{"id":3483,"date":"2022-06-05T07:03:45","date_gmt":"2022-06-05T07:03:45","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3483"},"modified":"2022-09-02T03:40:19","modified_gmt":"2022-09-02T03:40:19","slug":"sharhin-littafin-abdulkadir-na-lubna-sufyan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-abdulkadir-na-lubna-sufyan\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin \u2018Abdulkadir\u2019 na Lubna Sufyan"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan Littafi: <strong>Abdul\u0199adir<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciya: <strong>Lubna Sufyan<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka Buga Littafi: <strong>Bakandamiya Hikaya (Online)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar Bugu: <strong>2022<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai Sharhi: <strong>Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manufar Sharhi: <em>Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Dangane da marubuciyar<\/h2>\n\n\n\n<p>An haifi Lubna Sufyan ne a \u0199aramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana \u0199arama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun diploma a \u0253angaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato Babbar Diploma, Higher National Diploma (HND) a garin Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance \u0257aya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani. Zuwa yanzu ta rubuta litattafai sama da guda goma sha \u0257aya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun ha\u0257a da; <em>Rai Da \u0198addara, Wata Bakwai, Akan So, Rayuwar Mu, Abdul\u0199adir, Mijin Nobel, Martabar Mu, Al\u0199alamin \u0198addara<\/em> da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Har&#8217;ilayau, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da \u0199ungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su Give North Education, Women In Arewa, Women In Finance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma \u0199wararra ce wajen ha\u0257a \u0257uwatsun \u0199awa na adon mata. A ta\u0199aice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi \u0199arfi.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar kuma na \u0257aya daga cikin mambobin \u0199ungiyar marubuta na Fikra Writers Association, kuma tana garin Katsina ne da zama a yanzu haka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Labarin a Ta\u0199aice<\/h2>\n\n\n\n<p>Alhaji Ahmad Bugaje yana da matan aure har guda hu\u0257u. Matar shi ta farko ita ce Hajiya Safiyya wadda ake kira da Hajja. Ta haifi yara takwas tare da shi, su ne Muhsin, Yazid, Khadija, Mubarak, Abdul\u0199adir, Zahra, Nazir da kuma Zainab. Matar shi ta biyu kuma ita ce Hajiya Saratu wadda ake kira da Mama. Tana da yara biyar da Alhaji Ahmad dukkan su maza. Ahmad (wanda ake kira da Babangida), Yasir da Yazid wa\u0257anda suka kasance &#8216;yan biyu, sai kuma Salim da Khalid.<\/p>\n\n\n\n<p>Hajiya Sakina ita ce matar shi ta uku da yaransu ke kira Mami, wadda kuma ita ka\u0257ai ce ya aura a bazawara, don shekararta \u0257aya da wata uku da yin aure Allah ya yi wa mijinta rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Ya kuma rasu a lokacin ya barta da cikin wata shida. Ta haifi yarinyarta mace, bayan ta yayeta ne suka ha\u0257u da Alhaji Ahmad Bugaje. Bai aureta ba sai da ya yi mata al\u0199awarin ri\u0199e mata yarinyar ta.&nbsp; Bayan Waheedah, ta haifi yara uku da shi, su ne, Sa&#8217;adatu (wadda ake kira da Amatullah), Aminu da kuma Habib. Hajiya Halima kuwa da yaran duka ke kira Anty, ita ce mata ta hu\u0257u kuma amarya a gidan Alhaji Ahmad, &#8216;yar tsohon Wazirin Kano ce da Allah ya yi wa rasuwa ya aura. A cikin matan shi ita ka\u0257ai ce take aikin gwamnati, domin kuwa da aikinta ya aure ta. Allah ya azurta su da yara shida, saboda ta fi sauran matan shi haihuwa gab da gab, kusan abinda akan kira da kwanika ko gwarne. Yaran su ne, Nusaiba, Nabila, Kabiru, Adnan da Baraka.