{"id":4045,"date":"2024-02-06T19:38:00","date_gmt":"2024-02-06T19:38:00","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4045"},"modified":"2024-05-29T17:00:07","modified_gmt":"2024-05-29T17:00:07","slug":"matsalar-rubutun-online-shi-ne-babu-amana-sumayyah-abdulkadir-takori","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/matsalar-rubutun-online-shi-ne-babu-amana-sumayyah-abdulkadir-takori\/","title":{"rendered":"Matsalar rubutun online shi ne babu amana &#8211; Sumayyah Abdulkadir (Takori)"},"content":{"rendered":"\n<p>A ci gaba da gudanar da shirin tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon ta tattauna da marubuciya Sumayyah Abdul\u0199adir Takori game da abubuwan da suka shafi rubutu da kuma rayuwar marubuciyar. Ga yadda hirar ta kasance:<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarki in ba za ki damu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> An haife ni a jihar Kano Unguwar Kabara, a \u0199aramar hukumar Municipal, a shekara ta 1988.&nbsp; Na halarci Fedwa Nursery School ta cikin FCE Kano, da kuma makarantun firamare guda biyu; Masallaci Special Primary school, da Gidan Galadima Primary School, wanda na kammala a shekara ta 1998. Daga nan na wuce \u0199aramar Sakandire a &#8216;Izazuddeen Foundation Sani Mainagge, 1999-2001. Na halarci Special Education School, Kano 2001-2002; sai babbar sakandire a (WTC Kano) a shekarar 2002-2005.<\/p>\n\n\n\n<p>A shekarar 2006 na wuce jami&#8217;ar Bayero na karanci Diploma a (Social Policy and Administration) 2006-2008. A 2012 na wuce karatun Digiri na farko a jami\u2019ar Bayero inda na karanci ilmin zamantakewar \u0257an&#8217;adam (Sociology), wanda na gama a shekarar 2015. Daga nan kuma na wuce digiri na biyu duk a jami\u2019ar Bayero, inda na nazarci fannin ilmi na musamman (MA Ed Special Education). A halin yanzu ni ma&#8217;aikaciya ce ta gwamnatin tarayya, \u0199ar\u0199ashin Federal Ministry of Humanitarian Affairs and Poverty Alleviation, a hukumar kula da masu bu\u0199ata ta musamman (National Commission for Persons with Disabilities).<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na fara rubutu a 2002. A makarantar Sakandire da Islamiyyarmu Zubairiyyah Islamiyya kawai na tsinci kaina cikin yawan rubutu da biro a littafi, amma ban ta\u0253a tunanin bugawa ba. Na tashi na gan ni cikin yawan rubuce-rubuce a makaranta, na boko da na addini.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1-1024x809.jpeg?strip=all\" alt=\"Hira da Sumayyah Abdulkadir Takori\" class=\"wp-image-4155\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1-1024x809.jpeg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1-300x237.jpeg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1-768x607.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1.jpeg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-1.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Sumayyah Abdulkadir ke karbar shedar karramawa daga Aliyu Tanko, shugaban sashen Hausa na BBC a wurin taron Gasar Hikayata ta 2023.<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu. <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Daga lokacin zuwa yanzu na wallafa littafai guda 30 har wanda nake kan yi yanzu. Sun ha\u0257a da:<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/siradin-rayuwa-1\/\">Sira\u0257in Rayuwa<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Tuna Baya Shine Ro\u0199o<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Alheri<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Girma Ya Fa\u0257i<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>A Bari Ya Huce<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Al\u0199awari Bayan Rai<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Zuciyar Mutum Birninsa<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Wasan \u0198anin Miji<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Zumuntar Kenan<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Rayuwar Rayhana<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Kwana Sittin<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/sanadin-kenan-1\/\">Sanadin Kenan<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Auren Kwangila<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Aalimah<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Masarautarmu<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Amana Ta<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Yiwa Kai Hisabi<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Babban Goro<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Yakanah<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Aure Ko Boko<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Hasna&#8217;u &#8216;Yar Najeriya<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Kulsum<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Fahhimah<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Na Huce<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/sakacin-waye-1\/\">Sakacin Waye?