{"id":3495,"date":"2022-06-11T17:31:13","date_gmt":"2022-06-11T17:31:13","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3495"},"modified":"2022-07-13T01:35:54","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:54","slug":"fasalin-tonon-silili-a-cikin-littafin-dambarwar-siyasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/fasalin-tonon-silili-a-cikin-littafin-dambarwar-siyasa\/","title":{"rendered":"Fasalin tonon silili a cikin littafin &#8216;Dambarwar Siyasa&#8217; na gajerun labaran gasar Aminiya-Trust, 2020"},"content":{"rendered":"\n<h2 class=\"wp-block-heading\">1.0 Gabatarwa<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuta labarai na amfani da hanyoyi da yawa na bayar da labari ko gina labari a Hausa, sannan duk labarin da za a ba da ko a samar ko a rubuta ko a gina akwai hanyoyin da ake bi domin samun nasarar kai wa ga gaci. Abin lura a nan shi ne babban buri ko manufar duk masu bayar da labari ko rubutawa shi ne isar da sa\u0199o da kuma nisha\u0257antarwa, hakan kuwa bai yiwuwa sai ta hanyar amfani da hanyoyi ko wasu matakai domin su jawo hankalin masu sauraro ko karatu zuwa gare su, ta amfani da dabara ko irin salo da kuma kalmomin da suka za\u0253a domin samar ko gina labarin. Hakan ke nuna cewa matakai da ake bi domin samar ko gina labari har ya amsa sunansa su ne tubalai ko bulaluwan da suke sanya wa labari ya amsa sunansa. Daga cikin irin wa\u0257annan matakai akwai:<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\" type=\"a\"><li>Bayyanawa<\/li><li>Larabtawa<\/li><li>Jan Ra\u2019ayi<\/li><li>Gardantawa<\/li><li>Tonon Silili (Malumfashi, 2019:20-30)<\/li><\/ol>\n\n\n\n<p>Wannan ma\u0199ala za ta mayar da hankali ne a kan yin tsokaci, dangane da labaran da ake samu masu fasalin tonon silili a cikin littafin \u201c<em>Dambarwar Siyasa<\/em>\u201d wanda ke \u0257auke da gajerun labarai guda 15 da suka samu ta dalilin gasar gajerun labaran Hausa da Jaridar Aminya \u2013 Trust tare da ha\u0257in gwiwar Gandun Kalmomi da kuma Open Arts Foundation a shekarar 2020 wanda aka yi bikin ba da kyauta ga gwaraza a 5 ga wata yuni, 2021 a Hotel 17, Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">1.1 Ma\u2019anar Fasali<\/h2>\n\n\n\n<p>Fasali na nufin tsari ko shiri. Sannan fasali na zama a matsayin kashi ko yana yi (CNHN,2006:136)<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice fasali shi ne yanayi ko hanya tsarin da ake ni ko amfani da shi domin fasalta ko shirya ko tsara abu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">2.0 Ma\u2019anar Gasa<\/h2>\n\n\n\n<p>Gasa wata dabara ce ta gano ko fiddo da gwani daga cikin gwanaye. Haka kuma an \u0257auke ta a matsayin siyasa ce wadda kan sanya al\u2019amari ya bun\u0199asa, ya watsu tare da barbazuwa a tsakanin al\u2019umma ko ana so ko ba a so. (\u018aan Amarya:433)<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan ana kallon gasa a matsayin wani al\u2019amari da ake shiryawa kuma a gudanar da shi a tsakanin mutum biyu ko fiye kan wani abu ko al\u2019amari.<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice gasa hanya ce ta yin hamayya ko yin kasayya ko yin takara tsakanin mutum biyu ko fiye a kan wani al\u2019amari domin a fiddo da za\u0199a\u0199uri daga cikin gwanaye, saboda haka ana iya gudanar da irin wannan al\u2019amari na gasa ta fuskoki iri daban-daban da suka ha\u0257a da karatu da sana\u2019o\u2019i da rubutu da aure da sarauta da sauran su (\u018aan Amarya, 2019:433)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"><strong>2.1 Waiwaye Dangane Da Samuwar Gasa A Rubutattun Labaran Zuben Hausa<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Ha\u0199i\u0199a a iya cewa gasa a fagen rubutun labaran Hausa ta taka muhimmiyar rawa, idan ma ba ta zama ita silar samuwar rubutun zuben Hausa ba. Sannan hukumomi da cibiyoyi da \u0199ungiyoyi da gidauniyoyi sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da littattafan rubutattun labaran zuben Hausa Hausa ta sigar gasa tun daga da har zuwa yanzu. Tasirin hakan ya sanya har yanzu abun ke \u0199ara bun\u0199asa da samun tagomashi.<\/p>\n\n\n\n<p>A tarihin gasar rubutun zuben Hausa an fara ta ne a shekarar 1927, sai dai babu sunan labari, kuma babu labarin da aka samar. Sai gasar shekarar 1929 wadda Hukumar Inganta Al\u2019adu ta \u0199asa da \u0199asa ta samar wanda an samu sunayen labaran da aka shiga da su da marubutan labaran.