{"id":1835,"date":"2021-12-27T14:26:34","date_gmt":"2021-12-27T14:26:34","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=1835"},"modified":"2022-07-13T01:35:57","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:57","slug":"yadda-ake-samar-da-badoki-a-wajen-gina-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-badoki-a-wajen-gina-labari\/","title":{"rendered":"Yadda ake samar da badoki a wajen gina labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alar da ta gabata mun kawo muku yadda ake samar da gan\u0257oki a labari inda muka yi bayani kuma muka kawo misalan irin yadda ake samar da gan\u0257okin, <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-gandoki-a-cikin-labari\/\">wato za\u0199uwa da son jin cigaban labari<\/a>. A ma\u0199ala yau, za mu tattauna ne a kan yadda ake samar da ba\u0257oki.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda na fa\u0257a tun a waccan ma\u0199alar, ba\u0257oki kishiyar gan\u0257oki ne. A gan\u0257oki murna da za\u0199uwa makaranci yake yi ya ji abin da zai faru a gaba, amma a ba\u0257oki fargabar da tsoron abin da zai iya faruwar ne suke fusgar manazarcin labarin. Za mu fi fahimtar darasin idan aka bayar da misali, don haka zan sake bu\u0257ewa da wani misalin a cikin labarina Kukan Jini.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"kukan-jini\"><strong>Kukan Jini<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p><em>A cikin jerin irin ni&#8217;imtattun ranakun nan ne kyawawa da ke \u0199ayace da ni&#8217;imar dadda\u0257ar iska mai ka\u0257awa ha\u0257e da wani irin \u0199amshin \u0199asa mai da\u0257i, da yake ba a da\u0257e da fara yayyafi ba aka \u0257auke. Sai dai duk da haka garin akwai alamar hadarin da ke nuni da za&#8217;a iya yin ruwa a kowanne lokaci.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Yamma ta fara yi wajen misalin \u0199arfe hu\u0257u da rabi zuwa biyar, har na fara harha\u0257a kayana da niyyar na rufe shagon nawa na tafi gida, don kuwa na san tunda har hadarin nan ya taso ba zai bar mutane su sake da garin ba. Ba lallai ba ne ma a \u0199ara yin ciniki, duba da yadda jama&#8217;a sai ficewa suke yi daga cikin kasuwar cikin sauri-sauri, kowa \u0199o\u0199ari yake yi ya isa gida kada ruwan nan ya tare shi a waje.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>A daidai lokacin ne kuma ta shigo mini cikin rumfar shago da gudu-gudu cikin alamar ru\u0257u da firgici kamar wata wacce ta ga mutuwa, haka kuma cikin \u0199arfin&nbsp; hali ba tare da jiran komai ko neman izinina ba ta shige can cikin shagon tana magana mai gauraye da haki.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Malam don Allah ka rufa mini asiri ka taimaka mini.&#8221; Tuni kuma ta samu bayan wata \u0199atuwar akwati cikin tarin akwatunan sayarwar da ke shagon ta \u0253uya ba tare da jiran abin da zan ce ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Gaba\u0257aya sai ta ba ni mamaki ta kuma \u0257aure mini kai, lokaci guda kuma zuciyata ta fara \u0257arsa mini lallai ba ta da gaskiya, don haka ne na bu\u0257i baki zan yi mata magana amma ganin taron wasu \u0199artin da suka ci burki a \u0199ofar shagon nawa suna wani haki da waige-waige ya hana&nbsp; ni, don kuwa zuciyata tana raya mini ita suka biyo, kuma ga dukkan alamu idan har suka kama ta ba za ta ji da da\u0257i ba. To amma kuma me zai sa su biyo ta? Don kuwa kwata-kwata ba ta yi mini kama da mara gaskiya ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Daga inda nake a tsaye ina iya jin muryar \u0257aya cikin su yana tambayar mutum biyun da suka riga shi zuwa wurin.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ina ta yi? Kun gan ta kuwa?&#8221; Wanda aka tambaya \u0257in ya ba shi amsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Wallahi ba mu gan ta ba, amma na tabbata wani shagon ta shiga a nan. Don haka yana da kyau mu duba sosai.