{"id":3505,"date":"2022-06-17T12:57:38","date_gmt":"2022-06-17T12:57:38","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3505"},"modified":"2022-07-13T01:35:53","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:53","slug":"salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-2\/","title":{"rendered":"Salon bayar da labari da salon ginin labari 2"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alarmu da ta gabata, mun tsaya da bayani ne a kan <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-1\/\">salon bayar da labari<\/a>, inda muka ce salon bayar da labari ya kasu zuwa gida biyu. Akwai salon tauraro cikin fage, da kuma salon tauraro wajen fage.<\/p>\n\n\n\n<p>Mun bayyana yadda salon bayar da labari na tauraro cikin fage, wato labarin da ake bayarwa ta bakin shi tauraron yake. Sannan mun fara jero wasu \u0199a&#8217;idoji da muka ce ana kula da su a cikin irin salon, wa\u0257anda da su ne yanzu za mu \u0257ora a wannan sabuwar ma\u0199alar da amincewar Allah.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022<strong>Iyakar da ta shafi shekaru<\/strong>: A wannan salon kuskure ne tauraro ya bayar da labarin abin da ya girme wa shekarunsa, da abin da bai girme wa shekarun nasa ba amma dai lokacin da abin ya faru yana jariri, ko yaro daga shekara \u0257aya har zuwa shekara bakwai. Saboda yaro ba zai yiwu ya san me yake faruwa ba balle har ya iya ri\u0199ewa ya ba da labari, idan ma ya sani zai manta indai bai wuce shekaru bakwai ba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;<em>Lokacin ina jariri na yi farinjini, don kuwa duk wanda ya gan ni sai ya \u0257auke ni yana mini wasa, ga shi kuma dama kullum cikin tsafta nake.&#8221;<\/em>&nbsp;&nbsp; Irin wannan misalin kuskure ne kamar duk sauran misalan, sai dai shi ma a yi masa dabara, a nuna cewa labari aka ba wa tauraron, misali:<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;<em> An ce fa da ina yaro na yi farinjini, wai duk wanda ya gan ni sai ya \u0257auke ni, saboda kullum tsatsaf nake.<\/em>&#8221; Hakan ba kuskure ba ne tunda labari aka ba ka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022Iyaka dangane da mutuwa<\/strong>: Kuskure mafi girma da za a samu a wannan salon bayar da labarin shi ne a ji shi mai bayarwar ya mutu. Babu yadda za a yi a irin wannan salon daga karshe a nuna tauraron labarin ya fadi ya mutu. Idan haka ta faru to wanene zai karasa labarin kenan? Idan kuma labarin ya je har \u0199arshe ta yaya aka yi matacce ya ba da labarin?<\/p>\n\n\n\n<p>Sai dai kamar dukkannin misalan baya, ana iya yin wata dabarar a kashe tauraron. Misali ana iya cewa shi tauraron ya gama rubuta labarin nasa ne gaba\u0257aya a wani littafi, don haka littafin nasa wani ya karanta ya samu labarinsa tun kafin ya mutu, wata\u0199ila ma labarin dalilin mutuwarsa ko kashe kansa labarin ya \u0199unsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka nan idan ma ba a gama labarin ba to marubuci yana iya yin dabara ya \u0257ora alhakin \u0199arasa labarin a kan shi wanda ya karanta labarin, ta yadda zai yi ta bibiyar &#8216;yan&#8217;uwa da abokai da kuma wa\u0257anda labarin ya shafa don ha\u0257a kan \u0199arshen labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>Da wannan kuma muka kawo \u0199arshen dokokin da za mu tattauna game da salon bayar da labari a \u0199ar\u0199ashin salon tauraro cikin fage. Yanzu kuma za mu matsa zuwa gaba insha Allahu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Salon ginin labari <\/h2>\n\n\n\n<p>Wannan salon ya \u0199unshi tubalan gini har guda shida kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Mi\u0199a\u0199\u0199en salo<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo tafiyar kura<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sassau\u0199an salo<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo \u0257anmagori<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ragon salo<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo mai karsashi<\/p>\n\n\n\n<p>Za mu \u0257auki kowanne \u0257aya bayan \u0257aya mu tattauna insha Allah.