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma daga gasar shekarar 1932\/1933 aka fara samun labaran zube na \u0199asa, wanda Hukumar Fassara ta sanya. Baya ga haka gasar shekarar 1978 wadda kamfanin NNPC da ke Zariya ya sanya ita ce gasa ta farko da ta fara samar da littattafan labaran zuben Hausa masu \u0257auke da fasalin soyayya.<\/p>\n\n\n\n<p>Gasar shekarar 1980 wadda Hukumar kula da Nazarin Al\u2019adu ta Tarayya ta sanya ta samar da littattafan labaran zube guda 4 da littafin wa\u0199a guda da wasan kwaikwayo 1 da littafin wasa kwakwalwa guda 1. Sai Gasar Rubutattun Labaran Zube ta shekarar 1988 wadda Hukumar kula da Kyautata Fasaha da Al\u2019adu ta sanya ta samar da littattafan zube guda shidda da aka gina su kan rayuwa ta zahiri. Akwai Gasar \u0198ungiyar Inuwar Marubuta Littattafan Hausa da ke Kano da aka yi a shekarar 2007 ta samar da littafi 3. Bugu da \u0199ari Ita kuwa gasar 2007-2009 wadda Gidauniyar Tunawa da Injiniya Bashir \u0198araye ta sanya, ta samar da littattafan labaran zube guda 9 a shekaru biyu wato a shekarar 2007 da 2008 sai littattafan wasan kwaikwayo guda 5 a shekarar 2009.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da Gasar Mata Zalla Ta Gidan Rediyon BBC mai taken \u201c<em>Hikayata<\/em>\u201d ta samar da gajerun labaran zuben Hausa da suka zama za\u0199a\u0199urai guda 18 a tsakanin shekarar 2016 (Shekarar da aka fara gasar) zuwa 2021. Sannan da \u0199arin guda 54.<\/p>\n\n\n\n<p>Wato 1 \u2013 3 a kowace shekara sannan da \u0199arin 54 a tsakanin shekarar 2016 -20121, wato daga na&nbsp;&nbsp; 4 \u2013 12 a kowace shekara, wa\u0257anda ake karantawa a shirin \u201c<em>Adikon Zamani<\/em>\u201d sai gasar PLBS da MMB ta shekarar 2018 ta samar da labaran zuben Hausa guda 15. Sai gasar Gusau Institute da aka fara daga shekara 2018 \u2013 2021 ta samar da littattafai 12. Sai gasar \u018aangiwa ta 2020 ta samar da labarai 12, da gasar Aminiya Trust ha\u0257in gwiwa da Open Arts da Gandun Kalmomi a 2020 ta samar da labaran zube guda 15. Gasar Sana\u2019a da Ilimi Foundation a shekarar 2021 ta samar da littattafai guda 5. Yayin da gasar Dar Al-Andulus a shekarar 2021 ta samar da labaran zuben Hausa guda 24.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">2.2 Gasa Mai Tsayayen Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Duk gasar da aka yi a baya ana barin jigon gasar a sake ne wato za\u0253in marubuta ne su yi rubutu kan abin da suke da sha\u2019awa, wato ba a sanya jigo ta\u0199amaimai da a kansa ake son a rubuta labarin ba. Amma daga shekarar 2013 aka fara samun gasa mai tsayayen jigo. Ga misalin abin.<\/p>\n\n\n\n<p>Gasar Makarantar Malam Bamba\u0257iya, gasa ce da makarantar ta sanya a kan jigon <em>Almajiranci <\/em>a shekara ta 2013 ( Makarantar Malam Bamba\u0257iya makaranta ce da aka assasata a shafin sadarwa na Fesbuk \u0199arkashin jagorancin Malam Ibrahim Malumfashi)<\/p>\n\n\n\n<p>Baya ga haka a shekarar 2018 Pleasant Libarary And Book Club&nbsp; Ha\u0257in Gwiwa da Makarantar Malam Bamba\u0257iya sun yi gasa akan jigon <em>Talauci<\/em> wanda aka samar da labarai guda 15 da ba da awalaja daga na \u0257aya har zuwa na sha biyar \u0257in.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a shekarar 2020, Jaridar Aminiya-Trust Ha\u0257in Gwiwa da Open Art Foundation da Gandun Kalmomi da ke Kaduna. sun gabatar da gasa akan jigon <em>Siyasa<\/em>, an bayar da kyaututtuka ga za\u0199a\u0199uran gasar sannan an buga littafi mai suna \u201c<em>Dambarwar<\/em> <em>Siyasa<\/em>\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a shekarar 2020 akwai Gasar Dangiwa Literary da aka gabatar, akan jigon<em> Muhalli da Matsalolinsa Da Ayyukan Bankin Bada Lamunin Gina Gidaje<\/em>, an bayar da awalaja ga wa\u0257anda suka samu nasara daga na 1-13, sannan aka samar da littafi mai suna \u201c<em>Muhalli Sutura<\/em>\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 2021 Cibiyar &nbsp;Dar Al-Andulus da ke Kano ta gabatar da gasa kan jigon \u201c<em>Kan Sha\u2019anin Tsaro\u201d <\/em>wanda an bayar da kyauta daga 1-5 da takardar shaida (Certificate) da buga labarai 30 da aka shiga gasar da su a cikin littafin da aka sanya wa suna \u201c<em>Gane Mani Hanya<\/em>\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 2021 Wata \u0198ungiyar Marubuta da ke Kano ta saka gasa