{"id":4021,"date":"2023-10-28T06:37:31","date_gmt":"2023-10-28T06:37:31","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4021"},"modified":"2025-02-01T12:13:34","modified_gmt":"2025-02-01T12:13:34","slug":"burin-da-nake-da-shi-bai-wuce-na-fitar-da-littafi-kasuwa-ba-rabiatu-s-k-mashi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/burin-da-nake-da-shi-bai-wuce-na-fitar-da-littafi-kasuwa-ba-rabiatu-s-k-mashi\/","title":{"rendered":"Burin da nake da shi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba &#8211; Rabi&#8217;atu S. K. Mashi"},"content":{"rendered":"\n<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi&nbsp;tattaki mun za\u0199ulo muku fitacciya kuma shahararriyar marubuciya mai suna Rabi&#8217;atu SK Mashi. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu, dama sauran abubuwa da suka danganci rayuwarta. Ku kasance damu domin jin ko wace ce Rabi\u2019atu Mashi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Malama Rabi\u2019a, muna son jin tarihinki a ta\u0199aice idan babu damuwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Da farko dai sunana Rabi\u2019atu. An haife ni a garin Mashi na jihar Katsina. Na yi primary da secondary duk a cikin garin na Mashi, yanzu haka na tsaya a matakin N.C.E. ne. A bangaren Islamiyya, Alhamdulillahi, dan kuwa&nbsp; na yi sauka da hardar fiye da rabi na Alkur\u2019ani Mai Girma, ba ni da aure, muna dai fata a gaba. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Madalla, to ko za mu iya sanin dalilin da ya tsunduma ki a cikin harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya yawan<strong> <\/strong>karance-karance ne, da kuma sha\u2019awar shi kansa rubutun. Duk lokacin da nake karantu yakan matu\u0199ar burge ni, na ji ina so ni ma na dinga rubutawa ina aika nawa sa\u0199on. Duk lokacin da nake karantu, idan na ga an yi ba yadda nake so ba, sai in ji dama ni ce nake rubutawa da ba zan yi hakan ba. Na kan samu littafi na rubuta nawa ko da a ce zan shekara ban \u0199arasa labarin ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>&nbsp;To, wane irin \u0199alubale kike kai a yanzu, ko kuma kika ta\u0253a fuskanta a rubutunki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>\u0198alubalen da na fuskanta dai bai wuce na wani daya ta\u0253a satar mun littafi ba tare da izini na ba, kuma a lokacin da nake kan rubuta shi, abin ya ta\u0253a mini rai sosai. Dan lokacin ba \u0199aramar bada\u0199ala aka yi da ni ba, daga \u0199arshe ma sai na daina rubuta littafin, na bar masa na ga shin da me zai \u0199arasa labarin?<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"787\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2-1024x787.jpg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4027\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2-1024x787.jpg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2-300x231.jpg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2-768x590.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2.jpg?strip=all 1280w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2.jpg?strip=all&amp;w=512 512w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-2.jpg?strip=all&amp;w=450 450w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ko za mu iya sanin zuwa yanzu littatafai nawa kika rubuta kuma wanne ne bakandamiyarki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>&nbsp;Amsa: <\/strong>Na rubuta littafai za su kai goma sha takwas zuwa ashirin (18 &#8211; 20). Bakandamiya ta shi ne <em>Hafsatul Kiram<\/em><strong><em>.<\/em><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Madalla, to ko za mu iya sanin ta\u0199aitaccen labarin bakandamiyar taki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> <em>Hafsatul Kiram<\/em> labari ne akan wata budurwa da aka yiwa auren ha\u0257i da \u0257an uwanta mashayi kuma manemin mata. Saboda kyawawan halayenta tare da kyautata zaton za ta iya canja shi. Ta kar\u0253i auren \u0257an uwanta hannu bibbiyu saboda biyayyar iyaye, ta sha wahala sosai a hannunsa, ya nuna mata \u0199iyayya sosai kafin ta samu nasarar karkato da hankalinsa gare ta da kuma samun soyayyarsa.&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wane irin buri kike da shi a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Burin da nake da shi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba, ina nan da wannan burin in sha Allah. \u0181angaren shahara kuma Alhamdulillah duk in da ya kamata na kai na kai, duk da ban yi suna ba sosai, amma dai ina jin dadin yadda aka sanni sanadin rubutuna.