{"id":3724,"date":"2022-09-02T04:23:41","date_gmt":"2022-09-02T04:23:41","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3724"},"modified":"2023-10-14T15:42:36","modified_gmt":"2023-10-14T15:42:36","slug":"sharhin-littafin-alkalamin-kaddara-1-2-na-lubna-sufyan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-alkalamin-kaddara-1-2-na-lubna-sufyan\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Alkalamin Kaddara&#8217; 1 &#038; 2 na Lubna Sufyan"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan Littafi: <strong>Al\u0199alamin \u0198addara (1&amp;2)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciya: <strong>Lubna Sufyan<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka Buga Littafi: <strong>Bakandamiya Hikaya (Online)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar Bugu: <strong>2022<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Yawan Babi: <strong>Littafi na \u0257aya: 11, Littafi na biyu: 41; Jimilla: 52<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai Sharhi: <strong>Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Manufar Sharhi:<em> Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Gabatarwa<\/h2>\n\n\n\n<p>Akan ce ka gode wa Allah a kowane irin yanayi ka tsinci kanka, saboda komai \u0199uncin da kake ciki wani ya fi ka. Haka kuma komai jin da\u0257in da kake ciki shi ka wani ya fi ka. Kuma masu iya magana na cewa &#8216;\u0198addara ta riga fata&#8217; wato abin duk da Allah ya \u0199addara zai same ka, to baya yake da abinda kowa zai yi maka fatan ya same ka. Kowa da irin wannan tasa \u0199addarar, in ka ci ta wani ta fi taka da\u0257i, ta wani kuma in da za ka ji sai ka yi kuka. Shin da wacce irin tawada al\u0199alamin \u0199addarar mu ya yi mana rubutu, wacce irin \u0199addara ce ke kan kowannen mu, ya za mu yi idan muka wayi gari wata mummunar \u0199addara ta afka mana? Wa\u0257annan da ma wasu tarin abubuwa duk suna nan a \u0199unshe cikin wannan hamsha\u0199in littafi mai suna Al\u0199alamin \u0198addara.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tarihin marubuciyar a ta\u0199aice<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuciya Lubna Sufyan an haife ta ne a \u0199aramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana \u0199arama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatun Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun Diploma a \u0253angaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma wadda da turanci ake ce wa Higher National Diploma (HND) a Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar mafi yawancin marubuta, marubuciyar ita fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance \u0257aya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani, domin abu ne mai wuya ka fa\u0257i sunanta a duniyar marubuta da makarantan wannan zamani ba a samu wanda ya santa ba. Zuwa yanzu marubuciyar ta rubuta litattafai sama da guda goma sha \u0257aya. Wasu daga cikin litattafan da ta rubuta sun ha\u0257a da;<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li><em>Rai Da \u0198addara<\/em><\/li><li><em>Wata Bakwai<\/em><\/li><li><em>Akan So<\/em><\/li><li><em>Rayuwar Mu<\/em><\/li><li><em>Abdul\u0199adir<\/em><\/li><li><em>Mijin Nobel<\/em><\/li><li><em>Martabar Mu<\/em><\/li><li><em>&nbsp;Al\u0199alamin \u0198addara <\/em>da dai sauransu<\/li><\/ul>\n\n\n\n<p>Har&#8217;ilayau kuma, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da \u0199ungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su GiveNorthEducation, WomenInArewa, WomenInFinance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma \u0199wararra ce wajen&nbsp; ha\u0257a \u0257uwatsun \u0199awa na adon mata. Sannan kuma tana aikin juyar da bayanan murya zuwa rubutu (transcription). A ta\u0199aice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi \u0199arfi.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar kuma na \u0257aya daga cikin mambobin \u0199ungiyar marubuta na Fikra Writers Association. Lubna Sufyan ta yi aure a shekarar 2022, kuma tana zaune ne a garin Kaduna yanzu haka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Labarin a Ta\u0199aice<\/h2>\n\n\n\n<p>Mahaifin Tasneem mai suna Muftahu wanda aka fi sani da Abba, wani mutumin kirki ne talaka mai neman na kanshi domin ganin ya rufa wa kanshi da ahalinsa asiri. Amma matarsa Bara&#8217;atu wacce ake kira da Ummi irin matan nan ne da basu da godiyar Allah. Duk abinda ya kawo bata godewa, kuma sai ta fita ta je inda take so ba tare da ta tambaye shi ba, yaran kuwa bata kula d su yadda ya kamata. Kullum cikin maula take tare da kiran babu. Bisa wannan dalili ne har \u0199addara ta kai Tasneem wani gida a matsayin &#8216;yar aiki har yaron gidan ya yi mata fya\u0257e. Wannan ne ya jawo silar da ta fara biye-biyen maza domin ta kula da \u0199annenta.<\/p>\n\n\n\n<p>Hankalin Tasneem ya yi matu\u0199ar tashi sakamakon asirinta da ya tonu tun a daren ta na farko da auren Rafiq. Domin kuwa Ya gano cewa bata zo gidan shi da budurcinta ba Wannan yasa ta shiga tashin hankalin da har zuwa \u0199arshen littafi na biyu bata fita daga cikin shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Alhaji Mustafa Shettima wanda tsohon lauya ne, \u0257an kasuwa kuma \u0257an siyasa ya kasance yana iya yin komai don ganin ya cimma burikansa na siyasa. Ciki kuwa har da yi &#8216;yarsa auren dole ta hanyar ro\u0199onta da ta auri wanda bata ta\u0253a gani ba, ita kuma ta amince saboda biyayyarta, duk kuwa da cewa tana da wanda take so wato Muneeb.<\/p>\n\n\n\n<p>A gefe kuma ga Altaaf da matarsa Majida wa\u0257anda ke neman haihuwa ruwa a jallo amma basu samu ba. Kwatsam! Sai Altaaf ya gano cewa yana da yara &#8216;yan biyu a wani \u0199auye wa\u0257anda Nuwaira ta haifa ba tare da ya sani ba bayan ya mata fya\u0257e shekaru da dama da suka wuce.