akan jigon \u201cDogaro da Kai da Hanyoyin samar da Tsaro da Illolin Shaye-shaye\u201d gasar da aka kira da suna \u201c<em>Gasar Hikimata\u201d<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">2.3 Gasar Gajerun Labarai<\/h2>\n\n\n\n<p>Gasa a kan gajerun labaran Hausa, wani sabon shafi ne aka bu\u0257e a cikin adabin Hausa, kuma yun\u0199uri ne da zai sanya adabin Hausa ya yi gwajin kafa\u0257a da adabin Ingilishi da ma adabin kowane harshe a duniya, domin gajerun labarai sun jima da samuwa da kuma watayawa a cikin zube da adabin sauran harsuna a duniya (Malumfashi, 2019) sai dai a cikin zuben Hausa an fara samunsa a shekarar 2016 aka fara samun gasar gajerun labarai, Wato tun daga gasar Hikayata ta BBC da aka fara a shekarar 2016 har zuwa yau. Da gasar Pleasant Library and Book Club ha\u0257in gwiwa da Makarantar Malam Bambadiya (PLBC\/MMB) da aka yi a shekarar 2018. Da gasar Aminiya Trust tare da ha\u0257in gwiwar Open Arts da Gandun Kalmomi da aka yi a shekarar 2020, haka gasar \u018aangiwa ta shekarar 2020, da gasar Dar Andulus da aka yi 2021 da gasar Tsibirin Gobir ta 2022, duk labaran gajerun labarai ne da suke farawa daga kalmomi 1000 suke kuma tsayawa a kalmomi 4000 zuwa 5000. (Sabe, 2020, Gidan Marubuta,2021)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">3.0 Ma\u2019anar Tonon Silili<\/h2>\n\n\n\n<p>Tonan Silili na nufin tonon asiri ko banka\u0257en sirri (CNHN, 2006:396)<\/p>\n\n\n\n<p>A wani \u0199aulin tonon silili shi ne za\u0199ulo tare da bayyana duk wani abu da ke sakaye da ake so wasu su sani don mugunta ko fahimtarwa, yawancin irin wa\u0257annan abubuwa mutane ba su san su ba ko kuma ana kaffa-kaffa da su domin ba a son a sani, idan kuma aka bayyana su ta kowane irin fuska zai iya cutar da wani ko wasu ko wani abu ko kuma ya ankarar da wa\u0257ansu game da illa ko kyawon tsarin abun, in marubuta suka yi haka a cikin labaransu, to a nan an yi tonon silili ke nan. (Malumfashi, 2019)<\/p>\n\n\n\n<p>Ana iya kallonm tonon silili a matsayin kai wa matu\u0199a wajen tonon asiri da ake aiwatarwa cikin salo da azancin rubutu tare da goyon bayan jan ra\u2019ayi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">3.1 Fasalin Tonon Silili A Cikin Littafin Dambarwar Siyasa<\/h2>\n\n\n\n<p>A Wannan Littafi Na Dambarwar Siyasa a iya cewa fasalin tonon silili ya wataya a cikin littafin sosai domin kusan duk labarai akwai tonon silili, sai dai wani labarin an yi tonon sililin da yawa, a wani labarin kuwa ka\u0257an aka ta\u0253a. Misali:<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cNi ne kan gaba wajen kawo wa mutanen unguwa kayan masarufi domin jan hankalinsu. Ina cikin masu bin malamai da \u2018yan tsibbu domin neman sa\u2019a. Kuma ni ne lambawan wajen jagorantar matasa wajen \u0199addamar wa \u2018yan adawar da ke hamayya da mu\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Dimokura\u0257iyyar Talaka:2020:4<\/p>\n\n\n\n<p>(Rufaida Umar Ibrahim)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan ga\u0253a marubuciyar tayi tonon silili ta hanyar bayyana yadda \u2018yan siyasa ke raba kayan masarufi ga masu \u0199aramin \u0199arfi don su yaudare su su ka\u0257a masu \u0199uri\u2019a a lokacin za\u0253e, wanda da an za\u0253e su ba a sake jin ko \u0257uriyarsu. Sannan ta bayyana yadda suke bin \u2018yan tsibbu domin samun biyan bu\u0199atarsu ba tare da fawwala lamarinsu ga Allah ba, sannan da yadda suke amfani da \u2018yan daba don farmakar masu yin adawa da su. A wannan ga\u0253a an yi tonon silili dangane da mugun halin \u2018yan siyasa tun daga tushe, tun daga masu ci (Wa\u0257anda suke kan mada\u0253un iko) har masu neman takara, yadda suke da halin rowa da rashin taimakon talakawa da gajiyayyu da duk masu son taimako, musamman da abincin da za su kai bakin salati. Amma da zarar an ka\u0257a \u0199ugen siyasa sai a ga suna rige-rigen raba abin masarufi irin su kayan abinci ga al\u2019umma domin jan hankalinsu su zabe su. Kuma da sun ci ba a \u0199ara ganinsu sai wani za\u0253en ya zo wannan yaudara da sauran dangoginta haka&nbsp; marubuciyar ta tona sililinta, sannan a zahiri ma haka \u2018yan siyasa ke yaudarar mutane, sannan an tona sililin \u2018yan siyasa yadda suka yi imani da matsafa da bokaye da aka fi kira da \u2018yan tsibbu, wurin neman bu\u0199atarsu wato ba su yi imani da cewa Allah ke ba da mulki ba, sai dai \u2018yan tsibbu. A rayuwa ta zahiri `ma abin da ke faruwa ke nan har ta kai fagen da lokacin siyasa ya zo tun daga fitar da \u2018yan takara zuwa ya\u0199in neman za\u0253e, har zuwa lokacin za\u0253e akan ci gaba da cin karo da ayyuka irin su sacewa da yanke mahaukata ko kashe mutane da cire masu al\u2019aura ko wani sashe na jiki ko \u0257auke gawarwaki daga cikin \u0199aburbura ko yanke wani sashe na gawan, ko abin da ya shafi lalata da yara \u0199anana ko mahaukata mata ko luwa\u0257i ko rufe dabbobi da ran su da sauran su, wa\u0257annan abubuwa galibi ana aiwatar da su ne domin cika umurni ko wasu sharu\u0257\u0257a da \u2018yan tsibbu suka bayar ga \u2018yan siyasa domin samun mulki.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan an tona sililin yadda \u2018yan siyasa ke amfani da matasa a matsayin gugar yasa ko karnukan farautarsu masu yi musu bangar siyasa. Domin duk wanda yake adawa da su za su sanya matasa da aka lalata tunaninsu ta hanyar ba su kayan maye masu gusar da hankali da tunani da muggan makamai su \u0199addamar wa abokan adawar iyayen gidansu. A siyasa ta zahiri ma haka abin ke faruwa, yawancin lokuttan ma ana ala\u0199anta wasu ayyukan ta\u2019addanci na zubar da jini babu cas, babu as da matasa marasa tunani ke yi, tushensa daga bangar siyasa ne, bayan \u2018yan siyasa sun ci moriyar ganga sun kuma yada kwaurenta, sai matasan sun \u0257auki makamai tun da an riga an nuna masu hanya.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA je, a gabatar da za\u0253en, kuma a bayyana Nuhu Agaji a matsayin wanda ya lashe za\u0253en zan fita yanzu na yi hira da \u2018yan jarida tare da bayyana wa duniya ina goyon bayan mataimakina, ina so jibi ka fito ka yi hira da \u2018yan jarida ka shaida wa duniya cewa ka fita daga jam\u2019iyyas BSC saboda rashin adalci da aka yi muku, aka tursasa ku wajen tabbatar da Nuhu Agaji a matsayin \u0257an takara bayan shi ya zo na uku, sannan ka sanar da komawarkajam\u2019iyyar PHD, a kan kai ma za ka je neman kujerar Gwamna\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Tubka Da Warwara, 2020:12-13<\/p>\n\n\n\n<p>(Mubarak Idris Abubakar)<\/p>\n\n\n\n<p>A nan marubucin ya yi tonon silili dangane da yadda \u2018yan siyasa suke zama marasa al\u0199ibla ko masu fuska biyu har su aiwatar da ba yadda za a yi a zarge su, saboda yaddab suke wasa da \u0199wa\u0199walwa ko tunanin mutane kamar yadda aka nuna gwamna Audu Maikaji ya nuna goyon bayansa ga mataimakinsa Nuhu Agaji, sannan a sirrance ya zuga tare da tsara wa shugaban jam\u2019iyya Babangida Soja gadar zaren da za su shirya wa Nuhu Agaji ba tare da an gane ba. Wanda hakan ne ke faruwa a duniyar siyasa ta zahiri domin idan mutane sun kai dubu masu takarar kowanensu shugaba a ke\u0253ance tsakanin shi da kowa zai nuna shi yake so, sannan ana turo \u0257an takara a \u0199urarren lokaci wanda ake kira (Late comer)kuma a mara masa baya ya samu kujerar.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan a zahiri duk \u0257an siyasar da ya bar wata jam\u2019iyya yakan ce, adalci ke ba a yi masa a jam\u2019iyyar da ya baro ba. wanda galibi \u0199arya suke yi duk wanda ya nemi takara bai samu ba zai bar jam\u2019iyyar ko idan ya ga alamun jam\u2019iyyar za ta dur\u0199ushe.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA ha\u0199i\u0199anin gaskiya kuwa korona farin ciki muka yi da zuwanta. Dalili shi ne ta samar mana da hanyar \u0199afar ungulu da ku\u0257a\u0257e cikin ruwan sanyi\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Ranar \u0198in Dillanci, 2020:2(Ubaida Sani)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan \u0253angare marubuciyar ta yi tonon silili irin yadda shuwagabannin siyasar \u0199asar nan suka ci karen su babu babbaka da dukiyar al\u2019umma a \u0199ar\u0199ashin ofisoshinsu da ikonsu da sunan Korona&nbsp; wato Cutar Sar\u0199ewar Numfashi da ake fama da ita (Covid 19\/ Corona Virus).