&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ki na da wata uwar\u0257aki ko kuma maigida a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya ba ni da maigida ko uwardaki a \u0253angaren rubutu, sai dai mutanen da suke \u0199ara mun karfin gwiwa ta \u0253angaren rubutu, su ne, Abdulazeez (Ililee), Abdul Jega, Najibullahi da kuma Ahmad Funtua.&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>To mun ji ko wani marubuci da irin salonsa a harkar rubutun, Malama Rabi\u2019a ke Salon wane marubuci ne ya fi burgeki, har kike ganin zai iya zame miki allon kwaikwayo?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya salon rubutun Halima K\/Mashi yana matukar burgeni sosai.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3-768x1024.jpg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4028\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3-768x1024.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3-225x300.jpg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-3.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A wane yanayi rubutu ya fi yi miki da\u0257i?&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> To ba zan iya cewa ba, saboda ni ba ni da ke\u0253a\u0253\u0253an lokacin yin rubutu, ina yin sa a ko wane lokaci ya zo mini, cikin dare ne ko da asuba ko da rana, kai ko da cikin mota ne a yayin tafiya ina iyayin rubutu na, shiyasa ba ni iya cewa ga lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin Adabin Hausa ya tasirantu da adabin wani yare? idan e, wanne irin tasiri ya yi? idan kuma bai tasirantu ba me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Adabin Hausa ya tasirantu da yaren Larabci ne, saboda kalmominmu da yawa suna kamanceceniya da juna.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Kasancewar rubutun novel da rubutun fim kamar \u0257anjuma ne da \u0257anjummai shin kina sha&#8217;awar rubutun fim? Idan hakane, me ya sa? idan ba haka ba ne, saboda me?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina da sha&#8217;awa sosai, ina so kamar yadda nake rubutawa ana karantawa na rubuta a hau, na zauna ina kallon wasu da yanayin da na tsara musu, kuma suna fa\u0257in kalaman da na rubuta a bakinsu. Kayya! Ba ni tunanin akwai wanda zai \u0199i damar nan idan ta zo masa, duk dai Hausawa sun ce shan koko daukar rai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wace irin shawara za ki bawa \u0199ananan marubuta masu tasowa a matsayinki na marubuciya da ta kwana biyu a harkar rubutu.?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Su ji tsoron Allah su tsarkake zuciyarsu a kan duk abinda zasu rubuta, su saka wa ransu&nbsp; za su yi ne domin fadakar da al\u2019umma ko wa\u2019azantarwa da tunatarwa, ba wai don neman suna ko kudi ba.&nbsp;Har ila yau, suke yin bincike sosai kafin su kai ga yin rubutun, sannan su tabbatar suna da jigo mai kyau, kuma su tsara labarin cikin salon da zai \u0199ayatar.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Mene ne yake jawo wa ki ga marubuci ya \u0257auki rubutu amma ya kasa \u0199arasawa, wacce irin shawara za ki bawa irin wa\u0257annan marubutan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya sau tari rashin tsara labarin ne daga farko har karshe kafin a fara, da rashin samun kwarin gwiwa daga wurin makaranta, gajiya, da tunanin wani labarin da suke ganin zai fi wancan samun kar\u0253uwa ko za su fi jin dadin rubuta shi.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4-768x1024.jpeg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4029\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4-768x1024.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4-225x300.jpeg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-4.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A duk cikin taurarin labaran da kika rubuta, wanne kika fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:&nbsp; <\/strong>A gaskiya na fi son <em>Hasfatul Kiram<\/em> saboda labarin ma na rubuta shi ne da halayen da nake fatan mai sunan ta tashi da shi, na ha\u0199uri, taimako da kuma juriya tare da kauda kai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A wacce \u0199ungiya kike rubutun, kuma mene ne manufar \u0199ungiyar taku?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina \u0199ungiyar Nagarta Writers Association, manufarmu ita ce kawo gyara da yin rubutu mai tsari da ma&#8217;ana, da kuma taimakawa \u0199ananan marubuta masu tasowa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Me za ki iya cewa akan lamarin kasuwancin online na littafi?