{"id":3471,"date":"2022-04-14T16:59:12","date_gmt":"2022-04-14T16:59:12","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3471"},"modified":"2022-09-02T03:40:29","modified_gmt":"2022-09-02T03:40:29","slug":"sharhin-littafin-akan-so-na-lubna-sufyan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-akan-so-na-lubna-sufyan\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Akan So&#8217; na Lubna Sufyan"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan Littafi: <strong>Akan So<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciya: <strong>Lubna Sufyan<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka Buga Littafi: <strong>Bakandamiya Hikaya (<strong>Online<\/strong>)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar Bugu: <strong>2022<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai Sharhi: <strong>Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manufar Sharhi: <em>Bun\u0199asa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Ta\u0199aitaccen tarihin marubuciyar<\/h2>\n\n\n\n<p>Lubna Sufyan &#8216;yar asalin \u0199aramar hukumar Ingawa ce da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana \u0199arama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina inda ta yi karatun Diploma a \u0253angaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma, Higher National Diploma (HND) a garin Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance \u0257aya daga cikin fitattun sunayen da ke fara zuwa zukatan masu karatun online da zarar an yi maganar marubutan online a wannan zamani. Zuwa yanzu ta rubuta litattafai sama da guda goma sha \u0257aya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun ha\u0257a da; Akan so, Rayuwarmu, Abdul\u0199adir, Rai Da \u0198addara, Mijin Nobel, Martabarmu, Al\u0199alamin \u0198addara da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar kuma na \u0257aya daga cikin mambobin \u0199ungiyar marubuta na Fikra Writers Association.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Labarin a ta\u0199aice<\/h2>\n\n\n\n<p>Fu&#8217;ad Arabi shi ne \u0257a na hu\u0257u cikin &#8216;ya&#8217;ya bakwai da Alhaji Salman Arabi da Hajiya Aisha suka mallaka. Fu&#8217;ad ya fita daban da sauran &#8216;yan gidansu. Domin ya kasance mai son kai, ta\u0199ama da kuma nuna isa. Bugu da \u0199ari baya kallon kowa da gashi bayan iyayensa da &#8216;yan uwansa sai kuma babban abokinsa wato Lukman. Tun tasowarshi ba shi da aiki sai buga wasan \u0199wallon \u0199afa. Ya sha \u0199in zuwa makaranta akan wasan \u0199wallon na \u0199afa. Tun suna duka da fa\u0257a har suka gaji suka soma ba shi goyon baya. Lokacin da ya shiga aji shida a sakandire ne ya samu \u0257aukaka zuwa \u0199asar Europe.<\/p>\n\n\n\n<p>Dole su Alhaji Salman suka \u0199yale Fu&#8217;ad ya tafi. Da \u0199yar ya dawo ya zana jarabawar WAEC ka\u0257ai.<\/p>\n\n\n\n<p>Can ya nemi gurbin karatu saboda aikinsa na wasan \u0199wallon \u0199afar ya sa zaman shi ya koma can.<\/p>\n\n\n\n<p>Fu\u2019ad da Safiyya sun yi aure ne ba tare da amincewar iyayensu ba, domin ana gab da \u0257aurawa Safiyya aure ta bi Fu\u2019ad suka je wani wurin aka \u0257aura musu aure. Sai dai rashin samun albarka daga iyayen nasu ya sa auren bai yi \u0199arko ba. cikin &#8216;yaya uku kacal da Malam Audu da Zainabu suka mallaka a duniya. Safiyya na da &#8216;ya guda \u0257aya tal, wata yarinya me \u0257ankaren wayo tare da saurin shiga rai da ake kira da suna Nana wacce ke fama da cutar daji. Likitoci sun bayyana cewa, domin Nana ta rayu sai an yi mata dashe (transplant). Idan ba a samu wanda ya yi daidai da ita ba, za ta iya rasa ranta