<\/p>\n\n\n\n<p>Wato duk lokacin da wata cuta ko annoba ko wani yanayi marar da\u0257i da ya faru,&nbsp; sai a yi amfani da shi ya zama hanyar takura wa al\u2019umma da cutar da su ta hanyar \u0199a\u0199aba masu wasu sharu\u0257\u0257a ko dokoki da sunan ana kare rayuwarsu ko ana matu\u0199ar kula da su&nbsp; ba a so wani abu ya cutar da su ko halaka su. Amma a ba\u0257ini da wannan cuta ko annoba ake amfani a samu ku\u0257i na tashin hankali musamman gwamnati da duk wani jam\u2019i da abin da ya shafa kai tsaye ko kaikaice. A duniyar siyasa ta zahiri ma haka abin yake ba ta canza zani ba. Domin an ga yadda gwamnati da mu\u0199arrabanta da sauran jami\u2019anta suka fantama sakamakon cutar shar\u0199ewar numfashi (Covid 19) musamman lokacin da aka gar\u0199ame jihohi (Lockdown) duk da cewa al\u2019umma sun shiga wani irin hali na tasku. A zahiri abubuwa da ke faruwa na annoba ko cuttuka sukan zama azaba ga al\u2019umma amma hatimin sa\u2019a ko rahama ga gwamnati da kuma duk wanda abin ya shafa. Misali watanda a faruwar abubuwa irin Allurar shan inna (Polio) da murar tsuntsaye (Bird flu) da cutar Ebola da Zazza\u0253in \u0181era (Lassa Fever). Duk a faruwar wa\u0257annnan abubuwa an takura al\u2019umma da cutar da ita da wai ana sunan ana sonta, yayin da gwamnati da jami\u2019anta ke darawa da sam barka da faruwar yanayin sakamakon romon da ake sha daga masu kawo tallafi na \u0199asashen \u0199etare da ku\u0257a\u0257en da ke fita lalitar gwamnati da sunan da\u0199ile yanayin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201c&#8230;&#8230;&#8230;&#8230;&#8230;..Don haka kowane manomi ya gaggauta zuwa bankin manoma domin bude bu\u0257e asusu. Gwamnati ta ware miliyan \u0257ari biyu domin wannan tallafin. Kuma manoma dubu biyu ne za su ci moriyarsa\u201d. Cikin murmushi Malam Nasiru ya dube shi \u201cHonarabul bana za a bayar da tallafin da gaske kenan?\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Dariya sakatare ya yi. \u201cAshe har yanzu Nasiru ba ka gama sanin siyasa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Komai Nisan Dare, 2020:30<\/p>\n\n\n\n<p>(Yaseer Kallah)<\/p>\n\n\n\n<p>A nan marubucin ya tona sililin \u2018yan siyasa yadda suke fitowa a kafafen ya\u0257a labarai su yi bayanan karya da yaudara da nufin za a taimaki manoma, su yi ta wahakar da bayin Allah sunan sanya masu rai alhaki \u0199arya da yaudara ce suke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da cewa a gwamnatance ana fitar da ku\u0257in da sunan an ba da tallafin noma, amma kashe mu raba ake yi ko sisin kobo ba a ba asalin manoman da aka fitar da ku\u0257in da sunansu, ko kuma a \u0257aya ko \u0253alli cikin kaso \u0257ari.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka abin ke faruwa a duniyar siyasa ta fili, domin akan fito da tsarin tallafawa manoma a sanya su bu\u0257e asusun ajiya a bankuna da samar da \u0199ungiyoyi, irin \u0199ungiyar manoman alkama da masara da shinkafa ko \u0199ungiyar manoman noman rani da sauran, wanda idan an fitar da ku\u0257in daga aljihun gwamnati, sai wasu jami\u2019an gwamnati su karkatar da ku\u0257in, ko kuma a yi kashe mu raba da galibin shuwagabannin manyan \u0199ungiyoyin manoman, sai a bar \u0199ananan manoma da hamma da tsammani ko jiran gawon shanu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cGanin tafiyar Farfesa ta samu kar\u0253uwa a birane da \u0199auyuka, ba\u0199in ciki hassada suka \u0199ara turnukezukatan su Alhaji Isiya a karshe dai suka yanke shawarar kawar da shi daga doron \u0199asa\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Hassada Ga Mai Rabo, 2020:40<\/p>\n\n\n\n<p>(Mustapha Sufyanu Jikan Malam)<\/p>\n\n\n\n<p>Marubucin ya bayyana yadda \u2018yan siyasa ke yi wa mutumin kirki idan ya fito takara ya samu kar\u0253uwa wato ko dai su yi kisan mummu\u0199e ko su yi wa mutum sharri ko su tsara yadda za su kashe shi ba tare da kowa ya sani ba domin samun biyan bu\u0199atarsu, kamar yadda aka yi wa Farfesa duka.<\/p>\n\n\n\n<p>A duniyar siyasa akan yi wa \u0257an siyasa sharri ne daga abokan hamayyarsa da suke ba a jam\u2019iyya \u0257aya, amma sharrin cikin gida shi ake kira \u201cyarfe\u201d ko \u201cyarfen siyasa\u201d wanda ma\u0199iya na cikin jam\u2019iyya ke yi wa wanda ba su so ko wanda ya fi su kar\u0253uwa ko samun goyon baya daga jama\u2019a kamar yadda ake tuggun da su Alhaji Sambo da Alhaji Isiya suka yi wa Farfesa, haka abin ke faruwa a zahiri a duniyar siyasa, domin kuwa masu azancin magana na cewa \u201cda \u0257an gari a kan ci gari\u201d\u2019 kuma munafukinka na gindinka\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cLokacin za\u0253e ya zo muka yi masa magu\u0257i ya ci za\u0253e domin ya saki ku\u0257i sosai. Shekara biyu bayan ya ci za\u0253e babu aiki guda \u0257aya da zai nuna. Matasa ba