{"id":3977,"date":"2023-10-06T16:09:11","date_gmt":"2023-10-06T16:09:11","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=3977"},"modified":"2023-10-06T16:10:32","modified_gmt":"2023-10-06T16:10:32","slug":"kadan-daga-kaidojin-rubutun-hausa-domin-marubuta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/kadan-daga-kaidojin-rubutun-hausa-domin-marubuta\/","title":{"rendered":"Kadan daga ka&#8217;idojin rubutun Hausa domin marubuta"},"content":{"rendered":"\n<p>Marubuta da dama na fama da \u0199arancin fahimtar \u0199a&#8217;idojin rubutun Hausa, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mafi yawancinsu ba harshen Hausa suka karanta ba. Wasu sun fara rubutu ne kawai saboda suna da sha&#8217;awa, ba tare da sun san da zaman \u0199a&#8217;idojin ba. Sanannen abu ne cewa da yawan mutane na yaudarar kansu ta hanyar tunanin za su iya amfani da kasantuwarsu Hausawa su yi rubutu da Hausa hakan nan ba tare da bin \u0199a&#8217;idojin harshen ba. Irin wa\u0257annan mutane da dama za ka same su cikin da na sani daga baya, domin da zarar tafiya ta fara nisa za su fahimci cewa dole su koma su fahimci wa\u0257annan \u0199a&#8217;idojin, matu\u0199ar dai suna so su cimma nasara a rubutunsu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan dalili ne ya sa na yi wannan \u0257an rubutu domin haskakawa &#8216;yan&#8217;uwana marubuta wa\u0257annan \u0199a&#8217;idojin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Haruffan Hausa<\/h2>\n\n\n\n<p>Kamar sauran mafi yawancin yaruka, harshen Hausa yana da nasa haruffa da ake amfani da su wajen rubutun Hausar boko. Wa\u0257annan haruffa kuwa an samo su ne daga haruffan turanci. Shi harafi \u0199wayar sauti ne da ke \u0257auke da wata magana cikakkiya kuma mai ma&#8217;ana. Shi kuwa sauti, a iya cewa shi ne duk wani amo da kunne ke iya shaidawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Haruffan Hausa sun rabu gida biyu, wato ba\u0199a\u0199e da wasulla.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Ba\u0199a\u0199e<\/h3>\n\n\n\n<p>Bb Cc Dd Ff Gg Hh Jj Kk Ll Mm Nn Rr Ss Tt Ww Yy Zz<\/p>\n\n\n\n<h4 class=\"wp-block-heading\">Ba\u0199a\u0199e masu goyo<\/h4>\n\n\n\n<p>Su irin wa\u0257annan ba\u0199a\u0199en wani lokaci akan kira su da ba\u0199a\u0199e masu aure, gwamammu ko kuma tagwaye. Ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>fy, gy, gw, ky, kw, \u0199y, \u0199w, she, ts, &#8216;y<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Wasulla<\/h3>\n\n\n\n<p>Aa Ee Ii Oo Uu<\/p>\n\n\n\n<h4 class=\"wp-block-heading\">Wasulla masu aure<\/h4>\n\n\n\n<p>Irin wa\u0257annan wasullan, kamar dai ba\u0199a\u0199e masu goyo, akan kira su da tagwaye ko gwamammu. Su ne kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>ai, au, oi, ui<\/p>\n\n\n\n<h4 class=\"wp-block-heading\">Haruffa masu \u0199ugiya<\/h4>\n\n\n\n<p>Haruffa masu \u0199ugiya mun yi bayaninsu a baya, na \u0199ara kawo su a nan ne kawai domin fayyacewa. Wani lokaci akan kira su da haruffa masu tan\u0199wara. Dukkansu guda biyar ne. Ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Manya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>\u0181, \u018a, \u0198, \u0198Y, \u0198W<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u0198anana<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>\u0253, \u0257, \u0199, \u0199y, \u0199w<\/p>\n\n\n\n<p>Rashin amfani da wa\u0257annan haruffa a inda ya dace na iya hana ma&#8217;anar kalma ta ha\u0199i\u0199a fitowa fili, ko kuma ya sauya ma&#8217;anar kalma ko jimlar gaba \u0257aya. Ga misalin yadda ake amfani da su:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>\u0253arawo ba barawo ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0257aki ba daki ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0199arfe ba karfe ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0199yaure ba kyaure ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0199warya ba kwarya ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Amfani da babban ba\u0199i<\/h2>\n\n\n\n<p>Da babban ba\u0199i ake fara rubutu a farkon sakin layi, da gaban aya, da farkon sunaye, da gaban wa\u0199afi mai ruwa, aya ruwa biyu, alamar motsin rai, alamar tambaya da karan tsaye. Don haka wajibi ne mai rubutun Hausa ya kiyaye su sosai.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Sunayen yanka<\/h3>\n\n\n\n<p>Duk sunan yanka da babban ba\u0199i ake fara rubuta shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Aisha ba aisha ba<\/li>\n\n\n\n<li>Kamal ba kamal ba<\/li>\n\n\n\n<li>Kano ba kano ba<\/li>\n\n\n\n<li>Afirka ba afirka ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Sunayen ranaku<\/h3>\n\n\n\n<p>Su ma sunayen ranakun mako ba a fara rubuta su da \u0199aramin ba\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Litinin ba litinin ba<\/li>\n\n\n\n<li>Talata ba talata ba<\/li>\n\n\n\n<li>Laraba ba laraba ba<\/li>\n\n\n\n<li>Alhamis ba alhamis ba<\/li>\n\n\n\n<li>Juma&#8217;a ba juma&#8217;a ba<\/li>\n\n\n\n<li>Asabar ba asabar ba<\/li>\n\n\n\n<li>Lahadi ba lahadi ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Sunayen watanni<\/h3>\n\n\n\n<p>Duk sunayen watannin shekara da babban ba\u0199i ake fara rubuta su.