cikin watanni shida ko \u0199asa da haka. Mutun na farko da ake sa ran ko nashi zai zo daidai da nata shi ne mahaifinta, wato Fu\u2019ad Arabi wanda aka fi sani da &#8216;Moh&#8217; wanda bai ma san da ita ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuwa Fu\u2019ad tun asali baya son haihuwa, domin har zuwa ya yi aka yi masa aikin da ya kashe masa \u0199wayoyin haihuwarsa gaba \u0257aya don kada ya haihu, wato vasectomy. Fu&#8217;ad ya sake Safiyya ne yayin da ta nuna tsananin bacin ranta a sabili da ya gaya mata ya yi vasectomy. A tunanin shi ya sake ta ne domin shi ba zai iya bata abinda ta ke so ba, wato &#8216;ya&#8217;ya. Saboda haka bayan ya saketa ya sa kafanshi ya bar gida da ma kasan baki daya. Bai san da cikin Nana ba sam, itama Safiyya ta sani ne bayan tafiyan shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya san Nana ne ranar da ya dawo bayan shekara sha daya da ya je gidansa da Safiyya. A nan yayi arba da ita a karo na farko.<\/p>\n\n\n\n<p>Nana na son ganin mahaifinta kafin ta rasu, a gefe kuma masoyanta na fata babanta ya zama dai dai da abinda likitoci ke so domin ta tsira da rayuwarta. To amma ita Safiyya tana ganin wannan abu ba mai yiwuwa bane, domin ta san halin Fu\u2019ad da yadda yake da son rai. Kuma maganar da ya yi mata na \u0199arshe kafin ya bar \u0199asar ita ce; &#8220;I don&#8217;t do happily ever after. Daga ranar da kika yarda da soyayyata ya kamata ki san ban yi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban yi kama da wanda zai yi asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Ina da su Haneef, ina da su Fa&#8217;iza. A duk lokacin da na ji marmarin ganin yara zan je gidansu in ga nasu.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Dr. Jana ita ce likitar da ke kula da Nana. Auren soyayya suka yi da mijinta Jabir. Suna matu\u0199ar son junansu, kuma sun aminta da juna sosai. Sannan Allah ya azurta su da zuri&#8217;a. To sai dai kuma, aikin da Jana ke yi na neman zama matsala a tsakaninsu, wanda hakan ya sa Jabir ya fara tunanin \u0199ara aure. Aina abokiyar aikin Jabir ce, domin waje guda suke aiki. Tana burge Jabir sosai saboda kamun kai, hankali da kuma nutsuwarta, wanda akarshe ya aureta.<\/p>\n\n\n\n<p>Nuriyya matashiya ce mai kamun kai da ri\u0199on addini, sai dai ta yi rashin samun nagartacciyar uwa. Domin kuwa, ita kullum \u0199o\u0199ari take yi ta sa ta a hanyar ba\u0257ala. Ta kamu da son wani bawan Allah mai suna Farhan wanda ya taimaka mata a rayuwa sakamakon mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki. A dai dai lokacin da ya yi yun\u0199urin aurenta, a dai dai wannan lokaci ne kuma mahaifinsa ya turje akan shi \u0257ansa ba zai auri mace irin Nuriyya ba, ya kuma ba shi za\u0253i ko su ahalinsa ko Nuriyyar. Wannan dalili ne yasa Farhan bin mahaifinsa suka bar \u0199asar. Bayan tafiyar su ne Nuriyya ta ha\u0257u da Nawaf, wanda ya maye mata gurbin Farhan ta fannoni da dama har suka yi aure. Allah ya jarabci Nawaf da shaye-shaye da kuma ba\u0199in kishi na nunawa a kasuwa. Ita kuma Nuriyya duk da irin son da take yi wa Nawaf, ta kasa cire Farhan daga zuciyarta.