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> To gaskiya abun ya yi matu\u0199ar burgeni da yadda marubuta ke cin moriyar fasaharsu, kuma abun ya samu karbuwa sosai ga makaranta har ma da marubutan saboda yadda har masu buga littafin suka fara dawo da har\u0199allarsu online \u0257in, wannan ci gaba ne sosai a zamanance ga rubutun.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Kin ta\u0253a siyar da littafi? idan kin siyar wanne ne?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> A gaskiya ban ta\u0253a siyarwa ba, amma ina saka ran siyarwa a gaba in sha Allah.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Kin ce an ta\u0253a satar miki littafin da kike rubutawa, shin wanne mataki kika \u0257auka akan satar da aka yi miki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Ba ni ce na \u0257auki mataki ba \u0199ungiya ce, manyan \u0199ungiyata sun same shi an yi maganar fahimta sosai kuma ya bada hakuri akan hakan, sai dai ni na gaza \u0199arasa musu labarin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Kun ta\u0253a yin gamayya wajen rubuta littafi ke da wasu? Idan kun ta\u0253a, ya ya sunan littafin?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Mun yi gamayyar rubuta littafi da wasu ba mutum \u0257aya ba. Mun rubuta <em>Ba Ni Ba Ne<\/em> ni da Amratu A Mashi, mun rubuta <em>A Yini \u018aaya<\/em> da wani da na kasa tuna sunansa, mun rubutu <em>Dodon Jatau<\/em> da suanan RAZ, wato Rabi&#8217;atu SK Mashi da Amrah A Mashi da kuma Zahra BB, mun rubuta <em>Masarautarmu <\/em>har ila yau tare da su, da wani shi ma na manta sunansa. Sai kuma mun rubuta <em>Amanar Aure<\/em> da <em>Haka So Yake<\/em> tare da Abdul Jega. Mun rubuta <em>Mafarin So<\/em> da <em>Duniya Gidan Kashe Ahu<\/em> tare da Mrs Umar.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5-768x1024.jpeg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4030\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5-768x1024.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5-225x300.jpeg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Rabiatu-SK-Mashi-5.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Daga \u0199arshe, me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Wani babban ci gaba ne da ya zo wa marubuta da makaranta koma in ce al\u2019umma baki daya, yana taimakawa marubuta tare da basu damarmaki na baje kolin fasaharsu har ma su ci moriyar hakan, ga sau\u0199i da kuma dadin amfani. Muna godiya tare da fatan wata rana za a dawo mana da Application dinsa, wato manhajar.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi hirar ne da Rabiatu SK Mashi a ranar Talata, 15 ga watan Satumba 2020; 9am \u2013 6pm kai tsaye a tsohuwar Taskar Bakandamiya (yanzu <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Bakandamiya Encyclopaedia<\/a>). An kuma tace tare da sabunta hirar a ranar 20 ga watan Satumbar 2023.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa: <\/strong>Maryam Haruna tare da Hauwa&#8217;u Muhammad<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tacewa da sabuntawa: <\/strong>Asma\u2019u Abdallah (Fulani Bingel)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi&nbsp;tattaki mun za\u0199ulo muku fitacciya kuma shahararriyar marubuciya mai suna Rabi&#8217;atu SK Mashi. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu, dama sauran abubuwa da suka danganci rayuwarta. Ku kasance damu domin jin ko&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/burin-da-nake-da-shi-bai-wuce-na-fitar-da-littafi-kasuwa-ba-rabiatu-s-k-mashi\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Burin da nake da shi bai wuce na fitar da littafi kasuwa ba &#8211; Rabi&#8217;atu S. K. Mashi<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4068,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[78],"tags":[79,81,89],"class_list":["post-4021","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-interviews","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews","tag-rabiatu-sk-mashi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/10\/Hira-da-Rabiatu-S-K-Mashi.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4021","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4021"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4021\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4068"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4021"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4021"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4021"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}