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Janairu ba janairu ba<\/li>\n\n\n\n<li>Fabarairu ba fabarairu ba<\/li>\n\n\n\n<li>Muharram ba muharram ba<\/li>\n\n\n\n<li>Rajab ba rajab ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kalmomin jama&#8217;u<\/h2>\n\n\n\n<p>Duk kalmomin jama&#8217;u ha\u0257a su ake yi waje guda. Ga misalan kalmomin jama&#8217;u da yadda ake rubuta su.<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>kowa\u0257anne ba ko wa\u0257anne ba<\/li>\n\n\n\n<li>koyaushe ba ko yaushe ba<\/li>\n\n\n\n<li>kowanne ba ko wanne ba<\/li>\n\n\n\n<li>kowacce ba ko wacce ba<\/li>\n\n\n\n<li>ko&#8217;ina ba ko ina ba<\/li>\n\n\n\n<li>komai ba ko mai ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Har\u0257a\u0257\u0257un kalmomi<\/h2>\n\n\n\n<p>Har\u0257a\u0257\u0257un kalmomi da karan-\u0257ori ake rubuta su, in kuwa ba a yi hakan ba, lallai an za\u0253a wa Daidaitacciyar Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>gaya-wa-jini-na-wuce<\/li>\n\n\n\n<li>a-kori-kura<\/li>\n\n\n\n<li>bi-da-bi<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Nuna mallaka<\/h2>\n\n\n\n<p>A \u0199a&#8217;idar rubutun Hausa, akwai yadda ake rubuta mallaka. Mallaka iri biyu ne a nahawun Hausa, doguwa da gajeruwa. Sannan in ana maganar mallaka, akwai abubuwa guda biyu da ya kamata a lura da su, wato mai mallaka da kuma abinda aka mallaka.<br>Ga misalan mallaka:<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Doguwa<\/h3>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>riga tamu ba riga don mu ba<\/li>\n\n\n\n<li>naki \u0257akin ba na ki \u0257akin ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Gajeruwa<\/h3>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>rigarka ba rigar ka ba<\/li>\n\n\n\n<li>\u0257akinki ba \u0257akin ki ba<\/li>\n\n\n\n<li>gidanku ba gidan ku ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Harafin M ko N?<\/h2>\n\n\n\n<p>Wani lokaci marubuci kan kasa tantance harafin da ya dace ya saka a tsakiyar kalma, wato ya kasa tantance m ne ko n. To amma, harafin m ya kamata a yi amfani da shi idan har ba\u0199in da ya biyo b, f, ko m ne.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>bambanci ba banbanci ba<\/li>\n\n\n\n<li>ambato ba anbato ba<\/li>\n\n\n\n<li>shimfi\u0257a ba shinfi\u0257a ba.<\/li>\n\n\n\n<li>famfo ba fanfo ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>To amma kalmar da za a iya saka harafin n \u0257in ba \u0257aya suke da wa\u0257ancan ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>tankiya ba tamkiya ba<\/li>\n\n\n\n<li>tuntu\u0253e ba tumtu\u0253e ba<\/li>\n\n\n\n<li>santsi ba samtsi ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">\u0198arshen kalma<\/h2>\n\n\n\n<p>Harafin n ake amfani da shi a \u0199arshen kalma ko da kuwa ba\u0199in da ya biyo baya b, \u0253, f ko m ne.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>&#8216;yan fashi ba &#8216;yam fashi ba<\/li>\n\n\n\n<li>yawan magana ba yawam magana ba<\/li>\n\n\n\n<li>kejin zomo ba kejim zomo ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Harafin R da D<\/h2>\n\n\n\n<p>Aikatau mai \u0199arewa da (ar) da (d) su ne kamar su shigar da, fitar da, kawar da da dai sauransu. To in za a rubuta su, ba a ha\u0257e su da kalmomin da ba su \u0199are da (r) \u0257in ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Misali:<\/strong><\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Ta kawar da shi ba ta kawadda shi ba<\/li>\n\n\n\n<li>Ya fitar da ita ba ya fitadda ita ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Nanata ba\u0199a\u0199e masu goyo<\/h2>\n\n\n\n<p>Mun mun yi magana game da ba\u0199a\u0199e masu goyo a baya, yanzu kuma za mu yi bayani ne game da yadda ake rubuta su a cikin kalma ne. A \u0199a&#8217;ida ba a maimaita asalin ba\u0199in, ga yadda ya kamata a rubuta su:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>tsattsaga ba tsatstsaga ba<\/li>\n\n\n\n<li>fyaffyace ba fyafyfyace ba<\/li>\n\n\n\n<li>Shasshaka ba shashshaka ba<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Wato dai, harafin farko na harafin kawai ake maimaitawa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Marubuta da dama na fama da \u0199arancin fahimtar \u0199a&#8217;idojin rubutun Hausa, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mafi yawancinsu ba harshen Hausa suka karanta ba. Wasu sun fara rubutu ne kawai saboda suna da sha&#8217;awa, ba tare da sun san da zaman \u0199a&#8217;idojin ba. Sanannen abu ne cewa da yawan mutane na yaudarar kansu&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/kadan-daga-kaidojin-rubutun-hausa-domin-marubuta\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Kadan daga ka&#8217;idojin rubutun Hausa domin marubuta<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":4014,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[6,88],"class_list":["post-3977","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-kaidojin-rubutu","tag-rubutun-hausa"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Kadan-daga-kaidojin-rubutun-Hausa-domin-marubuta.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3977","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3977"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3977\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4014"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3977"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3977"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3977"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}