{"id":2849,"date":"2022-01-24T17:01:02","date_gmt":"2022-01-24T17:01:02","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=2849"},"modified":"2022-07-13T01:35:56","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:56","slug":"sharhin-littafin-dama-sun-fada-mini-na-jibrin-adamu-jibrin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-dama-sun-fada-mini-na-jibrin-adamu-jibrin\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Dama Sun Fada Mini&#8217; na Jibrin Adamu Jibrin"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan Littafi:<strong> Dama Sun Fada Mini<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubici: <strong>Jibrin Adamu Jibrin<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Kamfanin \u018aab&#8217;i: <strong>A. A. Bature<\/strong> <strong>Publishers<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Yawan Shafuka: <strong>200<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar Bugu: <strong>2020 an sake bugawa 2021<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai Sharhi: <strong>Muttaka A. Hassan (Abu Ahmad)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manufar Sharhi: Bun\u0199asa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"dangane-da-marubucin\">Dangane da marubucin<\/h1>\n\n\n\n<p>An haife shi a Jos, cikin Nassarawa, unguwar &#8216;yan shanu, a shekara ta dubu \u0257aya da \u0257ari tara da casa&#8217;in (1990) miladiyya. Ya fara karatun firamare a Saint Michael Primary School, Jos. Daga bisani ya dawo jihar Kano garin Rano inda ya ci gaba da karatu a Special Primary Rano, ya kammala a shekarar 2004. Daga nan kuma ya wuce babbar Sakandire G.S.S Rano inda ya yi karatu a \u0253angaren kimiyya (Science), ya kammala a 2010. Daga nan ya shiga Kwalejin Ilimi Da Shari&#8217;a ta Malam Aminu Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) in da ya samu kwalin diploma a bangaren Shari&#8217;a (Law). Daga kuma nan bai ci gaba da karatu ba. Yana zaune a garin Rano tare da matarsa da \u0257iyarsu \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya fara rubutu a shekarar 2007, in da ya fara da labarun ya\u0199i. Daga bisani ya ajiye ya dawo rubutun soyayya, zamantakewa, da gwagwarmayar rayuwa musamman \u0253angaren Shari&#8217;a. Ya rubuta littafai da dama kamar: Shari&#8217;a Sa\u0253anin Hankali, Kukan Jini, Tufkar Makaho, Dama Sun Fa\u0257a Mini da sauransu. Ya samu nasarar lashe gasanni da dama.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"labari\">Labari<\/h1>\n\n\n\n<p>Zainab da Aliyu ma&#8217;aurata ne da suke matu\u0199ar \u0199aunar juna, soyayyar da suke yi wa juna abar sha&#8217;awa ce ga kowa, musamman yadda suke sadaukarwa da juna lamuransu. Lokacin da Zainab ta samu ciki, Aliyu ya sake ninka kulawar da yake ba ta. Koda yake bayan cikin ya tsufa ne tauraruwar matsalar rayuwarsu ta haska, in da Zainab take yawan munanan mafarkai da wasu halittu masu muni suna mata barazanar ta haihu ta ba su jaririnta su sha jininsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Watarana tana kwance a jikin mijinta sai ta yi mummunan mafarki, wai tana na\u0199uda dodanni sun zagayeta suna tan\u0257ar baki. A lokacin da jaririn ya diro duniya suka daka masa wawa, sai ta farka a razane. A nan ne mijinta ya tambaye ta abin da ya tashi hankalinta, ta sanar da shi. Aikuwa sai mijin ya yi \u0253arin zance ya furta &#8220;DAMA SUN FA\u018aA MINI.