<\/p>\n\n\n\n<p>Yadda ta kasance a tsakani da kuma yadda labaran suka ha\u0257e waje guda shi ne yadda labarin ya tafi a cikin wannan littafi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Wato ko da jin sunan wannan littafi &#8216;Akan So&#8217; na san masu karatu za su iya fahimtar babban jigon wannan labari shi ne soyayya da kuma abin da so ka iya sa mai yin sa ya aikata. Kuma duk tirka-tirkar da ke cikin labarin za ka iske ta samo asali ne daga son da wani ke yi wa wani ko wata ke yi wa wani a cikin wannan labari. Domin an nuna irin yadda sabon shiga a so kan ji idan so ya kama shi kamar yadda a babi na goma sha uku marubuciyar ta ce &#8220;Wannan wane irin abu ne. Sati \u0257aya kenan. Da duk numfashin da za ta ja ta fitar da tunanin shi a ciki. Ta ma rasa me take ji game da shi. Saboda wani irin yanayi ne take ji kala-kala. Ko lomar abinci za ta kai baki yana nan cikin kanta. Da shi take komai a manne. Bata da ikon bacci mai lafiya ba tare da shi a cikin mafarkinta ba. Gashi wani irin mafarki take yi da duk in ta farka sai ta ji shi kamar gaske. Kalaman da suke wa juna a mafarkin ya fi komai \u0257aga mata hankali&#8230;.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a shafi na goma sha hu\u0257u kuma an sake nuna mana yadda shi ma Fu\u2019ad ya ke ji dangane da Safiyya a inda marubuciyar ta ce &#8220;A &#8216;yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun fa\u0257a saboda ba shi da wata wadatacciyar nutsuwa&#8230; Ta ina ma zai fara ce masa shi Fu\u2019ad yau tunanin mace ya saka shi a gaba. Tunanin macen ma kucaka &#8216;yar \u0199auye. Abin da \u0257an nauyin fa\u0257a. Tunda shi bai san me ya sa ma yake jin abinda yake ji \u0257in ba&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Anan za mu iya fahimtar yadda asalin soyayya ta fara shiga tsakanin taurarin labarin guda biyu da kuma irin \u0199alubalen da soyayyar tasu za ta fuskanta duba da irin yanayin halayyarsu da kuma yadda ala\u0199a ta ha\u0257a su tun da fari. A \u0199ar\u0199ashin wannan jigon kuma in aka yi duba da kyau za a ga wasu \u0199ananan jigogi wa\u0257anda suka taru suka bada darussa masu dama a cikin labarin kamar:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 A babi na shida, sakin layi na farko an nuna mana muhimmancin tarbiyya da ilimi da kuma yadda iyaye ke \u0199o\u0199arin ganin sun ba &#8216;ya&#8217;yansu tarbiyya. Kamar yadda marubuciyar ta ce &#8220;Dai-dai gwargwado daga Alhaji har Hajiya sun yi iya bakin \u0199o\u0199arinsu wajen ganin sun ba yaransu tarbiyya da ilimi na boko da addini&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Haka kuma an nuna mana irin matsalar da yin aure ba tare da amincewar iyaye ba ka iya haifarwa a cikin wannan labari. Dubi yadda a babi na ashirin \u0257aya daga cikin taurarin labarin ya ce, &#8220;Abin da ka yi ba \u0199arami bane ba. Ban ce ba zai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala Fu\u2019ad. Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu&#8230;&#8221; da kuma inda a can gaba a babi na talatin da biyar yayin da al&#8217;amura suka fara kwa\u0253e musu inda Fu&#8217;ad ya fara zargin Safiyya akan rashin lafiyar &#8216;yarsa inda yake riyawa a zuciyarsa &#8220;&#8216;Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane sai na Safiyya. Sofi ta \u0253oye mishi ita gashi yanzun mutuwa za ta yi&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Da abu ya yi tsamari kuma sai maganar ta fito fili inda yake cewa, &#8220;Saboda ke ba zan san abubuwa da yawa ba akan Nana.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda ke na rasa shekaru goma sha \u0257aya na rayuwa tare da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba ke ya kamata ki yi kuka ba Sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha \u0257aya a cikin kanki da za ki dinga dubawa kina samun sau\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p>Ba ni da komai!!!<\/p>\n\n\n\n<p>Ba ni da abinda zan duba nata banda watanni!!!<\/p>\n\n\n\n<p>Wallahi ban san yadda akai zuciyata ta yi kuskuren sonki ba&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ita kuma ta ba shi amsa da cewa, &#8220;Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba!&nbsp; Kai ka za\u0253i ka bar ni. Saboda me za ka ga laifina? Ya kake so in yi? Meye ban yi Akan sonka ba? Saboda me za ka \u0257auka kai ka\u0257ai ne za ka rasa Nana? Ko ka \u0257auka ka fini sonta ne?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan hali da suka tsinci kansu a ciki ya sa shi yin nadamar abin da suka aikata wanda har ya sa shi yake cewa &#8220;Za mu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah da ya \u0257ora mata ne kawai zai iya. Sofi za mu gyara komai. Zamu ba kowa ha\u0199uri. Inna da Baba. Su Abba. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana&#8230;&#8221; ita ma nadamar ta kamata sosai inda har take cewa &#8220;&#8230; &#8220;Komai zai gyaru in suka yafe mana. Mun yi kuskure na \u0257aukar za mu iya tsara rayuwarmu da kanmu&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna mana matsalar shaye-shaye da inda wani lokaci abokai ne kan ja ra&#8217;ayin wasu matasan har su shiga harkar. Kamar yadda a babi na talatin da hu\u0257u marubuciyar take bayyana mana yadda Nawaf ke ji a ranshi da cewa &#8220;Yana tsoron kar\u0253ar \u0199wayoyin da ke hannun Auwal, don bai san kalar \u0199arfinsu ba. Codeine \u0257in ma don ya zamana kowa a ajinsu yana sha ne. Kullum kallon \u0199aramin yaro suke mishi. Shi ne abin da ya fara jan hankalinshi. Shekara \u0257aya kenan ya kasa dainawa. Sam ba ya jin da\u0257i in har bai sha ba&#8230;&#8221; kuma a dalilin hakan ya sa ya ci gaba da shan \u0199wayoyin har bayan fitarsa daga makarantar. Kuma shaye-shayen ya sa ya zamana yana \u0199untatawa &#8216;yan uwansa ba don yana so ba, dubi abinda yake ce musu a lokacin da yake kwance a gadon asibiti &#8220;&#8230;Ku yafe min. Na saka ku \u0253acin rai da yawa a rayuwata. Ku taya ni ro\u0199on Allah ya yafe min&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna mana yadda tsanstar soyayyar iyaye take ga &#8216;ya&#8217;yansu, da kuma irin yadda suke da muhimmanci a wajen &#8216;ya&#8217;yan nasu. Dubi dai yadda Fu&#8217;ad ya shiga taitayinsa bayan gane kuskurensa kamar yadda marubuciyar ta bayyana &#8220;Gaba \u0257aya jikin shi rawa yake. Ko ina na jikin shi \u0253ari yake. So yake ya ce Abba ya yafe mishi kalma ko \u0257aya ta \u0199i fitowa daga bakinshi.<\/p>\n\n\n\n<p>So yake ya fa\u0257a wa Abba yau ya ga wautar da ya aikata. So ya ke ya fa\u0257a mishi yau ya gane amfanin neman shawara. Ya gane irin \u0199aunar da suke mishi. Ya gane ba takura mishi suke yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya gane irin wannan ranar suke guje mishi&#8230;&#8221; Sannan an nuna mana yadda ya yi nadama har yake cewa &#8220;Abba na gane soyayyarku mai girma ce a gareni. Wallahi na gane duk wata soyayya \u0199asa take da ta iyaye. Abba ka yafe min. Ka yafe min ko zan samu in ga dai dai a rayuwata&#8230;.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wa\u0257annan akwai \u0199ananan jigogi da dama da marubuciyar ta ta\u0253o kamar su soyayyar ahali, muhimmancin abota, adalci a tsakanin ma&#8217;aurata da sauransu<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Salo da sarrafa harshe<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta yi \u0199o\u0199ari sosai wajen ba da labarin. Domin ta yi amfani da salo mai burgewa wajen isar da sa\u0199on labarin. Misali:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Tafiyar Kura: Marubuciyar ta yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda ta datsi labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi ta hanyar komawa baya ta kwance wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Koyarwa: An yi amfani da wannan salo sosai a cikin wannan littafi wajen koyar da darussa da dama da suka shafi zaman duniya, zaman ma&#8217;aurata da yadda za a zauna da ahali cikin harshe mai sau\u0199i yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo mai Armashi: Marubuciyar ta yi amfani da salo mai armashi sosai da sanya nisha\u0257i ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya a wasu lokutan.