<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Raunin Zuciya<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Amani<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Hauwa-Kulu<\/em><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Duk cikinsu na fi son <em>Rayuwar Rayhana<\/em>, saboda na ba wa character \u0257in littafin wasu daga cikin halayena.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Da kaina na dogara da kuma taimakon Ubangiji wurin rubutuna, sai taimakon iyayena da abokan arzi\u0199ina na jiki da na kan nemi gyara da shawarwarinsu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ki ka ta\u0253a karantawa da ya fi burge ki? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Suna da yawa musamman littafan Zainab Al\u0199ali, William Shakespeare, Abubakar Gimba, kafin na fara karanta su <em>Jiki Magayi, Budurwar Zuciya<\/em> na Haj. Balaraba Ramat Yakubu, da sauran iyayenmu a rubutu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kin ta\u0253a shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin ta\u0253a yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ban ta\u0253a shiga kowacce gasar marubuta ba a tsawon shekaru 20 da na kwashe ina rubutu sai a bana. Na shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa, na yi nasarar fitowa a sahun fitattu 12 da labarina mai suna <em>Duniyar Mafarkina<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p>Nasarorina a harkar rubutu ita ce soyayyar al&#8217;ummah. Idan Allah ya ba ka mutane ya gama ba ka komai. Alhmdulillah.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya ba na tsarawa, hasalima \u0257ora biro nake kawai akan takarda da niyyar fara rubuta labari, amma da jigonsa a raina, sai in nutsu in saurari kwakwalwa da zuciyata. Sai in ji kamar a cikin kaina ana ce min rubuta kaza rubuta kaza. A idanuna kuma sai in ga  majigin labarin na gilmawa daki-daki kamar a idona yake faruwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Bana sakin wanda na fara sai dai na samu takarda na adana ita sabuwar basirar da ta kutso min a ta\u0199aice, na ajiye a gefe. Sai na cigaba da wanda nake kan yi har sai na kai shi \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ki kan \u0257auki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan \u0257auke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina rubutun nake ha\u0257awa da binciken ba rabasu nake yi ba. Misali, sai na zo kan abinda nake son sani a labari sai in dakata in bincika ko in tuntu\u0253i masana ilmin abin.<\/p>\n\n\n\n<p>Yana \u0257aukata a \u0199alla watanni shida kafin na kammala labari \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina samun jigon labaraina ne daga kintacen rayuwar da za ta iya faruwa a zahiri ta hanyar kallon rayuwar mutanen da nake tare da su.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?  <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina ba wa taurarina halaye mabanbanta da ya dace da zubin labarin da na za\u0253a, birni ko \u0199auye, amma ban fiye basu halin ashararanci ba, ina dai basu halin masu zurfin ilmin boko wato halin &#8216;yan boko a yawancin lokuta.