&#8221; \u0198ar\u0199are kalaman nasa sai ya sa na ji gabana yana fa\u0257uwa sai ka ce wanda shi za&#8217;a kama, ni da ko laifin da ta yi musu ma ban sani ba. Na yi saurin mayar da fitilun idanuwana cikin shagon, watak&#8217;ila kuma hakan yana da nasaba da son \u0199ara gani ko ta samu kyakkyawar ma\u0253oya inda ba za a gan ta ba kada ta jaza mini masifa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Aikuwa ina juyawa muka yi ido biyu da ragowar gefen gyalenta da bai gama \u0253uya ba, na san duk wanda ya nufo shagon tun daga nesa zai iya hango ta. Don haka ne na sake juyawa wajen \u0199artin don ganin ko sun wuce, sanadin da ya sa na ji gabana ya sake fa\u0257uwa sakamakon gani da na yi biyu cikin su sun nufo shagon nawa gaba\u0257aya.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Irin yadda \u0253arawon da ya bi hanyar da ba ta \u0253ullewa yake yin mutuwar tsaye, haka ni ma na san\u0199are cikin rarraba ido kamar \u0257an dokar da aka ba wa cin hanci a cikin mutane. Wanda ya fara yi mini magana wani garjeje ne ba\u0199i firgita maza, cikin wata irin murya ta shi mara da\u0257i kamar an daki hujajjiyar ganka.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Malam ba ka ga wata &#8216;yar iskar yarinya ba da wani farin gyale a jikinta, mun biyo ta kuma muna kyautata zaton wani shagon ta shigo a nan ta \u0253uyar mana.&#8221; Ya \u0199are zancen yana mai gwararo mini jajayen idanuwan shi masu kama da na soja a filin daga&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da mai karatu ya zo \u0199arshen wannan shafi, cike da fargaba ko tunanin &#8220;Anya kuwa \u0199artin ba za su ga yarinyar ba tunda dai ta bar gefen gyalenta a waje? Ko kuwa ba za su gan ta ba? Idan sun gan ta to me za su yi mata kenan da suka biyo ta da gudu haka? Shin me ma ta yi musu?&#8221; Zai bu\u0257e shafin gaba ne zuciyarsa cike da tarin irin wa\u0257annan tambayoyi na fargaba, wa\u0257anda suke gauraye da sanya zumu\u0257in jin amsarsu a gaba, to ire-iren wannan salon shi ake kira Ba\u0257oki. A daidai wannan ga\u0253ar kuma muka kawo \u0199arshen dabarun gina farkon labari, sai dai kuma kafin mu tafi zuwa ga\u0253a ta gaba wato dabarun gina doron labari (tsakiya), akwai wasu muhimman ga\u0253o\u0253i da muka tsallake wa\u0257anda suke da bu\u0199atar mu yi musu komayya. Ku karanta <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/muhimmancin-zurfafa-bincike-wajen-rubutun-labari\/\">a wannan ma\u0199ala<\/a> ta gaba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alar da ta gabata mun kawo muku yadda ake samar da gan\u0257oki a labari inda muka yi bayani kuma muka kawo misalan irin yadda ake samar da gan\u0257okin, wato za\u0199uwa da son jin cigaban labari. A ma\u0199ala yau, za mu tattauna ne a kan yadda ake samar da ba\u0257oki. Kamar yadda na fa\u0257a tun&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-samar-da-badoki-a-wajen-gina-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Yadda ake samar da badoki a wajen gina labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3315,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[20,3,21,22,8],"class_list":["post-1835","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-badoki","tag-dabarun-rubutu","tag-gandoki","tag-rubutun-hausa-novel","tag-rubutun-labari"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/12\/Yadda-ake-samar-da-badoki.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1835","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1835"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1835\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3315"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1835"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1835"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1835"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}