&#8221; Haka ya sa ta tsare shi da tambayoyin wa\u0257anda suka fa\u0257a masa, da abin da suka fa\u0257a masa; sai dai ba ta samu amsa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wasu &#8216;yan kwanaki aka kuma, wai mace ta haifi mace, domin kuwa mafarki ta sake yi mai ban tsoro, da ta sanar da Aliyu ya sake furta DAMA SUN FADA MINI. Daga nan ne mijinta ya fara zama abin gudunta, domin kuwa gani take yi shi ma \u0257an \u0199ungiyar shan jini ne. Musamman da yake ya \u0199i ba ta amsar tambayoyinta, bugu da \u0199ari a cikin munanan mafarkan nata tana ganin rubutu a bayan rigar dodonni, sai kuma ta ji mijin nata ya fa\u0257i wannan rubutun na rigar. Daga kuma nan ne ta yi ta tuno irin tarin dukiyar da yake da ita, da yadda ya kulle wani \u0257aki ba ya bari a bu\u0257e, da yadda ta tsinci sa\u0199on kar ta kwana a wayarsa ana sanar da shi &#8220;Iya buhun mutane biyar aka samu.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan ya sa ta gudu ta koma gidan iyayenta, su kuma suka ce ko dai ya amsa tambayoyinsu ko ya sake ta. Ganin ya gaza aiwatar da ko \u0257aya suka maka shi a kotu.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"jigo\">Jigo<\/h1>\n\n\n\n<p>Ko iya \u0257an abin da muka tsakuro a labarin aka karanta za a fahimci babban jigon labarin shi ne zargi, ko kuma a ce zato, ko dai tuhuma. Domin dai tun daga haihuwar labarin (Mabu\u0257i) zuwa girmansa za mu iske an fara ne da zargi, sannan sar\u0199a\u0199iyar ko sa-toka-sa-katsin da aka yi ta yi duka dai a kan zargi ne. Mu fara da inda aka bu\u0257e labarin a shafi na hu\u0257u, tun a sakin layi na farko marubucin ya ce &#8220;&#8230;.Zainab wacce take ZARGIN mijinta Aliyu da zama \u0257an \u0199ungiyar asiri&#8230;.Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba \u0257an \u0199ungiyar asiri ba ne&#8230;.iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa &#8216;yarsu ba za ta zauna \u0257an shan jini ba&#8230;.&#8221; A nan za mu gane Zainab na zargin mijinta, shi ya kasa kare kansa, zuwa kotu da iyayenta suka yi kuwa tuhumarsa ce ta kai su. Idan an warware jigon za a iske yana \u0257auke da wasu \u0199ananan jigogi wa\u0257anda suka taru suka samar da darrusa da dama kamar:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Shafi na 167, sakin layi na 3 marubucin ya kawo mana fa\u0257ar Annabi (S.a.w) cewa:&nbsp; &#8220;Al-zanna zanbun, walau kana ha\u0199\u0199un&#8221; Watau dai &#8216;zato zunubi ne, ko da kuwa ya kasance gaskiya.&#8221;<\/li><li>Haka nan a shafi na 120, sakin layi na 2, nadamar Zainab ta fara in da take zance a zuciyarta cewa: &#8216;Shi ne ni kuma na \u0257auka huhu na mutane ake nufi na \u0199ara fusata Aliyuna?&#8217; A nan za mu fahimci matar da take zargin mijinta da tara buhun mutane har biyar, ta kuma gano huhun goro ake nufi, har ta yi wannan zancen a zuci, lallai nadamar zargin da ta yi ta riske ta.<\/li><li>Shafi na 167 sakin layi na hu\u0257u an nuna alkali na jawabi da cewa: &#8220;&#8230;mu guji yanke hukunci kai tsaye ba tare da bincike ba&#8230;&#8221; A nan littafin yana koyar da mu yana da kyau kafin yanke wa mutum hukunci, mu yi bincike.<\/li><li>&#8220;&#8230;.duk in da muka ha\u0257u da wani aljani ko boka ko mai sihiri, to kuwa mu yi takatsantsan da shi kada mu kuskura mu yarda da su&#8230;.&#8221; Shafi na 168 sakin layi na 2. Wannan darasi ne muhimmi, domin dai malamai ma suna ta bayani makamancin wannan. Wato sau tari aljani kan shigo rayuwar mutum ta siga mai kyau (ya nuna zai taimaka maka da magani ko wani abin duniya) sai tafiya ta yi nisa sai su yi ta \u0253atar da mutum a hankali.