{"id":3530,"date":"2022-06-26T15:52:31","date_gmt":"2022-06-26T15:52:31","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3530"},"modified":"2022-07-13T01:35:52","modified_gmt":"2022-07-13T01:35:52","slug":"hadakar-salo-sama-da-daya-wajen-samar-da-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/hadakar-salo-sama-da-daya-wajen-samar-da-labari\/","title":{"rendered":"Hadakar salo sama da daya wajen samar da labari"},"content":{"rendered":"\n<p>Hadakar salo shi zamu tattauna a yau. A ma\u0199alar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan salon bayar da labari, da kuma yadda marubuci zai ri\u0199a yin rubutu cikin hikima ta yadda zai ri\u0199a goce wa hasashen manazarcinsa wanda ka iya hakaito \u0199arshen labarin ya rage masa armashi.<\/p>\n\n\n\n<p>Mun bayyana yadda salon bayar da labari na tauraro cikin fage, wato labarin da ake bayarwa ta bakin shi tauraron yake, sannan mun bayyana dokoki da \u0199a&#8217;idoji da muka ce ana kula da su a cikin shi irin wannan salon a yayin rubutu. Haka nan mun tattauna a kan salon bayar da labari na tauraro wajen fage, wanda shi ma mun bayyana irin dokoki da \u0199a&#8217;idoji da ake so marubuci ya kula da su a yayin yin amfani da salon. Duba<strong>&nbsp;<\/strong><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/salon-bayar-da-labari-da-salon-ginin-labari-2\/\"><strong>salon bayar da labari<\/strong><\/a>&nbsp;don tunawa sai ka \u0257ora.<\/p>\n\n\n\n<p>A wannan ma\u0199alar za mu tattauna ne a kan&nbsp;<em>ha\u0257akar salo sama da \u0257aya wajen samar da labari<\/em>. Ita ma wannan ga\u0253ar tattaunawa ce mai muhimmanci, amma bari na yi mana wani kwatance ko bayanin da zai fito mana da muhimmancin da nake fa\u0257a.<\/p>\n\n\n\n<p>Na san za ku yarda da ni cewa idan aka samu \u0199wararriyar mace a fagen girki, aka ba ta tsurar shinkafa aka ce ta dafa, za ta iya dafawa har shinkafar ta yi da\u0257i a ci cikin armashi. To amma yaya kuke tunanin abin zai zama idan ba a ba ta tsurar shinkafa ba aka ha\u0257a mata da wani abin ha\u0257in, kamar wake, ko doya, ko dankali, da su kifi da nama, da tumatir da kayan ganyaye da mai da sauransu aka ce ta ha\u0257a da wannan shinkafar ta tashi girki? Na tabbata indai har \u0199wararriyar ce girkin da za ta yi da kayan ha\u0257in da yawa sai ya fi da\u0257i da burgewa a kan girkin tsurar shinkafa da za ta dafa.<\/p>\n\n\n\n<p>To kamar haka ne labarin da aka sa\u0199a shi da salo \u0257aya tamkar shinkafar da aka dafa ta tsura ce, haka nan labarin da aka \u0199ayata shi da salo mabanbanta wajen gina shi tamkar shinkafar da aka ha\u0257a ta da wake ko wani abin ha\u0257in da nau&#8217;in su kifi ko nama da kayan ganye wajen girka ta ne. Idan mun iya hakaito fifikon a zukatanmu, to bari mu tafi kai tsaye zuwa ga\u0253ar yadda ake ha\u0257a mabanbanta salon ya ba da irin wannan armashin a labari.<\/p>\n\n\n\n<p>Zan \u0257akko mana wani labari mai suna&nbsp;<em>Sawun <\/em><em>\u0181<\/em><em>arawo<\/em>, wanda a cikin farkonsa nake so mu yi darasin namu na yau, don haka ga yadda labarin ya fara kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p><em><strong>SAWUN <\/strong><\/em><em><strong>\u0181<\/strong><\/em><em><strong>ARAWO<\/strong><\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8216;Na rubuta da manyan ba<\/em><em>\u0199<\/em><em>i a saman littafin nawa daidai lokacin da na sake gyara zama irin na <\/em><em>\u0257<\/em><em>alibin da ya gurfana a gaban malami don <\/em><em>\u0257<\/em><em>aukar darasi, bambancinmu <\/em><em>\u0257<\/em><em>aya da shi kawai ni ba a gaban kowa na gurfana ba, amma kuma ni ma zama nake yi na jiran tsammani. Lokaci-lokaci ina kai dubana zuwa bakin <\/em><em>\u0199<\/em><em>ofa don ganin shigowar Abbanmu da har zuwa lokacin bai dawo daga masallaci ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; A daidai lokacin ne kuma ita ma Fatima ta shigo <\/em><em>\u0257<\/em><em>akin, na <\/em><em>\u0257<\/em><em>aga kai muka ha<\/em><em>\u0257<\/em><em>a ido sanadin da ya sa take yi mini dariya.