{"id":1082,"date":"2021-11-30T18:10:38","date_gmt":"2021-11-30T18:10:38","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=1082"},"modified":"2022-07-13T01:35:59","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:59","slug":"yadda-ake-samar-da-gandoki-a-cikin-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-gandoki-a-cikin-labari\/","title":{"rendered":"Yadda ake samar da gandoki a cikin labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alar da ta gabata, mun fara yin bayani game da <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-sanya-tsakure-taba-ka-lashe-da-somin-tabi-a-labari\/\">fa&#8217;idar samar da gan\u0257oki a cikin labari<\/a>, muka ce matsayin gan\u0257oki da ba\u0257oki a cikin labari, da yadda suke armasa labari, tamkar matsayin dabbobi ne a cikin gidan zoo da irin yadda samuwarsu a ciki yake \u0199ara wa gidan kwarjini da armashi ga masu ziyara. Irin yadda wanda ya je kallon dabbobi a gidan zoo zai ji idan ya je ya tarar babu dabbobin kirki a ciki, sai tarin karnuka da akuyoyi ko kaji, haka karatun labari zai \u0199i yi wa manazarci armashi idan a cikin labarin babu gan\u0257oki da ba\u0257oki.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan shi ya sa muka ce za mu fa\u0257a\u0257a bayaninmu game da yadda ake samar da gan\u0257oki a waccan ma\u0199alar, to cikin amincewar Allah za mu yi bayani yanzu daidai gwargwadon yadda za&#8217;a fahimta.<\/p>\n\n\n\n<p>Da farko mun ce ana amfani da dabarar mai jan kunne ta \u2018what happens next? &#8216; , to hikimar ita ce: Kana cikin nuna tauraronka yana matu\u0199ar bu\u0199atar ku\u0257in gaggawa da zai yi wani muhimmin al&#8217;amari da shi a cikin labarin ya rasa, kwatsam kuma sai ka nuna cewa ga shi ya tsinci wasu ma\u0199udan ku\u0257a\u0257e a jaka da za su ishe shi ya yi wannan gagarumin al&#8217;amarin har ma ya samu canji. A daidai wannan ga\u0253ar da tauraron yake murna ya samu ku\u0257in biyan bu\u0199atarsa, to shi ma fa mai karatu murna yake yi cewa tauraronsa ya samu ku\u0257in wannan muhimmin al&#8217;amarin. Ashe kuma a baya ka nuna cewa tauraron mutum ne mai gaskiya da amana, don haka kafin ya yi amfani da ku\u0257in kawai sai ka nuna cewa ga wasu marayu sun zo wurin shi suna cigiyar ku\u0257in kayan gadonsu da aka sayar za a raba musu ya \u0253ata.<\/p>\n\n\n\n<p>Kun ga kenan dolen tauraron ya \u0257auki ku\u0257insu ya ba su tunda shi mai amana ne kamar yadda ka labarta a baya, don haka sai kawai a ji tauraron ya \u0257akko musu ku\u0257insu ya ba su suna ta yi masa godiya suna murna da amanarsa sun tafi. To daga nan ne bayan ya ba su ku\u0257in shi kuma mai karatu zai fara tunanin \u2018what happens next?&#8217;&nbsp; ma&#8217;ana a ina kenan kuma tauraron zai sake samo wasu ku\u0257a\u0257en da zai yi wannan muhimmin al&#8217;amarin nasa? Yana cikin wannan tunanin kuma sai ka samar wa da tauraron mafita ta hanyar da bai ta\u0253a zato ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Irin wannan tunanin shi zai ri\u0199a ri\u0199e makarancin labarinka ba tare da ya sani ba har ya je \u0199arshensa. Ba sai lallai da matsala irin wacce muka yi misali ba, ana iya sa\u0199a gan\u0257oki a labari ta mabanbanta fuskoki iri-iri. Ana iya sa\u0199a gan\u0257oki da soyayya, abota, rashin jituwa da duk sauran al&#8217;amuranmu na yau da kullum. A don haka za mu bayar da wani \u0257an ta\u0199aitaccen misali da wani labarina mai taken Nisan Kwana.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"nisan-kwana\">Nisan Kwana&#8230;<\/h2>\n\n\n\n<p>(Sai da gwaji)<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;<em>A cikin tsakar rana mai tafasa ruwan kai, a cikin tsakiyar kwaltar mai cike da cunkoso, yana tsaka da tafiya, sai ga shi tsidik a tsakiyar jama&#8217;a kamar an jefo shi, a kan tsakiyar siddin babur \u0257insa roba-roba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Yana zuwa ya ri\u0199a danna amsakuwwar babur \u0257in da niyyar cincirindon mutanen da suke wurin su ba shi hanya ya wuce. Amma kuma abin da ya ba shi mamaki shi ne ganin wata mota mai \u0199irar &#8216;Jeep&#8217; da take a gindaye a tsakiyar titin, ta tare hanya ta yadda babu wurin wucewa wadatacce, sai dai motoci su ri\u0199a ratsewa a hankali ta bayanta.