{"id":3294,"date":"2022-01-30T18:35:50","date_gmt":"2022-01-30T18:35:50","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=3294"},"modified":"2022-07-13T01:35:55","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:55","slug":"salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-1","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-1\/","title":{"rendered":"Salon bayar da labari da salon ginin labari 1"},"content":{"rendered":"\n<p>A yau za mu yi bayani ne a akan salon bayar da labari da kuma salon ginin labari. Idan ba ku manta ba, a ma\u0199alar da ta gabata, mun yi bayani game da <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/muhimmancin-zurfafa-bincike-wajen-rubutun-labari\/\">fa&#8217;idar yin bincike a wajen ginin labari<\/a>, inda muka ce mutunci, \u0199ima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a \u0199asa wanwar a duk lokacin da ya tafka wani gingimemen kuskure yake kuma da&#8217;awar daidai ya yi a cikin labarinsa. Muka ce ta hanyar bincike ne marubuci zai zama shakundum, ya zama komai da ruwansa ta yadda zai iya yin rubutu a kowanne fanni kuma rubutun ya \u0199ayatar da duk wanda ya karanta. Muka kawo hanyoyin yin bincike, da cikakken bayanin kowanne.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"h-salon-bayar-da-labari\">Salon bayar da labari<\/h2>\n\n\n\n<p>Kafin mu tattauna a kan wannan salo mu fara sanin ma&#8217;anar salo mana. Salo wata dabara ce ko hanya da marubuci yake bi wajen isar da sakonsa ga makaranta cikin hikima da gwanintar harshe ta hanyar tsara kalamai da ayyuka. Ana son salo ya zama \u0199a\u0199\u0199arfa ko nagartacce, wato ya zamana ana karanta rubutu yanayin salon da aka yi amfani da shi ya ri\u0199a tafiya da hankalin mai karatu. Ba wai salo ya zama rarrauna ko mi\u0199a\u0199\u0199e ba irin wanda babu wani abu na armashi a cikinsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Misalin yadda za a fahimci muhimmancin salo a cikin labari shi ne, irin misalin mutane biyu da suka sayi atamfa ko shadda iri \u0257aya masu tsada \u0257aya. \u018aaya a cikin su ya kai wa tela wanda ya iya \u0257inki sosai, \u0257ayan&nbsp;kuma ya kai wa tela wanda bai iya \u0257inki ba. Duk tsadar shaddar ko atamfar da telan da bai iya \u0257inki ba ya \u0257inka, ba za ta burge mutane ba har ta ja hankalinsu idan an saka a jiki kamar ta telan da ya iya \u0257inki. Za ku yarda da ni cewa atamfa ko shadda mafi araha za ta iya fin ita mai tsadar jan hankali idan ta samu tela mai kyau. To haka shi ma rubutun labari yake. Shi ya sa wani lokacin sai ka ga wani wanda labarinsa bai kai naka samun jigo mai kyau ba, idan ya samu salo mai kyau sai ya fi naka \u0199ayatarwa, har ma ya yi nasara a gasa naka bai yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubucin da ya iya salo da \u0199ir\u0199ira tamkar telan da ya iya \u0257inki ne, hakanan marubucin da bai iya fitar da salo da al\u0199alaminsa ba tamkar tela ne da bai iya \u0257inki ba. Shi ya sa mabanbantan marubuta za su iya \u0257aukan jigon labari \u0257aya amma ka tarar banbancin da\u0257in labaransu tamkar banbancin gar\u0257in koko da madara ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Domin samun \u0199arin fahimta, za mu nazarci wa\u0257annan misalan na Rarraunan Salo da kuma Nagartaccen Salo:<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"rarraunan-salo\"><em>Rarraunan salo;<\/em><\/h3>\n\n\n\n<p>i- Na je wajenta jin hirarta mai da\u0257i ta bar ni a tsaye ta \u0199i fitowa.<\/p>\n\n\n\n<p>ii- Har na fara gyangya\u0257i na gaji na tafi.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"nagartaccen-salo\"><em>Nagartaccen salo;<\/em><\/h3>\n\n\n\n<p>i- Na je ba wa ruhina abincin da yake muradi na da\u0257a\u0257an kalamanta masu yi mini da\u0257i kamar ana sosa mini kunne, ta bar ni a tsaye kamar kwatar raken da aka dasa.<\/p>\n\n\n\n<p>ii- Har idanuwana suka fara nauyi, na fara gani dishi-dishi na yi gaba kafin bacci ya yi gaba da ni.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin lura, duk wa\u0257annan misalan abu \u0257aya ake so a ce a cikin su, abin tambaya a nan shi ne wa\u0257anne daga cikin hu\u0257un ne za su fi jan hankalin mai karatu? Ga wasu misalan:<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"rarraunan-salo-1\"><em>Rarraunan salo;<\/em><\/h3>\n\n\n\n<p>i- Motar mai kyau ta shige cikin asibitin da mai gadi ya bu\u0257e \u0199ofar.<\/p>\n\n\n\n<p>ii- Kallon \u0199ofar asibitin ka\u0257ai ya isa ka fahimci asibitin masu ku\u0257i ne.