{"id":3967,"date":"2023-09-17T18:11:58","date_gmt":"2023-09-17T18:11:58","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3967"},"modified":"2023-10-21T17:29:45","modified_gmt":"2023-10-21T17:29:45","slug":"burina-shi-ne-na-zama-babbar-marubuciya-da-duniya-za-ta-yi-alfahari-da-irin-rubutunta-rukayya-ibrahim-lawal","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/burina-shi-ne-na-zama-babbar-marubuciya-da-duniya-za-ta-yi-alfahari-da-irin-rubutunta-rukayya-ibrahim-lawal\/","title":{"rendered":"Burina shi ne na zama babbar marubuciya da duniya za ta yi alfahari da irin rubutunta &#8211; Rukayya Ibrahim Lawal"},"content":{"rendered":"\n<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ta ke yi da fitattun marubuta na wannan zamani, a wannan karon mun samu tattaunawa kai tsaye da gwarzuwar marubuciya Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu da ma sauran abubuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwarta.<\/p>\n\n\n\n<p>Ga dai yadda hirar ta kasance:<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Malama Ru\u0199ayya, za mu so mu ji tarihin rayuwarki a ta\u0199aice, in ba za ki damu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Da farko dai sunana Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal, wacce a duniyar marubuta aka fi sani da Ummu Inteesar. An haife ni a shekarar 1997, na yi Primary School \u0257ina a Family Support Model Primary School Sokoto, daga 2003 zuwa 2009, daga nan na shiga Nana Girl Secondary School Sokoto na yi JSS \u0257ina inda na fice daga makarantar zuwa Abdul Rashid Adisa Raji Speacial School, a can na yi candy na a shekarar 2015. A lokacin ban samu damar komawa makaranta ba sai a 2017, inda na shiga Ummaru Ali Shinkafi Polytechnic Sokoto, ban shekara ba na fice saboda wasu dalili. Nan ma ban kuma shiga wata makarantar ba sai a shekarar 2019 na shiga Shehu Shagari College of Education Sokoto, inda na karanta ECCE (wato Early Childhood Care and Education) yanzu haka na kammala har na kar\u0253i sakamakona.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka ma na yi karatun addini a Islamiyyar Sahabi Abubakar Siddik da ke cikin garin Sokoto. A can na yi saukar Al\u0199ur&#8217;ani ta farko a shekarar 2012, na sake yin sauka ta biyu a Islamiyyar dare mai suna Tahafizul \u0198ur&#8217;an Wattarbiyatul Islamiyya a 2013. Bayan sauka na karanta littattafai da dama na addini, wanda kuma har yanzu ana kan neman ilimi. Wannan shi ne ta\u0199aitaccen tarihina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ma Sha Allah! To, a wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya abin da ya ja ra&#8217;ayina shi ne yadda matsaloli suke faruwa a society namu, a lokacin baya akwai wani abun da ke faruwa wanda yake ci mini tuwo a \u0199warya, na rasa hanyar magance shi, sai na nemi wata marubuciya na ba ta labarin domin ta rubuta shi tare da kawo mafita, ta yi iya bakin \u0199o\u0199arinta amma sa\u0199on bai isa yadda nake so ba, ganin hakan ya sa na fara tunanin me zai hana ni na rubuta, tunda a baya ina da ra&#8217;ayi a kan rubuce-rubucen.<\/p>\n\n\n\n<p>Dangane da fara rubutu kuma, na fara sakin littafina ne a November 2019, Soyayyar Meerah shi ne na farko da na fara saki, duk da ba shi ne littafin farko da na rubuta ba. Sai dai sauran suna rubuce ne a exercise book \u0257ina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Za mu so mu ji sunayensu da kuma bakandamiyarki daga cikinsu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Littafaina da suka watsu a media yanzu guda tara ne, ban da wasu gajerun labarai, sai wani na ha\u0257aka da muka fara ni da wata \u0199awata.<\/p>\n\n\n\n<p>Sunayen labaran gasu kamar haka;<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li>Soyayyar Meerah<\/li>\n\n\n\n<li>&#8216;Yar Gantali<\/li>\n\n\n\n<li>Rikicin Masoya<\/li>\n\n\n\n<li>A Sanadin Kama<\/li>\n\n\n\n<li>Halittar Allah Ce<\/li>\n\n\n\n<li>Wata Unguwa<\/li>\n\n\n\n<li>Gidan Duhu<\/li>\n\n\n\n<li>Sharri Kare Ne<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Sai wanda zai fita nan ba da jimawa ba in Sha Allah.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8216;Yar Gantali shi ne bakandamiyata domin shi ya kawo ni duniyar rubutu.