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Cikin takaici ya kafe babur \u0257in a gefen hanya ya nufi wajen motar, bisa ji da ya yi jama&#8217;ar da suka kewayeta suna ta hayaniya. Sai da ya \u0199arasa wajen ya fahimci kamar da gayya direban motar ya ajiyeta a tsakiyar hanyar. A tare da shi wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce mutane suka kewayeta suna ta ba ta ha\u0199uri, yayin da ita kuma ta yi burus kamar bata ji ba, kamar ita ce ma ta sa direban ya ajiye motar a haka.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Me yake faruwa ne?&#8221; Matashin ya yi tambayar da ya jawo hankulan dayawan jama&#8217;ar wurin kan shi, duk da dai babu wanda ya tamka masa in bacin nazarin shi da ya ga kamar suna yi. Gaba\u0257aya jikin shi a rufe yake da kayan tsere ta yadda babu abin da za a iya gani a jikinsa sai farin sandan wuyansa, kan shi sanye da irin hular nan ta kwano.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Me yake faruwa a nan ne?&#8221; Ya sake maimaita tambayar ta shi jin an rasa mai amsa masa. Wani dattijon mutum ne da ya fara manyanta ya shiga yi masa bayanin abin da ya faru cewa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Wallahi bawan Allah ka ga muna zaune a nan wasu yara sun zo wucewa da keke wannan baiwar Allahn..&#8221; Ya nuna matashiyar budurwar.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Mai tu\u0199ata ya buge yaran, shi ne ya fito yana duba su ta sakko tana yi masa masifa wai ya wuce su tafi ya rabu da &#8216;yan talakawan nan, wa ya ce basu iya keke ba su hawo kan hanya. Shi ne fa mun zo muna yi mata magana kawai sai ta \u0257aga hannu ta mare ni ko duba girmana bata yi ba duk da na san ko mahaifinta ba zai girme ni ba, bayan tarin shekaru da na kwashe ba a mare ni ba.&#8221; \u0198walla ta kawo idanuwansa, ya saka hannun riga yana gogewa a raunane ya ci gaba da cewa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;To shi ne fa wai a hakan ma ta tare hanya wai sai ta ga uban da ya tsaya mana da har za mu tare ta da maganar banza, bayan ta saka waya ta kira mahaifinta ta fa\u0257a masa \u0199arya da gaskiya ya ce yana zuwa.&#8221; Tsohon bai gama sauke numfashi ba matashiyar budurwar ta sake kwa\u0257a masa tafi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ni ce nake yi maka \u0199arya?&#8221; Ta tambaye shi da tsiwa abin da ya yi matu\u0199ar ba wa matashin saurayin mamaki kenan sanadin da ya sa ya daka mata tsawa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ke ba ki da kunya ko? Wannan babban mutumin da ya girmi ubanki za ki mara a gaban taron jama&#8217;ar yara da \u0199annensa?&#8221; Ya tambayeta yana nuna mata yatsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Na mare shi ko zaka rama masa ne?&#8221; Ta tambayi matashin saurayin.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ok! So kike na rama masa kenan?&#8221; Shi ma ya tambayeta tare da cire hular kan shi wacce ta bayyana tsananin kyan surarsa da kwarjininsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Baba ri\u0199e mini hular nan na rama maka marin ka.&#8221; Ya furta hakan tare da ba wa tsohon hular \u0199arfen da ya cire ya nufi kan matashiyar budurwar gadan-gadan. Sosai saurayin kyakkyawa ne, kuma ya yi mata kwarjini. Amma saboda shegen jiji da kai irin nata, da ta\u0199amar su suke da garin ta dake tana jiran shi ya \u0199arasa wajen nata ta ga \u0199arshen rashin kunyarsa kamar yadda zuciyarta take raya mata.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ke &#8216;yar gidan uban waye da za ki daki sa&#8217;an ubanki kuma ki tare wa mutane hanya?&#8221; Ya watsa mata tambayar cikin muryar shi da ta ka\u0257a hantar cikinta.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kana so ka sani ne?&#8221; Ta yi masa tambayar da bata bari ya amsa ba ta ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;To bari na nuna maka.&#8221; Kawai sai ta \u0257aga hannu za ta mare shi, ya yi caraf ya ri\u0199e hannunta tare da watsa mata wani murmushi na mugunta sannan ya ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ni za ki mara?&#8221; Bata amsa ba ya ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Tunda ke kin kasa nuna mini ke &#8216;yar gidan uban waye bari ni na nuna miki ko ni waye.&#8221; Bai jira komai ba kawai ya yi amfani da \u0257aya hannun nasa ya ri\u0199e hannunta kamar almara, ai kuwa sai ya karya ta \u0253aras kamar yadda ake karya guntun itace. Sanadin da ya sa ta \u0199wala wata razananniyar \u0199ara ta azaba yayin da kowa a wurin kuma ya wage baki cikin tsananin mamakin ganganci da tarar aradu da ka irin na matashin saurayin, wasu ma tuni sun \u0257ora hannu a ka, don sun tabbata ha\u0199i\u0199a ya kira wa kansa ruwa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Zan baki adireshina koda za ki neme ni.