<\/p>\n\n\n\n<p>Ashfaq, wanda mutuwar mahaifansa da ta &#8216;yan uwanshi har guda biyu tare da \u0253acewar \u0199anin shi \u0257aya suka sa shi neman ku\u0257i ido rufe domin kauce wa \u0199addarar talauci kuma na kwance yana jinyar raunin harbin da aka yi mishi da bindiga sakamakon har\u0199allar miyagun \u0199wayoyi da ta ha\u0257a shi da wasu. Ga kuma \u0199aninsa watau Tariq wanda shi kuma yake fama da jarabar shan kayan maye wadda ya kasa dainawa, duk kuwa da cewa har gidan nahaukata ya ta\u0253a zuwa a dalilin hakan.<\/p>\n\n\n\n<p>Rafiq na cikin tashin hankali na sanin cewa matar da ya aura ta san wasu mazan a waje, sai kuma wani sabon tashin hankalin ya fa\u0257o mishi, domin kuwa baya iya tu\u0199i sai dai a tu\u0199a shi, duk kuwa da cewa yana iya tuno lokacin da yake tu\u0199in da kanshi. A gefe kuma \u0199anwar shi da aka yi wa auren dole ta kira shi tana neman ya zo ya \u0257auke ta sakamakon azabar da take sha a gidan mijin ya ishe ta. A daidai lokacin da ya gano cewa hatsarin mota ne da ya yi ya sa ya manta rayuwarsa ta baya, a daidai wannan lokacin ne kuma ya gano cewa wannan hatsarin ne ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa da &#8216;yarsa wa\u0257anda ya kasa tuno ko da sunan su balle rayuwar da suka gudanar a tare.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Ko daga \u0257an ta\u0199aitaccen bayanin da aka yi dangane da labarin a dun\u0199ule, na san cewa mai karatu zai iya fahimtar cewa babban jigon wannan labari shi ne &#8216;\u0198addara&#8217; kamar yadda sunan littafin ma ya nuna. Dalilin fa\u0257ar wannan magana kuwa ba \u0253oyayye ba ne, saboda kusan duk taurarin da ke cikin labarin an fi maida hankali ne akan irin yadda \u0199addarar su ta kasance daga farko, tsakiya da kuma \u0199arshen labarin. Kuma batun &#8216;\u0198addara&#8217; shi ne wanda aka fi magana a kai.<\/p>\n\n\n\n<p>Wasu na iya ganin soyayya a matsayin babban jigon Al\u0199alamin \u0198addara. Wannan za ta iya kasancewa. Saboda an dabaibaye labarin cikin harkokin soyayyar da ta kasance tun farko a tsakanin Rafiq da Tasneem, Rafiq da Samira, Fadila da Nawfal, Zafira da Muneeb inda ta \u0199are da da soyayyar \u0253angare uku wadda ta wanzu a tsakanin Hamna, Tariq da kuma Tasneem duk kuwa da cewa ita Tasneem \u0257in bata san cewa Tariq \u0257in yana sonta ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wannan babban jigo da na yi bayani, marubuciyar ta yi amfani da \u0199ananun jigogi masu yawan gaske wa\u0257anda su ne suka ha\u0257u suka goya wa labarin baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu ka\u0257an daga cikin su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna mana irin yadda soyayya take da \u0199arfin canza rayuwar mutum gaba \u0257aya, da kuma irin yadda rashin masoyi ka iya jawo dagulewar rayuwar mutum. Misali, dubi yadda Muneeb yake bayyanawa Zafira irin yadda yake ji a ranshi da ya ji za ta auri wani, &#8220;Bazan iya ba, na kasa tuna yadda rayuwata take ba tare da soyayyarki ba, wallahi bansan ya duniyata zata kasance babu ke a ciki ba&#8230;&#8221; (Littafi Na 1, babi na 11)<\/p>\n\n\n\n<p>Dubi kuma yadda aka bayyana wata \u0253oyayyiyar soyayyar da ke tsakanin Tariq da Hamna,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;kuma kullum sai ta mishi text \u0257in gaisuwa da safe, da dare kuma ta sake tura mishi wani, duk da ba kullum take samun amsa ba, bata damu ba, a kalar son da take ma Tariq bata jin wani sauran aji a tare da ita, wani lokaci cikin dare takan farka haka kawai da tunanin shi manne a zuciyarta da yake hanata sukuni, haka zata \u0199are daren da yin salloli da neman mafita. (Littafi na 2, babi na 38)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Matsalar sangarta yara da iyaye ke yi saboda mugun so tare da kauda kai akan laifukansu, musamman iyayen mu mata ba sabon abu ba ne amma yana da hatsarin gaske. Domin kuwa shi ya jawo lalacewar Altaaf har ya \u0257auki mugayen halaye wa\u0257anda har suka kai shi ga aikata munanan laifuka, ciki kuwa har da fya\u0257e. Ba laifi ba ne don iyaye sun so &#8216;ya&#8217;yansu, amma in soyayyar ta yi yawa sai gata ta yi yawa, hakan kuma ke jawo matsala mai girman gaske. Kuma marubuciyar ta yi \u0199o\u0199ari sosai wajen fayyace irin yadda iyaye masu irin wannan tunanin suke ji kamar yadda ta bayyana da cewa, &#8216;..tunda ya bar gidanta kuma ta shiga \u0257aki ta kwanta don zazza\u0253i take ji ya rufeta, tunani take tunda ya fita daga gidan na lokacin da rayuwar Altaaf \u0257in ta gur\u0253ata haka bata sani ba, tunanin inda ta yi kuskure take yi ta rasa.&nbsp; (Littafi na 2, babi na 30)<\/p>\n\n\n\n<p>Da kuma inda ta ce,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Ba za ta ce ga asalin abinda take ji akan \u0199addarar da ke faruwa da Altaaf ba, tana kula da kallon da Baba yake mata jiya kamar laifinta ne abinda yake faruwa da Altaaf \u0257in yanzun. In tambayar ta yayi ba za tai mishi musu ba. Amma kuma bata jin dana sani a \u0199asan zuciyarta, bata san ko don Altaaf \u0257in ya canza ba ne ba yanzun. Abu \u0257aya ta sani, in za&#8217;a bata damar komawa baya, ba zata sake abu \u0257aya akan yadda ta taso da Altaaf ba, bata dana sanin gatan da ta nuna mishi ko ka\u0257an, in zata iya mishi fiye da wanda take bashi a yanzun zata yi . Wannan kalar \u0199aunar kawai ta sani. Yanzun ma da zata iya \u0257auke mishi damuwar da take bayyane akan fuskar shi zata \u0257auke ya samu sau\u0199i. (Littafi na 2, babi na 33)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Talauci ba hauka ba ne, kuma in da kwa\u0257ayi to fa akwai wula\u0199anci. An nuna mana irin yadda illar kwa\u0257ayi da son abin duniya suke akan mahaifiyar su Tasneem, domin har ta kai ga tana zagin &#8216;yarta tare da tursasa ta akan ta fita yawon siyayya da wani don ta samu abin duniya ba tare da duban matsalar da hakan ka iya jawowa ba. Kamar yadda a littafi na 1, babi na 1 take cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ke wacce irin yarinya ce marar rabo? Arzi\u0199i na binki kina runtse ido? In ke halin \u0199uncin da muke ciki ba ya damunki sai aka ce miki ni ba ya damuna? Don ubanki yaushe za ki yi hankali?