<\/li><li>Wani darasi kuma da littafin ya zo da shi shi ne kuskuren da mata suke yi na binciken wayar mazajensu. In da matsalar take, matsawar mutum ya \u0257arsa zargi a zuciyarsa, to yana da wahalar gaske shai\u0257an bai kawo masa \u0257auki ya jefo wani abu da zai \u0257arsa masa wasu-wasi tare da \u0199arfafa masa gwiwa a kan lallai abin da yake zargi gaskiya ne ba. Kamar dai yadda ya faru a shafi na 52-53, Zainab ta \u0257auki wayar Aliyu saboda zargin wata tana turo masa sa\u0199on soyayya, sai kuma ta ci karo da batun da ya rikitata har ma ya kusa zama sanadiyyar rugujewar aurensu.<\/li><li>Har wa yau, an nusar da mu sakacin \u0199in ri\u0199e addu&#8217;a, kamar dai yadda ya faru ga mahaifan Aliyu. Da kuma muhimmancin addu&#8217;a kamar yadda ya faru a \u0199arshe, an haifi jaririn, &#8216;yan \u0199ungiyar asirin sun zo amma addu&#8217;a ta zama katanga tsakaninsu.<\/li><li>Sannan kuma, an nusar da mu ko da mun yi addu&#8217;a sai mun zamto masu ha\u0199uri. Domin dai ba nan take da an yi addu&#8217;a za a kar\u0253a ba, saboda ta yiwu an jinkirta tabbatuwar addu&#8217;ar ne saboda jarabtar imaninmu. Kamar dai yadda ta faru ga Aliyu, tare da cewa ya kasance mai yawan ibada, sadaka, kyauta da kyawawan halaye, amma matsalolinsa ba su yanke lokaci \u0257aya ba.<\/li><\/ul>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"salo-da-sarrafa-harshe\">Salo da sarrafa harshe<\/h1>\n\n\n\n<p>Idan har akwai abin da ya mayar da littafin zakaran gwajin dafi, to babu kamar salo da sarrafa harshe. Domin an yi amfani da salalai iri-iri ka\u0257an daga ciki a iya cewa akwai tsoho da kuma sabon salo. Misali:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Koyarwa: An yi amfani da wannan salo wurin koyar da darasin da ya shafi kimiyya da fasaha, duba shafi na 5-6, 21-22, 31-33, 57-60 da sauransu. Duka idan mutum ya bibiyi shafukan zai ga yadda aka koyar da kimiyya da fasaha a sassau\u0199an harshe.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai matu\u0199ar jan hankali, ta hanyar amfani da wasu gwala-gwalan kalmomi da suka yi wa rubutun ado tare da samar da armashi, ta yadda mutum yana karantawa yana \u0199ara jin da\u0257in labarin. Har&#8217;ilayau an yi amfani da salon magana mai kama tunani matu\u0199a.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sarrafa Harshe: A nan ma marubucin ya kwarzanta harshe matu\u0199a, ta yadda ya ri\u0199a amfani da azanci, da hikima, da kuma tarin karin magana da suka doshi hamsin. Su kansu karin maganar da aka yi amfani da su sun kasu aji-aji, idan an ta\u0199aice dai a iya cewa an yi amfani da sababbi da kuma tsofaffi, ta yadda marubucin ya ri\u0199a yi wa wasu karin maganar gyaran fuska suna komawa sababbi. Misali: &#8220;Mara gaskiya ko a kan doki yake, sai ya yi \u0257ingishi.&#8221; (Shafi na 14) sakin layi na 3, da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"zubi-da-tsari\">Zubi da tsari<\/h1>\n\n\n\n<p>An tsara labarin tare da kasa shi zuwa babi-babi, daga na \u0257aya zuwa na goma shabiyar, sannan kowane babi yana \u0257auke da kannun labari. A ta\u0199aice dai, ya samu kyakkyawan zubi da tsari, don idan muka koma muka duba jigon labarin (zargi) za mu iske tun daga mabu\u0257i an yi wa jigon shimfi\u0257a a kan tabarma mai kyau. Ta yadda za mu ga tun daga farko har \u0199arshe kowace jumla na \u0199arfafar &#8216;yar&#8217;uwarta ne, watau an samu cikakkiyar yarjejeniyar kalmomi wurin gina labarin. Misali: Babi na 1, Aliyu ya yi furucin &#8220;Dama Sun Fa\u0257a Mini&#8221; (kuma sunan babin ne) furucin Aliyu ya jawo zargin Zainab. Da aka shiga babi na biyu mai suna AN KUMA, IN JI \u018aAN SHAYI DA AKA YANKE SHI