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da wannan yawa nasu, hakan bai sa yaran kansu ya rabu ba, domin suna son junansu kuma suna girmama na gaba da su. Sannan suna da ha\u0257in kai tare da zumunci da kuma damuwa da junansu. Domin ko \u0199urjewa wani ya yi aka ce ga shi can kwance, to yanzu za ka gansu \u0257uuu duk sun yo kanshi. Wannan dalili ne ya sa kusan ko&#8217;ina suka je nan da nan ake gane su. Hatta Waheedah da ba Alhaji Ahmad ya haifeta ba haka suke mata, saboda ba sa nuna mata wani bambanci, komai a tare suke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Abdul\u0199adir tun yana da \u0199arancin shekaru yake sha&#8217;awar aikin soja, kuma har ya girma yana da wannan ra&#8217;ayi. Yana da zafi sosai, kuma ba ya \u0257aukar raini balle \u0257aga \u0199afa. Saboda takurawa \u0199annensa da yake yi ne a gida ma har suka sa mishi suna &#8216;Commander&#8217; a \u0253oye. Yayan shi Yassar ne ka\u0257ai yake \u0257an saurarawa a duk cikin gidan saboda sun fi jituwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Waheedah tana da sanyin rai da sau\u0199in hali, ga ha\u0199uri da ladabi da biyayya. Wannan yasa kowa ke sonta. Tana da wata \u0199awa da ke ma\u0199wabtaka da su mai suna Nuriyya. Duk da cewa gidan su Nuriyya talakawa ne, hakan bai sa Waheedah ta \u0199yamace ta ba. Sha\u0199uwar da suka yi ne ma ya sa har \u0257inki da sauran abubuwa na yau da kullum akan yi musu tare. Domin har ce musu ake yi &#8216;yan biyu. Babban abin da ya raba su shi ne, Nuriyya tana da son abin duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Yau da gobe, duk da ba\u0199in hali irin na Abdul\u0199adir da takura da dukan da yake yi wa yaran gidan da zarar sun yi laifi ko wani \u0257an kuskure bai hana zuciyar Waheedah kamuwa da \u0199aunarsa ba. Wannan kuwa ya faru ne tun tana da \u0199arancin shekaru. Sai dai ta \u0253oye soyayyar a zuciyarta domin da fari ita kanta bata san cewa abinda take ji a ranta sunan shi so ba saboda \u0199arancin shekaru. Shi kuwa Abdul\u0199adir sam ba shi da burin auren mace irin Waheedah, wannan yasa ko sau \u0257aya bai ta\u0253a kawota a ranshi ba. Amma bayan ya zo bikin \u0199annensa, a wannan lokaci sai ya ji zuciyarsa ta fara bugawa Nuriyya, domin tana da siffa irin ta macen da yake so, sai dai ya \u0199i bayyana mata saboda a lokacin yana tsaka da kar\u0253ar horo a makarantar Sojoji ta NDA da ke Kaduna, kuma ya \u0199udurce a ranshi cewa sai ya kammala tukunna ko da zai sa ranshi a wani al&#8217;amari da ya shafi aure.<\/p>\n\n\n\n<p>A gefe kuma, Yazid ya kamu da son Waheedah sosai, sai dai shi ma bai fa\u0257a mata ba saboda yana tunanin ta yi yarinya da yawa. Ita kuma Nuriyya, ta samu wani saurayi mai suna Anas wanda yake sonta tsakaninsa da Allah, sai dai ita kuma bata son shi, tana dai kula shi ne kawai saboda yana kashe mata ku\u0257i. A \u0199arshe dai Mahaifinta ya aura mata shi duk da bata so ba. Hakan ya sa Abdul\u0199adir ya ji ba da\u0257i sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>Da Yassar ya gane cewa Yazid na son Waheedah, sai ya yi marmaza ya sanar mishi da cewa ai suna soyayya da Abdul\u0199adir. Shi kuma saboda ba zai iya ha\u0257a soyayya da \u0199aninsa ba sai ya ja baya, a \u0199arshe ma ya yi nesa da garin. Abdul\u0199adir kuwa, da dai ya ji cewa ai Waheedah tana son shi, sai ya nemi ji daga bakin ta. Ko da ya samu tabbaci, sai nan take ya samu mahaifinsa da maganar aure.<\/p>\n\n\n\n<p>Kowa na gidan sai da ya jinjina maganar auren, amma hakanan aka yi tunda sun nuna suna so. Bayan an yi auren da wasu &#8216;yan shekaru ne Nuriyya ta kaso nata auren ta fito, ta kuma zo ta aure wa babbar \u0199awarta miji, wato Waheedah.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Na san ko daga \u0257an wannan tsakure mai karatu zai iya fahimtar cewa babban jigon wannan labari shi ne soyayya. Domin an zuba gagarumar soyayya a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu shi da kan shi zai ji ya fa\u0257a soyayyar jaruman cikin wannan labari. Sannan duba da irin yadda soyayyar da kowa daga cikin jaruman ke yi wa juna ba tare da sanin juna ba zai nuna maka cewa ba \u0199aramin \u0199o\u0199ari marubuciyar ta yi ba wajen tsara labarin. Kusan tun a farko-farkon labarin aka nuna mana yadda Waheedah ta kamu da son Abdul\u0199adir amma bata fa\u0257a mishi ba. Kamar yadda a babi na biyar marubuciyar ta ce: &#8220;Jikinta gaba \u0257aya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdul\u0199adir \u0257in lokacin da ya ri\u0199o ta babu abinda take hasasowa, so take ta ji ta a kwance a \u0257aki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gaba \u0257aya har kanta, ba za ta \u0199i bacci ya \u0257auke ta cike da tunanin shi ba, don a \u0257aki ne kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuma Abdul\u0199adir zuciyarsa ta fara bugawa Nuriyya wacce \u0199awar Waheedah ce sai dai bai fa\u0257a mata ba. Dubi yadda marubuciyar da bada misalin yadda yake ji game da Nuriyyar a babi na takwas: &#8221; idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya \u0199an\u0199ance su yana \u0199are mata kallo, wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautinshi, don ba shi da ala\u0199a ko ka\u0257an da ki\u0257an da yake tashi a wajen.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A gefe guda kuma ita Nuriyya tana kishin son da Waheedah ke yi wa Abdul\u0199adir kuma tana fatan da ma ace ita za ta same shi, wannan ya sa ta yi ta bita da \u0199ullin ganin ta samu kusanci da shi ta hanyar yin shisshigi a cikin al&#8217;amuransa kamar yadda marubuciyar ta bayyana a babi na takwas da cewa: &#8220;Binshi take tana kallon hannun shi da yake ri\u0199e da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta. Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata fa\u0257o, \u0199arshen abinda zai faru shi ne Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdul\u0199adir \u0257in take kallo ko zata ga alamun so, kamar yadda yake bayyane a fuskar Waheedah, amma bata ga komai ba, asalima kamar ranshi a \u0253ace yake. Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta ta\u0253a samun Abdul\u0199adir \u0257in. Tana jin za ta yi komai don kar hakan ya faru.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kuma Yazid wanda yake Yaya ne a wajen Abdul\u0199adir ya kamu da son Waheedah ba tare da ya sanar mata ba. Domin shi ma dai har&#8217;ilayau marubuciyar ta bayyana yanayin da yake ji game da ita a babi na takwas inda take cewa:&#8221; tun \u0257azun ya kula da yanayin fuskarta kafin su taho, bai san lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi da doka mata. Wannan yasa duk wanda ya karanta labarin zai so jin yadda wannan rikicin soyayya zai wakana, kuma waye zai yi nasara waye kuma zai fa\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>To sai dai kuma, bayan wannan babban jigo da na yi bayani. An yi amfani da \u0199ananun jigogi masu tarin yawa wa\u0257anda su ne suka ha\u0257u suka ba wa labarin goyon baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu daga cikin su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 A babi na 15 sakin layi na \u0199arshe, marubuciyar ta koyar da mu darasin yin nazari mai zurfi kafin \u0199addamar da maganar aure ta hanyar kawo mana zance zucin da Abba yake yi dangane da maganar auren Waheedah da Abdul\u0199adir da cewa: &#8220;Sosai yake jinjina al&#8217;amarin auren Waheedah da Abdul\u0199adir, shi kam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, don jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah ya yi yawa, zafin Abdul\u0199adir ko su da suka haife shi addu&#8217;a suke binshi da ita&#8221; wannan ke.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Haka kuma a babin dai na 15 an nuna mana rashin dacewar yanke hukunci akan abin da mutum ke zato har sai ya tabbatar saboda gujewa abinda zai iya faruwa a sakamakon hakan. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa &#8220;Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar \u0199anin nashi, har ranshi, duk tsawon shekarun nan ya \u0257auka soyayya suke da Waheedah \u0257in, yana kuma da tabbacin ba shi ka\u0257ai bane yake zaton hakan. Wani zafi ya ji \u0199irjinshi na yi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi Abdul\u0199adir \u0257in na son ta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, don yadda take tambayarshi akan Abdul\u0199adir \u0257in kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata \u0253angaren.