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Mutuwa mai tonon silili! An nuna mana yadda mutuwa iya tarwatsa ahali gaba \u0257aya, domin kuwa mun ga yadda hakan ya wanzu ga su Ashfaq bayan mutuwar iyayen su.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan mun ga yadda mutuwar mahaifi ta \u0199ara jagula rayuwar su Tasneem da \u0199annenta.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Rashin tsayayyen namiji a gida ba \u0199aramin abu ba ne, kuma mun ga irin illar da ke cikin hakan a rayuwar Altaaf. Shi kanshi Altaaf \u0257in daga baya sai da ya fahimci matsalar da ke cikin hakan kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;A tsawon rayuwar shi ba wai ya damu da Baba bane, asali ma komin shi Ammi ce, ku\u0257in kashewa, kayan sakawa, matsalar makaranta, ba zai tuna rana \u0257aya da Baba ya \u0257auki ku\u0257i ya bashi ba, ko ya bashi kaya a matsayin wannan shi ya siya mishi. In ma yana yi \u0257in sai dai ko ta hannun Ammi hakan ke faruwa kuma bata ta\u0253a fa\u0257a mishi ba. Maganar da ta wuce minti sha biyar bata ha\u0257a shi da Baba. (Littafi na 2, babi na 30)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Marubuciyar ta fito da illar da ke cikin zuwa gidan miji ba tare da&nbsp; budurci ba ga &#8216;ya mace. Domin ta bayyana yadda duk soyayyar da ke tsakanin Rafiq da Tasneem ta fara barazanar tarwatsewa tun a farkon labarin. (Littafi na 1, babi na 1)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Biye-biyen mata ba aiki ba ne nagari. Kuma marubuciyar ta nuna mana haka a wurare da dama a cikin labarin, musamman akan rayuwar Altaaf.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An kuma nuna mana illar shaye-shaye akan rayuwar Tariq da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Idanuwan shi kafe suke akan kwalaben kodin \u0257in da ke gabanshi. Hannuwan shi da suke a dumtse har \u0199ai\u0199ayi suke mishi na son \u0257aukar kwalbar. Zai iya rantsewa har kan harshen shi yana jin \u0257an\u0257anon ha\u0257in da yake cikin kwalbar da ya fi komai tafiyar mishi da damuwa. (Littafi na 1, babi na 1)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022&nbsp; Soyayyar &#8216;yan uwa tana girma da muhimmanci sosai, kuma marubuciyar ta nuna yadda hakan ya yi tasiri akan Rafiq da &#8216;yan uwan shi, watau fawzan, Aroob da Zafira. Kamar yadda ta nuna akan Su Tasneem da \u0199annenta da kuma Altaaf da \u0199aninsa Aslam da kuma \u0198anwarsu Barrah. Su ma su Ashfaq hakan ya yi tasiri sosai akan tasu rayuwar tun daga farko har \u0199arshen labarin.&nbsp; Dubi dai yadda hankalin Rafiq ya tashi cikin \u0257an \u0199an\u0199anin lokaci a littafi na 1, Babi na 2 akan rayuwar Fawzan.&nbsp; &#8220;Na zo gida ne, babu kowa sai Asabe. Ta ce Fawzan yana nan, kuma \u0257akin shi a kulle. Ban san ko meye ba&#8230; Kawai bana jin yanayin na min da\u0257i.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna irin yadda auren dole ke wargaza wa &#8216;ya&#8217;ya mata rayuwarsu akan Zafira sakamakon aurenta da Omeed. Dubi hujjojin da mahaifin Zafira ya yi amfani da su wajen bayyana mata dalilin shi na son ta auri wanda ya za\u0253a mata,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ba \u0199aramin gida bane ba, yaro ne da ya fito daga gidan mutunci&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;&#8230;Ina son ki sani yana da matu\u0199ar muhimmanci a wajena, zan rasa abu da yawa in baki amince ba, a karo na farko ina ro\u0199onki da ki amince Zafira&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ina son ki auri \u0257an gidan Alhaji Yusuf Modibbo ne&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Auren ki da shi na da muhimmanci a wajena. Karki ce a&#8217;a Zafira. Na riga na amsa musu&#8230;&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>(Littafi na 1, babi na 11)<\/p>\n\n\n\n<p>To dubi kuma yadda aka bayyana ka\u0257an daga cikin matsalar irin wannan auren, wanda shi ne rashin barin matar ta ziyarci danginta a littafi na 1, babi na 2 da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Duk sanda kaso kake zuwa ka ga naka &#8216;yan uwan&#8230; Ban san me yasa kake hanani zuwa ganin nawa ba.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ha\u0199i\u0199a fya\u0257e wani abu ne da ya zama ruwan dare a wannan zamanin. Kuma marubuciyar bata yi \u0199asa a gwiwa ba wajen bayyana irin yadda hakan yake da illa ga rayuwar &#8216;ya&#8217;ya mata ba. Domin ta bayyana yadda hakan ya zama silar lalacewar Tasneem ta fara bin maza, da yadda Nuwaira ta kasa samun mijin aure, da kuma yadda ya zama silar mutuwar Arifa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Tsakanin mata da miji sai Allah. Wannan littafi ya \u0199ara tabbatar da wannan maganar ta hanyoyi da dama. Dubi yadda Tasneem ke \u0199o\u0199arin kwantar wa da Rafiq hankali duk da cewa ciwon zuciya da tashin hankali na damunta.