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"682\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-1024x682.jpg?strip=all\" alt=\"Hira da Rukayya Ibrahim Lawal\" class=\"wp-image-3986\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-1024x682.jpg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-300x200.jpg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-768x512.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-1200x800.jpg?strip=all 1200w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2-930x620.jpg?strip=all 930w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2.jpg?strip=all 1280w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2.jpg?strip=all&amp;w=512 512w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-2.jpg?strip=all&amp;w=450 450w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal kenan yayin da take kar\u0253ar shaidar girmamawa daga hannun Mai Girma Gwamna Dikko Ra\u0257\u0257a na Jihar Katsina a wurin bikin Gasar \u018aangiwa Literary da aka gudanar a 2022<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Idan har ubangida shi ne wanda ya koya wa mutum rubutu to ni kam gaskiya ba ni da shi, sai dai daga baya na samu masu duba mini rubutuna bayan na kammala, wa\u0257annan mutanen kuwa su ne:<br>Yaya Ibrahim Muhammad Indabawa da kuma Yaya Yusuf Gumel, Jibrin Adamu Jibrin Rano, da Mutta\u0199a A Hassan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ki ka ta\u0253a karantawa da ya fi burge ki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> littafin gwanina Abubakar Auyo mai suna Jarrabi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kin ta\u0253a shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin ta\u0253a yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina shiga gasanni sosai. Alhamdulillahi! Nasarori an samu ana kuma kan samu. A shekarar 2020 na ci wata gasa da wata \u0199ungiyar marubuta ta saka, na yi ta 3. Sai a 2021 kuma na samu Satifket na shiga zagayen biyun \u0199arshe a gasar Majalisar Marubuta, a wannan shekarar labarina ya fito a cikin 25 mafiya zarra a gasar BBC. A 2022 kuma na samu satifket na girmamawa a gasar Aliyu Muhammad Research Library Gusau Institute, da kuma a gasar \u018aan Giwa Literary. A wannan shekarar kuma labarina ya fito a cikin uku da za a karrama a gasar Gusau Institute da za a gudanar a watan Disamba In Sha Allah.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ma Sha Allah. To, idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Wasu lokutan ina fitar da sekelaton na labari, na kan yi blocking kuma nakan fitar da profile character, wasu lokutan kuma kai tsaye na ke fara labari idan komai na labarin yana kaina. A ta\u0199aice dai ba yadda ba na yi, don har a tsakiya na kan faro labari kafin in yi farko da \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na kan samu littafi na rubuta sabuwar idea ne, kuma na kan iya ha\u0257a rubutun labari biyu a lokaci \u0257aya musamman a lokutan baya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ki kan \u0257auki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan \u0257auke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Bincike shi ne abu mafi cinye mini lokaci a rubutu, na kan yi jira iya jira har zuwa lokacin da binciken nawa zai kammala, wala&#8217;alla na fara labarin ko ban fara ba ba na ciyarwar sai na tabbatar da komai ya yi mini yadda nake so. Na kan \u0257auki Wata \u0257aya har zuwa biyu ma, wani har shekara ya danganta da yadda idea na labarin ke zuwa mini.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina samun jigona ne daga tunani, wani lokacin kuma idan ana hira na ji wani abin da ya kamata na rubuta sai na \u0257auke shi a matsayin jigo, wasu lokutan na kan samu jigo a cikin bacci, ko kallon hoton wani abu, ko yayin da nake tafiya a hanya. Hanyoyin dai da yawa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Kamar yadda na fa\u0257a maka nakan fitar da profile character kafin na fara rubutu. Sannan kowane tauraro a labari sunansa da \u0257abi&#8217;arsa da shekarunsa suna a rubuce, ka ga ba zancen mantawa kenan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko kin ta\u0253a amfani da wani \u0253angare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Tabbas na ta\u0253a yin wannan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala lokacin rubuta shi?