&#8221; Wannan kuwa ya faru ne bayan Yassar ya shiga nadamar fa\u0257a wa Abdul\u0199adir cewa ya gano suna soyayya ne da Waheedah, alhalin kuwa shi a wannan lokacin ba sonta yake yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Wani babban darasi kuma da aka koyar a cikin labarin shi ne &#8216;barin halas ko don kunya&#8217;, domin mun ga yadda Abba ya rufe Abdul\u0199adir da fa\u0257a a lokacin da ya ce misi Nuriyya yake so ya aura a babi na 21, inda ya ce, &#8220;Ban ta\u0253a yarda da baka da hankali ba sai yau Abdul\u0199adir, wallahi yau ka tabbatar min da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, \u0199awar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita ka zo kana fa\u0257a min kana so ka aura.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Haka kuma, Hajja, wato mahaifiyar Abdul\u0199adir ita ma ta \u0199ara \u0199arfafa wannan darasi a babi na 22 inda ta ce, &#8220;Ita ma Nuriyyar don ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah ta yi idan ka zo mata da wannan maganar zata dubi amintakar da ke tsakanin su ta \u0199i amincewa. Amma na ga alama yadda ka sa \u0199afa ka shure duk wata kunya da ake halittar \u0257an Adam da ita haka ita ma ta yi fatali da tata.&#8221; da kuma Yassar inda shi ma ya ce, &#8220;&#8221;Mahaukaci ne kai wai? Don ubanka allurar sojojin kai ka mi\u0199a musu suka caka maka ita? Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amma al&#8217;ada ta haramta maka shi, kunya ta haramta maka, ko mutuwa Waheedah ta yi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa da za su ga rashin kyautawar haka&#8230;&#8221; Duk a cikin babi na 22<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An kuma nusar da mu yadda ya kamata mu zauna da mutane, musamman a irin halin da muke ciki yau, kamar yadda marubuciyar ta ce, &#8216;Amma rayuwar haka take tafiya, wanda ya fi kusa da kai shi ya fi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki ba su ba ne wanda za su \u0257auki abu su baka, mutanen kirki su ne wanda za ku yi tarayya tare da su ba su cutar da kai ba. Babi na 27<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 &#8220;Babu inda ha\u0199uri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya ta\u0253a sa ki ji ha\u0199urinki ya yi yawa. Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau. Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gur\u0253ata na masu kirki&#8230;.karki bari hakan ya faru da ke kin ji?&#8221; babi na 30. Wannan shi ke koyar da mu muhimmancin ha\u0199uri da kuma dagewa akan halaye nagartattu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 &#8216;Bai san ko ka\u0257an cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a \u0199asa da sati \u0257aya bayan ya aureta ya fara kula da su, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya ha\u0257a su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba ka san ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai \u0253oyayyayun halayen da ba mutum bane yake \u0253oye su don kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi \u0199ar\u0199ashin inuwa \u0257aya ya kama suke bayyana. (Babi na 33) Wannan ya koyar da mu muhimmancin yin bincike da \u0199o\u0199arin fahimtar halin mutum tun kafin a yi aure.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022&nbsp; Sannan kuma, an nusar da mu, musamman mata da kada su dubi ku\u0257i ko wadatar wanda za su aura, amma su kasance masu wadatar zuci, kamar yadda marubuciyar ta bayyana a babi na 33 da cewa, &#8216;a wasu lokutan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshi\u0199in aurenta da samun farin ciki akan auren mai ku\u0257i, wasu kuma hange-gange shi ne yake halakar da su, ki ga mace cikin rufin asiri, kin ganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan \u0199yallin ya haska miki shi, sai ki ga kamar ta samu duk wani abu da shi ne burinki a zaman aure.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wa\u0257annan akwai \u0199ananan jigogi da dama da marubuciyar ta ta\u0253o a cikin wannan littafi irin su amintar da ke tsakanin &#8216;yan uwa, \u0199awance, zaman mace da mijinta, muhimmancin iya girki da aikace-aikacen gida ga mace, biyayya ga iyaye da kuma illar son abin duniya, musamman ga mace.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Salo da Sarrafa Harshe<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta baje basira sosai wajen bada labarin wannan littafi. Domin ta yi amfani da salo iri daban-daban kuma duk masu burgewa wajen isar da sa\u0199on labarin a sau\u0199a\u0199e.