{"id":3721,"date":"2022-09-01T15:32:06","date_gmt":"2022-09-01T15:32:06","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3721"},"modified":"2023-09-30T10:47:44","modified_gmt":"2023-09-30T10:47:44","slug":"gurbin-magani-cikin-karin-maganar-hausa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/gurbin-magani-cikin-karin-maganar-hausa\/","title":{"rendered":"Gurbin magani cikin karin maganar Hausa"},"content":{"rendered":"\n<p>A \u0199ar\u0199ashin kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Wasu masana, sun yi hasashen cewa, kalmar ba ta rasa nasaba da kalmar \u2018gwaji, wato a gwada abu a ga ko zai yi. Suna ganin kalmar \u2018hatsin bara\u2019 ce, wato ha\u0257e-ha\u0257en kalmomi ne na Hausa suka samar da ita. Kalmomin su ne: \u201cma\u201d da \u201cyi\u201d da kalmar \u201cgani\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan Bahaushe ya sami wata cuta ko rashin lafiyar da yake son kawarwa, sai ya sami &#8216;yan ganyayyakinsa da saiwowi ya harha\u0257a ya ce: \u201cMa gwada wannan mu gani\u201d, har dai kalmar ta koma &#8216;ma yi wannan mu gani\u201d. Daga baya ta koma, &#8216;ma yi ma gani\u201d, har ya zuwa kalmar ta koma: \u201cmagani\u201d, ma\u2019ana, bari mu yi ma gani (Bunza: 135).<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Ma&#8217;anar magani<\/h2>\n\n\n\n<p>Dangane da \u0199unshiyar ma\u2019anar kalmar magani, har ila yau wasu masana da \u0257aliban nazarin al\u2019adun Hausawa sun sha \u0257auki-ba-da\u0257i kan ha\u0199i\u0199anin gano ma\u2019anarta.<\/p>\n\n\n\n<p>Da farko ga yadda Kamusun Hausa na Jami\u2019ar Bayero Kano (2006) ya fassara ta:<\/p>\n\n\n\n<p>(i) Abin da ake sha ko shafawa a jiki ko \u0257urawa a jini ta hanyar yin allura, don neman samun lafiya.<\/p>\n\n\n\n<p>(ii) Abin da samuwarsa kan kore wani daban, misali, tarko yana maganin Beraye.<\/p>\n\n\n\n<p>(iii) Sammu, wato harha\u0257a wasu abubuwa da yin surkulle da nufin cutar da wani, musamman abokin gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>(iv) Harha\u0257awa ko yin wasu abubuwa na musamman don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu.<\/p>\n\n\n\n<p>Kasancewa magani ba a yin rayuwa babu shi ya sa Bahaushe ya kirkiri wasu maganganun azanci da su. Ga kuma misalansu a kasa kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>1. Maganin kada a yi kada a fara.<\/p>\n\n\n\n<p>2. In kura ta na maganin zawo ta yi wa kanta.<\/p>\n\n\n\n<p>3. Jan biro maganin takaddarin \u0257alibi.<\/p>\n\n\n\n<p>4. Gobara daga kogi maganinta Allah.<\/p>\n\n\n\n<p>5. Sana&#8217;a goma maganin baccin rana.<\/p>\n\n\n\n<p>6. In ka san halin mutum ka sha maganin zama da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>7. Tafiya maganin gari mai nisa.<\/p>\n\n\n\n<p>8. \u018aauri maganin bajewar kaya.<\/p>\n\n\n\n<p>9. Hadarin \u0199asa maganin mai kabido.<\/p>\n\n\n\n<p>10. Karen bana maganin zomon bana.<\/p>\n\n\n\n<p>11. Maganin shege sai \u0257an gatan uwa.<\/p>\n\n\n\n<p>12. Maganin Bawa sanda.<\/p>\n\n\n\n<p>13. Maganin ma\u0199i gudu ban kashi.<\/p>\n\n\n\n<p>1.4 maganin \u0199iyayya rabuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>15. Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.<\/p>\n\n\n\n<p>16. Hannu da yawa maganin \u0199azamar miya.<\/p>\n\n\n\n<p>17. Idan so cuta ne ha\u0199uri magani ne.