{"id":1841,"date":"2021-12-27T15:35:08","date_gmt":"2021-12-27T15:35:08","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=1841"},"modified":"2022-07-13T01:35:57","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:57","slug":"muhimmancin-zurfafa-bincike-wajen-rubutun-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/muhimmancin-zurfafa-bincike-wajen-rubutun-labari\/","title":{"rendered":"Muhimmancin zurfafa bincike wajen rubutun labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alunmu na baya, mun tattauna akan abubuwan da suka zama muhimmai marubuci ya sani wajen gina farko-farkon labari, misali gina jigo, salo da makamantansu. Kafin mu ci gaba da abubuwan da suka shafi tsakiyar labari, bari mu duba wani muhimmin abu \u2013 zurfafa bincike wajen gina labari.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda muka sani bincike wata hanya ce da ake bi wajen neman sanin abin da ba a sani ba, ko kuma \u0199ara wa kai sani akan abin da ba a yi masa sani na ha\u0199i\u0199a ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bincike don gina labari ya \u0199unshi duk wasu bayanai da marubuci zai tattaro ya tsara su ya yi amfani da su wajen gina labarin. Dolen kowanne marubuci ne ya ri\u0199a yawaita bincike a kan dukkan abin da yake rubutawa, idan kuwa ba haka ba to tabbas zai yi danbarwa. Marubuci ya ri\u0199a sakawa a ransa cewa rubutun da zai yi rubutu ne da kowa zai iya karantawa tun daga kan mai&#8217;ilimi da jahili, babba da kuma yaro, malamai da \u0257alibai, idan kuwa haka ne dolen shi ne duk abin da zai rubuta ya tabbatar daidai ya rubuta.<\/p>\n\n\n\n<p>Mutunci, \u0199ima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a \u0199asa wanwar a duk lokacin da ya tafka wani gingimemen kuskure yake kuma da&#8217;awar daidai ya yi a cikin labarinsa. Kowa ya san marubuci ba likita ba ne amma kuma idan wani marubucin ya yi maka rubutu a kan aikin likita sai ka \u0257auka wani shugaban likitocin duniya ne saboda tsabar binciken da ya yi wajen rubutun nasa, don haka ko likita ne ya karanta labarin ba zai ta\u0253a ganin makusa ba a rubutun balle har ya kushe masa.<\/p>\n\n\n\n<p>Na ta\u0253a fa\u0257a a wata tattaunawa da aka yi da ni cewa akwai wata marubuciya da ta ta\u0253a yin rubutu a kan shari&#8217;a, rubutun nata ya samu kar\u0253uwa sosai musamman a wurin mata, sai dai kuma ga duk wanda ya san ilimin shari&#8217;a ba zai ta\u0253a \u0257aukar littafin da daraja ba, don kuwa rashin bincike ya sa ta yi wa doka karantsaye, shi kansa tauraron littafin ta saka shi ya aikata laifin da hukuncinsa shi ne kisa kai tsaye a musulunce da kuma tsarin doka irin ta kundin \u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma saboda rashin bincike ta wanke tauraron da molanka ba tare da ta kashe shi ba, wanda hakan kuskure ne, don kuwa tana nuna wa masu karatu su ma su je su aikata irin wannan laifin ba za&#8217;a kashe su ba, za&#8217;a yi musa hukunci irin na tauraron labarinta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda na fa\u0257a marubuci zai iya zama likita da zai fa\u0257a wa jama&#8217;arsa cuta da kuma maganin ta, marubuci zai iya zama malami da zai fa\u0257a wa jama&#8217;arsa abin da Allah Yake so da wanda ba Ya so, marubuci zai iya zama Al\u0199ali da zai sanar da jama&#8217;a doka da laifuffuka ya kuma sanar da su hukuncin kowanne laifi ta yadda zai zamana darasi ga wanda yake tunanin aikatawa ya fasa kada shi ma a yi masa irin hukuncin da aka yi wa tauraron labarin marubucin. Sai dai fa duk hakan zata faru ne idan marubucin ya yi bincike.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta hanyar bincike ne marubuci zai zama shakundum, ya zama komai da ruwanka ta yadda zai iya yin rubutu a kowanne fanni kuma rubutun ya \u0199ayatar da duk wanda ya karanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Hanyoyin yin bincike suna da yawa, kuma kowacce marubuci ya bi ta yi, to amma akwai manya-manyan hanyoyi guda uku da suke gaba da sauran wa\u0257anda ya kamata mu tattauna a kan su yanzu.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-tuntu\u0253ar-masana\">Tuntu\u0253ar masana<\/h3>\n\n\n\n<p>Hanya ta farko ita ce ta hanyar tuntu\u0253ar wani masani a kan maudu&#8217;in da za ka yi rubu a kai, wannan hanyar ta fi kowacce hanya kai waye don kuwa a cikinta ba a fiya samun matsala ba tunda tattaunawa ce ta baki da baki, fuska da fuska, ka kuma tambayi duk abin da ya shige maka duhu. Idan kana so ka yi rubutu ne a kan shari&#8217;a to yana da kyau ka samu wani lauyan ko alk&#8217;ali ko kuma wani mai ilimi a kan shari&#8217;a ya yi maka bayani musamman ma akan wani hukunci da kake son yi a cikin labarin. Idan an yi tattaunawar ta waya ma hakan babu laifi.