{"id":3957,"date":"2023-09-08T18:31:47","date_gmt":"2023-09-08T18:31:47","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3957"},"modified":"2023-09-09T10:43:45","modified_gmt":"2023-09-09T10:43:45","slug":"ginin-rubutun-labari-tare-da-lubna-sufyan-1","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/ginin-rubutun-labari-tare-da-lubna-sufyan-1\/","title":{"rendered":"Ginin rubutun labari tare da Lubna Sufyan &#8211; 1"},"content":{"rendered":"\n<p>A lokuta mabanbanta, tare da manya da ma marubuta masu tasowa, idan har mun zo tattaunawa akan rubutu, tambayar ba ta wuce ta yadda kowa yake tsare-tsaren shi kafin fara rubutu, kuma a irin tattaunawar nan ne na fuskanci dukkanmu muna da rauni ta wasu \u0253angarorin, amma babu abinda neman \u0199arin ilimi ba ya amfanarwa. Saboda idan aka tara marubutanmu dukkansu, to kaso mafi rinjaye daga cikinmu ba wai aji muka shiga muka koyi rubutun ba, wayar gari muka yi kwatsam muka tsinci kawunanmu a cikin duniyar rubutun. Sai dai wasu a cikinmu kuma daga baya soyayyar rubutun ta yi mana wata irin shiga da ta sa muka zurfafa wajen bincike da karance-karance da suka shafi rubutu don ganin mun inganta rubutun yadda zai \u0199ara samun kar\u0253uwa a wajen masu karatu, har ma wata rana mu cimma mafarkanmu akai.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan aka zo maganar Adabi gaba \u0257ayan shi, akwai mutane irin su Jibril Adamu Jibrin Rano da yake matu\u0199ar \u0199o\u0199ari wajen kawo mu\u0199alu da suka shafi inganta rubutu, musamman ta \u0253angaren Daidaitacciyar Hausa da kuma \u0199a&#8217;idojin rubutu. Abubuwa guda biyu kenan da nake da matu\u0199ar rauni akan su, shi ya sa zan ba wa duk marubucin da zai bibiyi wannan mu\u0199ala da zan fara, da ya duba shafin shi a manhajar Facebook, da kuma <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/author\/jibrinajr1\/\">wannan link na rubuce-rubucensa<\/a> a nan Bakandamiya Hikaya, domin \u0199aruwa da irin wa\u0257annan mu\u0199alun, saboda ni zan yi magana ne akan nawa hanyoyin da nake bi wajen gina jigo ya zama cikakken littafi. Wato abinda ake kira da &#8216;Book mapping&#8217; a turance.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">1. Jigo <\/h2>\n\n\n\n<p>Duk wanda yake bibiyar litattafaina, zai fahimci cewa ina \u0257aya daga cikin marubutan da suke son &#8216;Realistic fiction.&#8217; Wato \u0199ir\u0199irarren labari, amma irin labarin da ba ya sauka daga al&#8217;adunmu da kuma abinda zai iya faruwa a zahiri. Shi ya sa a duk lokacin da zan nemi jigo, ina fara dubawa ne a kusa da ni, me na gani da ya ta\u0253a zuciyata? Wane labari na ji ya faru, wane abu ne idan na \u0257auke shi zai \u0199ayatar da masu karatu? Aure ko zawarci? Cin amana ko gagarumar soyayya?<\/p>\n\n\n\n<p>Idan \u0257aya daga ciki na ce zan \u0257auka, an yi rubutu akai ya fi a \u0199irga, to ni wanne \u0253angare ne zan ta\u0253a da zai bambanta da sauran? \u0181angaren da idan an fara karantawa ba zai gunduri mai karatun ba, \u0253angaren da zai ri\u0199e masu karatu daga farkon shi har zuwa \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<p>Idan na samu wannan \u0253angaren, to zan gina jigona ne akai, in samu takarda da biro in rubuta jigon.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali;<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Jigo: Zumunci, \u0253angaren zumuncin da yake \u0199ulluwa ba tare da ala\u0199a ta jini ba.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Sa\u0199on da nake son isarwa: Anan ina zurfafa tunani, sai in fito da duk wani sa\u0199o \u0199arami ko babba da nake so in isar wa masu karatu, yadda idan na fara rubutun, zan \u0257auko wannan takardar in duba in ga shin labarin na tafiya tare da wa\u0257annan sa\u0199onnin ko kuwa akasin hakan.