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"nagartaccen-salo-1\"><em>&nbsp;Nagartaccen salo;<\/em><\/h3>\n\n\n\n<p>i- Rantsattsiyar motar ta sulala cikin asibitin da mai gadi ya bu\u0257e wawakeken \u0199yaurensa irin yadda maciji yake sulalawa raminsa.<\/p>\n\n\n\n<p>ii- Kallon \u0199ofar asibitin ka\u0257ai ya wadatar ka fahimci asibitin na masu yatsu dayawa ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan abin da ya shafi salon sarrafa harshe kenan, idan mun fahimta to mu koma kan asalin batunmu na farko, wato <em>Salon bayar da labari, <\/em>wanda shi ma ya kasu zuwa kashi biyu:<\/p>\n\n\n\n<p id=\"salon-tauraro-cikin-fage\"><strong>Salon tauraro cikin fage<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Salon tauraro wajen fage<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Za mu \u0257auki kowannensu \u0257aya bayan \u0257aya mu tattauna muhimman abubuwa da suka shafe shi na \u0199a&#8217;idoji da dabaru insha Allahu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022Tauraro cikin fage<\/strong>: Wannan shi ne salon bayar da labari wanda tauraro da kansa yake bayar da labarin ga manazarci. Misali;<\/p>\n\n\n\n<p><em>\u201cDa yake dare ya tsala, wajen misalin sha\u0257aya da rabi, ban kula da yaron da yake gabana ba kawai sai maganarsa na ji, wacce ta haifar mini da fa\u0257uwar gaba. &#8220;Wai ga shi!&#8221; Ya ce da ni yana mi\u0199o mini wani abu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8216;Na yi amfani da hasken gilashin wayar hannuna na haska askakken ran\u0199walelen kansa da ya yi mini kama da na fatalwu, wani irin kallo da na ga yana yi mini da da\u0199wa-da\u0199wan idonsa ya sa na fara ji a jikina tabbas ba mutum ba ne&#8230;&#8217;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Ta hanyar nazartar wannan misali za mu ji cewa tauraron, ko tauraruwar da kanta ce take bayar da labarin. Dayawan mutane sun tafi a kan cewa wannan salon ya fi tasiri wajen isar wa da manazarta sa\u0199on da ake so a isar musu cikin sau\u0199i a zukatansu. Ana cewa wa\u0199a a bakin mai ita ta fi da\u0257i, to haka ma labari a bakin mai shi ya fi armashi, idan labarin tausayi ne an fi jin tausayinka sosai da wannan salo, idan ma labarin barkwanci ne an fi darawa sosai da wannan salo.<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kuma salo ne mai matu\u0199ar sar\u0199a\u0199iya da wuyar sha&#8217;ani idan marubuci bai sanya kula ba, amma idan za a sanya kulawa salon yana da sau\u0199i sosai. Za mu nazarci wasu daga cikin dokoki, ko \u0199a&#8217;idojin wannan salo yanzu insha Allah.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022Amfani da shu\u0257a\u0257\u0257en lokaci na farko<\/strong>: A cikin wannan salon, kuskure ne amfani da kowanne lokaci indai ba shu\u0257a\u0257\u0257en lokaci ba. Irin wannan salon ana bayar da labarin abin da ya riga ya faru ya wuce ne, don haka dole ne labarin ya \u0199unshi shu\u0257a\u0257\u0257en lokaci na farko a yayin labarta shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin da nake nufi shi ne, wata\u0199ila tauraron yana bayar da labarin tsohuwar soyayyarsa ne, ko kuma labarin wani \u0199alubale da ya ta\u0253a fuskanta, ko labarin wata tafiya da ya yi da sauransu. Don haka wajen bayar da labarin dole marubuci ya ri\u0199a sa\u0199a labarin a kan shu\u0257a\u0257\u0257en lokaci. Misali;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;<em>Ranar da al&#8217;amarin zai faru, gaba\u0257aya sai na tashi duk jikina babu \u0199wari, ashe alhinin mutuwarta ne ya fara ta\u0253a ni tun daga lokacin ban sani ba<\/em>.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>A nan &#8220;Ranar da al&#8217;amarin zai faru&#8221; da mai ba da labarin ya yi amfani da ita, shi yake nuna mana cewa al&#8217;amarin ya riga ya faru har ya wuce, wato dai labari kawai yake ba mu. Sannan muna da masaniyar ya san labarin tun daga farkonsa har \u0199arshen shi a ransa, don haka yana ba mu labarin irin alhinin da ya tsinci kansa tun kafin ya samu labarin mutuwarta ne. Amma kuskure ne marubucin da yake tsaka da amfani da wannan salo sai kuma a ji ya ce;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;<em>Yau na tashi gaba\u0257aya jikina babu \u0199wari, ashe alhinin mutuwarta ne ya fara ta\u0253ani tun daga lokacin ban sani ba.&#8217;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Kalmar yau da ya saka ita take nuna mana cewa ba labarin abin da ya shu\u0257e yake ba mu ba, yana ba mu labarin abin da yake faruwa ne, wato Lokaci Na Yanzu Na farko kenan. Shi kuma labarin da yake faruwa a lokacin ba a sanin me zai faru a gaba, idan haka ne yaushe har ya san cewa za ta mutu bayan tashin shi kenan?