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Tafiyar Kura: Marubuciyar ta yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda ta fara bada labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi a hankali a hankali ta hanyar komawa baya ta kawo wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba. Hakan zai sa mai karatu ya dinga fahimtar batun da ake kai ko wanda za a shiga ba tare da ya sha wahala ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai jan hankali da armashi sosai da sanya nisha\u0257i ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu jan hankali, motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya da nisha\u0257i a wasu lokutan.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Koyarwa: Babban salon da aka yi amfani da shi a cikin wannan littafi shi ne salon koyarwa, an yi amfani da wannan salo sosai ta yadda a kusan kowane shafi sai ka tarar da ana&nbsp; koyar da darussa da dama da suka shafi zaman duniya, zaman ma&#8217;aurata da yadda za a zauna da ahali cikin harshe mai sau\u0199i yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sarrafa Harshe: Har ila yau an yi amfani da kalmomi masu tsima jiki, sa tausayi, kwantar da hankali da kuma gyaran tunani duk a cikin wannan littafi. Wani lokaci ma sai mai karatu ya ji kamar zaunar da shi aka yi ana mishi nasiha game yadda lamarin ke faruwa. Ko da yake an samu \u0199arancin karin magana, an samu zambo da habaici da dai sauransu a cikin wannan littafi.<\/p>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari marubuciyar ta yi amfani da sassu\u0199ar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai an samu kalmomin turanci masu \u0257an dama cikin labarin wa\u0257anda yawan da suka yi ka iya jawo na\u0199asu ga bun\u0199asar Adabin Hausa a tsakanin makaranta.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Zubi da Tsari<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta yi wa wannan littafi shimfi\u0257a mai kyau tun daga farkonsa har zuwa \u0199arshe. Da fari dai ta tsara wannan littafi ne a zubin babi-babi, daga babi na farko zuwa na 35. Sannan ya samu tsari mai kyau, domin tun daga farkon labarin aka nuna mana matsalar da ta afku a tsakanin ma&#8217;aurata kuma taurarin labarin, wato Abdul\u0199adir da Waheedah. Haka kuma an fara nuna mana halin wasu daga cikin taurarin labarin tun a babi na farko kamar su Waheedah, Abdul\u0199adir, Nuriyya, Yassar da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani abin \u0199arin armashi da burgewa shi ne, tun daga nan, duk bayanan da suka biyo baya \u0199ara fayyace labarin suke yi, kama daga wanda ake kan yi har zuwa wanda ake komawa baya a warware. Wato dai an samu zagi a tsakanin jumloli da babin labarin. Domin an fara ne da bayyana mana halin da Waheedah take ciki na rashin lafiya da kuma irin \u0199e\u0199asashshen halin mijinta wanda shi ne sanadiyar kwanciyarta a asibiti da kuma irin ro\u0199on da take mishi na ya &#8216;sau\u0199a\u0199e mata auren shi&#8217; domin ta huta.&nbsp; Sannan a gefe an hasko mana irin yadda ita kuma Nuriyya ko a jikinta bata damu da irin halin da Waheedah ke ciki ba duk kuwa da cewa ita ce babbar \u0199awarta kuma gashi ta aure mata miji.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan littafin ya ci sunan shi &#8216;ABDUL\u0198ADIR&#8217;, saboda tun daga farkon littafin babu inda ba za ka taras da sunan shi ba. Duba da cewa labarin kacokan akan wuyar shi ya rataya, lallai wannan ba zai zamo a fake ba. Sannan ita ke musu girki da wankin kayan su ko ba ranar girkinta ba ne, amma daga ranar da ta \u0199i yin wanki sai ga shi Nuriyya ta je ta \u0253ata wa Abdul\u0199adir kaya wanda hakan ya fara hasaso mana yiwuwar rabuwar su, domin mun jiyo shi ya fara yi mata fa\u0257a da cewa, &#8220;Aikin ki kenan, kullum baki san abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba. Hankalin ki bai baki ba&#8217;a ha\u0257e gaba \u0257aya kaya wajen wanki ba? Idan kin ha\u0257a wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki ha\u0257a farare da masu kala? Ke mahaukaciya ce?