&#8221; Cewar matashin saurayin yana kallonta har yanzu kuma dariyar muguntar yake yi mata. Ya saka hannu ya zaro biron da ke sa\u0199ale a gaban rigarsa, ya juya tafin karyayyen hannun budurwar ya fara rubuta adireshinsa a jiki, yayin da ita kuma babu abin da take yi sai kuka tana bin shi da kallo kamar a mafarki. Yana gama rubutawa kuwa ya mi\u0199e ya kar\u0253i hular kwanon shi a hannun dattijon ya ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ga adireshina nan za ki ga har da lambar wayata koda za ki neme ni! Kai kuma malam ka janye wa mutane wannan motar idan har ba so kake yi kai ma na karya ka ba!&#8221; Ya \u0199are yana kallon direban nata.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Ai kuwa babu shiri direban jiki na rawa ya shiga ya janye motar ya ba wa mutane hanya matashin saurayin ya sallami kowa ya ba wa dattijon ha\u0199uri ya saka hular \u0199arfen shi ya hau babur \u0257in shi bayan ya \u0257aga wa matashiyar budurwar hannu, gami da gwalo ya cilla a guje ya bar wurin&#8230;.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Ta yaya aka samar da gan\u0257okin?<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>\u2022Tun daga lokacin da mai karatu ya ji jarumar ta sa direbanta ya gindaya mota a kan titin da tarin jama&#8217;a ke wucewa ya tabbatar cewa ta taki wani abin, a ransa zai fara tunanin &#8216;wace ce ita haka?&#8217; Da ya ji kuma ta mari dattijo sannan ta kira mahaifinta ya zo ya \u0257aure mata gindi, mai karatu zai fara cewa &#8216;wata\u0199ila &#8216;yar wani hamsha\u0199in \u0199asar ne wanda ya sangarta ta da gata, ba ya son abin da zai \u0253ata ranta.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022Sai kuma kawai aka sake jefo wa mai karatu jarumin, da wani salo na tarar aradu da fa\u0257in goshi. Tunda mai karatu ya tabbata cewa jarumar &#8216;yar mai fa\u0257a a ji ne, ya san tabbas jarumin ba zai iya karyata ya ci bulus ba sai idan ya taki wani abin shi ma. A ransa zai fara tunanin &#8216;To shi wannan jarumin me ya taka? Ko shi ma wani \u0199usan ne a \u0199asar?&#8217; To idan ba \u0199usa ba ta yaya za ka ta\u0253a &#8216;yar manya kuma ka rubuta mata adireshin ka da gadara?<\/p>\n\n\n\n<p>Da wa\u0257annan tunane-tunanen za ka ri\u0199e zuciyar mai karatu, ka saka masa za\u0199uwa, zumu\u0257i, da \u0257oki ya ji ya matsu ya bu\u0257a wani sabon shafin don gani irin wainar da za a toya. To wannan shi ne ta\u0199aitaccen misali na gan\u0257oki, wato dai a sanya wa mai karatu \u0257okin labari a ransa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku duba ma\u0199ala ta gaba inda muka <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-badoki-a-wajen-gina-labari\/\">tattauna game da ba\u0257oki<\/a>, wanda shi kuma kishiyar gan\u0257oki ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Kafin sannan kamar kullum, \u0199ofar gyara, sharhi, tambaya ko \u0199arin bayani a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alar da ta gabata, mun fara yin bayani game da fa&#8217;idar samar da gan\u0257oki a cikin labari, muka ce matsayin gan\u0257oki da ba\u0257oki a cikin labari, da yadda suke armasa labari, tamkar matsayin dabbobi ne a cikin gidan zoo da irin yadda samuwarsu a ciki yake \u0199ara wa gidan kwarjini da armashi ga masu&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-gandoki-a-cikin-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Yadda ake samar da gandoki a cikin labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3332,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,8,19],"class_list":["post-1082","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-rubutun-labari","tag-writing-tips"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/10\/Yadda-ake-sanya-gandoki-a-labari.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1082","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1082"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1082\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3332"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1082"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1082"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1082"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}