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Mi\u0199a\u0199\u0199en salo<\/strong>: Tun daga yanayin sunan wannan salo muna iya hasaso al\u0199iblarsa, saboda duk abin da aka ce mi\u0199a\u0199\u0199e to a mi\u0199e yake sam\u0253al kamar rula babu wani bau\u0257iya ko kwana-kwana. Labari ya kan amsa wannan suna ne idan ya zamana babu kwan gaba kwan baya, haka nan babu cukurkudewar zarurruka a cikinsa, kenan dai an \u0257akko shi daga farkon samuwarsa zuwa \u0199arshen ti\u0199ewarsa. Kamar daga haihuwar tauraron zuwa mutuwarsa ko kuma wani wuri da aka \u0199ar\u0199are labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>Mafi yawan labaran da aka gina su da mi\u0199a\u0199\u0199en salo ana \u0257ora labarin ne kai-tsaye a kan tauraron labarin, wato shi yake kwashe kaso casa\u2019in da doriya na labarin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Salo tafiyar kura<\/strong>: Shi kuma wannan salon kishiyar salon farko ne, a mi\u0199a\u0199\u0199en salo mun ce ana farawa ne daga farkon labari, shi kuma wannan salon ana fara labari ne daga tsakiya ko karshe sannan a koma farko sai a sake komawa karshe. Wato labarin zai tafi ne kamar yadda kura take tafiya.<\/p>\n\n\n\n<p>An ce kura ba ta tafiya kaitsaye, sai ta yi ta kwana-kwana. Idan za ta je gabas sai ta fara yin kudu sannan ta dawo yamma sannan ta koma arewa, daga nan sai ta yi gabas. To shi ma rubutu mai irin wannan salon na tafiyar kura haka ake sa\u0199a zararrukansa ta hanyar yin wasa da hankalin mai karatu, sai an yi gaba da tunaninsa kamar za a kai shi gabas, sai a dawo da shi yamma a ba shi wani labarin da ya faru kafin wanda ake kan ba shi. Wannan salon ya fi kowanne salo tasiri wajen rike mai karatu musamman idan salon ya ha\u0257u da gwani.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Sassau\u0199an salo<\/strong>: Shi ma wannan salon daga sunansa ana iya fahimtar hanyar da ya bi, irin wannan salon shi ne salon da aka yi amfani da sassau\u0199ar Hausa da zubi da tsari, maganganun taurari da ayyukansu, ta yadda makaranci ba zai sha wata wahala ba wajen fahimtar yadda ginin labarin yake. Yawancin irin wannan salon labarin, manazarci mai hikima yana iya hasaso abin da ya \u0199unsa, wanda hakan yana daga cikin raunin labari a iya hasaso abin da ya \u0199unsa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Salo \u0257anmagori<\/strong>: Kamar yadda muka sani idan an ce &#8216;\u018aanmagori&#8217; shi ne mai wasa kansa da kansa, to shi ma wannan salo kwatankwacin hakan ne domin dai marubuci ne da kansa yake fitowa a matsayin \u0257aya daga cikin jaruman labarin ya yi ta ba ka labarin abubuwan da suka faru a kansa, wanda kuma da cikakken sunansa yake amfani. Misalin irin labari mai wannan salo akwai labarin <em>Gan\u0257oki&nbsp;&nbsp; <\/em>na Bello Kagara, <em>Ruwan Bagaja<\/em>&nbsp;&nbsp; na Abubakar Imam ko labarin <em>Kukan Jini<\/em>&nbsp;&nbsp; nawa da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Ragon salo<\/strong>: Shi wannan salon shi ne salo mai gundura wanda idan aka yi amfani da shi da kyar makaranci yake iya karanta littafin yayin da wani makarancin ma da ya fara yake ajiyewa. Yawancin abubuwan da suke mayar da salo ya zama rago sun hada da; yadda marubuci zai yi ta \u0199ago masifu yana lafta wa jaruminsa ba tare da jarumin ya yi wani kuskure ba, \u0199aga abubuwan da ba za su ta\u0253a iya faruwa ba da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u2022 Salo mai karsashi<\/strong>: Wannan wani salo ne da ake amfani da kalmomi na azanci da gwanintar harshe cike da barkwanci, ko wasu kalmomi na nisha\u0257i da kan saka karsashi da tsayawa a ran mai karatu