&#8221; (32)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Ba\u0257oki na gaske:<\/strong> &#8220;&#8230; Aure ko? Auren cin amana, a yi lafiya Abdul\u0199adir, wallahi ba baki na yi maka ba, alhakin Waheedah ba zai barku ba.&#8221; Ai kuwa alhakin bai bar su ba, domin a \u0199arshe da saki uku Nuriyya ta koma gida. (Babi na 22)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Ba\u0257oki na Giri:<\/strong> &#8220;&#8221;Ban shigo da nufin yin fa\u0257a da ke ba, har ku\u0257in hidimar gida na tura miki \u0257azun&#8230; Kin ga Azumi ya kusa, saura kwanaki ka\u0257an, ana yafewa juna kafin azumi, ba ma kyau fa\u0257a kafin azumi. Bazan iya sakin ki ba Waheedah&#8230; Ko meye nai miki me zafi haka ha\u0199uri za ki yi ki dawo. In ke za ki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi&#8230; Bazan iya ba.&#8221; (Babi na 25)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Murna:<\/strong> &#8216;Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin \u0199aunar su fal cikin ranshi, yana kuma mamaki har lokacin yadda \u0199addarar rayuwa ta kawo su inda suke yanzun. Cikin ranshi yake wa Allah godiya yana \u0199arawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci.&#8217; (Babi na 17)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Tsoro:&nbsp;<\/strong> An yi amfani da wannan dabara sosai a cikin wannan littafi ta yadda a koyaushe mai karatu cikin fargaba da zumu\u0257in jin abinda zai faru yake. Misali: &#8220;Aurenka zaka sau\u0199a\u0199e min!&#8221; (Babi na 01) haka kuma an yi amfani da wannan dabara a kusan kowane babi da ke cikin wannan littafi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Al&#8217;ajabi:<\/strong> &#8216;Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar \u0199anin nashi, har ranshi, duk tsawon shekarun nan ya \u0257auka soyayya suke da Waheedah \u0257in, yana kuma da tabbacin ba shi ka\u0257ai bane yake zaton hakan. Wani zafi ya ji \u0199irjinshi na yi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi Abdul\u0199adir \u0257in na son ta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, don yadda take tambayarshi akan Abdul\u0199adir \u0257in kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata \u0253angaren. (Babi na 15)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Tausayi:<\/strong> &#8220;Ka sau\u0199a\u0199e min aurenka, don Allah ka sau\u0199a\u0199e min aurenka.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Take fa\u0257i tana kamo hannun shi, da sauri ya ri\u0199e hannun nata yana dumtsewa, yana jin siraran yatsunta da suke barazanar \u0253allewa a kowane lokaci cikin nashi, su suka sa shi sassauta ri\u0199on da ya yi mata. &#8220;Anty ku ce ya sau\u0199a\u0199e min, don Allah ku ce Sadauki ya sake ni!&#8221; &#8220;Kun ji, ku ce kar ya fita daga \u0257akin nan bai raba ni da auren shi ba&#8230;&#8221; (Babi na 02)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>\u018aarsau na Mamaki:<\/strong> Akance sai halayya ta zo \u0257aya ake zama wuri \u0257aya ma har a \u0199ulla ala\u0199a, Abba na ganin \u0199aryar zancen a abinda Abdul\u0199adir yake fa\u0257a mishi, don ta kowacce fuska Abdul\u0199adir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yadda akai suka fara soyayyar ba. (Babi na 15)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Hoton Zuci:<\/strong> Sannan an yi amfani da dabarar saka hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa. Misali, &#8220;..<\/p>\n\n\n\n<p>Nuriyya kettle ta \u0257auka da nufin \u0257ora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen \u0257in, ga kuma ruwan da ta zubar don ta cika kettle \u0257in, ta kuma taka shi tana nufar inda socket zai yi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da ta yi sama, kettle \u0257in ma ta yi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle \u0257in a gefe da ruwan ciki da ya mungule gaba \u0257ayan shi, ita kuma akan mazaunanta ta yi warwas a \u0199asa. Ta \u0257auki wasu da\u0199i\u0199ai tana sauke numfashin wahala kafin ta ja \u0199afafuwanta ta mi\u0199e. (Babi na 31)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tauraron Labari<\/h2>\n\n\n\n<p>Babu ko tantama na san cewa ko daga jin sunan wannan littafi mai karatu zai iya fahimtar cewa babban tauraron wannan labari shi ne Abdul\u0199adir A. Bugaje. Domin bayan sunan shi da aka yi amfani da shi a matsayin sunan littafin, gaba \u0257aya matsalolin littafin in aka kasa su goma to tara da rabi shi suka yi wa zobe. Da fari dai kowa ya san irin halin shi na ba\u0199ar zuciya da tsaurin ido, amma a iya cewa matarsa Waheedah ta fi kowa ganin irin matsalolinsa, tun da har ya iya auran babbar \u0199awarta ba tare da ya fa\u0257a mata ba, kuma da ta zo gidan ta baje sha\u0199iyanci babi-babi yana kallo amma bai damu ba har sai lokacin da al&#8217;amari yayi tsami a tskananinsa da Waheedah.