{"id":3968,"date":"2023-09-23T20:59:38","date_gmt":"2023-09-23T20:59:38","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3968"},"modified":"2023-09-23T20:59:44","modified_gmt":"2023-09-23T20:59:44","slug":"alamomin-daidaita-rubutu-12-da-yadda-ake-amfani-da-su","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/alamomin-daidaita-rubutu-12-da-yadda-ake-amfani-da-su\/","title":{"rendered":"Alamomin daidaita rubutu 12 da yadda ake amfani da su"},"content":{"rendered":"\n<p>Alamomin daidaita rubutu wani fanni ne na rubutu, ko kuma a ce na ilimi mai zaman kansa. Wannan fanni ya shafi wasu \u0199a&#8217;idoji ne da tilas ne a yi amfani da su a cikin rubuce-rubuce, matu\u0199ar dai ana so a yi rubutun bisa tsari da nagarta. Amfani da alamomin daidaita rubutu yadda ya dace yana sau\u0199a\u0199a fahimtar abinda aka rubuta ga masu karatu. \u0198in yin amfani da su, ko amfani da su ta hanyar da bai dace ba kuwa na sa karatun marubuci ya gundiri masu karatu kuma su kasa fahimtar sa\u0199on da ke ciki.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ya sa a cikin wannan mu\u0199ala zan bayyana wa\u0257annan alamomi da kuma yadda ake amfani da su a cikin rubutu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>1. AYA (Full Stop .):<\/strong> Aya alama ce da ke zuwa a \u0199arshen jumla. Alamar aya kuwa shi ne ( . ) sannan kuma ana amfani da su wajen raba haruffan da aka ta\u0199aita su a cikin suna. Alamar aya na nuna kammaluwar magana ce a cikin jumla, ko kuma dakatawa na \u0257an wani lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Hausawa jajirtattun mutane ne.<\/li>\n\n\n\n<li>Abdulhadi A. Abubakar<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Idan kun lura da kyau za ku ga cewa an yi amfani da alamar aya a \u0199arshen jumlar farko domin nuna alamar dakatawa, a jumla ta biyu kuma domin nuna rarrabuwar ta\u0199aita haruffa a rubutun suna.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>2. WA\u0198AFI (comma ,):<\/strong> Shi ma dai alama ce ta dakatawa, amma shi dalatarwarsa ba ta kai tsawon na aya ba. Amafnin wa\u0199afi shi ne a ba wa mai karatu damar hutawa kafin ya ci gaba da karatu. Sannan kuma, duk inda aka saka wa\u0199afi, to da \u0199aramin ba\u0199i za a tashi da rubutu ba da babban ba\u0199i ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Da ace ni ne kai, da ba haka zan yi ba.<\/li>\n\n\n\n<li>Ko da suka isa bakin kasuwar, sai suka yada zango a nan.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>3. WA\u0198AFI MAI RUWA (semi colon ;):<\/strong> Wannan ma alama ce ta dakatawa, sai dai ita dakatarwarta ta fi ta wa\u0199afi tsawo, amma ba ta kai ta aya kuma tsawo ba. Ana amfani da wannan alama ne a cikin jimla mai tsawo don ta rarrabe abubuwan da suke da ala\u0199a da juna.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Ana dubawa sai ga mage tsuru-tsuru; da gari ya waye aka kai ta gidan mai ita.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Ana kuma iya amfani da alamar wajen rubuta kalmomi kamar haka,<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Jibgege; Shar\u0253e\u0253e. d.s<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>4. AYA RUWA BIYU (colon :):<\/strong> Alama ce da ake sakawa a gaban batu, wato topic kenan da Turanci, wani lokaci kuma akan kira su da tagwan aya. Wannan alama tana nuni ne da za a fayyace wa mai wani abu a gaba dalla-dalla.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Asibiti: Wurin da ake kula da marasa lafiya.<\/li>\n\n\n\n<li>Wushirya: Tazarar da ke tsakanin ha\u0199oran mutum na gaba da ke sama.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>5. ALAMAR MOTSIN RAI (exclamation mark !):<\/strong> Alama ce da ake sakawa a gaban duk wata kalmar da ke nuna mamaki, firgici, murna, annushuwa ko tashin hankali.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Wayyo!<\/li>\n\n\n\n<li>Wohoho!<\/li>\n\n\n\n<li>Ahayye!<\/li>\n\n\n\n<li>Tir\u0199ashi!<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>6. BAKA BIYU (brackets ()):<\/strong> Ana amfani da wannan alama ne domin yin sharhi ko fayyace wata kalma da ta gabace ta. Ta hanyar yin amfani da alamar baka biyu, marubuci na iya bayyana ma&#8217;anar wata kalma da ya rubuta a baya domin mai karatu ya fahimci abinda yake nufi sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u0198walla (hawaye)<\/li>\n\n\n\n<li>Aisha ta ci na jaki (duka).