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Wata Duniya shi na fi shan wahalar rubutawa saboda na \u0257auko wani jigo na musamman da ba na jin an ta\u0253a yin rubutun Hausa novel a kai. Ga kuma zurfaffen bincike, don kusan kowacce gaba ta labarin bincike ne ya gina ta.<br>Littafin da ya fi mini sau\u0199in rubutawa shi ne Rashin Gata, domin shi gajeren labari ne da na rubuta a zama \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne irin \u0199alubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake \u0199alubalen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> To dama a rayuwa ba za a rasa \u0199alubale ba, in ko da akwai \u0199alubalen da na fuskanta bai wuce yadda wasu &#8216;yan&#8217;uwa da kuma abokan mu&#8217;amala suke sukar harkar rubutun da nake yi ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Duka taurarin labaraina masu halayen kirki ina son su, amma na fi son yaro Abdurraza\u0199 (jarumin cikin Halittar Allah Ce) yadda ya sha wahala da kuma jajircewar da ya yi a baya su ne suka saka nake tausayi da \u0199aunarsa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"682\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-1024x682.jpg?strip=all\" alt=\"Hira da Rukayya Ibrahim Lawal\" class=\"wp-image-3989\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-1024x682.jpg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-300x200.jpg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-768x512.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-1200x800.jpg?strip=all 1200w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3-930x620.jpg?strip=all 930w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3.jpg?strip=all 1280w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3.jpg?strip=all&amp;w=512 512w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Rukayya-Ibrahim-Lawal-3.jpg?strip=all&amp;w=450 450w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na sha shiga irin wannan yanayin ma. Ina magance hakan ta hanyar karance-karance da kallace-kallace ko kuma na \u0257auki tsawon lokaci ina bacci, to daga na tashi sai ka ga abin ya kau.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> In ga labarina ya samu kar\u0253uwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Rubutun dai ne.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Saboda hakan na da tasiri a rayuwata.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A naki ra&#8217;ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Kowanne daga cikinsu yana da fa&#8217;idarsa, sai dai wallafawar ta fi saboda ko yaya ne ba za ka nemi labarin ka rasa ba matu\u0199ar da kwafe a hannunka sa\u0253anin na online da watarana a matsayinka na marubucinsa ka kan iya rasa shi gaba-\u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al&#8217;umma?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> A gaskiya marubuta mutane ne masu matu\u0199ar tasiri a cikin al&#8217;umma, domin kuwa suna aike wa mutane sa\u0199onsu da gyararraki ta hanyar yin amfani da kaifin basirarsu suke warware matsalolin da ke addabar wasu mutanen. Don haka marubuta suna da matu\u0199ar tasiri. Tabbas sa\u0199on da suke aikawa yana isa cikin gaggawa kuwa, domin da yawan mutane sun gyara rayuwarsu a dalilin wasu rubutuka da suka karanta.<br>Ni kaina akwai wa\u0257anda suka fa\u0257a mini sun \u0257auki darussa da dama a dalilin rubutuna, kai zan iya cewa wannan abun ma ya zama gama-gari yanzu, don ga shi nan muna gani, ko a haka na bar ka nasan kin fahimci sa\u0199on ya fita.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Akwai guda biyu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wane ne tauraronki a cikin marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Taurarona a maza shi ne Abdul&#8217;aziz Sani Madakin Gini, a mata kuwa akwai Halima K. Mashi, Jamila Umar Tanko, Abubakar Auyo. Idan kuma aka dawo online akwai A&#8217;isha Ali Garkuwa, Jibrin Adamu Jibrin Rano, Balkisu Garkuwa. wa\u0257annan su ne madubina a rubutu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce shawara za ki bawa &#8216;yan&#8217;uwanki marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Shawarar da zan ba su ita ce, su tsarkake al\u0199alummansu sannan su yi rubutu mai ma&#8217;ana da fa&#8217;ida, wanda ko bayan ransu mutane za su yi alfahari da su. Kuma su dinga lalubo muhimman jigo na abubuwan da suke addabar al&#8217;umma a wannan zamani, kuma su guji wula\u0199anci domin wula\u0199anta \u0257an&#8217;dam ba shi da amfani, ba wai don kana ganin ka zama wani a yanzu ba sai ka tsiri wula\u0199anci, wannan abu ne da zai iya rusa \u0257aukakar da ka samu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne burinki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> To, burina shi ne na zama babbar marubuciya wacce duniya za ta yi alfahari da irin rubutukana, kuma rubutuna ya tasirantu a zuciyar mutane ta yadda za su gyara tasu rayuwar.