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Halayen Taurarin Labari<\/h2>\n\n\n\n<p>\u2022 Abdul\u0199adir ba\u0199i ne dogo mai \u0199ananan idanuwa. &#8216;Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, don gajerun cikin gidan ba su wuce su hu\u0257u ba, amma tsayin da Abdul\u0199adir yake da shi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu \u0257aya da shi. Nabbe burinsa shi ne zama soja. Tun yana da \u0199arancin shekaru yakan ce shi Soja zai zama, tun suna \u0257aukar abin \u0199uruciya har ya fara tasawa yana cigaba da jaddada musu \u0199aunar shi da aikin Soja, ko a hanya yagan su sai ya je sun gaisa. Baya son raini ko ka\u0257an, kuma yana da saurin hannu<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Waheedah siririya ce fara mai \u0257an matsakaicin tsayi. tana da kyau da in za ka tsaya ka kalleta sosai za ka ga bashi da ala\u0199a da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi take yin shi, gashi babu wanda zai ce ya ta\u0253a ganin \u0253acin ranta balle kuma fa\u0257a. Tana da ha\u0199uri sosai, wannan yasa kowa ke ganin cewa basu dace da Abdul\u0199adir ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Nuriyya na da fa\u0257a sosai, ba za ka \u0257aga mata \u0257an yatsa ka sauke ba tare da ta lan\u0199wasa shi ba, ba fara bace, za ka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma la\u0199abi da masu kalar cakuleti. Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, don kowane irin kaya Nuriyya ta sa sai ka ga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa za su iya kiranta gajera, amma a dire take, tun da &#8216;yan shekarun tan nan za ka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta \u0199arasa fitowa. Gashi fuskar nan tana \u0257aukar kwalliyar da ke \u0199ara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya ba ka sake kallonta ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Yasaar shi ne wanda ya fi kowa kusanci da Abdul\u0199adir a duk cikin &#8216;yan uwansa. Yana da ha\u0199uri sosai kuma yana son \u0257an uwan nasa, sannan shi ka\u0257ai ne yake iya fa\u0257a wa Abdul\u0199adir magana ya saurare shi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Alhaji Ahmad Bugaje mutum ne tsayayye, ba zaka rasa rikici a gidanka ba ko da mata \u0257aya ka ajiye, ballantana har hu\u0257u, sai dai suna \u0199o\u0199arin duk wani rikici da zai faru a tsakanin su ba ya \u0199arasawa kunnuwan shi sai dole. Duk abinsu suna shakkar \u0253acin ran shi, shi ya sa aka samu wadataccen ha\u0257in kai a tsakanin yaran, don suna son junansu sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hajiya Safiyya na da son girma tamkar ita ta yanke wa \u0199asa cibiya, yawan fa\u0257a, \u0257aukar zuga da son yaranta da kuma matsananciyar rowa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hajiya Halima jinin sarauta ce, hakan yasa tana da izza, ko ka\u0257an bata shiga harkar kowa, kuma ba ta \u0257aukar raini ko ya yake, za ka iya cewa tana da fa\u0257a in har ka shiga gonarta. Sannan tana da matu\u0199ar kirki da kyauta irin ta saraki.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sakina macece mai yawan ha\u0199uri da kau da kai, tana da sanyin hali da ko surutu bai dameta ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Halayen Hajiya Saratu kuwa, tana da fuska biyu, a gabanka ba ka da mai \u0199aunarka kamar ta, a bayan idonka kuwa ba ka da ma\u0199iyi kamarta, tana da gulma da ha\u0257in husuma, ga jarabtar cin bashi da Allah ya \u0257ora mata.