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;In kuka za ka yi ka yi, in wani abu kake son fasawa ka tashi in raka ka akwai abin fasawa da yawa a gidan&#8230; Ko me kake jin yi, idan akaina za ka huce ka yi, ka yi ko me kake tunanin zai sama maka sau\u0199i Sugar, don Allah, ganin ka haka na karya min zuciya&#8230;&#8221; (Littafi na 2, babi na 29)<\/p>\n\n\n\n<p>Da kuma inda aka nuno Majida wadda duk da fushin da ta yi da Altaaf bayan ya bayyana mata cewa yana da yaran da ya samu &#8216;yan gaba da Fatiha take \u0199o\u0199arin ganin ta kwantar mishi da hankali bayan ta sauko da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Mi za mu yi yanzun? Yaran fa?&#8221; (Littafi na 2, babi na 35)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Zina mummunan aiki ne da ke kawo matsalolin da Allah ka\u0257ai yasan yawansu a cikin Al&#8217;umma. Marubuciyar ta yi \u0199o\u0199ari sosai wajen nuna illar hakan akan tauri irin su Altaaf, Tasneem da Fadila. Amma kuma an nuna yadda kowa \u0199addarar shi ke canzawa domin Wadata da su Yaks basu shiga irin wannan hali ba duk da cewa suma sun yi. Hakan ke nuna cewa in Allah ya so sai ya yafe maka kuma ya rufa maka asiri, ko kuma ya bari sai ka koma gare shi tukunna<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Wani Muhimmin \u0253angare da marubuciyar ta ta\u0253o kuma shi ne irin yadda masu Makarantun ku\u0257i ke shiga \u0199alubale a \u0199o\u0199arin su&nbsp; na ganin sun farantawa yaran mai ku\u0257i ko dai saboda kwa\u0257ayin abinda suke samu a wajen iyayen yaran ko kuma don ganin yaran basu bar makarantar ba. Kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Numfashi Principal ta sauke. Kanta har ya fara ciwo, sosai ta gaji da Altaaf a makarantar ta, babu yadda zata yi ne kawai shi yasa. (Littafi na 2, babi na 12)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna mana yadda yin za\u0253i mummuna ke sa watarana mutum ke \u0199arewa cikin da na sani da nadama. Kalli yadda aka bayyana halin da Altaaf ya shiga da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;&#8230;tun lokacin da yaima Nuwaira abinda yai mata yake neman hawaye ko zai samu sau\u0199i amma ya rasa su, haka lokacin da Wadata ya ce baya son ganin shi, da lokacin da yai ma Ashfaq abinda yai mishi, da duk wani lokaci bayan ya gane yayi kuskuren da ba duniyarshi kawai zai ta\u0253a ba har lahirarshi. Kuka yake yau na abinda ya rasa, kuka yake na yadda za\u0253ukan da yayi a rayuwarshi suka jefa kokwanto a cikin lahirarshi. Kuka yake na komai da komai. (Littafi na 2, babi na 30)<\/p>\n\n\n\n<p>Dubi kuma yadda Tasneem ta tsare Ummi take cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Na fa\u0257a miki idan aurena ya mutu a daren farko ke ce, ke ce Ummi, tun a daren ya mutu bai fa\u0257a min ba ne sai yau. Kin rasa surikin da kike mafarkin samu Ummi, bazan yafe miki ba kamar yadda Abba ma ba zai yafe miki ba&#8230;&#8221; (Littafi na 2, babi na 31)<\/p>\n\n\n\n<p>Ga kuma halin da Ummi ta shiga biyo bayan wannan maganar,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Zuciyarta na fara wata irin dokawa kamar zata fito daga \u0199irjinta. Yadda lokaci ya \u0199ure mata take gani, bango ta kama tana mi\u0199ewa, da gudu ta \u0257auki buta tana zagayawa ban\u0257aki don cikinta ya ka\u0257a. Tana da tabbaci babu abinda zai hanata dakuwa a hannun mala&#8217;iku saboda laifukanta masu girma ne, tana tsoron mutuwa, amma bata ta\u0253a jin tsaronta irin na yau ba.&#8217;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Saboda ba wai rasuwar shi take ma kuka ba a wannan lokacin, \u0257an abinda yake kawowa da zata rasa shi ne matsalarta. Yanzun kuma sosai take kukan rasuwar shi, take kukan yadda bata da tabbacin ya yafe mata laifukan da ta dinga yi mishi da \u0199uncin data dinga saka shi, bata ma ta\u0253a ganin laifinta ba balle ta yi tunanin ta bashi ha\u0199uri. (Littafi na 2, babi na 31)<\/p>\n\n\n\n<p>Shi kanshi mahaifin Altaaf yayi tashi nadamar kamar yadda marubuciyar ta bayyana da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ina amsa sunan mahaifinka ne kawai, amma ban ta\u0253a zame maka shi ba. Wannan kuskurena ne, bazan \u0257ora shi akan kowa ba. Duk da na sha gaya ma kaina \u0257an Ammin shi ne fiye da yadda yake \u0257anka&#8230; Ko ba komai ya kwanta a cikin ta, \u0199aunar da ke tsakanin su abune da ba za ka ta\u0253a fahimta ba&#8230;&#8221; (Littafi na 2, babi na 33)<\/p>\n\n\n\n<p>Ammi, wacce ta yi sanadiyar lalacewar Altaaf ma ta yi tata nadamar,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Amma yau cikin idanuwa Barrah ta kalleta tana fa\u0257a mata ta cuci Altaaf, cikin su ma ba kowa ba sai Altaaf, yaron ta da take jin in aka bata dama zata kwashe sauran shekarun da suka rage mata a duniya ta mi\u0199a mishi, yau shi Barrah take fa\u0257a mata ita ce sanadin duk wani abu mummuna da ya same shi, ba wannan ba ne yasa hawayenta suke zuba yau, gaskiyar maganar Barrah \u0257in, mi\u0199ewa Ammi ta yi daga falon saboda zazza\u0253in da take ji ya saukar mata, \u0257akinta ta koma ta kwanta, har lokacin hawayen takaici ne suke zubar mata, a karo na farko a tsawon lokaci da take kuka da idanuwanta, a karo na farko a rayuwarta da da na sani ya kawo mata ziyara, yanayi ne ba\u0199o a wajenta, rufe idanuwanta ta yi ko zata samu sau\u0199i, amma sai duk wani abu da ta yi ba dai-dai ba a farkon aurenta da duk wani abu akan tarbiyar yaranta suka soma kawo mata ziyara suma. (Littafi na 2, babi na 38)<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan wa\u0257annan kuma akwai \u0199ananan jigogi da dama da marubuciyar ta ta\u0253o a cikin wannan littafi domin su koyar da mai karatu darussa da dama irin su \u0199alubalen rayuwar mata a jami&#8217;a, illar mugayen abokai, matsalar ta\u0253uwar \u0199wa\u0199walwa da dai sauran su.