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Kaiii&#8230; Young Barrister! Don zumu<\/em><em>\u0257<\/em><em>i har ka zo ka wani zauna kamar wanda zai <\/em><em>\u0257<\/em><em>auki darasi?&#8221; Ta jefe ni da kalaman zolaya daidai lokacin da take <\/em><em>\u0199<\/em><em>o<\/em><em>\u0199<\/em><em>arin samun wuri ta zauna. Ni ma murmushin na yi sannan na amsa ina kallon ta.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Ai darasin da ma na zo <\/em><em>\u0257<\/em><em>auka tunda na san dole na <\/em><em>\u0199<\/em><em>aru da wata hikimar ta tsofaffin hannu, kuma ke ma kin san ba zumu<\/em><em>\u0257<\/em><em>i ba ne ya kawo ni kawai dai so nake na ji wanda zai taka wannan sawun <\/em><em>\u0253<\/em><em>arawon, don kuwa da alama kamar labarin zai yi da<\/em><em>\u0257<\/em><em>i shi ma&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Ai zumu<\/em><em>\u0257<\/em><em>in kenan&#8221; Ita ma ta amsa bayan ta zauna.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Amma kuma ban ga laifinka ba fa, don kuwa ni ma kaina jikina yana ba ni kamar labarin zai yi da<\/em><em>\u0257<\/em><em>i sosai.&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Ato dai!&#8221; Na fa<\/em><em>\u0257<\/em><em>i kana muka yi dariya gaba<\/em><em>\u0257<\/em><em>aya lokaci guda kuma muka mayar da kallonmu bakin <\/em><em>\u0199<\/em><em>ofar <\/em><em>\u0257<\/em><em>akin tare da amsa sallamar Mahaifinmu da ya shigo a daidai lokacin shi da su Usman da suka dawo daga makaranta su ma. Ya kalle mu ya yi dariya ganin yadda gaba<\/em><em>\u0257<\/em><em>aya muke farin ciki da dawowarsa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Ashe ku har kun zo kun zazzauna kuna jira na kenan?&#8221; Ya tambaye mu.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Ai ina sani na <\/em><em>\u0199<\/em><em>i dawowa sai da na bari na yi sallar la&#8217;asar saboda labarin gaba mai <\/em><em>\u0257<\/em><em>an tsaho ne, tazara tsakanin Azahar da La&#8217;asar ta yi mana ka<\/em><em>\u0257<\/em><em>an mu gama, kuma ba na so mu fara ba mu gama ba a kira salla mu tashi, shi ya sa ma na yi hakan.&#8221; Ya <\/em><em>\u0199<\/em><em>are daidai lokacin da yake cire malum-malum ya samu wuri ya zauna.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&nbsp;&nbsp;&nbsp; &#8220;Sai ku jira ni na ci abinci kenan!&#8221; ya fa<\/em><em>\u0257<\/em><em>i daidai lokacin da ya ga Ummanmu ta shigo <\/em><em>\u0257<\/em><em>auke da kayan abincinsa. Muka amsa da &#8220;To&#8221; kana muka ci gaba da hirarmu har zuwa lokacin da ya gama komai ya samu nutsuwa sannan ya nisa ya fara da cewa&#8230;.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Kafin ya fara \u0257in mu yi wani nazari. Idan kuka kalli wannan labari ya fara ne da salon&nbsp;<strong>Tauraro Cikin Fage<\/strong>, tunda labarin kaina nake bayarwa ni da &#8216;yan&#8217;uwana da mahaifina. A \u0253angaren Salon Ginin Labari kuma za mu iya cewa&nbsp;<strong>Mi<\/strong><strong>\u0199<\/strong><strong>a<\/strong><strong>\u0199\u0199<\/strong><strong>en Salo<\/strong>&nbsp;na \u0257auka. To bari mu \u0199ara matsawa ga\u0253a ta gaba cikin labarin kuma ku ga sauyin da za a samu.<\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Zare na farko da zan fara sa<\/em><em>\u0199<\/em><em>a muku labarin da shi cikin tarin zararrukan labarin namu shi ne zaren wata hira tsakanin wasu marasa gaskiya biyu da suke waya kowannan su a sirrancen gudun kada wani ya gan su ko kuma ya ji abin da suke tattaunawa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Da wa nake magana?&#8221; Alhajin ya tambaya cikin wata irin murya da ta yi kama da irin muryar wanda aka tilasta wa yin magana.