabatai, mun yi bayani ne game da <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-murhun-girka-jigo-a-labari\/\">tsarin murhun girka jigo a labari<\/a>, inda muka bayyana madogara uku da suka zama kamar duwatsu uku na murhu da idan babu su babu labari. A cikin bayaninmu mun tsaya ne a kan misali na farko a \u0199ar\u0199ashin <em>dabarun gina farkon labari,<\/em> inda muka ce <em>ta sigar bayani<\/em>&nbsp;&nbsp; ana dun\u0199ule abin da labari ya \u0199unsa a ta\u0199aitattunkalmomi don tafiya da hankalin manazarci da dasa masa \u0199aunar karanta labarin a zuci.<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan ma\u0199alar insha Allahu za mu yi bayanin yadda ake bayyana abin da labari ya \u0199unsa <em>ta hikima<\/em> ba tare da an bayyana wa mai karatu ya fahimci cewa bayyana masa abin da labarin ya \u0199unsa ake yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Kafin fa\u0257a\u0257a bayanin, mu fara nazartar wannan misalin mai zuwa tukuna:<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"ka\u0257aici\"><strong>KA\u018aAICI<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p><em>Cikin yanayin \u0199ara da razana matashin saurayin ya furta &#8220;Wayyo Allahna!&#8221; Lokaci guda kuma ya yi zumbur ya mi\u0199e tsaye yana dube-duben wurin da ya zauna, a \u0253angare guda kuma ya dafe mazauninsa da hannu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Me ya faru?&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ya aka yi?&#8221; Abokanan hirarsa biyu kowa da tambayar da yake yi masa suna kallon shi kamar wa\u0257anda ya tsorata su.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kunama ce ta harbe ni wallahi.&#8221; Ya ba su amsa yana sosa mazaunin nasa, yayin da su kuma suka yi ha\u0257in bakin tambayar shi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Kunama kuma?&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Eh wallahi!&#8221; Ya ba su amsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Kun gan ta kuwa da girmanta.&#8221; Ya sake yin maganar yana mai nuna musu \u0199atuwar kunamar da ta sake \u0257ana \u0199arinta sama tana jiran kotakwana ta mayar da martani. Lokaci guda kuma ya \u0257an matsa daga inda take tare da nemo wani tsinke da zai tsire ta da shi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Sai dai kuma har ya kai hannu zai soketa da tsinken, kamar wanda aka yi wa wahayi, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya fasa, tare da sauke wata ajiyar zuciya. Kawai kuma sai ya \u0257an saka tsinken ya ta\u0253a ta da shi, sanadin da ya sa ta yi wani gare tana neman ma\u0253oya cikin tarin yayin da yake wurin \u0199arinta a \u0257age.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Meye hakan? Ka kasheta mana kana ganin za ta gudu!&#8221; Guda cikin abokanan nasa mai amsa suna Buba ya hau yi masa ihu, yayin da shi kuma kawai ya \u0257aga kai ya kallesu ganin sun zubo masa ido ya ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>\u0198yale ta kawai, ai ba ta harbe ni sosai ba.&#8221; Gaba\u0257ayan su sai suka bi shi da kallo kamar wa\u0257anda suka rasa abin da zasu ce masa na irin wautar da yake shirin yi, lokaci guda kuma \u0257aya matashin saurayin Ilu ya cire takalminsa far\u0257o zai zafga mata amma caraf Zaidu , wato shi matashin saurayin da ta harba \u0257in ya ri\u0199e masa hannu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Don Allah kada ka kasheta Ilu.&#8221;&nbsp; Zaidu ya yi maganar tare da \u0199wace takalmin hannunsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Mece ce ribarmu ta kasheta?&#8221; Ya sake tambaya yana kallon matasan biyu da suke yi masa kallo na \u0199ololuwar mamaki da rashin fahimta.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kai mece ce ribarka na barinta ta tafi bayan cutar da kai ta yi?&#8221; Shi ma Buba ya zaburo da tambayar shi tare da nufar cikin yayin zai mutsittsiketa da \u0199afarsa, amma bai kai ga wurinta ba Zaidu ya yi zunbur ya sha gabansa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kada ka kasheta don Allah Buba!&#8221; Zaidu ya yi maganar yana marairaicewa da muryarsa mai sanyi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ni ma da kasheta zan yi sai na yi wani tunani.