{"id":198,"date":"2021-10-16T15:45:58","date_gmt":"2021-10-16T15:45:58","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=198"},"modified":"2022-07-13T01:36:02","modified_gmt":"2022-07-13T01:36:02","slug":"maanar-jigo-da-yadda-ake-samar-da-shi-a-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/maanar-jigo-da-yadda-ake-samar-da-shi-a-labari\/","title":{"rendered":"Ma&#8217;anar jigo da yadda ake samar da shi a labari"},"content":{"rendered":"\n<p>Bisa sunna ta rayuwa komai yana da mafari ko tushe, kafin ka fara gini kana bu\u0199atar ha\u0199a fandisho, kafin ka yi shuka kana bu\u0199atar hu\u0257a ko saran shuka, amma shi yin rubutu na zube JIGO shi ne abin bu\u0199ata na farko kafin komai. Wannan shi ne dalilin da ya sa tunda dabarun rubutu muke so mu koya daga tushe, ba za mu tsallake jigo ba don gudun kada mu yi tuya mu manta da albasa. Sai dai duk da haka za mu yi \u0199o\u0199arin ta\u0199aita bayani sosai, mu fito da iyaka muhimman abubuwa da suka shafi jigo.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"1-ma-anar-jigo\">1. Ma&#8217;anar jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Kalmar jigo tana da ma\u2019anoni guda biyu wato ma\u2019ana ta lugga (literal meaning) da kuma wadda aka ba wani fannin ilimi isdilahi (technical meaning).<\/p>\n\n\n\n<p>Jigo a luggance na nufin abin da ake amfani da shi wajen banruwa a lambu. Muhimmancin jigo a lambu shi ne ya samar da su kansu tsirran ta hanyar amfani da shi wajen banruwa. Idan babu jigo babu ruwa, idan babu ruwa babu tsirrai, idan babu tsirrai su kuma babu lambu. Ganin muhimmancin jigo ga lambu, irin muhimmancin sa\u0199o a labari ya sa manazarta suka yi&nbsp; amfani da kalmar a matsayin manufa ko kuma sa\u0199o na labari, wanda shi ma a labari idan babu sa\u0199o babu manufa, idan babbu manufa kuma babu labari. (East da Wasu, 1948:47)<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aangambo, (1981:6) cewa ya yi &#8220;Jigo shi ne sa\u0199o ko manufa ko abin da labari ya \u0199unsa, wato abin da yake magana a kai.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A sau\u0199a\u0199a\u0199\u0199iyar jumla, jigo shi ne sakon da ake so labarin ya isar ga manazarci (mai karatu). Marubuci zai za\u0253i wani maudu&#8217;i ko kuma matsala ko ga\u0253a da ya yi rubutunsa a kai da niyyar haskakawa ko kuma isar da wani sa\u0199o akan wannan jigon ko maudu&#8217;i ga mai karatu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"2-ta-yaya-ake-samar-da-jigo\">2. Ta yaya ake samar da jigo?<\/h2>\n\n\n\n<p>Hanyoyin samar da jigon labari suna da yawa, ya danganta da yanayin kowanne marubuci.<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Wata rana ina zaune ina danna waya, sai na ci karo da hoton wani zobe na zinare da ya yi matu\u0199ar \u0199ayatar da ni a wayar, kawai sai na ji a raina ya kamata na yi wani rubutu da zai motsa tunani a kan wannan zoben. Daga haka kawai na samar da jigon labarin ZOBENA.<\/li><li>Wata rana labarin wani yaro da ya mari mahaifiyarsa ya riske ni. Abin ya \u0257aure mini kai, gani nake ta yaya za a yi duk soyayyar da ke tsakanin uwa da \u0257a amma har ya iya marinta. Da na bincika sai aka ce mini ai a shege ta haife shi babu aure, wai gori wani abokinsa ya yi masa ya koma gida a fusace yana mata \u0199orafi har ta kai shi ga mari. Tun daga lokacin da na fahimci cewa ba kowanne shege ba ne idan yana tuna ciwon abin da uwarsa ta yi masa yake iya girmama ta, sai na \u0257auki jigon na rubuta labarin ZANEN DUTSE don ankarar da mata illar kusantar namiji da haihuwa kafin aure.<\/li><li>Wata rana ina zaune na yi tunanin tunda nake ban ta\u0253a yin rubutu a kan siyasa ba, sai kawai na ji ina so na yi hakan. Da tunanin hakan na samar da jigon labarin TUFKAR MAKAHO.<\/li><li>Shi kuwa labarin RIKITACCE ina bacci na yi mafarkin jigonsa, da na farka na ji ban manta ba kawai sai na hau yin rubutu.