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Salo da Sarrafa Harshe<\/h2>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta baje basira iya basira wajen bada labarin wannan littafi. Domin ta yi amfani da salo iri daban-daban kuma duk masu burgewa wajen isar da sa\u0199on labarin a sau\u0199a\u0199e.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Misali:<\/h3>\n\n\n\n<p>\u2022 Salon Koyarwa: Babban salon da marubuciyar ta yi amfani da shi a cikin wannan littafi shi ne salon koyarwa, domin ta yi amfani da wannan salo a kusan kowane shafi na littafin. Ta koyar da darussa da dama da suka shafi zaman rayuwa ta yau da kullum, zamantakewa a tsakanin ma&#8217;aurata, yadda za\u0253i mai kyau yake da muhimmanci a rayuwa da yadda za\u0253i mummuna ke da tasiri wajen rugaza rayuwa. Duk wannan ta yi shi ne cikin harshe mai sau\u0199i yadda mai karatu zai fahimta ba tare da wata wahala ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Salo Mai Armashi: An yi amfani da salo mai jan hankali da armashi sosai da sanya nisha\u0257i ga mai karatu ta hanyar kawo misalai masu jan hankali, motsa zuciya da kuma sa mai karatu dariya da nisha\u0257i a wasu lokutan.<\/p>\n\n\n\n<p>Salon Tafiyar Kura: An yi amfani da salon tafiyar kura ne a cikin wannan littafi, inda marubuciyar ta fara ba da labarin daga tsakiya sannan ta ci gaba da warware shi a hankali a hankali ta hanyar komawa baya ta kawo wani batu sannan ta dawo ta ci gaba daga baya kuma ta sake komawa ta kwance wani a baya kafin ta kuma dawowa ta ci gaba. A zahiri ma, ta kwashe kusan dukkan littafi na \u0257aya ne wajen kawo matsalolin da ke \u0199unshe cikin labarin, yayin da kuma ta kwashe kusan dukkan littafi na biyu ta hanyar fayyace matsalolin da ta kawo a littafi na \u0257aya tare da kawo wasu kuma ta fayyace su. Hakan zai sa mai karatu ya dinga fahimtar batun da ake kai ko wanda za a shiga ba tare da ya sha wahala ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bugu da \u0199ari marubuciyar ta yi amfani da sassu\u0199ar Hausa wajen rubuta labarin ta yadda kowa, zai fahimta. Sai dai an samu kalmomi da jumlolin turanci masu \u0257an dama cikin labarin wa\u0257anda da yawansu tana kawo fassarar su a cikin baka biyu (), sai dai duk da haka yawan amfani da su na&nbsp; iya jawo na\u0199asu ga bun\u0199asar Adabin Hausa a tsakanin makaranta. Sannan ta \u0257an yi amfani da Hausar Zamfara\/Sokoto a wasu wuraren da basu canza komai ko kawo tangar\u0257a a cikin labarin ba sai ma \u0199ara mishi armashi da ta yi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Sarrafa Harshe: Har&#8217;ila yau an yi amfani da kalmomi masu tsima jiki, sa tausayi, kwantar da hankali da kuma gyaran tunani duk a cikin wannan littafi. Wani lokaci ma sai mai karatu ya ji kamar zaunar da shi aka yi ana mishi nasiha game da yadda lamarin ke faruwa. Ko da yake an samu \u0199arancin karin magana, an samu kalamai na hikima masu yawa a cikin littafin.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Misali:<\/h3>\n\n\n\n<p>&#8216;\u0199auna bata cika sai da ganin kuskuren juna. (Littafi na 2, babi na 32)<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Da gaske ne ba&#8217;a komawa baya a goge kuskure&#8230;&#8221; (Littafi na 2, babi na 33)<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Ba ihu ba, ko gaba \u0257aya Abuja da ma\u0199otanta za su taru baya jin za su iya fitar da shi daga \u0257akin Rafiq, duk abinda zai yi sai dai yayi. Ba zai yi kuskure kuma ya ce ba za&#8217;a fa\u0257a mishi gaskiya ba. Shi ya koya musu ganin kuskuren junansu, kuma shi ya koya musu gyarama juna kuskure ba tare da tunanin banbancin shekaru ba indai za su yi hakan da babu raini a ciki. Babu abinda zai canza don koyarwarshi ta biyo ta kanshi yau. (Littafi na 2, babi na 34)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Zubi da Tsari<\/h2>\n\n\n\n<p>Labarin Al\u0199alamin cukurku\u0257a\u0257\u0257en labari ne da ke cike da tarin sar\u0199a\u0199iya, ba don salo ko tsaurinsa ba. Sai don yadda yake cike da \u0199warewa da \u0253atar da bakin duk wani zare da sau\u0199a\u0199awa mai karatu hasashe ko kintatar inda aka dosa. Ma&#8217;ana dai, duk yadda mutum yake tunanin labarin zai kasance, sai ya ga ba haka ba ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta gabatar da zubi da tsarin Al\u0199alamin \u0198addara daidai yadda ya dace da yanayin halayyar taurarin littafin da kuma yadda \u0199arshen labarin ya kasance, ta yadda mai karatu zai \u0199agara ya ga yadda za ta kaya, tare da jefo ba-zata a wasu lokutan. Ta kuma yi amfani da nau\u2019o\u2019in mutuwa wajen kawar da wasu taurarin wa\u0257anda ci gaba da kasancewarsu, za ta haramta warware sar\u0199a\u0199iya cikin littafin. Misali, an kashe baban su Tasneem, kuma an kashe iyayen su Ashfaq da biyu daga cikin &#8216;yan uwansu.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta&nbsp; zayyana labarin Al\u0199alamin \u0198addara ne a cikin litattafai biyu. Ta kasafta littafi na \u0257aya ne zuwa shi babi-babi har goma sha \u0257aya, littafi na biyu kuma ta raba shi zuwa babi-babi har arba&#8217;in da \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p>Gaba \u0257aya labarin ya faru ne a tsakanin garin Kano, Kaduna da kuma Abuja. Sai kuma wani \u0253angare muhimmi da ya faru a \u0199asar Indiya.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ba\u0257oki Na gaske: &#8220;Allah ya \u0257auke maka farin ciki kamar yadda kai min, Allah ya tsayar maka da dukkan al&#8217;amuranka kamar yadda ka tsayar mana da namu, Allah ya tarwatsa maka rayuwarka ta fannin da baka ta\u0253a zato ba, A-Tafida ko? In shaa Allah sunan ka kanshi sai ya zamar maka tashin hankali kamar yadda ya zamar mumin, ka ji ni? Wallahi ba zaka ta\u0253a samun wadataccen farin ciki ba.