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan a kan wani kasuwanci za ka yi rubutu a matsayinka na marubuci, yana da kyau ka samu irin wannan \u0257an kasuwar ka samu ilimin hanyar kasuwancin a wurinsa, don gudun kada ka yi rubutun da duk wanda ya san irin wannan kasuwancin zai yi maka dariya da zarar ya karanta rubutun saboda kuskuren da ka tafka.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan a asibiti ne ka nemi likita, idan a makaranta ne ka nemi malami ko lakcara, idan a kan tsaro ne ka nemi \u0257an sanda da sauran jami&#8217;an tsaro, idan a kan tarihi ne ka nemi masanin tarihi ko tsoho da dai duk sauran wanda ka san rubutun naka ya shafe su.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-nazarin-littattafai\">Nazarin littattafai<\/h3>\n\n\n\n<p>Hanya ta biyu ita ce ta hanya bincikar wasu littattafai da suka shafi abin da za ka yi rubutunka a kai, ka duba duk wani muhimmin batu da kake so ka sani.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-nema-a-yanargizo\">Nema a yanar gizo<\/h3>\n\n\n\n<p>Hanya ta uku ita ce ta yin bincike a yanar gizo (Internet) ka nemi duk abin da kake nema, yawanci kuma wannan hanyar an fi yin amfani da ita idan ana son a yi bincike na gaggawa, ko kuma binciken wani wuri da ya yi maka nisa (kamar \u0199asar waje), ko kuma binciken abubuwan da ba ka da sukunin mallakarsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Yanayin sauyawar zamani ya sa wannan hanyar ta fi kowacce hanya sau\u0199i a duk hanyoyin yin bincike, domin kuwa ko nan Bakandamiya ta ishe mu abar misali. Dukkan wa\u0257annan mu\u0199alun tun daga jigon labari da duk sauran muhimman abubuwa da suka shafi Adabi idan marubuci ya bincika zai samu, ga shi kuma kullum \u0199ara \u0257ora sababbin abubuwa ake yi ta yadda za a ce kusan komai za a samu. Muhawara mai ma&#8217;ana wacce sai mutum ya share kwanaki yana tsarata ne idan shi zai rubuta, kawai zai sameta cikin sau\u0199i a shashin muhawara na Bakandamiya, banda sauran fannoni na ilimi sosai iri-iri.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi ya sa a wurina ba zai zama uziri ba ga marubuci ya ri\u0199a yin rubutu karazube babu bincike, domin kuwa duk wani ilimi da yake nema idan ya bincika zai samu. Zan rufe ma\u0199alar tamu ta yau da maganar <strong><em>Nelson Mandela<\/em><\/strong> da ya ce<em> &#8220;Ilimi shi ne makami mafi \u0199arfi ko tasirin da za a yi amfani da shi a canza duniya<\/em>.&#8221; A ra&#8217;ayina marubuci shi ya fi kowa kusanci da wannan maganar, domin kuwa marubuci ne yake amfani da baiwa da iliminsa wajen canza wa duniya tunani ta hanyar rubuce-rubucensa, shi kuwa ilimi yana samuwa ne ta hanyar bincike, don haka yana da kyau mu ri\u0199a yin bincike.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku duba wannan makala da ta yi nazari akan <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari\/\">salon bayar da labari<\/a>.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alunmu na baya, mun tattauna akan abubuwan da suka zama muhimmai marubuci ya sani wajen gina farko-farkon labari, misali gina jigo, salo da makamantansu. Kafin mu ci gaba da abubuwan da suka shafi tsakiyar labari, bari mu duba wani muhimmin abu \u2013 zurfafa bincike wajen gina labari. Kamar yadda muka sani bincike wata hanya&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/muhimmancin-zurfafa-bincike-wajen-rubutun-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Muhimmancin zurfafa bincike wajen rubutun labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3312,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,24,22,8],"class_list":["post-1841","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-muhimmancin-bincike","tag-rubutun-hausa-novel","tag-rubutun-labari"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/12\/Muhimmancin-bincike-a-labari.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1841","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1841"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1841\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3312"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1841"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1841"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1841"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}