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sarrafa Harshe: Har ila yau an yi amfani da kalmomi da za su sa mai karatu ya ji kamar da shi labarin ke faruwa. Ko da yake an samu \u0199arancin kwarzanta harshe ta hanyar yin amfani da karin magana, zambo da sauransu, marubuciyar ta maye gurbin su da misalai masu jan hankali wa\u0257anda suka \u0199ara wa labarin armashi.<\/p>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari marubuciyar ta yi amfani da sassu\u0199ar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai ta yi amfani da kalmomin turanci masu yawa a cikin labarin wa\u0257anda yawan da suka yi ka iya sa wasu makarantar su ji da\u0257i wasu kuma su ji akasain haka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">&nbsp;Zubi da tsari<\/h2>\n\n\n\n<p>An tsara ko kasa wannan labari ne a zubin babi-babi, daga na \u0257aya zuwa na arba&#8217;in da takwas. Littafin ya samu tsari mai kyau, domin tun daga babi na farko aka fara nuna mana irin soyayyar da ke tsakanin Safiyya da kuma &#8216;yarta Nana. Haka kuma an nuna mana irin halin wasu daga cikin taurarin labarin tun a babi na farko. Wani abin \u0199arin armashi shi ne, tun daga nan, kowace jumla da ta biyo baya a labarin tana \u0199arfafa ta bayanta ne. Sannan an samu zagi a tsakanin jumloli da babin labarin ta yadda na gaba ke \u0199ara fayyace na baya. Domin an fara ne da bayyana mana halin da Nana take ciki na rashin lafiya da kuma irin bau\u0257a\u0257\u0257en halin mahaifinta na rashin son yara wanda shi ka\u0257ai ne ake tunanin zai iya taimaka mata ta rayu. Sannan a gefe an hasko mana irin yadda mu&#8217;amala ta fara tsami a tsakanin Dr. Jana da mijinta Jabir sakamakon aikin da take yi. To duk sauran babin da suka biyo baya suna \u0199ara fayyace wa\u0257annan abubuwan ne.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Sannan an yi amfani da<\/h2>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Ba\u0257oki na Gaske:<\/strong> &#8220;Innalillahi wa inna ilaihir raji&#8217;un take furtawa a cikin zuciyarta. Ba mafarkin komai take ba da gaske ya faru. Da gaske ne ta bar komai ta zo ta auri Fu\u2019ad. Ta baro Inna da Baba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta watsar da duk wata tarbiya da suka gina mata shekaru goma sha takwas. (Babi na 18 sakin layi na \u0199arshe). Da kuma cewar mahaifin Safiyya. &#8220;Na bar muku ita kyauta. Wallahi na yafe muku ita. Kamar yadda mahaifiyarta ta fa\u0257a. Ba za mu yi mata baki ba. Sai dai zan tsine mata duk ranar da ta zo min gida.&#8221; (Babi na sha tara)<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ya sa tun daga nan mai karatu zai iya fahimtar cewa tun da har ta watsar da iyayen ta ta auri wani akan so, to tabbas fushin su sai ya ta\u0253a ta ko yaya ne. Wani \u0199arin abin dubawa game da wannan labarin shi ne, ba wannan ne ka\u0257ai ba\u0257okin da aka yi amfani da shi ba, amma duk ba\u0257okin na gaskiya ne, ma&#8217;ana duk sun faru daga \u0199arshe, har ma da \u0199ari.