<\/li><\/ul>\n\n\n\n<p>Abin lura, hanyoyin samun jigo suna da yawa. Akwai masu cewa samun jigon labari ne yake yi musu wahala, su yi \u0199o\u0199ari su ri\u0199a fa\u0257a\u0257a tunaninsu suna zurfafa shi a kan duk matsalar da suke so su yi rubutu a kanta, insha Allahu al&#8217;amarin jigo zai ri\u0199a zuwa musu da sau\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"3-raunin-labari-game-da-jigo\">3. Raunin labari game da jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Raunin labari game da jigo shi ne rashin haskakken jigo a rubutun. Me kuka fahimta da hakan?<\/p>\n\n\n\n<p>Shin ba ku ta\u0253a karanta labari kun gama kun yi nadamar karantawa ba? Akan yi nadamar karanta labari, ko kallon fim \u0257in da bai samu haskakken jigo ba, saboda wayargari ake yi labarin ba shi da wata ma&#8217;ana ta a zo a gani, ko kuma wani darasi da mutum zai \u0257auka a cikinsa. Hakan sai ya jawo makaranci ya yi ta tsaki yana nadamar \u0253ata lokacinsa wajen karanta abin da ba zai amfane shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan har mutum zai yi tsaki silar karanta labari, to ina kuma ga al\u0199alan gasa wa\u0257anda ba labarin shi ka\u0257ai suka karanta ba? \u018aaruruwan labarai ne suke shiga manyan gasa, shin ta yaya labari zai zama abin a kalla idan ba a tace an tsefe ba?<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"4-ta-yaya-zan-haskaka-jigon-rubutuna\"><strong>4. Ta yaya zan haskaka jigon rubutuna?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Hasken jigo ya dogara ne da irin yadda aka zaro shi a cikin al&#8217;umma, shi ya sa za\u0253ar jigon da ya dace a rubutu yana da matu\u0199ar muhimmanci. A bisa yadda tsarin \u0257an&#8217;adam yake, ya fi yarda da abin da ya ji ko ya gani ya faru da shi ko waninsa, ashe kenan idan kana so ka kama tunanin manazarcinka, zana masa rubutunka a cikin irin tarin matsaloli ko abin farincikin da ke kewaye da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin da nake so na ce, son samu marubuci wajen \u0257akko jigon labari ya \u0257akko irin jigon da ya shafi al&#8217;umma walau kai tsaye ko a kaikaice.<\/p>\n\n\n\n<p>Mun san cewa girgizar \u0199asa gaskiya ce kuma ana yin ta, to amma fa duk wanda ya \u0257akko jigon girgizar \u0199asa a wannan \u0199asar tamu ta Najeriya ba lallai ne rubutun na shi ya kama ranmu yadda ya kamata har ya isar mana da sa\u0199o ba, akan wanda zai \u0257akko jigon abin da muka sani kuma yake damun mu irin su rashin tsaro, rashin ruwa, rashin wuta, rashin tituna da sauran su. Abin da nake so na ce a ta\u0199aice shi ne &#8216;hirar shanu a bar wa \u0257an fulani da mahauci, hirar kifi kuma sai masunci&#8217;.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi ya sa duk lokacin da za ka za\u0253i jigo na rubutu, musamman rubutu irin na gasa, yana da kyau ka duba wasu abubuwa&#8230;.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"5-me-zan-duba-wajen-za\u0253ar-jigon-gasa\"><strong>5. Me zan duba wajen za\u0253ar jigon gasa?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Indai har gasa ce mai bu\u0257a\u0257\u0257an jigo ba ke\u0253a\u0253\u0253e ba, marubuci yana da bu\u0199atar ya duba abubuwa uku da za su zamo kamar duwatsu uku na \u0257ora tukunyar jigon sa.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"a-lokaci\"><strong>a. Lokaci<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p>Lokacin da mutum zai yi rubutu yana da matu\u0199ar muhimmanci, da lokacin rubutunka za ka auna irin jigon da kake bu\u0199atar ka girka wa al&#8217;ummarka har su ci suna santi. Za a fahimci wannan ga\u0253ar sosai idan muka je ga\u0253a ta gaba.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"b-abin-da-lokacin-ya-zo-da-shi\"><strong>b. Abin da lokacin ya zo da shi<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p>Bayan duba lokaci, sai a duba abin da lokacin ya zo da shi. A shekaru biyar zuwa shida baya, an samu yawaitar yawan fya\u0257e ga \u0199ananan yara, matsalar ta saka mutane da yawa kuka, yayin da wasu suke Allah wadai! Shin ko za ku iya tuna irin yadda aka ri\u0199a rububin duk rubutun da aka yi shi a kan fya\u0257e a wannan lokacin? Idan ban manta ba hatta gasar mata zalla ta Hikayata BBC da jigon fya\u0257e kazar shekarar ta yi nasarar \u0199yan\u0199yashe \u0199wanta.