&#8221; (Littafi na 2, babi na 19) Kuma duk wa\u0257annan abubuwan sun faru da Altaaf a cikin littafin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Ba\u0257oki Na Giri: &#8220;Da baku zo ba&#8230; Da sai dai ya mutu? Nuri me yasa ba zaku fa\u0257a min abin da yake damuna ba? Me yasa bana iya tu\u0199i?&#8221; (Littafi na 1, babi na 2)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Mamaki: Akwai wani abu tattare da ita da ya kasa fahimta, musamman yadda suna ha\u0257a ido duk wata fara&#8217;a da ke fuskarta ta \u0257auke, mamaki, shakku, da wani abu da Rafiq ya kasa fahimta yana maye gurbin fara&#8217;ar, sosai take kallon shi. Zuciyarshi ta ci gaba da dokawa, ji yake tamkar ya santa a wani waje, kusancin da yake ji a tsakanin su ya mishi wani iri. (Littafi na 1, babi na 1)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Tausayi: &#8220;Muneeb karka tafi&#8230; Don Allah ka tsaya tukunna&#8230; Wallahi bansan ya zan yi ba. Innalillahi wa inna ilaihir raji&#8217;un&#8230;. Karka barni tukunna ka tsaya in sake ganin ka&#8230;.&#8221; (Littafi na 1, babi na 11)<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo ma Aroob, gaba \u0257aya cikin kwana biyu rayuwar su ta hargitse, bata ta\u0253a zaton zata kai ranar da Rafiq zai bu\u0257e musu \u0199ofa yana nuna musu hanya da hannun shi ba, sosai abin ya mata wani iri, yadda ya nuna gaba \u0257aya sun takura mishi. (Littafi na 2, babi na 34)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Tsoro: &#8220;Yaya&#8230; Innalillahi wa inna ilaihir raji&#8217;un, Yaya me kayi? Me kai mata? Na shiga uku Yaya&#8230; Ka kasheta ko?&#8221; (Littafi na 1, babi na 7)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 \u018aarsau Na Murna: &#8220;Oh! Wato Addu&#8217;a kika zauna kina min ko? Dame-dame kike ro\u0199a? Fa\u0257a min, hancina ya shige ciki kamar naki ko?&#8221; (Littafi na 1, babi na 2)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Hoton zuci: marubuciyar ta yi&nbsp; amfani da dabarar saka hoton zuci sosai a cikin wannan littafi ta yadda mai karatu zai ji kamar yana wurin abin ke faruwa.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">&nbsp;Misali:<\/h3>\n\n\n\n<p>&nbsp;&#8216;Inda idanuwan Haj. A&#8217;i suke Tasneem ta kai nata, kwance akan kujera wani matashin saurayi ne da Tasneem bata iya ganin fuskarshi ba, saboda kanshi a juye yake, \u0199afarshi \u0257aya a \u0199asa, kusan rabin jikinshi ma ba a kan kujerar yake ba. Juyi \u0257aya zai yi ya fa\u0257o \u0199asa. (Littafi na 1, babi na 6)<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Runtsa idanuwan shi Altaaf yayi yana bu\u0257e su, yayi hakan yafi a \u0199irga, kalaman uku na amsawa a ko ina na jikin shi &#8216;Ka aure ta&#8217;. Dube-dube yake cikin motar, daga gaba har ya juya baya yana hango robar ruwa, jikin shi na \u0253ari ya \u0199arasa ya \u0257auka, bai damu da zafin da ruwan ya \u0257auka ba, bu\u0257ewa yayi yana \u0257aga robar ya sha, amma baiji ya dawo dai-dai ba, iska bata kai mishi inda ya kamata, da sauri ya bu\u0257e murfin motar yana \u0257aga robar ya she\u0199a ruwan daga kanshi zuwa fuskar shi yana wankawa, bakin shi ya bu\u0257e yana jan iska ta ciki saboda tashin hankali.&nbsp; (Littafi na 2, babi na 35)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Taurarin Labari<\/h2>\n\n\n\n<p>Al\u0199alamin \u0198addara littafi ne da ke \u0257auke da taurari masu tarin yawa, wasu manya, wasu kuma masu take musu baya. Akwai taurari guda biyu da suka fi fice, wa\u0257anda ana iya cewa ma gaba \u0257aya su suka \u0257auki nauyin labarin a kafa\u0257un su. Wa\u0257annan taurari kuwa su ne Altaaf Tafida da Kuma Rafiq Mustafa Shettima. Sai dai duk da wannan, Rafiq ya fi Altaaf shiga gwagwarmaya da rikici mai yawa. Kuma \u0199alubalen da ya fuskanta ya fi na kowa a cikin labarin.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Halayen Taurarin Labari<\/h3>\n\n\n\n<p>Ga ka\u0257an daga cikin halayen wasu taurari da suka fito a cikin labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Rafiq Mustafa Shettima:<\/strong> Rafiq mutum ne mai ri\u0199o da addini sosai tare da sanin ya kamata. Yana son iyayen shi da &#8216;yan uwanshi sosai kuma yana \u0199o\u0199arin kamanta adalci a dukkan al&#8217;amuran shi. A ko ina Rafiq ya samu kanshi zai iya cewa baisan menene rashi ba, kalmar bata ta\u0253a \u0199arasowa taku hamsin kusa da inda yake tsaye ba ma. Idan akwai abinda gaba \u0257aya rayuwar shi da ta \u0199annenshi ta ta&#8217;alla\u0199a akai bai wuce \u0199in yin kuskure ba, a cikin rayuwarsu ta makaranta, da ta yau da kullum. Ko da yaushe cikin yin abinda Alhaji Mustafa zai yaba suke yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Banda &#8216;yan uwanshi da suke ciki \u0257aya, mutane shida ne suke da kusanci da shi. Abdallah, Faruk, Zaid, Muneeb, Arfan sannan Samira. Ita ka\u0257ai ce macen da take cikin rayuwarshi take kuma da kusanci da shi wanda babu ala\u0199a ta jini. Ita ma dalilin babanta, Alhaji Habibu da ya kasance babban aminin Alhaji Mustafa ne, kuma abokinshi a kasuwanci da siyasa.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Altaaf Tafida<\/strong>: shagwa\u0253a\u0253\u0253e ne kuma sangartacce na nunawa a kasuwa. Kamar wannan bai isa ba kuma yana shaye-shaye tare da bin mata. Bashi da kunya kuma baya tsoron ja da kowa saboda mahaifiyar shi ta \u0257aure mishi gindi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Tasneem Muftahu<\/strong>: Tana da tausayi tare da sanin ya kamata, amma \u0199o\u0199arin ganin ta kare \u0199annenta daga fa\u0257awa halaka yasa ita ta za\u0253i ta fa\u0257a duk da ta san cewa hakan kuskure ne.