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ai ba za ka gane da wa kake magana ba yanzu tunda ka ci moriyar ganga ka watsar da korenta. Kuma ni ma da ma ba wai na kira ka ba ne don ka gane da wa kake magana, kawai dai na kira ka ne saboda in fa<\/em><em>\u0257<\/em><em>a maka cewa na gane dukkan mugunnufinka na gaba a kan kisan Alhaji da kake shiryawa, kuma ko tantama kar ka yi sai na tarwatsa shi, ba zan ba ka damar cika <\/em><em>\u0199<\/em><em>udirinka ba, ba zan bari ka kashe Alhaji ba. Don haka ka&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kai dalla dakata malam! Sha-sha-sha kawai!&#8221; Alhajin ya katse masa zancen nasa ba wai don ya <\/em><em>\u0199<\/em><em>arasa ba, lokaci guda kuma ya <\/em><em>\u0257<\/em><em>ora da cewa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kai har kana da <\/em><em>\u0199<\/em><em>warin guiwar da za ka iya tsorata ni? Ko kuwa kana tunanin har ka yi <\/em><em>\u0199<\/em><em>arfin da za ka iya karawa da ni? Kodayake ba zan hana ka yin abin da kake son yi ba, don kuwa wata<\/em><em>\u0199<\/em><em>ila ajalinka ne ya matso kusa tunda na san ka fi kowa sanin wane ne ni idan aka shigo gonata. Don haka kawai ina ganin sai mu zuba tunda ga fili ga kuma dawakai!&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Mu sake dakatawa mu yi nazari, a wannan ga\u0253ar kuma za ku ga labarin ya sauya zuwa salon&nbsp;<strong>Tauraro Wajen Fage<\/strong>, yanzu ba ni ne nake ba da labarin da lamirina ba, mahaifina ne yake ba da labarin wasu da lamirinsu. To ku sake biyo ni zuwa ga\u0253a ta gaba cikin labarin ku ga wata dabarar.<\/p>\n\n\n\n<p><em>\u201c&#8230;Abbanmu ya yi shiru a iyaka nan yana kallon mu, bayan ya yi murmushi ne kuma ya ce.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kodayake ba ta nan ya kamata na fara da labarin nan ba idan har ina son ya tafi a daidai, don haka ina ganin za mu jingine wannan ga<\/em><em>\u0253<\/em><em>ar a nan ne, amma kuma kada ku damu za mu dawo mu biyo ta kanta a gaba nan ba da da<\/em><em>\u0257<\/em><em>ewa ba.&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em><strong>FARKO:<\/strong><\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Labarin sawun <\/em><em>\u0253<\/em><em>arawo ya fara sa<\/em><em>\u0199<\/em><em>uwa ne da safe wajen misalin <\/em><em>\u0199<\/em><em>arfe goma na wata ranar Asabar cikin wani irin yanayi na sanyi da hazo da garin ya tashi da shi, kasancewar a lokacin ana cikin tsakiyar sanyi irin mai ratsa <\/em><em>\u0199<\/em><em>ashin nan, wanda hakan shi ne ya sa duk da ranar da ta fara yi amma dayawa cikin jama&#8217;a ba su fito ba suna cikin gida kwance cikin bargo a du<\/em><em>\u0199<\/em><em>un<\/em><em>\u0199<\/em><em>une.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>To a daidai wannan lokacin ne kuma shi <\/em><em>\u0253<\/em><em>arawon mai hikima ya cire sawunsa ya yi musanye da sawun wani ya la<\/em><em>\u0253<\/em><em>a<\/em><em>\u0253<\/em><em>a ya bi cikin hazo da sanyin da ya sauyawa gari yanayi ba tare da wani ya gan shi ba ya <\/em><em>\u0253<\/em><em>ace <\/em><em>\u0253<\/em><em>at!<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan kun kula da wannan ga\u0253ar kuma abubuwa biyu ta \u0199unsa. Na farko dai cikin hikima an yi wa mai karatu&nbsp;<strong>Tsakure<\/strong>, ko&nbsp;<strong>Somin Ta<\/strong><strong>\u0253<\/strong><strong>i<\/strong>&nbsp;na abin da zai faru a gaba cikin labarin (wayar da alhaji da wani ke yi.) Na biyu kuma mun sauya daga mi\u0199a\u0199\u0199en salon da muka faro labarin mun koma&nbsp;<strong>Salo Tafiyar Kura<\/strong>&nbsp;da kuma&nbsp;<strong>Salo Mai Karsashi<\/strong>. Kusan gaba\u0257aya da irin wannan salon na gina labarin&nbsp;<em>Sawun <\/em><em>\u0181<\/em><em>arawo<\/em>, wanda kuma yana \u0257aya daga cikin labaraina da suka fi tara masoya saboda yadda salonsa yake da jan hankali.<\/p>\n\n\n\n<p>Mu \u0257an \u0199ara gaba ka\u0257an cikin labarin ku ji.