A GABA. A nan ma dai zargin ne ya tsananta, domin Aliyu ne ya kuma furta dama an fa\u0257a masa! Haka ma yake a babi na 4 mai suna GARIN TONE-TONEN KAZA&#8230;.a nan an bayyana yadda garin binciken wayar miji Zainab ta binciko abin da ya tsananta zarginta har ta yi yaji. Abin burgewa, da ta yi yaji kamar marubucin ya san mai karatu zai ce me ya faru a gaba sai ya ba wa abin da ke biye da shi suna DUK GIRMAN GONA TANA DA KUNYAR \u0198ARSHE, watau dai ta tabbata ma&#8217;auratan sun rabu. To haka ya yi ta faruwa daga farko har \u0199arshe, watau kowane babi, na \u0199arfafar na baya (ko a ce kowace jumla na yi wa wata zagi) har dai zuwa lokacin da matsalar ta kai kololuwa, da kuma yadda aka sauko.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hange: An yi amfani da dabarar hange, an hasko wa mai karatu wani abu da zai faru a labarin tun kafin a zo kansa, watau dai an lasa masa zuma a baki. Misali: &#8220;Zainab wacce take zargin mijinta Aliyu da zama \u0257an \u0199ungiyar asirin da ya bayar da abin da zata haifa ga \u0199ungiyar tasu, Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba \u0257an \u0199ungiyar asiri ba ne, sai iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa &#8216;yarsu ba za ta zauna da \u0257an shan jini ba,&nbsp;da kuma Al\u0199ali da mu\u0199arrabansa da mu kanmu &#8216;yan kallo wanda da mu aka kawo \u0199arshen tirka-tirkar.&#8221; (Shafi na 4)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Waiwaye: Harwayau, ana cikin tafiya sai aka dawo baya aka tuna wa mai karatu wani abu da ya faru a littafin, sannan aka yi gaba. Misali: &#8220;Huhu \u0257aurin goro yake nufi kenan?&#8221; Ta tambayi kanta cikin girgiza kai, lokaci guda kuma wata \u0199wa\u0199walwarta mai adana shu\u0257a\u0257\u0257un abubuwa ta danna mata tariyar baya ta mayar da ita&nbsp; zuwa kan sa\u0199on kartakwanan da ta karanta a cikin wayar Aliyu, wanda yana \u0257aya daga cikin dalilan da suka sa ta \u0199ara tsananta zarginta gare shi.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Mai gida ba a samu wannan huhun duka ba. Na mutum biyar kawai aka samu.&#8221; Ta tuno yadda sakon yake a rubuce cikin wayar salular ta Aliyu. (Shafi na 119) sakin layi na 3 da na 4.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ba\u0257oki Na Gaske: &#8220;Na je kallon rikicin tun wancan satin ina jira na koma wani satin na ga yadda za ta kaya kamar yadda Al\u0199alin ya ce zai ci gaba da sauraron \u0199arar. Sai da ka yi magana ka ankarar da ni ashe fa kusan matsala \u0257aya ce ta haifar da shi, ga shi aure yana shirin mutuwa a sanadinsa&#8230;.&#8221; (Shafi na 7) sakin layin na farko. Tabbas aure ya kusa mutuwa, domin dai sai da ta yi yaji, kuma iyayenta suka goyi bayanta.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ba\u0257oki Na Giri: &#8220;Shi ke nan Iman ki je gida ki tona min asiri kamar yadda kike so, ki je gida ki fa\u0257a wa Umma da Baba cewa ni \u0257an mafiya ne kamar yadda kike zargi. Sai dai ina so ki sani cewa kamar yadda nake ro\u0199on ki akan kar ki tafi gidan ku yanzu, haka ke ma watarana za ki zo ki ro\u0199e ni akan ki dawo \u0257akin ki bayan kin \u0199aryata kanki cewa ni ba \u0257an mafiya ba ne, daidai lokacin da ni kuma ba ni da bu\u0199atarki, wata\u0199ila ma na nemo wacce za ta yarda da ni za ta iya rufa min asiri a cikin kowane hali.&#8221; (Shafi na 68).<\/p>\n\n\n\n<p>Tare da cewa ta tafi gidan nasu, bayan matsalar ta warware kuma ba ta ro\u0199e shi ba (kamar yadda aka fa\u0257a a shafin na 68) sannan bai nuna ba ya bu\u0199atarta ba, hasalima ya dawo da ita ne saboda yana \u0199aunarta.