&#8221; Ya yi shiru kamar wanda zai biya musu darasi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Idan har kunamarnan mace ce, yanzu haka na san tana da masoyi wanda yake son ta kamar yadda nake son Sufi, yanzu haka idan na kasheta shikenan na raba su da ita har abada kamar yadda ni ma aka raba ni da Sufina. Zafin rabuwa da masoyi na musamman ne, na \u0257an\u0257ane shi ban ji da\u0257i ba, don haka ba na fata ko ma\u0199iyina ya sake \u0257an\u0257anar ra\u0257a\u0257insa. Shi ya sa ba zan kashe ta ba kamar yadda ba zan bari a kashe ta ba. Ina so yadda ta baro gida lafiya ta koma ta tarar da masoyinta lafiya.&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Ba wai maganar da yake yi ba ce kawai ta ba wa abokanan nasa mamaki, sai dai yanayin yadda yake maganar ne da kuma hawayen da yake zuba a idanuwansa ya sa duk jikinsu ya yi sanyi. Ba don komai ba sai don sanin irin walagigi da guguwar soyayya ta yi da matasan biyu da kowa ya kwana da sanin labarin soyayyarsu a cikin \u0257an \u0199auyen&#8230;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan muka kalli wannan misalin, za mu ga a cikin shafi biyu na farkon littafin an bayyana gaba\u0257aya al\u0199iblar labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022Su waye taurarin?<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022Mene ne jigon labarin?<\/p>\n\n\n\n<p>Duk mai nazari zai iya fahimtar hakan da iyaka wannan rubutun da ya karanta, sauran abubuwan da ya kamata ya sani kuma sai ya shiga cikin labarin sosai. Al-muhim dai dole za a dasa masa son jin ta yadda aka haihu a ragaya game da matasan.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wannan kuma akwai ragowar ga\u0253o\u0253in da ake gina farkon labari da su, wato irin su:<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"ii-tsakure\"><strong>ii- Tsakure<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"iii-ta\u0253a-ka-lashe\"><strong>iii- Ta\u0253a ka lashe<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"iv-somin-ta\u0253i\"><strong>iv- Somin ta\u0253i<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Asalin kalmar tsakure daga tsakurowa aka samo ta, wato dai a nan marubuci yana so ya nuna wa mai karatu cewa ya tsakuro masa wata ga\u0253a ne a can cikin tsakiyar labarinsa, wata\u0199ila don yana tunanin ga\u0253ar za ta yi wa shi mai karatun amfani, ko kuma yana so ya nuna masa muhimmin darasin da yake cikin labarin nasa da idan ya yi jimirin karatu zai tarar a gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku duba makalarmu ta farko da ta yi <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/maanar-jigo-da-yadda-ake-samar-da-shi-a-labari\/\">cikakken bayani game da jigo<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta\u0253a ka lashe da somin ta\u0253i ma duk kusan abu \u0257aya suke nufi. Akwai wata al&#8217;ada ta mahauta masu sayar da balangu, idan mai saya ya je kafin ma ya fa\u0257i na nawa za a ba shi sukan \u0257an yanko masa tsokar somin ta\u0253i ya ci, ta yadda idan ya ci zai ji da\u0257in suyar ya saya da yawa. To shi ma wannan hikimar kenan, ana tsakuro wa manazarci wata dadda\u0257ar ga\u0253a ce da za ta tsaya masa a rai ta yadda hankalinsa ba zai kwanta ba sai ya karanta labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai misalai na kowannen su, sai dai kuma idan aka tsawaita zance a wuri \u0257aya yana kawo gundira ga mai karatu. Don haka ba sai mun kawo nasu misalan ba za mu \u0199ara zuwa ga\u0253a ta gaba, kuma ta \u0199arshe a cikin ga\u0253o\u0253in dabarun rubuta farkon labari.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>V- Sanya rintsi ko za\u0199uwa a farkon labari<\/strong>: Idan har marubuci ba zai yi amfani da duk salo biyar \u0257in da muka kawo bayanansu a baya ba, wato dai yana so kawai ya bu\u0257e farkon labarinsa da asalin masomar labarin. To yana da kyau matu\u0199a ya kula da wasu muhimman abubuwa biyu wajen samar da farko mai armashin da zai iya jan hankalin mai karatu. Abubuwan su ne:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Gan\u0257oki<\/li><li>Ba\u0257oki<\/li><\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"su-\u0257in-me-suke-nufi\">Su \u0257in me suke nufi?