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kurakurai da Gyararraki<\/h2>\n\n\n\n<p>An samu kuskure babba guda \u0257aya a cikin wannan littafi. Kuskuren kuwa shi ne, a farko-farkon littafin an bayyana irin yadda abin da ya faru a tsakanin Waheedah da Abdul\u0199adir&nbsp; ya jawo rashin jituwa a tsakanin shi da sauran &#8216;yan uwansa kuma har littafin ya \u0199are ba a nuna sun shirya ko ba su shirya ba. Abin da kawai aka nuna shi ne ya saki Nuriyya kuma sun koma kamar yadda suke da Waheedah da kuma hajja. Wannan shi ne babban kuskuren da aka yi, sai kuma kalmomin turanci da aka \u0257an yi amfani da su. Duk da dai su ba wasu masu yawa aka yi amfani da su ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abin Yabawa<\/h2>\n\n\n\n<p>Babban abin yabawa a cikin wannan littafi shi ne irin yadda marubuciyar ta bayyana yadda zamantakewar aure yake a wasu gidajen tare da kawo matsalolin da suke fuskanta ta hanyoyi masu sau\u0199i yadda kowa zai iya fahimta a sau\u0199a\u0199e. Sannan ta yi amfani da azancin maganganu na hikima da jan hankali wajen yin nuni da kuma kowayarwa ga mai karatu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kammalawa<\/h2>\n\n\n\n<p>A dun\u0199ule, an koyar da manya-manyan darussa ga mata da ma&#8217;aurata da ma al&#8217;umma baki \u0257aya a cikin wannan littafi. Don haka kai tsaye ina iya cewa wannan littafi ya kamata ace kowa ya same shi ya karanta, musamman ma&#8217;aurata da masu shirin yin aure, domin zai haskaka musu abubuwa da dama na zamantakewar aure.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Shawarwari<\/h2>\n\n\n\n<p>Ina \u0199ara jinjina ta musamman ga marubuciyar bisa wannan irin namijin \u0199o\u0199ari da ta yi. Kuma ina \u0199ara bata shawara akan ta \u0199ara jajircewa wajen ci gaba da kawo labarai masu koyar da darussa wa\u0257anda suka shafi rayuwar al&#8217;ummar mu.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuna iya karanta cikakken <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/abdulkadir-babi-na-daya\/\">littafin &#8216;Abdulkadir&#8217; a nan<\/a>.<\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau, kuna iya karanta <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-akan-so-na-lubna-sufyan\/\">sharhin littafin &#8216;Akan So&#8217;<\/a> daya daga cikin shahararrun littattafan marubuciyar.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Manazarta<\/h2>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y. da \u018aangambo, A. (1986) <em>Jagoran Nazarin Hausa<\/em>. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da &#8216;Yar Aduwa T.M. (1992) <em>Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1<\/em>. Ibadan: University Press Plc \u018aangambo, A. (1984) <em>Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa<\/em>. Kano: Triumph<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan Littafi: Abdul\u0199adir Marubuciya: Lubna Sufyan Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online) Shekarar Bugu: 2022 Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees) Manufar Sharhi: Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba Dangane da marubuciyar An haifi Lubna Sufyan ne a \u0199aramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-abdulkadir-na-lubna-sufyan\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin \u2018Abdulkadir\u2019 na Lubna Sufyan<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":3485,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"[\"title\",\"meta\",\"thumbnail\",\"content\",\"comments\",\"post-navigation\"]","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[42,29,43,41],"class_list":["post-3483","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-abdulkadir","tag-book-review","tag-lubna-sufyan","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/06\/Sharhin-littafin-Abdulkadir.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3483","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3483"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3483\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3485"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3483"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3483"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3483"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}