<\/p>\n\n\n\n<p><em>A wani katafaren asibiti ne na wani likita mai zaman kansa da ke wata unguwa ta masu yatsu da yawa mai gadin da yake aiki a wannan lokacin ya janye <\/em><em>\u0199<\/em><em>aton kyauren (Gate) <\/em><em>\u0257<\/em><em>in asibitin wata tsaleliyar mota mai numfashi ta sulala cikin asibitin kamar yadda maciji yake sulalawa cikin raminsa, sannu a hankali kamar ba za ta tafi ba har zuwa cikin harabar asibitin, wani fili da aka tanada don ajiye motoci.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>A nan wurin farar motar Jeep <\/em><em>\u0257<\/em><em>in ta samu matsuguni tare da daidaita sawunta kamar yadda sauran motocin wurin suka daidaita nasu, bayan kamar mintina uku zuwa hu<\/em><em>\u0257<\/em><em>u kuma mamallakinta wanda ya yi anko da kalarta cikin wata lallausar farar shadda <\/em><em>\u0257<\/em><em>inkin malum-malum da ta sha wani aiki irin na sarauta mai launin toka, kan shi sanye da wata farar hula damanga ya fito yana mai saka wani farin tabarau a idonsa, hannunsa na dama kuma yana ri<\/em><em>\u0199<\/em><em>e da wata ba<\/em><em>\u0199<\/em><em>ar leda wacce take cike da kaya, a <\/em><em>\u0253<\/em><em>angare guda kuma kamar wanda yake nazarin cikin harabar asibitin.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Ya saka hannu ya mayar da murfin <\/em><em>\u0199<\/em><em>ofar motar ya rufe tare da danna linzamin da ke hannunsa (wato remote), motar ta <\/em><em>\u0257<\/em><em>an yi wani <\/em><em>\u0199<\/em><em>ara, lokaci guda kuma ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da ainahin cikin asibitin wurin da ake kwantar da mutane, farin takalmi saucikin da ke <\/em><em>\u0199<\/em><em>afarsa yana ha<\/em><em>\u0257<\/em><em>uwa da da<\/em><em>\u0253<\/em><em>en kwalbar tiles <\/em><em>\u0257<\/em><em>in asibitin yana ba da wata <\/em><em>\u0199<\/em><em>ara &#8216; <\/em><em>\u0198<\/em><em>was! <\/em><em>\u0198<\/em><em>was! <\/em><em>\u0198<\/em><em>was!&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kun san me ya zo yi asibitin kuwa?&#8221; Cewar Abbanmu bayan ya <\/em><em>\u0257<\/em><em>an yi shiru yana nazarin fuskokinmu, yayin da mu kuma muka gya<\/em><em>\u0257<\/em><em>a kai alamar a&#8217;a damar da ya samu kenan ya ci gaba da cewa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ya je duba wani amininsa ne da aka kwantar a asibitin&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Irin wannan salon yana da wasu fa&#8217;idoji da ya kamata mu tattauna su. Amma kafin sannan \u0199ofar gyara, sharhi, tambaya ko \u0199arin bayani a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hadakar salo shi zamu tattauna a yau. A ma\u0199alar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan salon bayar da labari, da kuma yadda marubuci zai ri\u0199a yin rubutu cikin hikima ta yadda zai ri\u0199a goce wa hasashen manazarcinsa wanda ka iya hakaito \u0199arshen labarin ya rage masa armashi.&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/hadakar-salo-sama-da-daya-wajen-samar-da-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Hadakar salo sama da daya wajen samar da labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3535,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,51,19],"class_list":["post-3530","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-hadakar-salo","tag-writing-tips"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/06\/Hadakar-Salo.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3530","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3530"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3530\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3535"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3530"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3530"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3530"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}