{"id":1163,"date":"2021-12-05T21:23:38","date_gmt":"2021-12-05T21:23:38","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=1163"},"modified":"2022-07-13T01:35:58","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:58","slug":"sharhi-bisa-asalin-labarin-iliya-dan-mai-karfi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhi-bisa-asalin-labarin-iliya-dan-mai-karfi\/","title":{"rendered":"Sharhi bisa asalin labarin &#8216;Iliya Dan Mai Karfi&#8217;"},"content":{"rendered":"\n<p>Tun muna yara \u0199anana ake karanta mana labarin da ke littafin Iliya \u018aan Mai \u0198arfi wanda Malam Ahmadu Ingawa ya rubuta kuma kamfanin Gaskiya Corporation ya soma wallafawa a 1951. An ci gaba da wallafa a littafin \u0199ar\u0199ashin kamfanin NNPC a shekarun 1976 da 1980s har zuwa wannan lokaci da muke ciki ana ci gaba da wallafa shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Littafin na \u0199unshe da labarun nisha\u0257i na jarumtaka da \u0199uru da soyayya da ban al&#8217;ajabi da kuma ban tausayi. Marubucin littafin na Hausa, ya bayyana cewar ya rubuta shi ne domin mai karatu ya samu abokin hira daga hi\u0199ayoyin mutanen da suka shu\u0257e.<\/p>\n\n\n\n<p>Littafin na ba da labarin wani mutum ne mai suna Iliya wanda iyayensa talakawa suka haife shi a gidan gona. Bayan ya isa yaye, sai ciwon shan Inna ya kama shi. Ya zamana ba ya ko iya motsawa daga gadon da yake. Wata rana sai ba\u0199i suka ziyarci gidan, alhali iyayensa ba sa nan. Da suka nemi ya ba su ruwa ko wani abinci sai ya nuna musu cewar ba shi da lafiya. Don haka suka yi masa addu&#8217;a a cikin abin sha. Nan take da ya sha jikinsa yayi kyau har ya mi\u0199e tsaye.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutanen nan suka umarce shi da ya tafi zuwa birnin \u0198ib domin kawar musu da wani mugun dodo mai suna Gogaji. Bayan ya aiwatar da wannan aikin, sai kuma ya shiga duniya yayi ta bugawa da masu \u0199in gaskiya, da ma shi \u0257an gwagwarmaya ne. Haka dai har zuwa lokacin da ya\u0199i ya tasowa mutanen Birnin \u0198ib, sarki Waldima, wanda ya sa aka binne shi a wani rami amma matarsa watau Sarauniya ta yi dabara ta ha\u0199a rami tana kai masa abinci a \u0253oye. Lokacin da Waldima ya ga ya\u0199i ya doso su gadan-gadan, sai ya rasa inda zai sa kansa. Ya shiga \u0257aki yayi ta rusa kuka. Ganin haka Sarauniya ta shawarce shi da ya sa a tono Iliya ko da ransa ya taimaka musu. Bayan jayayya tsakaninsu, sai Sarki Waldima ya amince aka tono Iliya. Abin mamaki, sai ga shi nan kwance kan gado lafiya lau. Har ma ya \u0199ara \u0199iba da haske.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki Waldima ya nemi afuwar Iliya sannan ya sanar da shi halin da Birnin \u0198ib ke ciki. Iliya ya \u0257ebi askarawa goma suka shiga cikin dubunnan abokan gaba, cikin \u0199an\u0199anin lokaci suka karkashe su. Sai dai babu jima sai abokanen gabar suka tashi tangaram kamar ba su aka karkashe ba. Ganin haka askarawan nan goma suka koma fagen daga, amma Iliya bai shiga ba. Sai ya tafi can kan dutse shi da dokinsa \u0198walele, ya zurfafa cikin tunani da dogon nazari har bai san lokacin da ransa ya fita ba aka mai da shi dutse.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubucin ya \u0199ar\u0199are labarinsa da cewar, &#8220;ko yanzu idan ka je Birnin \u0198ib za ka iske Iliya da dokinsa a cikin siffar dutse.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"tsittsigen-littafin\">Tsittsigen littafin<\/h2>\n\n\n\n<p>Bisa binciken da muka yi, littafin Iliya \u018aan Mai\u0199arfi na da asali daga tatsuniyoyi da labaru na mutanen Rasha. Masu nazari sun bayyana cewar labarin Iliya daga wata tsohuwar tatsuniya ce mai suna Bylina. Ita wannan tatsuniya, ana rera ta ne kamar wa\u0199a, a ciki ake ambaton manyan gwarazan \u0199asar Rasha da irin gwagwarmayar da suka yi a zamaninsu. Yawanci labarun da ke ciki suna cike da kururutawa da zuzutawa da kambamawa. Wasu labarun ma ba su faru ba, haka dai ake rera su domin nisha\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>Tatsuniyar Iliya ta Belina, tana bayyana cewar ya kasance \u0257aya daga manyan dakarun da aka ta\u0253a yi a yankin wanda ake kira &#8216;Bogati&#8217; (bogatyr), watau jarumin mutum mai iya gwabzawa da dubunnan dakaru kuma ya karya su.