<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022<strong>Amfani da abin da aka ji aka gani ka\u0257ai<\/strong>: A cikin irin wannan salon, iya abin da mai bayar da labarin ya ji ko yake ji, ya gani ko yake gani yake da ikon bayar da labarinsa. Misali;<\/p>\n\n\n\n<p><em>Da na je \u0199ofar gidansu na tarar tuni jama&#8217;a sun taru, wasu sun yi alwala wasu suna kan yi, da alamu jira ake yi a gama shirya ta a yi mata salla.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Wannan duk abin da yake iya gani ne, idan ya ba da labarin shi babu matsala. Matsalar ita ce a ji shi a \u0199ofar gida amma yana suffanta irin yawan mutanen da suke cikin gidan. Misali kamar ya ce:<\/p>\n\n\n\n<p><em>Amma duk da yawan wa\u0257annan mutanen ba su kai na cikin gidansu yawa ba, acikin gidansu fa babu masaka tsinke, duk inda ka hanga mata ne sai koke-koke suke yi. Ita kuwa mahaifiyarta tana can a sume ana watsa mata ruwa ko za ta farfa\u0257o.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Ta yaya ya san yawan mutanen gidan shi da yake \u0199ofar gida? Ta yaya ya san cewa mahaifiyarta ta suma ana ta watsa mata ruwa? A irin wannan salo kuskure ne babba fa\u0257ar abin da ba ka gani ko ka ji ba. To amma akwai wata dabara da ake yi idan ana so a bayyana me yake faruwa a cikin gidan, don haka bari mu \u0257auki misalin da muka yi amfani da shi mu \u0257an yi masa kwaskwarima.<\/p>\n\n\n\n<p><em>Sai daga baya ake fa\u0257a mini cewa ashe wai duk da yawan wa\u0257annan mutanen na \u0199ofar gida ba su kai na cikin gidansu yawa ba, acikin gidansu wai babu masaka tsinke, duk inda ka hanga mata ne sai koke-koke suke yi. Ita kuwa mahaifiyarta ma aka ce suma ta yi ake ta watsa mata ruwa sannan ta farfa\u0257o.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan mun duba duk sa\u0199o \u0257aya aka isar, kuma babu wanda zai tuhume ka da cewa ya aka yi ka sani.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022<strong>Shiga zuciyar wani<\/strong>: A salon tauraro cikin fage haramun ne ga marubuci ya ri\u0199a shiga zuciyar wani ya fa\u0257i me ta \u0199unsa, ko da kuwa a kujera \u0257aya suke zaune. Misali:<\/p>\n\n\n\n<p><em>Kamar kullum, da zan fita na \u0257akko ku\u0257i Naira \u0257ari biyar ta cefane na ba wa Rabi, muka ha\u0257a ido da ita a ranta tana cewa &#8216;Ko ka fita babu wani abinci da zan girka, na samu ku\u0257in zubin adashe ne kawai.<\/em>&#8216;<\/p>\n\n\n\n<p>Ta yaya ya san abin da yake zuciyarta? Yin hakan kuskure ne, sai dai shi ma a yi amfani da &#8216;yan dabaru irin wancan. Bari mu sake \u0257aukar misalin.<\/p>\n\n\n\n<p><em>Kamar kullum, da zan fita na \u0257akko ku\u0257i Naira \u0257ari biyar ta cefane na ba wa Rabi, muka ha\u0257a ido da ita ina nazarin ta, duk da dai ban san abin da yake ranta ba amma ina zargin tunani take yi na fita ta je ta biya ku\u0257in adashe ta \u0199i yi mana girki kamar yadda ta saba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>A nan ma idan marubuci ya yi amfani da wannan dabarar zai isar da sa\u0199onsa ga manazarci, sannan babu wanda zai tuhume shi da sa\u0253a \u0199a&#8217;ida.<\/p>\n\n\n\n<p>Za mu dakata a nan, amma za ku iya ci gaba <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-2\/\">a ma\u0199ala ta gaba<\/a> inda muka kawo karshen bayanin a wannan maudu&#8217;i.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A yau za mu yi bayani ne a akan salon bayar da labari da kuma salon ginin labari. Idan ba ku manta ba, a ma\u0199alar da ta gabata, mun yi bayani game da fa&#8217;idar yin bincike a wajen ginin labari, inda muka ce mutunci, \u0199ima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a \u0199asa wanwar&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-1\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Salon bayar da labari da salon ginin labari 1<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3305,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,27,19],"class_list":["post-3294","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-salon-labari","tag-writing-tips"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/01\/Salon-bayar-da-labari.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3294","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3294"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3294\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3305"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3294"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3294"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3294"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}