ta yadda zai ri\u0199a jin yana so ya maimaila labarin saboda yanayin yadda aka bayar da shi, musamman wajen kwatantawa, siffantawa da kamantawa. Karatun labari mai irin wannan salon yana sanya nutsuwa da son maimaita karanta littafin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Abin lura<\/strong>: Ko ma dai wani irin salo marubuci ya yi amfani da shi ana so ya kula sosai ta yadda zai ri\u0199a goce wa hasashe ko iya hakaito \u0199arshen labarin daga manazarta. Daga cikin manyan rauni ko nakasu da yake hana labari armashi ko samun maki masu yawa a cikin gasa shi ne iya fahimtar akalar labarin na abin da zai faru a gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan matsalar ba &#8216;yar \u0199arama ba ce, &#8216;kamar yadda idan uwargida ta yi la\u0253e a \u0257akin amarya ta ji hirar da kuka yi idan ita ma ka je \u0257akinta za ka yi mata irin wannan hirar ba za ka burge ta ba haka shi ma wanda yake iya hakaito \u0199arshen labarinka ba za ka burge shi ba.&#8217; Wani lokacin ma wasu na iya jefar da labarin su ha\u0199ura da karanta shi ba tare da sun wani damu ba, ba don komai ba sai don za su iya \u0199arasawa kansu labarin a zuciyarsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma idan ya zamana labarinka yana zuwa da sa\u0253anin hasashen mai karatu, zai zamana kamar wanda ya yi tunanin za ka ba shi naira \u0257ari ne kai kuma sai ka ba shi dubu \u0257aya. Ko kuma ya tsammaci ka kai shi yawan sha\u0199atawa kai kuma ka kai shi Madina. Zaka tarar \u0257okinsa da \u0199aunar shi ga labarin ninkuwa suke yi a duk shafin da ya bu\u0257a.<\/p>\n\n\n\n<p>Don haka yana da kyau matu\u0199a mu sani cewa wannan ga\u0253ar tana kankaro mutuncin labari yadda ya kamata, musamman labarin gasa. Mu ri\u0199a yin \u0199o\u0199ari matu\u0199a wajen ba wa makarantanmu \u0199afa, ta yadda za su kasa fahimtar al\u0199iblarmu. Mu ri\u0199a yin rubutu kamar fa\u0257an \u0257andambe mai hikima, wanda zai yi kamar zai naushi abokin dambensa da hannun dama sai ya sauya ya naushe shi da hannun hagu. Ko kuma labarin namu ya zama kamar gidan kurege, ta yadda sai an tsaya a bakin \u0199ofar shi ana yi masa haya\u0199i da tunanin ya fito ta \u0199ofar za a ga ya faso wata \u0199ofar ta inda ba a zata ba ya gudu.<\/p>\n\n\n\n<p>A nan za mu dakata, amma kuna iya karanta makala ta gaba akan <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/hadakar-salo-sama-da-daya-wajen-samar-da-labari\/\">hadakar salo sama da daya wajen samar da labari<\/a>. Kamar kullum, \u0199ofar gyara, sharhi, \u0199arin bayani ko tambaya a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alarmu da ta gabata, mun tsaya da bayani ne a kan salon bayar da labari, inda muka ce salon bayar da labari ya kasu zuwa gida biyu. Akwai salon tauraro cikin fage, da kuma salon tauraro wajen fage. Mun bayyana yadda salon bayar da labari na tauraro cikin fage, wato labarin da ake bayarwa&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-2\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Salon bayar da labari da salon ginin labari 2<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3508,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,8,27,19],"class_list":["post-3505","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-rubutun-labari","tag-salon-labari","tag-writing-tips"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/06\/Salon-bayar-da-labari-2.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3505","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3505"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3505\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3508"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3505"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3505"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3505"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}