<\/p>\n\n\n\n<p>18. Ha\u0199uri maganin zaman duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>19. Mu wasa ne? Babarbare ya ba da magani an sha an mutu<\/p>\n\n\n\n<p>20. Magani a sha ka a warke<\/p>\n\n\n\n<p>21. Hauka maganinki turu.<\/p>\n\n\n\n<p>22. Haske maganin duhu.<\/p>\n\n\n\n<p>23. \u0198oshi maganin yunwa.<\/p>\n\n\n\n<p>24. Haihuwa maganin takaicin duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>25. Haihuwa maganin mutuwa<\/p>\n\n\n\n<p>26. Maganin biri karen maguzawa.<\/p>\n\n\n\n<p>27. Abu naka maganin a kwabe ka.<\/p>\n\n\n\n<p>28. Araha butu maganin mai wayo<\/p>\n\n\n\n<p>29. Riga-kafi ya fi magani.<\/p>\n\n\n\n<p>30. Anin wani bai yi wa wani magani.<\/p>\n\n\n\n<p>31. A busa a bari ba ya maganin \u0257an ban,<\/p>\n\n\n\n<p>32. Gida goma maganin gobara<\/p>\n\n\n\n<p>33. Bakar ajiya mai maganin bakar rana.<\/p>\n\n\n\n<p>34. Ciwon da ba ka da magani a mutu ya fi.<\/p>\n\n\n\n<p>35. Da tsohuwar zuma ake magani.<\/p>\n\n\n\n<p>36. Fitina sai ka ce shan maganin Bature.<\/p>\n\n\n\n<p>37. Gangar baka maganin hasarar fata.<\/p>\n\n\n\n<p>38. Gudu da mari ba ya maganin bauta.<\/p>\n\n\n\n<p>39. Gudu da mai ruwa ba ya maganin dau\u0257a.<\/p>\n\n\n\n<p>40. Haukar ba ni maganin amshi.<\/p>\n\n\n\n<p>41. Hannu da yawa maganin mai \u0199wange.<\/p>\n\n\n\n<p>42. Hauka maganinki \u0257anyar geza.<\/p>\n\n\n\n<p>43. Jini ba ya maganin kishin ruwa.<\/p>\n\n\n\n<p>44. Linzami da wuta maganin mahaukacin doki.<\/p>\n\n\n\n<p>45. Mu je mu gani maganin mai karya.<\/p>\n\n\n\n<p>46. Maganar ciki maganin mai tsegumi, bai ji ba balle ya karasa.<\/p>\n\n\n\n<p>47. Naman kura da magani yake karewa.<\/p>\n\n\n\n<p>48. Sha yanzu magani yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p>49. Yunwa maganin mugunyar dafuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>50. Zamani ba ka jin magani.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A \u0199ar\u0199ashin kiwon lafiya, kalmar magani sananniya ce ga kowane Bahaushe. Wasu masana, sun yi hasashen cewa, kalmar ba ta rasa nasaba da kalmar \u2018gwaji, wato a gwada abu a ga ko zai yi. Suna ganin kalmar \u2018hatsin bara\u2019 ce, wato ha\u0257e-ha\u0257en kalmomi ne na Hausa suka samar da ita. Kalmomin su ne: \u201cma\u201d da&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/gurbin-magani-cikin-karin-maganar-hausa\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Gurbin magani cikin karin maganar Hausa<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":3723,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[34,58],"tags":[62,64,63],"class_list":["post-3721","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-general-literature","category-hausa","tag-culture","tag-karin-magana","tag-language-and-culture"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/09\/Gurbin-magani-cikin-karin-maganar-Hausa.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3721","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3721"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3721\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3723"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3721"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3721"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3721"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}