<\/h2>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"gan\u0257oki\"><strong>Gan\u0257oki<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p>Gan\u0257oki a labari shi ne idan mutum ya fara karatu ya ri\u0199a jin labarin yana fusgar hankalinsa, ya ri\u0199a jin har ya matsu ya ji abin da zai faru a gaba cikin labarin. Wato dai a yi ta marubuci <strong>Jeffrey Archer<\/strong> da ya ce &#8216;marubuci ya tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shauki da son gano mai zai faru a cikin shafin da ya bu\u0257a \u0257in&#8217;, mai karatu ya ri\u0199a jin ba ya son ya ajiye littafin ma kwata-kwata.<\/p>\n\n\n\n<p>Kodayake ba a iyaka farkon labari ba, a gaba\u0257aya cikin labari ma sa\u0199a gan\u0257oki yana da matu\u0199ar muhimmanci ga labari. Duk labarin da ya samu gan\u0257oki mai kyau yana iya hana shagalalle yin salla a kan lokacinta, yana iya mantar da mai karatu cewa \u0199ir\u0199irarren labari yake karantawa ba labarin gaskiya ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Yana da kyau mu mayar da hankalinmu sosai a kan wannan ga\u0253ar, saboda hatta al\u0199alan gasa idan suka samu labari mai gan\u0257oki yana yi musu tasiri, ta yadda suna iya sha&#8217;afa da duba kura-kuran marubucin, su yi ta tafiya da\u0257in labarin yana fusgar su. Wani lokacin sai sun yi nisa za su tuna cewa ashe fa har da duba kura-kurai suke yi ba nisha\u0257i kawai ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba sai an fa\u0257a ba, duk labarin da ya ja hankalin al\u0199ali zai yi wuya shi al\u0199alin ya ba wa wannan labarin makin da bai kamata ba, irin haka ne ke jawo sai ka ga labarinka ya fi na wanda ya zo na \u0257aya jigo mai kyau, amma shi an ba shi na \u0257aya kai ba a ba ka ba. To abin tambaya shi ne ta yaya za a yi mu samar da gan\u0257oki a labaranmu? Wannan yanzu ya kamata mu tattauna kafin mu je ga\u0253a ta gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana samar da gan\u0257oki ne da dabarar da mai jan kunne yake kira \u2018what happens next&#8217; ma&#8217;ana me zai faru a gaba?Dabarar ita ce a ri\u0199a yanyanka labari yadda kafin a gama warware matsala guda an sake sa\u0199a wata, ana warware wacce aka sake sa\u0199awa kuma sai wata mai girma da ta fi ta baya ta sake rikitowa. A haka za a yi ta tafiya har a zo \u0199arshen labarin. Wannan salon yana sanya mai karanta labari ya \u0253ata lokacinsa yana karatu cike da za\u0199uwa da son jin me zai faru a \u0199arshen labarin ba tare da ya gajiya ba kamar yadda na fa\u0257a.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku ci gaba da karanta misalin da muka kawo <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-gandoki-a-cikin-labari\/\">a wannan ma\u0199ala ta gaba<\/a>, wanda zai \u0199ara mana fahimtar gan\u0257oki sosai insha Allahu. <\/p>\n\n\n\n<p>Kamar kullum, \u0199ofar gyara, sharhi, \u0199arin haske ko tambaya a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alar da ta gabatai, mun yi bayani ne game da tsarin murhun girka jigo a labari, inda muka bayyana madogara uku da suka zama kamar duwatsu uku na murhu da idan babu su babu labari. A cikin bayaninmu mun tsaya ne a kan misali na farko a \u0199ar\u0199ashin dabarun gina farkon labari, inda muka&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-sanya-tsakure-taba-ka-lashe-da-somin-tabi-a-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Yadda ake sanya tsakure, taba ka lashe da somin tabi a labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3336,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[2,58],"tags":[3,16,17,18],"class_list":["post-1002","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-writing-tips","category-hausa","tag-dabarun-rubutu","tag-somin-tabi","tag-taba-ka-lashe","tag-tsakure"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/11\/Tsakure-da-taba-ka-lashe.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1002","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1002"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1002\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3336"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1002"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1002"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1002"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}