aikin yi, mu da ya yi wa al\u0199awarin aiki ko ganinsa ba ma yi\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Baki Guba Ne, 2020:51<\/p>\n\n\n\n<p>(Basira Sabo Nadabo)<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar a nan ta yi tonon silili dangane da yadda \u2018yan siyasa ke amfani da matasa &nbsp;a matsayin gugar yasa domin cimma muradunsu na siyasa daga baya su watsar da su bayan romon baka da suka yi masu, kamar dai yadda abun yake a cikin wannan labari. Kuma ko a zahirance haka \u2018yan siyasa ke aiwatar da tsarin tsakaninsu da wa\u0257anda suka yi masu hidima, sukan yi wa al\u2019umma musamman matasa masu goyon bayansu \u0199aryar za su ba su jari ko samar masu aikin yi, ko hidimta masu a cikin harkokin rayuwa. Amma bayan sun tura motar ta tashi, sakamakonsu shi ne a buce su da \u0199ura ko a fesa masu haya\u0199i a bar su da \u0199auri da wato dai haka za a bar su, babu aikin yi, babu jari, babu tallafi, babu magana mai da\u0257i, wasu ma daga ranar sun gama ganin \u0257an siaysar gaba da gaba, kuma ko wayarsa suka buga idan sun yi sa\u2019a ta shiga ma ba zai \u0257auka ba. Wasu kuwa ko lambar wayar \u0257an siyasar mai yi ba za su samu ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cTana cikin zaman jiran nan ne sai ta fara bibiyar takardun, ta ga ashe bajat ne wanda aka fitar wa \u0199aramar hukuma. Ba ta san lokacin da ta doka salati ba, saboda yadda aka re\u0257e ku\u0257a\u0257e masu yawa a cikin bajat \u0257in, aka karkatar da su ta wata hanyar yaudara\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Tsaka Mai Wuya, 2020:56<\/p>\n\n\n\n<p>(Salim Yunusa)<\/p>\n\n\n\n<p>Tonon sililin a nan ya shafi yadda \u2018yan siyasa ke wanda\u0199a da ku\u0257a\u0257en al\u2019ummar da suke mulka ta hanyar \u0199arya da yaudarar tsara kasafin ku\u0257i a takarda, amma a zahiri a yi kwana da ku\u0257in. Wannan yaudara ta zama ruwan dare ga \u2018yan siyasa yadda ake ha\u0257a baki da masu ruwa da tsaki a yi kashe mu raba.<\/p>\n\n\n\n<p>Irin wannan kitimirmira haka take faruwa a duniyar siyasa ta zahiri, ko a sake maimaita kasafin ku\u0257in da ya gabata, domin a cire ku\u0257i fiye da sau \u0257aya, abin da ake kira \u201cCushen Kasafin Ku\u0257i\u201d da \u201cKasafin ku\u0257in boge\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cKi yi shiru ki saurare mu, munafuka. Mun san ki, mun kuma san inda gidanku yake. Ko ki janye takararki, ko kuma duk abin da ya same ki, to ke kika sayo wa kanki da hannunki\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Kawalwalniya, 2020:61<\/p>\n\n\n\n<p>(Mujaheed Ameen Lilo)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan fasali tonon sililin ya ji\u0253nci yadda \u2018yan soyasa ke yin amfani da \u2018yan ta\u2019adda suna yin barazana da nufin salwantar da rayukan abokan hamayyarsu ko cutarwa ga ahalinsu, kamar yadda aka yi wa Badariyya. Wanda hakan ke sanyawa wani lokaci sai dai kawai a ji \u0257an takara mai farin jini ko wanda al\u2019umma ke so ya shelanta janyewarsa daga takara, a rasa me ya sanya faruwar hakan, ba a san a sirrance aka yi masa barazanar kisa ko cutarwa ga ahali ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Wanda a zahiri hakan ta sha faruwa dangane da siyasa ta zahiri, hasali hakan ma abu ne wanda ya zama ruwan dare a duniyar siyasa ta zahiri.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cUmmi! Kin tuna irin cin kashin da Alhaji Bukar ya sa akka yi miki a kafafen sada zumunta lokacin da kike jam\u2019iyyar ANC?\u201d Hajir ya fa\u0257a bayan ya ri\u0199o hannayenta. Sannan ya ci gaba da cewa \u201cHaka ya sa aka yi wa Daddy. Yanxu ke ce abin son su tun da kin bar ANC kin dawo FAN\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Kazar Kwanci,2020:71<\/p>\n\n\n\n<p>(Maryam Umar Sakkwato)<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta yi tonon silili dangane da halin rashin kunya da rashin dattako na \u2018yan siyasa irin yadda suke cin mutuncin juna idan akwai bambancin Fati a tsakanisu, amma idan sun ha\u0257e a Fati \u0257aya sai su nuna wa duniya su masoyan juna ne. Har ana rungumar juna a gaban jama\u2019a don nuna \u0199auna da soyayya. Wannan kuwa haka abin yake a zahiri domin ha\u0257uwar jam\u2019iyya \u0257aya ga \u2018yan siyasa ita ce dangantaka mafi \u0199arfi.sannan duk soyayya ko \u0199iyyar \u2018yan siyasa tana cikin