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Tsoro: A wurare da dama an yi amfani da wannan dabara, inda aka ri\u0199a dasa wa mai karatu tsoro. Misali: &#8220;Zainaaaaaab.! Zainaaaaaaab.!! Zainaaaaaaab.!!!&#8230; Sai kin ba mu \u0257an da ke cikinkiiii&#8230;&#8221; Maganar su ta fizgi hankalinta gami da sake dugunzuma tunaninta, sai a lokacin ta ga ashe gaf suke da \u0199arasowa inda take suna masu \u0257aga hannayensu masu \u0257auke da farata cakar-cakar kamar takobi. (Shafi na 10) da saura a wasu shafukan.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Al&#8217;ajabi: &#8220;Murad.! Me ya faru?&#8221; Zainab ta tambaye shi tana mai \u0199ara yin nazarin shi ganin yadda a cikin \u0199an\u0199anin lokaci yanayin shi ya sauya.&nbsp;&#8220;Dama sun fa\u0257a min&#8221; ya ambata hakan daidai lokacin da ya goya hannayen shi a baya da alamar \u0199ololuwar damuwa a tare da shi. (Shafi na 13). A nan an \u0257arsa wa mai karatu al&#8217;ajabi, a ce mata ta yi mafarki wasu dodonni na binta suna so ta haifi jariri su shanye jininsa, ta farka a razane ta labarta wa mijin, shi kuma ya ce dama sun fa\u0257a masa!<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Darsau Na Mamaki: &#8220;Ban ga riba ba wajen fa\u0257a miki su waye IZAGA kamar yadda ban ga abin da yin hakan zai amfana mana ba sai dai ma ya jawo mana matsala&#8230;.&#8221; (Shafi na 65)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Murna: &#8220;Nan fa kowa ya shiga jandal cikin gode wa Ubangiji tare da \u0199ara gasgata \u0199arfin addu&#8217;a da \u0199arfin Allah wanda ya fi na kowa&#8230;.&#8221; (Shafi na 190) sakin layi na farko.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hoton Zuci: An yi \u0199o\u0199ari an samar da hoton zuci a wurare da dama, ta yadda mai karatu zai ri\u0199a ji tamkar yana kallon abin a zahiri. Misali &#8220;&#8230;kamar yadda \u0199udaje ke bin mushen da ke fitar da tiririn wari haka suke binta, hangamemen bakinsu mai ha\u0199ora cako-cako da za su yi saurin tuna maka da bakin manjagara ko tarko. Wani irin ba\u0199in jini yana falala daga bakin nasu babu kyan gani, duk ya \u0253ata ilahirin jikinsu tun daga kan wuya har \u0199irjinsu irin yadda yaro mai tumbudi ko yoyon baki kan yi da gaban rigarsa.&#8221; (Shafi na 9 da sauransu)<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"tauraro\">Tauraro<\/h1>\n\n\n\n<p>Babban tauraron labarin shi ne Aliyu, mijin Zainab. Shi ne wanda duk inda aka je aka dawo matsalolin shi suke yi wa zobe. A iya cewa matarsa Zainab ita ganin matsalolin take muraran, amma bisa al&#8217;ada inda duk matsalar mata ta kai ta kawo mijinta shi zai \u0257auke matsalar. Musamman ma shi Aliyu da ya kasance a wani yanayi mai kama da gaba zaki, baya \u0253auna, hagu da dama kuma sayaki da kura, babu wurin da zai jefa kansa. E mana, matarsa ita ce za ta iya zama yayyafin da zai sanyaya damuwarsa, amma kuma sai ya kasance ita ce sawun farko a cikin masu zarginsa.<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"halayen-taurarin-labarin\">Halayen taurarin labarin<\/h1>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Farawa da babban tauraro Aliyu. Matashi ne mai shekaru 32-33, kyakkyawa ne gwanin \u0199awa. Mai arziki ne, yana da yawan kyauta da ibada. Bugu da \u0199ari mutum ne mai matu\u0199ar farin jini. Shi ya sa kowa (maza da mata) ke son mu&#8217;amala da shi.