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Tsoro:<\/strong>&nbsp; An yi amfani da wannan dabara a wurare masu yawa a cikin wannan littafi, wasu sun faru da gaske wasu kuma ba su faru ba. Misali, &#8220;Option \u0257aya ne kawai Ansar. Shi ne transplant idan an samu match&#8230;&#8221; Shiru Dr. Jana ta yi. Cikin aikinta babu abinda ta fi tsana sama da wannan \u0253angaren. Kallon mutane a kullum lokacin da za ka fa\u0257a musu mutuwar wani nasu. Ko lokacin da za ka tarwatsa musu burinsu da magana \u0257aya&#8230; Muryar Jana can \u0199asa ta ce; &#8216;Rayuwa a hannun Allah take Safiyya. Zan iya cewa \u0199asa da wata shida. Idan Allah ya yi \u0199arfin ikon shi, shekara \u0257aya.&#8221; (Babi na uku)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Al&#8217;ajabi:<\/strong> &#8220;Safiyya kallon Fu\u2019ad take zuciyarta na wani irin dokawa. Shi ma kallonta yake lokaci \u0257aya maganganun Doctor \u0257in da ya jagoranci yi mishi surgery na vasectomy suka dawo mishi. Cikin harshen turanci yake fa\u0257a wa Fu\u2019ad \u0257in cewar, &#8216;Ko da bayan shekaru ko watanni matarka ta samu ciki karka zargeta. Ka \u0257auka jikinka ya warkar da kanshi. Yana faruwa ga wasu mutanen.&#8217; (Babi na 47)<\/p>\n\n\n\n<p>Fu\u2019ad ya ga abin al&#8217;ajabin da bai yi tsammani ba, domin ya sa an kashe mishi \u0199wayoyinsa na haihuwa a asibiti, amma sai ga shi bayan shekaru goma sha \u0257aya maganar da likitansa ya fa\u0257a masa wasu ko an yi musu hakan suna iya \u0199ara samun haihuwa ta tabbata.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Tausayi:<\/strong> &#8220;Ji ya yi an dafa shi. Hakan ya sa ya \u0257ago da kanshi daga cikin hannayenshi sannan ya juyo, Safiyya ce fuskarta a kumbure. Wasu hawaye suka zubo mata. Kama hannayenta ya yi yana gogasu kan fuskar shi. &#8220;Sofi, ta rasu. Nana ta bar mu har abada.&#8221; (Babi na 45)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Mamaki: <\/strong>&#8220;Ba ri\u0199o muka baku ba Fu\u2019ad. Aisha Fu\u2019ad Arabi. Mu muka haifeta. Amma &#8216;yarka ce Fu\u2019ad. Allah ne shaidar mu akan wannan zamu amsa sunan masu haihuwarta ne kawai.&#8221; (Babi na 46)<\/p>\n\n\n\n<p>Tabbas ko waye sai ya yi mamaki, ace mutane sun haifi yarinya nan take kuma su mallaka wa wani ita halak malak.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Murna:<\/strong> &#8220;Oh Allah. Ina bayin da suka sake ka suka kama waninka? Ha\u0199i\u0199a suna cikin \u0253ata mai muni.&#8221; (Babi na47 sakin layi na kusa da \u0199arshe)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hoton Zuci: An yi amfani da hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa. Misali, &#8220;Yadda ya yi da fuska ya ba Haneef tausayi. Don ya san bai saba ba sam. Kama hannunshi ya yi kamar yaro. Ya ja shi zuwa cikin shagon. Ko&#8217;ina a share yake tsaf. Da leda a shimfi\u0257e sai katifa an lailayeta da zanin gado. Kusurwar \u0257akin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin \u0199usa. Sai takalmansu can gefen wani bango akan siminti, wajen da alamu ledar \u0257akin ba ta kai ba. Haneef ya \u0199arasa ya cire takalminshi ya ajiye inda ya ga masu shagon na ajiye nasu. (Babi na 7 sakin layi na kusa da \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tauraron labari<\/h2>\n\n\n\n<p>Ko shakka babu Fu\u2019ad Arabi shi ne babban tauraron wannan labari. Shi ne \u0199ashin bayan labarin, kuma kaso 90% na matsalolin labarin shi ke \u0257auke da su a ka. Kuma ya shafa wa duk wanda ke kusa da shi wa\u0257annan matsaloli. A iya cewa shi ne silar samuwar matsala tsakanin Safiyya da iyayen ta, saboda da bai shiga rayuwar ta ba da bata fuskanci irin damuwar da ta tsinci kanta a ciki ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Halayen