{"id":216,"date":"2021-10-16T18:26:20","date_gmt":"2021-10-16T18:26:20","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=216"},"modified":"2022-07-13T01:36:02","modified_gmt":"2022-07-13T01:36:02","slug":"tsarin-yadda-ake-girka-jigo-ya-koma-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-yadda-ake-girka-jigo-ya-koma-labari\/","title":{"rendered":"Tsarin yadda ake girka jigo ya koma labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A makalar da ta gabata na dabarun rubutun labari, mun duba musamman&nbsp;<a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/maanar-jigo-da-yadda-ake-samar-da-shi-a-labari\/\">ma\u2019anar jigo da yadda ake samar da jigo<\/a>. A yau za mu duba yadda ake girka jigo ya koma labari.<\/p>\n\n\n\n<p>Da yake mun yi maganar girki, yana da kyau mu yi misali da wani nau&#8217;in abincin na Bahaushe da yadda ake girka shi, saboda samun \u0199arfin fahimtar yadda za a girka jigo.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"a-sanwar-jigo\">(a) Sanwar jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Bari mu \u0257auki miyar kuka, idan za ka ka\u0257a kuka ba iyaka garin kukar kake bu\u0199ata ba, bayan garin kukar kana bu\u0199atar sauran kayan masarufi da za su tallafi ita kukar idan an ka\u0257a ta ba da ma&#8217;ana. Misali kamar mu ce gishiri, magi, yaji da su mai da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>To haka shi ma jigo yake, ya \u0199unshi fuskoki guda biyu wa\u0257anda da su ake fara \u0257ora sanwa, akwai:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Babban Jigo<\/li><li>\u0198aramin Jigo<\/li><\/ul>\n\n\n\n<p>Kamar yadda garin kuka ko garin ku\u0253ewar da aka ka\u0257a a miya ya fi komai rinjaye, shi ma babban jigo shi ne muhimmin darasin da labarin yake koyarwa, wanda ana kallon labarin za a iya cewa shi ne darasin da aka koya ko kuma ake so a gujewa koya. Misalin hakan a cikin labarai shi ne kamar jigon \u201ckaruwanci\u201d a cikin labarin&nbsp;<em>&#8216;Yartsana<\/em>&nbsp;na Ibrahim Sheme, \u201cjarumta\u201d a cikin labarin&nbsp;<em>Ilya \u018aan Mai \u0198arfi<\/em>&nbsp;na Ahmadu Ingawa, da sauran su.<\/p>\n\n\n\n<p>Su kuma \u0199ananan jigon su ne kamar kayan masarufin da ake ha\u0257awa da su wajen \u0199ara da\u0257in labarin, sau tari kuma labari ba ya ta\u0253a girkuwa ya yi \u0257an\u0257ano idan babu su a ciki.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali: Idan marubuci ya \u0257auki jigon \u201csata\u201d a matsayin babban jigon labari, to akwai bu\u0199atar ya \u0199ara wasu \u0199ananan jigon kamar,<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Son zuciya: Ya nuna cewa son zuciyar \u0253arawon cikin labarin ne ya kai shi ga aikata satar.<\/li><li>Talauci: Ko kuma ya nuna talauci da halin matsin rayuwa ne ya ci \u0199arfin \u0253arawon har ta kai shi ga satar, da sauran su.<\/li><\/ul>\n\n\n\n<p>Ana \u0257ora babban jigon labari ne kai tsaye a kan gudanarwar babban tauraro, idan jigon na karuwanci ne, to ya zamana babbar tauraruwar labarin ce karuwar. Kamar Zainab (Asabe) a labarin littafin&nbsp;<em>&#8216;Yar Tsana<\/em>. Su kuma \u0199ananun jigo yawanci ana \u0257ora su ne a kan \u0199ananun taurari.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"b-samar-da-kamshi-yayin-dahuwar-jigo\">(b) Samar da kamshi yayin dahuwar jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Bayan an \u0257ora sanwar abinci, abu na gaba da ake saka ran ji shi ne tashin \u0199amshin abincin, yanayin yadda abinci yake \u0199amshi idan ana girkawa yanayin yadda zai jawo hankalin duk wanda ya sha\u0199i \u0199amshin ya ji yana kwa\u0257ayin \u0257an\u0257anawa. To game da girkin jigo ma akwai yadda ake yi wajen samar da wannan \u0199amshi, a sanya wa manazarcinsa kwa\u0257ayin ya karanta labarin, wanda kuma ana yi ne ta hanyoyi guda biyu:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Bayanin Jigo<\/li><li>Warwarar Jigo<\/li><\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"bayanin-jigo\">Bayanin jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Idan aka ce bayanin jigo wata ga\u0253a ce da marubuci zai yi amfani da ita wajen yi wa mai karatu bushara ko nune a kan jigon da zai gina rubutun labarin nasa, a wasu lokutan ma marubuci kan yi dangwalili ma&#8217;ana ya lasa wa makaranci za\u0199in zumar jigon da zai sa\u0199a labarin nasa a kai, amma a dun\u0199ule kuma a ta\u0199aice ta yadda shi makarancin labarin ba zai iya gane abin da labarin ya \u0199unsa ba gaba\u0257aya, amma kuma zai matsu sosai ya ji yadda za a warware masa cikumur\u0257ar.<\/p>\n\n\n\n<p>Domin fahimta sosai zan ba mu wani misali a cikin &#8216;yan ta\u0199aitattun kalmomi, da wani labarina mai suna:&nbsp;<em>Na Ji Na Gani<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong><em>Na Ji Na Gani<\/em><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>Tun bayan rasuwar Khadija rayuwa Salim ta sauya, bargon farinciki, walwala da jinda\u0257in da ta lullu\u0253a masa ya yaye na damuwa da \u0199uncin rayuwa ya maye gurbinsa. Lokaci guda zuciyarsa ta cika da tsananin \u0199iyayyar kusantar dukkan wata &#8216;ya mace, duniyar tunaninsa ta ta&#8217;azzara har ta kai ga ya samu babban tasgaro wajen gudanar da al&#8217;amuran rayuwar tasa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Khadija ita ce mace ta farko da ta fara farautar zuciyarsa a lokacin da bai shirya wa hakan ba, ta nuna masa \u0199ololuwar \u0199auna irin wacce uwa take nuna wa \u0257anta. A kowanne lokaci burinta ta gan shi cikin walwala da farinciki wanda hakan shi ya haifar ta dasa masa soyayyar ta a lambun zuciyarsa, har ma soyayyar ta yi ya\u0257o ta kara\u0257e ko ina a cikin lambun. Saboda tsabar sha\u0199uwar da ya yi da Khadija idan har ya wuni bai sanya ta cikin Idanuwansa ba babu makawa da zazzabi zai kwana cikin daren wannan rana.