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Sai kuma ina raba jigona zuwa gida uku kamar haka;<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>A. Farko (Kashi na farko)<\/p>\n\n\n\n<p>B. Tsakiya (Kashi na biyu)<\/p>\n\n\n\n<p>C. \u0198arshe (Kashi na uku)<\/p>\n\n\n\n<p>A mahangata, kuma yayin rubutu, kowanne a cikin jigon nan shi ma yana da \u0253angarori guda uku kamar haka;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>A. Farko<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Farkon kashin farko<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Tsakiyar kashin farko<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; \u0198arshen kashin farko<\/p>\n\n\n\n<p><strong>B. Tsakiya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Farkon kashi na biyu<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Tsakiyar kashi na biyu<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; \u0198arshen kashi na biyu<\/p>\n\n\n\n<p><strong>C. \u0198arshe<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Farkon kashi na uku<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; Tsakiyar kashi na uku<\/p>\n\n\n\n<p>&#8211; \u0198arshen kashi na uku<\/p>\n\n\n\n<p>Idan muka kalli wa\u0257annan rabe-raben na sama, akansu za mu iya gina jigo ta yadda zai tashi har ya zama cikakken littafi. Mene ne zai faru daga farko? Tsakiya da kuma \u0199arshe, a farkon labarin, za a fara ne daga tushe? Kan iyaye ko kakannin taurarin, sai a zo kan iyayen, sai kuma a fara hasko taurarin, inda kashi na farko zai \u0199are, sai a tsallaka kashi na biyu a ga abubuwan da za su faru, hargitsin da yake cikin labarin, daga farko, tsakiya da kuma \u0199arshen hargitsin, sai kuma kashi na \u0199arshe inda za&#8217;a warware duka \u0199ullin da yake cikin labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>Ina fitar da duk wannan ne saboda lokacin da zaren labarin ya fara \u0199wace min sai in \u0257auko takardata in duba in ga yadda na tsara abubuwan za su kasance. Don wani lokacin ma bayan na gama yin duk wannan, na kan rarraba shi zuwa shafi-shafi sai in yi tsokaci na ka\u0257an daga cikin abinda zai faru a shafin, duk da cewa lokuta da dama yanayin tsarin shafukan suna canzawa.<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;Wani abin da na yi hasashen zai faru gaba \u0257aya a shafin, sai ya \u0257auke ni shafuka uku idan na fara fa\u0257a\u0257awa bai kai \u0199arshe ba, amma dai yana taimaka min sosai a duk lokacin da na samu abinda ake kira da &#8220;Writer&#8217;s block&#8221; a turance, na kan duba in gani. Kuma za ku ga daga fara rubutun ma sai wasu abubuwan da ba ka tsara da su ba su dinga zuwa maka, za ka dinga cin karo da gyare-gyaren da ba za a rasa a jigon ba da zai \u0199ara wa labarinka armashi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">2. Yare da gari<\/h2>\n\n\n\n<p>Yare ne abu na biyu da nake dubawa bayan gina jigo, yaren taurarina, Hausawa ne? Fulani ko Barebari? Shin yaruka nawa ne ma nake so a cikin littafin gaba \u0257aya. Idan na rubuta su, sai kuma in tsallaka in za\u0253i gari. Garin da zan gina labarina a ciki kenan. Birni ne daga farko har \u0199arshe? Ko daga \u0199auye ne ake dawowa birni, ko kuma duka biyun ne, \u0199auye da birni. Idan na gama yanke hukunci, sai in fito da sunan birni, da \u0199auyukan. Sannan yaren da na za\u0253a, idan Hausawa ne, &#8216;yan asalin wacce jaha ce? A jahar tasu suke zaune ko kuma wani dalili ya sa sun baro tasu zuwa wata.<\/p>\n\n\n\n<p>Nakan fito da duka wa\u0257annan abubuwan, sai kuma in duba in ga wa\u0257anne abubuwa nake bu\u0199ata a wa\u0257annan garuruwan da na za\u0253a, na san garin? Na ta\u0253a zuwa? Idan na san garin dole ba zan rasa sanin wasu abubuwa dangane da garin ba, na kan bu\u0199aci abubuwa kamar haka;<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Sunayen unguwanni, inda masu hali sukafi zama, da kuma akasinsu, a wajen unguwanni ina \u0199arawa da duba shekarun da labarina zai ginu akai. Misali daga 1985 ne zuwa 2020, saboda haka ina bu\u0199atar sanin tsofaffin unguwanni da suka wanzu tun daga wancan \u0199arnin, da ma sababbi.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Makarantu, boko da Islamiyya. Haka suma wa\u0257annan , ina bu\u0199atar wanda suka wanzu daga \u0199arnin shekarar ginin labarin.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Gidajen cin abinci irin su restaurant.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Wuraren sha\u0199atawa.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Sunayen Otal<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Asibitoci na masu zaman kansu da kuma na gwamnati.