taurarin labari<\/h2>\n\n\n\n<p>\u2022 Bari mu fara da babban tauraron labarin wato Fu\u2019ad. Matashi ne \u0257an kimanin shekaru 22. Siriri ne, yana barin gashi akai sosai tare da son \u0199ananan kaya. Gwani ne a fagen \u0199wallon \u0199afa, yana da raina na \u0199asa da shi musamman talaka. Yana da son kai, ta\u0199ama da kuma nuna isa. Kuma duk abin da ya ce zai aikata to sai ya aikata shi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Safiyya ita ce wacce ke take masa baya a cikin taurarin labarin. Ba ba\u0199a bace, sai dai bata cika haske ba sosai. Gajeruwa ce ba kuma wata kyakkyawa bace a fuska, sai dai Allah ya bata idanu tubarkalla. Ba za ka kirata mummuna kai tsaye ba. Saboda jikinta na da kyau sosai. Tana da \u0199ira da dirin da mata da yawa za su yi hassada da ita saboda shi. Tana da ha\u0199uri sosai kuma bata fiye yawan surutu ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Haneef \u0257an uwan Fu&#8217;ad ne na jini, domin ya girme shi. Shi ne mutum na farko da Fu&#8217;ad ke saurare kafin Lukman. Yana da ha\u0199uri da juriya tare da son &#8216;yan uwansa. Musamman \u0199anin nashi wato Fu\u2019ad.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Lukman shi ne babban abokin fu&#8217;ad tun suna yara. Abotarsu ta yi girman da har sun zama tamkar &#8216;yan uwa na jini. Mutum ne mai ha\u0199uri da sanin ya kamata, kuma shi ne wanda ya zamo wa Fu&#8217;ad \u0257in tamkar wani bango da yake jingina a jikin sa a duk lokacin da wani abu ya faru.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Nana Yarinya ce &#8216;yar kimanin shekaru 12, tana da fara&#8217;a sosai tare da saurin shiga ran duk wanda ya ganta. Tana da wayon da har ya girmi shekarunta, domin wani lokaci in ta yi magana sai dai kawai a ri\u0199e baki.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Dr. Jana mace ce \u0257aya tamkar dubu. Tana matu\u0199ar son mijinta kuma tana da tsaron Allah sosai. Tana da \u0257abi&#8217;u masu kyau, ciki kuwa har da danne kishinta na mace ta yarda da mijinta ya \u0199ara aure har ma da raka shi siyo kayan lefe.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Nawaf matashi ne da Allah ya jarabta da Shaye-shaye. In ka cire wannan ba shi da wani mummunan hali face mugun kishin matarsa wanda shi ne ya zama silar ajalinsa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Nuriyya tsintacciya ce wadda mari\u0199iyarta da ta yi tunanin ita ce mahaifiyarta ta yi ta \u0199o\u0199arin ganin ta sa ta a hanyar ba\u0257ala amma Allah ya tsare ta. Tana da ha\u0199uri da juriya da halin rayuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Jabir kuma magidanci ne kuma ma&#8217;aikacin wani kamfani. Yana son matarsa sosai tare da ahalinsa. Duk da yana so ya \u0199ara aure, amma saboda soyayyar da yake yi wa matarsa da kuma irin matsyin da take da shi yasa sai da ya fara sanar mata kafin ma ya fa\u0257a wa wacce yake so \u0257in. Mutum ne mai \u0199o\u0199arin kamanta adalci a koda yaushe.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kammalawa<\/h2>\n\n\n\n<p>A dun\u0199ule labarin yana isar da sa\u0199onni ne masu tarin yawa a wuri guda. Daga cikinsu akwai garga\u0257i ga masoya wa\u0257anda wani lokaci idanuwansu kan rufe akan so har su je su yi abin da za su yi da na sani. Sannan an nuna muhimmancin iyaye da kuma yadda albarkar su ko fushinsu ke tasiri akan &#8216;ya&#8217;yansu. Sannan kuma an nuna muhimmancin ahali, da dangi da kuma abota mai tsafta. Haka kuma an nuna mana muhimmancin kyautatawa a tsakanin ma&#8217;aurata tare da ribar da za su samu yayin da suka yi wa juna adalci a