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Fim ya fi saurin isar da sa\u0199o. Abin da ya sa shi ne, ina ganin cewa kamar a fim \u0257in sa\u0199unan da nake son turawa za su fi saurin isa tare da tasirantuwa a zuciyar masu kallo.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce shawara za ki iya ba wa sabuwar marubuciya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Shawarata a gare ta ita ce, ta nutsu ta mayar da hankali sosai wurin samo jigo mai kyau da ma&#8217;ana domin shi rubutu abu ne da bai kamata a fa\u0257a masa haka kawai ba ba tare da sanin yadda yake ba. Ta kuma shiga bincike da nazari akan harshen Hausa da \u0199a\u2019idojin rubutu domin ta samar da labari mai ma&#8217;ana da da\u0257in karatu, sannan ta yi bincike a kan zahiriyar rayuwa. Matu\u0199ar ta yi hakan to rubutunta zai samu kar\u0253uwa nan da nan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce shawara za ki ba wa marubuta masu \u0257auko labari su kasa \u0199arasawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Shawarata a gare su shi ne, su fara tsara komai kafin fara rubutu, yawanci rashin tsarawar ke saka labari ya ficewa mutum a rai. Sannan zan ba mu shawara, Mu sa juriya mu cire tsoro ko fargaba, mu nace tare da jajircewa kuma mu kaifafa tunaninmu tare da yin bincike a kan abin da za mu yi rubutu a kai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Daga \u0199arshe, me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Abin da zan iya cewa game da bakandamiya hikaya, shafi ne mai kyau don adana littafai da karanta su, kuma yana da kyau marubuta suna amfani da shi don \u0253oye labaransu gudun rasawa.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi hira da Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal ne a ranar Talata, 08 ga watan Satumba 2020; 9am &#8211; 6pm kai tsaye a taskar Bakandamiya. An kuma tace tare da sabunta hirar a ranar 12 ga watan Satumba 2023.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa:<\/strong> Maryam Haruna tare da Hauwa&#8217;u Muhammad<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tacewa da sabuntawa:<\/strong> Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<br>12-09-2023<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ta ke yi da fitattun marubuta na wannan zamani, a wannan karon mun samu tattaunawa kai tsaye da gwarzuwar marubuciya Ru\u0199ayya Ibrahim Lawal. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu da ma sauran abubuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwarta. Ga dai yadda&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/burina-shi-ne-na-zama-babbar-marubuciya-da-duniya-za-ta-yi-alfahari-da-irin-rubutunta-rukayya-ibrahim-lawal\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Burina shi ne na zama babbar marubuciya da duniya za ta yi alfahari da irin rubutunta &#8211; Rukayya Ibrahim Lawal<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":3992,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,78],"tags":[79,81,84],"class_list":["post-3967","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-interviews","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews","tag-rukayya-ibrahim-lawal"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Hira-da-Rukayya-Ibrahim-Lawal.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3967","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3967"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3967\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3992"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3967"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3967"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3967"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}