<\/p>\n\n\n\n<p>Sunaye kuwa normal sunayenmu na Hausawa nake za\u0253a in saka wa jarumai na, da la\u0199anin \u0199auyukan da suka fito. Kamar Ibrahim Mansur Takai, Al&#8217;amin Bello Ma\u0199arfi, Bello Waziri \u0198araye, da sauran su. Mata kuma akwai irin su Rahane, Hauwa Kulu, Ru\u0199ayyah, Mairo, Altine,  Hadiza, Amina da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko kin ta\u0253a amfani da wani \u0253angare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Sau-tari ana cewa haka a kaina. Amma amsar ita ce a&#8217;a. Ina dai amfani da iya abinda na san yana faruwa ko zai iya faruwa. Hasali ma ban ta\u0253a rubuta (true life story) ba, duk labaraina na da can da na yanzu, \u0199ir\u0199irarrun labaru ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma a Rayuwar Rayhana kasancewar na ba wa jarumar littafin irin lalurar da nake ciki da halayena, shi ya sa wa\u0257anda suka san ni a zahiri ke tunanin labarina ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Amma banida ala\u0199a da labarin sai lalurar matsalar dana suffanta Rayhana da ita a cikin labarin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka ta\u0253a rubutawa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> <em>Kwana Sittin<\/em>. Na sha wahalar bincike akan sa akan lalurar (schizophrenia) da cututtukan da ke da ala\u0199a da ita, da kuma <em>Girma Ya Fadi<\/em>, wanda shi kuma na hargitsa \u0199wa\u0199walwata sosai a kansa, na je har Mara\u0257i ta Nijar a kansa.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2-1024x809.jpeg?strip=all\" alt=\"Hira da Sumayyah Abdulkadir Takori\" class=\"wp-image-4156\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2-1024x809.jpeg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2-300x237.jpeg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2-768x607.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2.jpeg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Sumayyah-Abdulkadir-Takori-2.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Sumayyah Abdulkadir yayin da ta karbi shedar karramawa Gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2023.<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne irin \u0199alubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake \u0199alubalen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Babu irin \u0199alubalen da ban ha\u0257u da shi a rubutu ba. Akwai lokacin da publisher \u0257ina da muka jima tare ya ha\u0257a jarin nawa gaba \u0257aya ya gudu da shi kuma har gobe bai biyani ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka lokacin da aka yi gobarar Sabon Gari sai yafe ku\u0257a\u0257ena masu yawa na yi gaba \u0257aya ba don littafaina sun \u0199one ba. Sai matsalar overprinting, da \u0199in biyan ku\u0257a\u0257en bashi daga &#8216;yan kasuwa da gangan. A \u0199arshe duka na yafe musu, ban ta\u0253a kai kowa kotu ko hannun &#8216;Yansanda da sunan shari&#8217;a akan sana&#8217;ar mu ba, a tsawon shekaru 20 da na kwashe ina rubutu da tarin matsaloli. Na da\u0257e ban ci gajiyar rubutuna ba. A cinye jarin, mahaifiyata ta sabunta min, a haka dai na mi\u0199e har na koyi kar\u0253ar rance kai tsaye daga (microfinance) duk don in cigaba, saboda sana&#8217;ar ta bi jiki na. \u0199alubalen da na yi ta fuskanta kala-kala bai sa na sare na barta ba har lokacin da duk marubuta suka barta. <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A duk cikin Taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na fi son Ya Himu da Rahanensa, a littafaina na baya kenan. A na yanzu-yanzu kuma na fi son jarumin <em>Sakacin Waye<\/em>, \u0257an \u0199abilar Berom, Hamzah Mustapha Mawonmase.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya in dai lafiya ta kalau basirar sabon rubutu ba ta ta\u0253a yanke min ba, sai dai in adanata zuwa wani lokaci don na huta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Masoya na gaskiya da na samu sanadinsa, gida da waje, birni da \u0199auye. Sannan yana \u0257ebe min kewa, yana tayani hira, yana mantar dani kowacce damuwa musamman ta lalurar da nake ciki.<\/p>\n\n\n\n<p>Masoyan da na ke da su a sanadinsa kuma suna sanya ni alfahari da shi da godiyar Ubangiji a kodayaushe, musamman wadanda suke tsaye tare da ni tun daga tushe har kawo yau, suna \u0257okin in fidda sabon littafi su karanta kullum. Zumunci da nake samu a duk garin da naje sanadin rubutu ya fi komai faranta min rai da rubutuna.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina karanta Alqur&#8217;ani ina kuma rubutu, sannan ina sa\u0199a zaren sabon labari.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> &#8216;Ba na\u0199asasshe sai kasashshe\/Na\u0199asa ba kasawa bace.<\/p>\n\n\n\n<p>Dalili? Na yarda cewa (there&#8217;s ability in every disability).<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A naki ra&#8217;ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Duka na yi su. Na san da\u0257in su da rashin da\u0257insu. Kowanne na da irin nasa amfanin da rashin amfaninsa. Amfanin na online shi ne yanzu bana bin &#8216;yan kasuwa akan su ba ni ku\u0257ina suna wahalar da ni.