<\/p>\n\n\n\n<p>Aka ce, lokacin da aka haife shi ya samu karaya a \u0199ashin bayansa, don haka ba ya iya tafiya ko&#8217;ina. A haka har ya shekara 32 a duniya. Wata rana wasu masu yawon wa&#8217;azi suka kawo ziyara garinsu mai suna Morum. Lokacin kuwa wasu arna da ake kira Tugar sun tarwatsa garin sun kama na kamawa sun kashe na kashewa. Raunana da tsofaffi irin su Iliya da iyayensa ne ka\u0257ai suka rage. Su ma ba sa nan suna gona suna ta aiki.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba\u0199in suka iske Iliya shi ka\u0257ai zaune a kusa da \u0257akin girki yana shan \u0257umi. Bayan sun fahimci irin na\u0199asar da yake da ita sai suka ba shi wani ruwa ya sha. Nan take ya mi\u0199e tsaye. Suka cigaba da zazzaga masa \u0199arfi har ya zama yana jin kansa kamar shi ne Sibyatogo (Svyatogor, shi ne watau Wargaji a littafin Iliya \u0257an Mai\u0199arfi). Shi Sibyatogo saboda tsananin \u0199arfin da yayi masa yawa har \u0199asa ba ta iya \u0257aukar sa. Saboda haka, sai ya hau kan tsauni ya ba wa wasu matafita takobinsa. Yayi musu wasiyyar su ba wa wani da zai gaje shi nan gaba. Shi kuma nan take ya zama dutse.<\/p>\n\n\n\n<p>A wata fa\u0257ar kuma, aka ce matafiyan sun garga\u0257i Iliya da kada ya kuskura yayi fa\u0257a da wani mai suna Sibyatogo. Wai shi ka\u0257ai ne duk duniya zai iya galaba akansa. Sai dai zuciya ta fisgi Iliya ya tarar da shi yana barci ya kabra masa takobi sau uku amma bai ko yi motsi ba. Can dai sai ya mi\u0199a hannu ya kamo Iliya ya jefa cikin aljihunsa. Nan fa Iliya ya ji kamar an jefa shi wata rijiya mai zurfi. Don haka ya nemi afuwa suka shirya. Suna tafiya sai suka ga wani \u0199aton akwati. Iliya ya shiga ciki ya kwanta amma ko kamu \u0257aya bai cika ba. Sai Sibyatogo ya shiga. Nan da nan akwati ya rufe da shi. Da ya ga lallai ba zai ku\u0253uta ba, sai ya jefowa Iliya takobinsa sannan ya huro masa dukkan \u0199arfinsa. An ce wasu mutane a \u0199asar Belarus da Ukrain da sauran yankunan tsohuwar Rasha yanzu haka suna bautar akwatin Sibyatogo. Sunan addinin nasu Rodnovery.<\/p>\n\n\n\n<p>Mu dawo zancen mu. Lokacin da ya ji \u0199arfi yayi masa yawa, sai matafiyan nan da suka warkar da shi suka yi masa umarnin ya tafi wajen Sarki Vladimir Krasnoye Solnyshko mai mulkin Kiev domin ya ceci al&#8217;ummar daga sharrin wani dodo mai suna Idolishche Poganoye wanda yake kashe mutane da ihunsa.<\/p>\n\n\n\n<p>A birnin Kiev aka na\u0257a shi sarautar shugaban askarawa. Ya zamana suna kare Rashawa daga harin abokan gaba. A cikin wannan arangamar wata rana maya\u0199a suka kawo hari, suka kama wata &#8216;yar sarauta mai suna&nbsp; Vassilisa. Ilya ya hau tare da sauran abokansa, Dobrynya Nikitich da Alyosha Popovich. Anan suka yi nasara suka halaka mutane da yawa. Sai kuma soyayya ta \u0199ullu tsakanin Iliya da gimbiya Vassilisa. Bayan wani lokaci ta yi ciki. Sai dai Iliya ba shi da lokacin da zai zauna cigaba da kula da ita. Don haka ya yi wasiyyar idan namiji ne ta sa masa suna Sokolnichek. Watau &#8216;Falcon&#8217; da turanci.<\/p>\n\n\n\n<p>Wata rana Sarki Tugar mai suna Tsar Kalin ya fusata ya shirya wani gagarumin ya\u0199i domin mur\u0199ushe birnin Kiev. Ya sa musu shara\u0257in su biya shi harajin zinariya zambar dubu bakwai idan suna son kansu da arziki. Lokacin kuwa Ilya sun \u0253ata da Sarki Viladimir har ya sa an \u0257aure shi tsawon shekara goma ba ci ba sha a kurkuku sakamakon wani sharri da waziri Mishatychka ya \u0199ulla masa.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarki Viladimir ya sa a duba ko Iliya na da rai, sai aka gan shi cikin \u0199oshin lafiya, ga abinci nan iri-iri gabansa. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon wani adikon sihiri da matarsa ta ta\u0253a ba shi. Cikin hanzari Sarki Viladimir ya nemi afuwa. Iliya ya yafe masa. Aka shiga shirin ya\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p>Can gefe guda kuma Sarki Tsar ya kama sarauniya Vassilisa tare da \u0257anta. Har ma ya koyawa \u0257an nata ya\u0199i ya zama gagara gasa. A fitowa ta farko sai ya aiko shi domin ya ya\u0199i Iliya. Bai sani ba ashe shi ne mahaifinsa na gaskiya.&nbsp; Bayan sun yi karon battar \u0199arfe ne Iliya ya gane shi ta hanyar zoben da ya gani a hannunsa. Yaro ya gane mahaifinsa da irin shaidar da mahaifiyarsa ta sanar da shi. Nan da nan suka shirya. Suka tunkari abokin gabarsu watau Sarki Tsar.<\/p>\n\n\n\n<p>An kai ruwa rana da bata kashi sosai har Iliya da \u0257ansa da taimakon wani masassa\u0199i mai suna Razumey suka karya rundunar Tsar kuma suka kashe shi. Sarki Viladimir da mutanen Kiev suka yi ta murna. Nan take Sarki Viladimir ya yi masa tayin matsayin waziri a fadarsa, amma Iliya ya \u0199i kar\u0253a. Ya za\u0253i ya koma gidan gona shi da matarsa su ci duniyarsu. Ya dan\u0199awa \u0257ansa Sokolnichek takobin Sibyatogo domin shi ma ya cigaba da gwagwarmaya kamar yadda ubansa yayi.<\/p>\n\n\n\n<p>Tatsuniyar ta \u0199are da cewar Iliya ya cigaba da zama da iyalinsa yana ta\u0253a noma yana ta\u0253a ya\u0199i har wata rana da tsufa ya cimmasa ya gina wani katafaren \u0257akin bauta (coci) a garin Pechersk Lavra da ke birnin Kiev. Ya cigaba da wa&#8217;azi har zuwa \u0199arshen rayuwarsa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"tasirin-tatsuniyar-iliya\"><strong>Tasirin tatsuniyar Iliya<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Tatsuniyar Iliya ta yi tasiri sosai a sassan duniya musamman wuraren da ake son motsa jarumtaka ko soyayya ko taimakon al&#8217;umma. \u0198asar Rasha ta gina wani jirgi mai suna Skorsky Ilya Morumet wanda take ta\u0199ama da shi a ya\u0199in duniya na \u0257aya. Haka nan a Amerika an yi wani fim a 1956 wanda ake kira Ilya Morumets of Morum. Littafin Iliya \u0257an Mai\u0199arfi na daga cikin manyan ayyukan da ake ambatawa cewar suna da asali daga wannan tatsuniyar.<\/p>\n\n\n\n<p>Masu binciken tarihi a Rasha da kewaye suna ta tono abubuwa da dama da suke cewa suna da ala\u0199a da wani \u0253angare na abin da tatsuniyar ke ambatawa. Misali, a shekarar 1988, wasu \u0199wararru masu binciken tarihi suka tono wani \u0199ashin baya a yankin Kiev. Suka yi aune-aune suka ce mamallakin \u0199ashin mutum ne dogo \u0199a\u0199\u0199arfa, kuma da alama yayi fama da ciwon \u0199ashin baya a lokacin da yake yaro \u0199arami. Sai dai ba su ambaci sunan kowa ba, amma sai mutane suka tafi akan cewar Iliya na \u0199auyen Morum ne.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tun muna yara \u0199anana ake karanta mana labarin da ke littafin Iliya \u018aan Mai \u0198arfi wanda Malam Ahmadu Ingawa ya rubuta kuma kamfanin Gaskiya Corporation ya soma wallafawa a 1951. An ci gaba da wallafa a littafin \u0199ar\u0199ashin kamfanin NNPC a shekarun 1976 da 1980s har zuwa wannan lokaci da muke ciki ana ci gaba&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhi-bisa-asalin-labarin-iliya-dan-mai-karfi\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhi bisa asalin labarin &#8216;Iliya Dan Mai Karfi&#8217;<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":3343,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[30],"class_list":["post-1163","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-malam-ahmadu-ingawa"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/12\/Sharhin-Iliya-Dan-Mai-Karfi.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1163","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1163"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1163\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3343"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1163"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1163"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1163"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}