<\/li>\n\n\n\n<li>Gobe za mu je birnin gwamna (Kaduna)<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>7. KARAN \u018aORI (hyphen -):<\/strong> Ana amfani da wannan kalma ne wajen ha\u0257a har\u0257a\u0257\u0257un suna.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Gama-gari<\/li>\n\n\n\n<li>Ru\u0257a-kuyangi<\/li>\n\n\n\n<li>Ci-bari-kallo<\/li>\n\n\n\n<li>Ba-ji-ba-gani<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>8. ALAMAR ZARCE (dash &#8230;):<\/strong> Alama ce da ake sakawa a gaban yankin maganar da ba a kammala ba, dalili, so ake mai karatu ya \u0199arasa da kansa.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Duk wanda ya ce kai na da nama&#8230;<\/li>\n\n\n\n<li>Wanda duk bai ji bari ba&#8230;<\/li>\n\n\n\n<li>Da wasa da yaro&#8230;<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>9. ALAMAR \u0198AULI (quotation marks):<\/strong> Alama ce da ke nuna cewa alamar da ke tsakaninsu maganar wani ce ba ta marubuci ba. Ana yin amfani da ita ne saboda mai karatu ya fahimci maganar da kyau, kuma duk abin da ke tsakaninsu haka yake babu ragi, babu \u0199ari. Ana rubuta su ne bayan wa\u0199afi, sannan da babban ba\u0199i ake rubuta duk kalmar farko da ta zo a cikinsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Ya yi gyaran murya, sannan ya ce, &#8220;Na yi murna da zuwan ku.&#8221;<\/li>\n\n\n\n<li>Bari ku ji abinda ta ce, &#8220;Mijinta dukanta yake yi kullum.&#8221;<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>10. ALAMAR TAMBAYA (question mark ?):<\/strong> Wannan alama ita kuma takan zo ne yayin duk da aka yi tambaya. Da babban ba\u0199i ake tashi bayan an yi amfani da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Waye a nan?<\/li>\n\n\n\n<li>Yaushe ka zo?<\/li>\n\n\n\n<li>Ashe sun tafi?<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>11. KARAN TSAYE (stroke \/):<\/strong> Alama ce da ake amfani da ita wajen raba kalmomi ko lambobi da ke da kusanci a tsakaninsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>09\/09\/2023<\/li>\n\n\n\n<li>Sama\/\u0199asa<\/li>\n\n\n\n<li>Malami\/malama<\/li>\n\n\n\n<li>Yau\/gobe<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>12. BA\u0198IN HAMZA (apostrophe &#8216;):<\/strong> Ana amfani da ba\u0199in hamza ne a tsakiyar kalma domin fitar da ma&#8217;anarta.<\/p>\n\n\n\n<p>Misali:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>ma&#8217;aikata ba maaikata ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0257an&#8217;uwa ba \u0257anuwa ba<\/li>\n\n\n\n<li>la&#8217;akari ba laakari ba<\/li>\n<\/ul>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Alamomin daidaita rubutu wani fanni ne na rubutu, ko kuma a ce na ilimi mai zaman kansa. Wannan fanni ya shafi wasu \u0199a&#8217;idoji ne da tilas ne a yi amfani da su a cikin rubuce-rubuce, matu\u0199ar dai ana so a yi rubutun bisa tsari da nagarta. Amfani da alamomin daidaita rubutu yadda ya dace yana&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/alamomin-daidaita-rubutu-12-da-yadda-ake-amfani-da-su\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Alamomin daidaita rubutu 12 da yadda ake amfani da su<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":4000,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[2],"tags":[85,86],"class_list":["post-3968","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-writing-tips","tag-daidaita-rubutu","tag-punctuation"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/09\/Alamomin-daidaita-rubutu-12-da-yadda-ake-amfani-da-su.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3968","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3968"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3968\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4000"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3968"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3968"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3968"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}