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Bara&#8217;atu\/Ummi:<\/strong>&nbsp; Mace masifaffiya mai yawan surutu da rashin godiyar Allah. Ko sallah bata cika yi akan lokaci ba amma ta fiye yawan \u0199orafi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Aslam<\/strong>: Mutumin kirki ne mai sanyin hali da kamala.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 <strong>Alhaji Mustafa Shettima:<\/strong>&nbsp; A zuciyar Alhaji Mustafa Shettima bayan zama cikakken Al\u0199ali yana da sha&#8217;awar siyasa, don haka duk wani taku nashi da hangen abinda gobe zata haifar mishi a cikar burinshi yake yin shi. Bayan \u0199alubale da dama da ya fuskanta a lokacin da ya fa\u0257a harkar siyasa za&#8217;a iya cewa ya shiga da \u0199afar dama, inda ya yi kwamishinan ilimi a lokacin mulkin Fashola. Daga nan ne ya tsaya takarar gwamna inda tun a za\u0253en primary aka kayar da shi, da yake shugaban \u0199asar lokacin nasu ne aka sake bashi kujerar kwamishina ya ri\u0199e. Yanzun kuma yana kan neman tsayawa kujerar mataimakin shugaban \u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta ko ina ana damawa da Alh. Mustafa, ta fannin kasuwanci inda yake da hannun jari da manyan &#8216;yan kasuwa, yake kuma da gidajen mai sama da guda goma. Da wahala ka shiga gari a cikin Najeriya ka kira Mustafa Shettima ba&#8217;a samu wanda yasan shi ba. Yanayin shi kawai yana cika idanuwan mutane tun kafin su san kowanene shi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kurakurai<\/h2>\n\n\n\n<p>Mutum tara yake bai cika goma ba. Akwai &#8216;yan kura-kure ka\u0257an a cikin littafin, wa\u0257anda ba za su tauye kyawun aikin da marubuciyar ta yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022&nbsp; An \u0199aranta littafi na farko an fa\u0257a\u0257a na biyu. Domin littafi na farko babi goma sha \u0257aya ne, shi kuwa littafi na biyu babi arba&#8217;in da \u0257aya ne.<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;\u2022 A cikin littafi na biyu, babi na 20 an nuna cewa marin da wadata ya yi wa Altaaf shi ne farkon lokacin da aka ta\u0253a marin shi. Alhalin kuma a baya an nuna malamar makarantarsu ta ta\u0253a marin shi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An nuna cewa Tariq yana ce wa Yasir abokin yaya a littafi na 1, babi na 40, alhalin kuma a baya an nuna cewa haushin shi yake ji saboda yana ganin kamar yasan abubuwa da yawa akan Ashfaq wanda shi \u0257in bai sani ba.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Tariq dama tun kafin ya ji yadda Yasir \u0257in da taimakon Allah ya kare rayuwar Ashfaq \u0257in a lokuta da dama da suka shiga hatsari kala daban-daban Yaya yake kiran shi, yanzun kalmar tun daga zuciyar shi yake jin tana fitowa, ba su hada jini ba, amman zumuncin su abune da yake da ya\u0199inin har \u0199arshen rayuwar su ne. (Littafi na 1, babi na 40)<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Duk sanda kuka fita tare sai an samu matsala&#8230; Ya akai harbin akanshi kawai ya tsaya? Maganin bindiga ka sha da bai same ka ba?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Babu sirri a tsakanin mu har sai da ka zo.&#8221; (Littafi na 1, babi na 1)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Kuskuren cusawa mai karatu fahimta ko ankararwa ta \u0199arfi da yaji ta shigo cikin littafin. Domin a&nbsp; rubutu musamman kalar wanda ake lura ko kiyaye \u0199a\u2019idojin rubutu, babu wani dalili ko dokar da ta yarda marubuci ya za\u0253i rubuta wata kalma da manyan ba\u0199i ba bisa \u0199a\u2019ida ba. Kuma duk muhimmancin kalmar kuwa. Ba daidai ba ne, sannan yana lalata gan\u0257okin labarin, domin yana sa mai karatu ya tsinkayi inda ake son zuwa. Ya zo a wannan littafin a wurare da dama kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Wai shi ne yake tunanin ganin \u0199arshe yake wa Zafira a yau. Inda yasan ALKALAMIN KADDARA ya yi musu wannan rubutun da ya so ta daga nesa, da bai bari ya \u0257an\u0257ani yadda soyayyarta a kurkusa take ba tunda yasan zai rasa ta. (Littafi na 1, babi na 11)<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Marubuciyar ta shigo cikin labarin A littafi na 1, babi na 2 da cewa: &#8220;\u018aaga mata gira ya yi duka biyun kafin ya matsar da kanshi saitin kunnenta yana fa\u0257a mata maganar da sirri ce kawai a tsakanin su.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 An yi kuskure wajen bayyana Altaaf a matsayin mai son karatu da naci wajen yin tambaya a littafi na 1, babi na 2 da cewa: In akwai abinda ya tsana bai wuce ya kasa fahimtar wani abu ba, ko a makaranta Allah ya mishi nacin tambaya. In bai gane komai ba sam hankalin shi ba ya kwanciya, Majida ta fara sashi ciwon kai.&#8217; Alhali kuma a littafi na biyu an nuna rashin maida hankalin shi akan karatu har sai da ya je jami&#8217;a tukunna, can ma abokai ne suka takura mishi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Labarin su Jawwad da Jawda sam bashi da hurumi a cikin littafin, domin ba a fara maganar su ba sai a littafi na 1, babi na 9 kuma daga nan har zuwa \u0199arshen littafi na biyu ba a ci gaba da shi ba kuma ba a fayyace dalilin wanzuwar su a cikin labarin ba ko kuma yadda rayuwarsu ta \u0199are.