<\/p>\n\n\n\n<p>Matsalar rubutun online shine babu amana. In daya ya saya zai iya turawa dubu babu yadda za ka yi. Amma na bugawa ya\u0257uwarsa da sau\u0199i tunda ka san adadin da ka buga. Matsalar na bugawa kawai kasuwancinsa ce wanda akan bashi muke yinsa amma ya fi security.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A naki ra&#8217;ayin, wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al&#8217;umma?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Sosai marubuta ke da tasiri don ana sauraron su sosai kamar yadda ake sauraron malaman makaranta, don haka nake so mu tuna hakan koyaushe mu tsarkake al\u0199alaminmu daga rubuta abinda zai cutar da tarbiyyar yara da al&#8217;umma.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong>  Eh akwai goron sabuwar shekara in Sha Allah mai suna&#8230; <em>Da Kyar Na Sha<\/em> (Labarin Aisha-Siddiqah). <\/p>\n\n\n\n<p><em>Tambaya:<\/em> Wane ne tauraronki a cikin marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p>Gaskiya suna da yawa na publishing da na online, duk ina da kyakkyawar ala\u0199a da su, muna zaman tare cikin aminci da mutunta juna da taimaka wa juna.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> A ganina kowannensu da irin yadda yake isar da sa\u0199onsa. Koda yake dukkansu \u018aanjuma ne da \u018aanjummai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa? <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Ka yi rubutu da kyakkyawar manufa ta isar da sa\u0199o mai kyau, ka yi rubutu don ra&#8217;ayin kanka ba don neman suna ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A duniyar rubutu \u0257aukaka ta Allah ce da \u0199o\u0199arin marubuci. Ka tsaya iya matsayin da Allah ya ajiyeka a rubutu sai ka zauna lafiya cikin wadatar zuci. Ban ta\u0253a rubutu don neman na yi suna ba sai don ina jin da\u0257in yin sa akan karan-kaina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne burinki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Burina fa\u0257akarwa da nisha\u0257antar da al&#8217;umma. Ina alfahari da rubutu, kuma kowanne mataki na kai a nan gaba ba zan manta da cewa litattafan da na wallafa su ne sanadin da duniya ta sanni ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Bakandamiya manhaja ce da ta zo da tsari mai ma&#8217;ana da ban sha&#8217;awa domin ta kawo maslaha  daga kokenmu na ya\u0257a littafanmu ba bisa doka ba da sauran matsalolin online da muke kuka da su. Kuma suna biyan marubuta abinda suka yi yarjejeniya da su cikin aminci babu cutarwa ba sa\u0253a al\u0199awari.  Ina ro\u0199on Ubangiji Allah ya taimaki Bakandamiya da ma&#8217;aikatanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Amin. Mun gode sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi wannan hira da Sumayyah Abdul\u0199adir ne a ranar 01 ga watan Disamba 2023. <\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa:<\/strong> Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ci gaba da gudanar da shirin tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon ta tattauna da marubuciya Sumayyah Abdul\u0199adir Takori game da abubuwan da suka shafi rubutu da kuma rayuwar marubuciyar. Ga yadda hirar ta kasance: Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/matsalar-rubutun-online-shi-ne-babu-amana-sumayyah-abdulkadir-takori\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Matsalar rubutun online shi ne babu amana &#8211; Sumayyah Abdulkadir (Takori)<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4154,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,78],"tags":[79,81,100],"class_list":["post-4045","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-interviews","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews","tag-sumayyah-abdulkadir"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/Hira-da-Sumayyah-Abdulkadir-Takori.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4045","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4045"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4045\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4154"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4045"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4045"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4045"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}