jam\u2019iyyar idan ana a jam\u2019iyya \u0257aya an zama masoya, idan an raba jam\u2019iyya an zama ma\u0199iya<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cA jiya da hantsi, kamar yadda kuka ji labarin taho-mu-gama da \u2018yan bangar siyasa mabambanta ra\u2019ayoyi suka yi, lokacin na ziyarci gidan Almustapha inda yake ba ni labarin yadda ya \u0257ora burinsa a kana Zulaihat wadda ke \u0199o\u0199arin a makaranta, da kuma son a daina muzgunawa \u2018yan uwanta mata. Kwatsam! Sai ga shi an kawo gawar Zulaihat wai \u2018yan bangar siyasa sun sassare ta a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>Ci Ga Rashi, 2020:84<\/p>\n\n\n\n<p>(Isma\u2019il Gambo)<\/p>\n\n\n\n<p>A nana tonon sililin ya shafi yadda \u2018yan siyasa ke amfani da \u2018yan bangarsu, suna zubar da jinin al\u2019umma domin biyan bu\u0199atarsu ta neman mulki da hawa mulkin ko ta halin \u0199a\u0199a tare da maida \u2018ya\u2019yan talakawa karnukan farautarsu. Amma kuma saboda son kai ba su sanya \u2018ya\u2019yansu a cikin irin wa\u0257annan miyagun ayyukan. Sannan ko siyasa ta zahiri haka abin ke faruwa, ba wai ayyukan zubda jini ba, a siyasa ta zahiri \u2018yan siyasa ko ya\u0199in neman za\u0253ensu ba su zuwa da \u2018ya\u2019yansu da matansu, ba a li\u0199a fastar \u0257an takara a \u0199ofar gidan ko \u0199ofar gidan \u2018ya\u2019yansa, wasu ko a motocin su na hawa ba a sanya fastar takararsu sai dai motocin ya\u0199in neman za\u0253e da motocin yaku-bayi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cSiyasa kasuwa ce, duk abubuwan da na \u0199irgo ba wanda zan yi, ba ni da hankali ne, sau uku fa ina nema, ina fa\u0257uwa. Daga hawa kawai sai in \u0253uge da ayyuka, tun ban fanshe ku\u0257in da na kashe a kamfen ba\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Kotun Allah Ya Isa!,2020:104 (Rufa\u2019i Abubakar Adam)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan ga\u0253a marubucin ya tona sililin \u2018yan siyasa dangane da manufarsu da halinsu na yaudarar al\u2019ummar da suka za\u0253e su, wato abin da suka furta za su yi daban, abin da kuma suke yi a zahiri daban. Haka abin yake a siyasa ta zahiri. Galibin \u2018yan siyasa sun \u0257auketa a matsayin kasuwa da suke aiwatar da kasuwancinsu, saboda haka hannun jari ne suka zuba, duk abin da suka kashe a lissafe suke da shi,&nbsp; idan sun ci kujerar, sai sun maida ku\u0257a\u0257ensu sun lissafa riba kafin su iya yi wa al\u2019umma wani abin kirki. Wasu \u2018yan siyasar ma kai tsaye suke fa\u0257a su ce \u201csayen kujerar ko takarar suka yi, saboda haka dole ne su maida ku\u0257in da suka kashe\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cKa gaggauta ficewa daga gida domin an turo \u2018yan ta\u2019adda su kashe ka\u201d. Nabila ta sanar da Abubkar Mai-Allah, \u0257an takarar jam\u2019iyyar NCC ta wayar salula\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Za\u0253in Allah, 2020:107<\/p>\n\n\n\n<p>(Faridat Husain Mshelia)<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda aka ambata a baya, a nan madai tonon sililin ya shafi yadda \u2018yan siyasa ke amfani da \u2018yan ta\u2019adda suna kashe abokan adawarsu. Wannan na nuna cewa kisa shi ne abu mafi sau\u0199in aiwatarwa ga \u2018yan siyasa tsakanin su da abokan hamayyarsu. Ko a rayuwar siyasa ta zahiri yana daga cikin babban kudirin \u2018yan siyasa barazanar kisa ko aiwatar da kisa ga abokan hamayyarsu wanda ya fi su cancanta ko wanda ake ganin mutumin kirki ne, kuma za\u0253in mutane. Kuma haka ya zama ruwan dare.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cKusan duk garin da muka je, idansuka fa\u0257i matsalarsu sai na fashe da kuka na munafunci. Tabbas kuksan nawa ba \u0199aramin karya musu zuciya yake yi ba tare da \u0257arsa soyayyata a zuciyarsu\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Tsalle \u018aaya,2020:120<\/p>\n\n\n\n<p>(Nasiru Kainuwa Ha\u0257ejia)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan ga\u0253a fasalin tonon sililin ya shafi amfani da yaudara da \u2018yan siyasa ke yi a lokacin ya\u0199in neman za\u0253e ta sigar jan ra\u2019ayi.<\/p>\n\n\n\n<p>Yadda suke ribatar mutane dangane da wasu halayensu na kirki da aka sani, ko wasu ayyuka ko sadaukarwa da suke yi wa al\u2019umma kamar aikin gayya ko kula da tarbiyyar \u2018ya\u2019yansu ko koyarwa a Islamiyya, domin su samu tausayawar mutane da amincewarsu, wanda sai bayan sun amince, sai munanan halaye su bayyana, ashe daman \u201ckowane gauta ja ne\u201d rashin rana ce ta sanya ba a gane.