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Na kan zurfafa bincike na daga manhajar Google har ma da neman mutane mazauna wa\u0257annan garuruwan don neman \u0199arin&nbsp; haske akan duk wani abu da nake nema. Irin wa\u0257annan binciken duk idan na kammala ina adana su ne ko da zan sake bu\u0199atar amfani da su a gaba. Sannan ta \u0253angaren yare, idan misali ina so in yi amfani da Fulatanci a matsayina na Bahaushiya, na kan duba in ga Fulanin wanne gari nake son sakawa, na Adamawa ko Gombe? To sai in zo in yi cigiya har sai na samu ko da mutum \u0257aya ne Bafulatani ko Bafulatana mazauna wannan jahar, don in yi musu wasu &#8216;yan tambayoyi game da al&#8217;adunsu da kuma sunayen da zai iya kasancewa zan bu\u0199ata a wajen rubutun. Zan kuma ro\u0199i alfarmar sake tuntu\u0253arsu idan na zo wani mataki a cikin rubutun da zan sake bu\u0199atar neman taimakon su. Wata\u0199ila ina so in \u0257an saka magana ne da yaren jefi-jefi, to wannan maganar da taurarina za su fa\u0257a sai in zo in tambayi yadda za a fa\u0257e shi da yaren, ni kuma in je in rubuta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar yadda na fa\u0257a ne daga farko, ina son ya kasance ban sauka daga kan abinda zai iya faruwa a zahiri ba, shi ya sa tun daga matakin farko zuwa \u0199arshe na kan yi iya \u0199o\u0199arina wajen binciko abubuwa irin wa\u0257annan. Misali a ce zan hasko cikin makarantar jami&#8217;a, mu \u0257auki ABU Zaria misali, to ina so duk wani wanda ya yi jami&#8217;ar ya gama, ko yake kan yi ya ji cewa nima \u0257in tamkar a nan na yi karatuna, saboda na zayyana abubuwan da suke faruwa a makarantar kamar yadda suke. To idan gari ne ma, ina so ko da ban ta\u0253a zuwa ba, to a cikin masu karatu mazauna garin su ji kamar ni \u0257in ma a garin nake zaune saboda yadda na fito da asalin al&#8217;adunsu, na yi magana kan makarantun da suke da su, bawai shaci-fa\u0257i ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bincike abune mai matukar muhimmanci a wajen duk wani marubuci, kuma kin yin bincike yana jawo nakasu mai girma ga labari. Shi ne za ka ga misali, ka dauki ma&#8217;aikacin wata masana&#8217;anta da albashin shi bai wuce dubu hamsin ba, amman yana hidimar wanda yake daukar albashin dubu dari biyar. Amman idan ka yi bincike zaka kaucewa faruwar irin wannan abin, kuma wannan binciken hanya ce ta karin ilimi a gareka dama makaranta gabaki daya. Ya zamana idan kana da ma&#8217;aikacin banki mai matakin karatun diploma to ka bincika ka san wanne irin aiki masu wannan matakin suke yi a bankuna, sannan ya yanayin albashinsu yake. Wadannan abubuwan suna matukar karawa labari armashi.<\/p>\n\n\n\n<p>A kashi na gaba za mu yi magana ne akan abinda ake kira &#8220;character development&#8221; a turance, wato gina su kansu jaruman littafin.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A lokuta mabanbanta, tare da manya da ma marubuta masu tasowa, idan har mun zo tattaunawa akan rubutu, tambayar ba ta wuce ta yadda kowa yake tsare-tsaren shi kafin fara rubutu, kuma a irin tattaunawar nan ne na fuskanci dukkanmu muna da rauni ta wasu \u0253angarorin, amma babu abinda neman \u0199arin ilimi ba ya amfanarwa.&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/ginin-rubutun-labari-tare-da-lubna-sufyan-1\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Ginin rubutun labari tare da Lubna Sufyan &#8211; 1<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":10,"featured_media":3961,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[2],"tags":[3,8],"class_list":["post-3957","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-rubutun-labari"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Ginin-rubutun-labari-tare-da-Lubna-Sufyan-1.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3957","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/10"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3957"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3957\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3961"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3957"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3957"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3957"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}