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekaru uku zuwa hu\u0257u kuma sai lokacin ya zo da yawaitar yadda mata suka ri\u0199a yanka mazajensu, a lokacin shi ma idan kana so ka ga ruwan sharhi da jinjina to ka \u0257ora al\u0199alamin rubutunka a kan wannan ga\u0253ar.<\/p>\n\n\n\n<p>Shekaru biyu zuwa uku baya kuma aka yi ebola, shekara \u0257aya zuwa biyu kuma aka yi corona, wanda babban misali shi ma kazar shekara ta gasar mata zalla ta Hikayata BBC ita ma da coronan ta yi nasarar \u0199yan\u0199yashe nata \u0199wan \u0257aukakar.<\/p>\n\n\n\n<p>A kula da wani abu, ba wai ina cewa dole ne sai ka yi rubutu a kan abin da lokaci ya zo da shi ba za ka iya yin nasarar girka labarin da manazarta za su yi santinsa, amma dai kula da hakan yana da matu\u0199ar muhimmanci. Idan kuma ba ka kula da za\u0253ar abin da lokaci ya zo da shi ba, to ka tabbata ka kula da ga\u0253a ta gaba yadda ya kamata&#8230;<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"c-su-wa-za-ka-yi-wa-rubutun\">C. Su wa za ka yi wa rubutun?<\/h3>\n\n\n\n<p>Wannan ga\u0253a ce mai muhimmanci ita ma, koda ka muhimmantar da ga\u0253o\u0253i biyu da suka gabata, to yana da kyau sosai ita ma wannan ga\u0253ar ka \u0199ara musu da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da za ka yi rubutu da ya shafi shari&#8217;a, yi tunanin cewa kamar wani al\u0199ali kake rubuta wa labarin. Yin hakan zai ba ka damar ka yi iyaka yinka wajen \u0257ora rubutun a kan irin layin da ya kamata.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan kana rubuta labarin gasa a matsayinka na marubuci \u0257alibin Adabi, yi tunanin cewa al\u0199alan gasar da za su duba labarinka su ma marubuta ne malaman Adabi ba \u0257alibai ba, ashe kenan wasu wa\u0257anda suka fi ka gogewa, da\u0257ewa da ilimin rubutun za ka tura wa rubutunka. Kai kanka ka san cewa dole ne ka zo musu da wani salo kafin har ka iya jawo hankalinsu ta \u0199arfi ta yaji.<\/p>\n\n\n\n<p>Za mu dakata a nan. amma a rubutu na gaba mun ci gaba da bayani akan <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-yadda-ake-girka-jigo-ya-koma-labari\/\">yadda ake girka jigo ya koma labari.<\/a><\/p>\n\n\n\n<p>Ga duk wanda yake da gyara, sharhi, \u0199arin haske ko tambaya \u0199ofa a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Bisa sunna ta rayuwa komai yana da mafari ko tushe, kafin ka fara gini kana bu\u0199atar ha\u0199a fandisho, kafin ka yi shuka kana bu\u0199atar hu\u0257a ko saran shuka, amma shi yin rubutu na zube JIGO shi ne abin bu\u0199ata na farko kafin komai. Wannan shi ne dalilin da ya sa tunda dabarun rubutu muke so&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/maanar-jigo-da-yadda-ake-samar-da-shi-a-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Ma&#8217;anar jigo da yadda ake samar da shi a labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3335,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,4,5,6,7,8,9,10],"class_list":["post-198","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-jigo","tag-jigon-labari","tag-kaidojin-rubutu","tag-maanar-jigo","tag-rubutun-labari","tag-samar-da-jigo","tag-yadda-ake-rubutu"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/10\/Maanar-Jigo.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/198","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=198"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/198\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3335"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=198"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=198"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=198"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}