<\/li><li>Zainab, kyakkyawa ce, mai kyawawan \u0257abi&#8217;u, hasalima da kyawawan halayenta ta saye zuciyar Aliyu har ya za\u0253e ta a matsayin matar aure, suka yi aure. Babbar matsalarta tana da kishi mai tsanani, wanda sai da ya haifar mata da nadama.<\/li><li>Khadija, buduruwar da dashen son Aliyu ke dawainiya da ita. Makaranta \u0257aya suke karatu, don haka koda yaushe take \u0199o\u0199arin ra\u0253arsa.<\/li><li>Ibrahim (mahaifin Aliyu) dattijon da aka la\u0199abawa maita shi da matarsa, kasancewar sun taso da wani irin ba\u0199in jini da suka rasa dalilinsa. Inda duk suka raba babu sa&#8217;a tamkar beguwa. Don haka ya kasance babu abin da suke buri tamkar rabuwa da ba\u0199in jinin da ke bibiyarsu.<\/li><\/ul>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"nagartar-littafin\">Nagartar littafin<\/h1>\n\n\n\n<p>Babu bu\u0199atar sai an yi dogon tsokaci a kan nagartar wannan littafi. Domin dai nagartarsa ce ta sa ya zamto zakara a mataki na farko a gasar Aliyu Muhammad Research Library Kaduna 2020, da kuma: Gasar Abubakar Imam Hausa Fiction Kano 2021.<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice dai, ko me aka fa\u0257a na nagarta ko yabawa a kan wannan littafi, a iya cewa an dora \u0199warya ne bisa gurbinta. Domin idan marubucin ya durfafi bangaren kimiyya da fasaha sai ka rantse digirin digirgir ne da shi a wannan fannin. Haka ma da ya dawo bangaren Shari&#8217;a. Babu ko shakka wannan littafi zai taimaka wa \u0257aliban da ke karatu a \u0253angaren kimiyya, kamar dai yadda zai taimaki duk marubucin da ya karanta shi musamman shafi na 7, zai samu hujjojin ri\u0199ewa a hannu ya tunkari wanda duk ya ce da shi marubuci ma\u0199aryaci ne!<\/p>\n\n\n\n<h1 class=\"wp-block-heading\" id=\"manazarta\">Manazarta<\/h1>\n\n\n\n<p>\u018aangambo A. (1984). <em>Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa.<\/em> Kano: Triumph<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya I.Y., da `Dangambo A. (1986). <em>Jagoran Nazarin Hausa<\/em>. Zaria: Madaba&#8217;ar Northern Nigeria Publishing Company Limited<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da \u2018Yar\u2019aduwa T.M. (1992). <em>Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1<\/em>. Ibadan: University Press Plc<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan Littafi: Dama Sun Fada Mini Marubici: Jibrin Adamu Jibrin Kamfanin \u018aab&#8217;i: A. A. Bature Publishers Yawan Shafuka: 200 Shekarar Bugu: 2020 an sake bugawa 2021 Mai Sharhi: Muttaka A. Hassan (Abu Ahmad) Manufar Sharhi: Bun\u0199asa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba. Dangane da marubucin An haife shi a Jos, cikin Nassarawa, unguwar &#8216;yan&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-dama-sun-fada-mini-na-jibrin-adamu-jibrin\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Dama Sun Fada Mini&#8217; na Jibrin Adamu Jibrin<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":3341,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[29],"class_list":["post-2849","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-book-review"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/01\/Sharhin-Dama-Sun-Fada-Mini.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2849","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2849"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2849\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3341"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2849"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2849"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2849"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}