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Kamar fa\u0257uwar rana haka a wani yammaci Khadija ta fa\u0257i, sai dai sa\u0253anin rana da idan ta fa\u0257i yau za ta sake fitowa gobe, ita Khadija tun ranar da ta fa\u0257i bata sake bayyanar masa ba. Ana cewa soyayyar farko kamar tabon halitta ne wanda ba ya fita, wata\u0199ila shi ya sa Salim ya kasa mantawa da Khadija, har ma yake ji a ransa kamar ba zai ta\u0253a \u0199ara son wata &#8216;ya mace ba a duniyarsa ballantana har ya yi aure kafin ya koma ga Allah.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Kwatsam kuma sai ga wata matashiyar budurwa Fatima wacce ta lashi kaifin takobin ceto rayuwarsa daga cikin tafkin ka\u0257aici da ya afka a dalilin rabuwar soyayya, tuni ta yi al\u0199awarin yin dashen soyayya a cikin \u0199onanniyar \u0199asar farfajiyar lambun makauniyar zuciyarsa wacce babu ko alamar danshi balle ruwan da tsiro zai yi sabon tofo&#8230;.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan mun yi nazarin wannan rubutu da kyau, za mu ga a cikin rubutu \u0199alilan an yi bayanin jigon labarin wato (ya\u0199in soyayyar da sabuwar budurwar za ta yi da makantacciyar zuciyar Salim irin ta wa\u0257anda wani abu mara da\u0257i yake sakawa su ci alwashi).<\/p>\n\n\n\n<p>Jodie Archer da Matthew L. Jockers sun ce jumlolin da fitattu kuma shahararrun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf kan yi amafani da su wurin bu\u0257e labaransu (mabu\u0257in labari), sukan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma \u0199asa da haka. Kenan dai suna amfani da hikima su bayyana jigon su a ciki ta\u0199aitattun kalmomi don kama zuciyar mai karatu, ya ji yana so ya karanta labarin irin yadda mai jin yunwa zai matsu ya kai abinci mai \u0199amshi zuwa bakinsa. Bayan wannan kuma sai,<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"warwarar-jigo\"><strong>Warwarar jigo<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Shi kuma warwarar jigo ya \u0199unshi yadda za a bi a warware sa\u0199on da ke cikin bayanin jigo a fili kowa ya fahimce shi. Ko kuma ana iya cewa warwarar jigo shi ne bayani daki-daki da ake yi a cikin labari don sa\u0199on ya fito fili, masu karatu su fahimce shi. In aka ce sa\u0199o a nan ana nufin jigo.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan muka yi amfani da misalin labarin Na Ji Na Gani da muka kawo, a warwarar jigo ne marubucin zai ri\u0199a warware zaren labarin daki-daki. Tun daga kan ta yadda Fatima za ta tunkari Salim da batun soyayya, shin za ta fa\u0257a masa baki da baki ne? Ko kuwa \u0199awarta ko wani za ta yi amfani da shi wajen sanar masa? Idan ta sanar masa wani \u0199alubale za ta fuskanta? Ta yaya za ta magance \u0199alubalen?<\/p>\n\n\n\n<p>A haka za a yi ta warware labarin ga\u0253a bayan ga\u0253a har zuwa lokacin da za a dangana da \u0199arshen labarin, inda za a nuna nasarar jawo hankalin Salim da Fatima zata yi bayan tarin gwagwarmaya da \u0199alubale.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku karanta makala ta gaba da ta yi&nbsp;nazarin <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-murhun-girka-jigo-a-labari\/\">murhun girka jigo<\/a>. <\/p>\n\n\n\n<p>Kamar kullum, \u0199ofar gyara, sharhi, \u0199arin haske ko tambaya a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A makalar da ta gabata na dabarun rubutun labari, mun duba musamman&nbsp;ma\u2019anar jigo da yadda ake samar da jigo. A yau za mu duba yadda ake girka jigo ya koma labari. Da yake mun yi maganar girki, yana da kyau mu yi misali da wani nau&#8217;in abincin na Bahaushe da yadda ake girka shi, saboda&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-yadda-ake-girka-jigo-ya-koma-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Tsarin yadda ake girka jigo ya koma labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3329,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[11,4,5,7,9],"class_list":["post-216","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-girka-jigo","tag-jigo","tag-jigon-labari","tag-maanar-jigo","tag-samar-da-jigo"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/10\/Yadda-ake-girka-jigo.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/216","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=216"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/216\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3329"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=216"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=216"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=216"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}