zamantakewarsu, da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Labarin zai sa ka shau\u0199i tare da duban rayuwa ta wani \u0253angare sabo wanda ba ka ta\u0253a tunanin akwai shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>In da marubuciyar kawai ta samu kubcewar salo shi ne yawaita amfani da kalmomin turanci da ta yi a cikin labarin. Domin ta yi amfani da kalmomin turanci sama<\/p>\n\n\n\n<p>da sau hamsin a cikin labarin. Ko da yake akwai wuraren da za a iya bata uzuri duba da irin sigar da labarin ya zo, akwai wuraren da za a iya amfani da kalmomin Hausa su zauna a wurin daram, amma sai aka yi amfani da na turanci. Misali, a cikin labarin akwai inda marubuciyar ta ce &#8220;Wani abu Fu\u2019ad ya ji ya tokare masa wuya. Already baya jin da\u0257in komai&#8230;.&#8221; (Babi na 10, sakin layi na uku)<\/p>\n\n\n\n<p>Wanda wannan &#8216;yar gajeruwar jumla ana iya sauya kalmar &#8216;already&#8217; da &#8216;tuni&#8217; ko &#8216;da ma&#8217; da makamantansu su ba da ma&#8217;anar da ake bu\u0199ata a wurin. Sannan kuma marubuciyar ta yi amfani da kalmar turanci ta &#8216;fuck&#8217; kusan sau goma a cikin labarin wanda wannan na daga cikin irin abubuwan da ya kamata a dinga kaucewa.<\/p>\n\n\n\n<p>In ka cire wa\u0257annan abubuwan guda biyu, to babu abin da za a ce wa wannan littafi sai sam-barka, domin ya nisha\u0257antar, ya \u0199ayatar, kuma ya ilmantar.<\/p>\n\n\n\n<p>Don karanta cikakken wannan littafi na <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/akan-so-babi-na-daya\/\">&#8216;Akan So&#8217; sai a latsa nan<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p>Kana ana iya duba <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-abdulkadir-na-lubna-sufyan\/\">sharhin &#8216;Abdulkadir&#8217;<\/a> wani daga cikin littattafan Lubna Sufyan.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Manazarta<\/h2>\n\n\n\n<p>\u018aangambo, A. (1984) <em>Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa<\/em>. Kano: Triumph<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y. da \u018aangambo, A. (1986) <em>Jagoran Nazarin Hausa<\/em>. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da &#8216;Yar Aduwa T.M. (1992) <em>Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1<\/em>. Ibadan: University Press Plc <\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan Littafi: Akan So Marubuciya: Lubna Sufyan Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online) Shekarar Bugu: 2022 Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees) Manufar Sharhi: Bun\u0199asa harshen Hausa da ciyar da adabi gaba Ta\u0199aitaccen tarihin marubuciyar Lubna Sufyan &#8216;yar asalin \u0199aramar hukumar Ingawa ce da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-akan-so-na-lubna-sufyan\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Akan So&#8217; na Lubna Sufyan<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":3474,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[40,29,41],"class_list":["post-3471","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-akan-so","tag-book-review","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/04\/Sharhin-Akan-So.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3471","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3471"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3471\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3474"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3471"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3471"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3471"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}