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 A littafi na 2, babi na 2, an tsarmo gabatarwa babu gaira ba sabab. Alhali ita gabatarwar&nbsp; ana saka ta ne a farkon littafi in da bu\u0199atar hakan. Kuma wani abin dubawa shi ne, saka shi a daidai wurin babu abinda ya yi face \u0199ara rikita mai karatu tare da sa tunanin shi ya tafi wani wuri can daban ya bar ainahin abinda ke gaban shi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abin Yabawa<\/h2>\n\n\n\n<p>Al\u0199alamin \u0198addara littafi ne da za a iya gabatarwa ga kowanne irin makaranci saboda akwai darussa masu yawa a cikinsa. Babban darasin shi ne, mutum ya yi takatsantsan da irin za\u0253ukan da yake yi. Saboda duk za\u0253in da ya yi watarana zai dawo ya same shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Littafin ya dace da matasa, \u2019yan jami\u2019a, samari da \u2019yammata, har ma da masu burin zuwa jami\u2019a. Sannan kuma ya dace da iyaye da matan aure da sauran rukununan mutane. Saboda su babban jigon labarin ya shafi kusan kowa da kowa ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Bisa wannan dalili, lallai wajibi ne a yaba wa marubuciyar bisa irin namijin \u0199o\u0199arin da ta yi wajen \u0199ir\u0199iro tare da tsara wannan labari cikin tsari da zubi mai tsafta ta yadda kowa zai iya amfana da shi idan ya karanta. Dubi dai yadda ta ajiye wata magana mai muhimmanci da cewa,<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Fadila ta tsammaci gori daga wajen Maimunatu, ko da wasa maganar bata ta\u0253a ha\u0257a su ba, asalima ba shiga harkarta take ba, sukan gaisa, in wani abu ya faru na farin ciki ko jaje a dangin \u0257ayan su sukan je ma juna, yaran su kuma babu wani abu wai shi &#8216;yan Ubanci a zamantakewar su, Hajiya Maimunatu ta tabbatar da hakan bata faru ba. Mace ce mai karamci a nata yanayin. Har abada kuma Fadila ba zata manta abinda sukai mata ba, tana da tabbacin cikin mata dubu kamarta ba za su wuce su biyar da suka taki irin sa&#8217;ar rayuwar data taka ba.&nbsp; (Littafi na 2, babi na 37) Wannan \u0257an yanki kawai na cikin labarin yana nuna yadda ya kamata a \u0257auki \u0199addara ne, kuma ko shi aka bar mutum da shi ya isa abin a gani kuma a yaba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Shawarwari<\/h2>\n\n\n\n<p>Zan so marubuciyar ta ci gaba da yin rubuce-rubuce irin wannan domin al&#8217;ummar mu su amfana daga tarin ilimi da kuma fasahar da take da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan ina mai bata shawarar da ta kauce wa saka sunaye masu kama da juna a cikin labarin ta na gaba domin hakan na iya ru\u0257ar da mai karatu. Sunayen da suka yi kama da juna a cikin wannan littafin sun ha\u0257a da:<\/p>\n\n\n\n<p>Rafiq<\/p>\n\n\n\n<p>Tawfiq<\/p>\n\n\n\n<p>Ashfaq<\/p>\n\n\n\n<p>Tariq<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kammalawa<\/h2>\n\n\n\n<p>Ha\u0199i\u0199a duk wanda ya karanta Al\u0199alamin \u0198addara tabbas zai \u0199aru ta hanyar da bai ta\u0253a tsammani ba, kuma sa\u0199onnin da ke cikin littafin na da \u0199arfin da za su iya canza wa mutum tunanin sa nan take.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga \u0199arshe, yana da kyau mai karatu ya fahimci cewa ilimi da alfanun da ke tattare da wannan littafin sun zarta adadi da kuma rinjayar kuskuren da na gano a littafin. Ko ba komai, mun fahimci yadda \u0199addara take a tsakanin mutane iri daban daban. Ina jinjina ga marubuciyar wannan littafi tare da fatan Allah ya \u0199ara basira da ilmi mai amfani.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuna iya karanta littafin Alkalamin Kaddara <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/alkalamin-1-kaddara-babi-na-daya\/\">na daya<\/a> da <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/alkalamin-kaddara-2-babi-na-daya\/\">na biyun<\/a> dukka anan Bakandamiya Hikaya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Manazarta<\/h2>\n\n\n\n<p>\u018aangambo, A. (1984) <em>Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa<\/em>. Kano: Triumph<\/p>\n\n\n\n<p>Junaidu, I. da \u2018Yar\u2019Aduwa T.M. (2002). Harshen da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited<\/p>\n\n\n\n<p>Sani, M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. Ibadan: University Press Plc<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y. da \u018aangambo, A. (1986) <em>Jagoran Nazarin Hausa<\/em>. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.<\/p>\n\n\n\n<p>Yahaya, I. Y., Zaria M. S., Gusau M.S., da &#8216;Yar Aduwa T.M. (1992) <em>Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1<\/em>. Ibadan: University Press Plc <\/p>\n\n\n\n<p>Zarru\u0199, R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don \u0198ananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. Ibadan: University Press Plc<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan Littafi: Al\u0199alamin \u0198addara (1&amp;2) Marubuciya: Lubna Sufyan Inda aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya (Online) Shekarar Bugu: 2022 Yawan Babi: Littafi na \u0257aya: 11, Littafi na biyu: 41; Jimilla: 52 Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees) Manufar Sharhi: Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba Gabatarwa Akan ce ka gode wa Allah a kowane&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-alkalamin-kaddara-1-2-na-lubna-sufyan\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Alkalamin Kaddara&#8217; 1 &#038; 2 na Lubna Sufyan<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":3733,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[65,29,43,41],"class_list":["post-3724","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-alkalamin-kaddara","tag-book-review","tag-lubna-sufyan","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2022\/09\/Sharhin-littafin-Alkalamin-Kaddara.png?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3724","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3724"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3724\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3733"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3724"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3724"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3724"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}