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka abin yake a rayuwar siyasa ta zahiri akwai masu addini da malaman islamiyya da dama da suka samu tausayawar mutane aka za\u0253e su da tsammanin za su yi wa al\u2019umma mulkina adalci a \u0199arshe suka yaudare su suka ci amanarsu kamar yadda ta kasance a wannan labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cAllah ya gafarta Malam, idan muka ci za\u0253e akwai tanadin kujerun Hajji da Umara kai da almajiranka, duk shekara. Sannan akwai mu\u0199ami na musammana da za a ba yar\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Yanayi,2020:125<\/p>\n\n\n\n<p>(Habib Sani Yahaya)<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan \u0253angare , marubucin ya bayyana wani salon yaudara da \u2018yan siyasa ke amfani da shi wajen jawo malamai na addini da shafa masu mai a baki ta hanyar yi masu alkawarin \u0199arya, domin su je su yi masu kamfen da addu\u2019o\u2019i.<\/p>\n\n\n\n<p>A rayuwar siyasa ta zahiri wannan abin shi ake ya yi, wato yadda \u2018yan siyasa ke amfani da malaman addini na musulunci da kiristanci da jawo su a jika da yi masu al\u0199awuran \u0199arya da yaudara, domin su amfana da matsayinsu wurin yi masu ya\u0199in neman za\u0253e da yi masu zabarin \u0199uri\u2019u ga magoya bayansu a coci\/majami\u2019u da masallatai domin cikar burinsu na \u0257arewa a kan kujerunsu, daga \u0199arshe su bar rikici tsakanin malaman addinan da \u0257alibansu ko magoya bayansu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">4.0 Kammalawa<\/h2>\n\n\n\n<p>A \u0199arshe a iya cewa fasalin tonn silili ko salon amfani da tonon silili a cikin hanyoyi ko matakan ba da labari ya mamaye littafin \u201cDambarwar Siyasa\u201d tun daga farko har karshe. Sannan sa\u0199on ya isa ta wannan fasali kuma hakan ya nisha\u0257antar.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Manazarta<\/h2>\n\n\n\n<p>CNHN, (2006).<em>\u0198amusun Hausa<\/em> <em>Na<\/em> Jami\u2019ar Bayero Kano. Zaria:Ahmadu Bello University Press<\/p>\n\n\n\n<p>Dambarwar Siyasa (2021) Aminiya-Trust, Gandun Kalmomi, Open Arts Foundation. Kaduna:Tast And Print Ventures<\/p>\n\n\n\n<p>Malumfashi, I. (2019), (ed). <em>Labarin Hausa A Rubuce<\/em>. Zaria: Ahmadu Bello University Press<\/p>\n\n\n\n<p>Malumfashi, I. (2019) Laccar Kwas \u018ain Hau 817 (Modern Hausa Fiction) .Kaduna:Jami\u2019ar Jihar Kaduna<\/p>\n\n\n\n<p>Malumfashi, I. (2019) Laccar Kwas \u018ain Hau 818 (Narratology) .Kaduna: Jami\u2019ar Jihar Kaduna<\/p>\n\n\n\n<p>Mujallar Inuwar Marubuta, (2008). Kano:Anka-Graphic Fagge<\/p>\n\n\n\n<p>Mujallar Malami, (2018) Shafi Adabi.Katsina:Pleasant Libarary And Book Club<\/p>\n\n\n\n<p>Sabe, B. A.(2020) (ed) Muhalli, Sutura. Katsina:Darma Digital Prints<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>1.0 Gabatarwa Marubuta labarai na amfani da hanyoyi da yawa na bayar da labari ko gina labari a Hausa, sannan duk labarin da za a ba da ko a samar ko a rubuta ko a gina akwai hanyoyin da ake bi domin samun nasarar kai wa ga gaci. Abin lura a nan shi ne babban&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/fasalin-tonon-silili-a-cikin-littafin-dambarwar-siyasa\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Fasalin tonon silili a cikin littafin &#8216;Dambarwar Siyasa&#8217; na gajerun labaran gasar Aminiya-Trust, 2020<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":7,"featured_media":3503,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[29,44,41],"class_list":["post-3495","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-book-review","tag-dambarwar-siyasa","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/06\/Dambarwar-Siyasa.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3495","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/7"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3495"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3495\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3503"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3495"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3495"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3495"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}