{"id":4060,"date":"2023-12-21T20:24:10","date_gmt":"2023-12-21T20:24:10","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4060"},"modified":"2023-12-21T20:24:16","modified_gmt":"2023-12-21T20:24:16","slug":"rubutu-dai-rubutu-ne-babu-wanda-ya-fi-wani-sai-wanda-ya-iya-tsara-labari-tare-da-salon-isar-da-sako-mai-armashi-danladi-haruna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/rubutu-dai-rubutu-ne-babu-wanda-ya-fi-wani-sai-wanda-ya-iya-tsara-labari-tare-da-salon-isar-da-sako-mai-armashi-danladi-haruna\/","title":{"rendered":"Rubutu dai rubutu ne, babu wanda ya fi wani sai wanda ya iya tsara labari tare da salon isar da sako mai armashi &#8211; Danladi Haruna"},"content":{"rendered":"\n<p>A yau hirarmu da marubuta ta yi babbar kamu, inda ta yi kacibis da hazikin marubuci, manazarci, kuma akawu, Danladi Haruna. Ga yadda hirar tamu ta kasance.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Assalamu Alaikum. Sunana dai Zakariyya Haruna wanda ake wa la\u0199abi da \u018aanladi. An haife ni ne a jihar Kano, unguwar Gya\u0257i-gya\u0257i ranar 12 ga Yuli, 1981. Na yi karatun zamani da na Muhammadiyya daidai gwargwado. Ina da matakin ilimi na Masta a fannin gudanar da kasuwanci watau Master of Business Administration. Haka kuma ina da shaidar \u0199warewa ta cikakken akawu watau Associate Chartered Accountant na \u0198ungiyar \u0198wararrun Akantoci ta Nijeriya watau Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN). Ina da satifiket da dama na \u0253angaren rubutu da nazari da na manhajojin kwamfuta da sauransu. Suna da dama wa\u0257annan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Madalla, Tun yaushe ka fara rubutu? Kuma mene ya ja hankalinka har ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Rubutu na jima ina ta\u0253awa. Tun lokacin muna firamare kasancewa ta mai son karatu da sauraron rediyo, da sauran labarun almara da na hikayoyi da sauransu. Haka dai sannu a hankali har mai karatu ya riki\u0257e zuwa marubuci. Kodayake, rubutun da nake ganin na saka ni a gwadaben marubuci, shi ne wani littafi da na rubutu mai suna <strong><em>Furar Dan\u0199o <\/em><\/strong>a shekara ta 2002. Daga kansa kuwa na ci gaba da rubutu iri daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya<\/strong>: Wanne irin matsaloli ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Yawancin rubuce-rubucena ina yin su bisa son rai ne. Wani lokaci yana iya zama tamkar bahaya. Idan ya taso wajibi ne a fitar da shi. Kuma ka san cewar aikin sa kai ya fi bauta ciwo. Don haka, koda akwai wasu matsalolin akan rufe ido yi abin da ya dace. To amma yawancin matsalolin marubuta sun ha\u0257a da rashin lokacin aiwatar da bincike, da rashin goyon bayan wasu daga al&#8217;umma da kuma matsalar kasuwa. Wanda idan marubuci don samun kasuwa yake a halin yanzu, to sai dai ya \u0257ora hannu a ka kurum. Muna fatan samun warwarewar matsalolin da suka baibaye marubuta nan ba da jimawa ba.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1-1024x809.jpeg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4063\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1-1024x809.jpeg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1-300x237.jpeg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1-768x607.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1.jpeg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-1.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuci Danladi Haruna<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Ni Kusan kullum ina rubutu. Ina rubuta labarin \u0199ir\u0199ira a intanet. Sai dai littatafan da na rubuta cikakku duka &#8211; duka goma 10 ne. Daga ciki an wallafa guda 3 rak, watau <strong><em>Saura \u0198iris, Tekun Labarai <\/em><\/strong>da kuma <strong><em>\u0181arayin Zamani. <\/em><\/strong>Ana samun Tekun Labarai a shafukan sayar da littattafai na Okada da na Konga da nan Bakandamiya. Shi kuwa \u0181arayin Zamani ana iya samunsa kyauta a gidan archive.org. Na sake shi kyauta ne saboda jama&#8217;a su karanta su \u0199aru da ilimin sanin hanyoyin kare kansu daga maha&#8217;intan da ke cutar mutane ta intanet. Kuma Alhamdulillahi kwalliya ta biya ku\u0257in sabulu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne littafi ka fi so a duk cikin littattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Littattafai na duka ina sonsu amma wanda na fi jin dadin karanta shi da kaina shi ne <strong><em>\u0181<\/em><\/strong><strong><em>arayin <\/em><\/strong><strong>Zamani<\/strong>, saboda abubuwan da na ambata a ciki wa\u0257anda suka shafi harkar kwamfuta da intanet da kuma kare kai daga masu satar zamani ta waya ko ta intanet. Littafin na da amfani ba wai domin nisha\u0257i ba kawai, har ma da yadda za ka fahimci &#8216;yan damfarar intanet da yadda za ka kare kanka. Sau tari idan ina karanta shi sai na yi ta mamakin irin abubuwan da ya \u0199unsa kamar ba ni ne na rubuta shi ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne littafi ne da ka ta\u0253a karantawa kuma ya fi burge ka?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Na Hausa dai har yau Magana Jari Ce ba na gajiya da karanta ta. A na Ingilishi kuma suna da yawa kamar littafan James Brown ko na Sydney Sheldom musamman Digital Fortress da Sky Is Falling da sauransu. Littattafan nazari kuwa ba a gajiya da su na Hausa ko na Ingilishi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye kake farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Kamar yadda na fa\u0257a a baya, ina tsara dukkan rubutun da zan yi daki-daki ta hanyar <em>synopsis <\/em>sannan na yi <em>block<\/em>. Sai kuma na fitar da hawa da gangara da sauka da tsalle da tashi duka. Sau tari ina \u0257ora rubutuna akan doran nan da ake kira story line ko story act da sauransu. Duk da haka wani labarin na iya zuwa lokaci guda na rubuta shi. Daga nan kuma ba zan kara tunawa da shi sai na waiwaye shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Ina iya ha\u0257a labarai biyu ko fiye ma a lokaci guda ina rubuta su musamman gajerun labarai. Wani lokaci ma garin \u0199o\u0199arin rubuta wani sai ka ga fikirar wani ta samu. Don haka kurum da zarar na ji fikirar ta zo, sai shi ma na aza harsashin rubuta shi. Wani zubin ma, labarin da na tuno daga karshe nake fara kammalawa kafin na kammala wanda na fara tun farko.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ma sha Allah! Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka ta\u0253a rubutawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Littafin <strong><em>Hanyar Jidda <\/em><\/strong>na soma rubuta shi tun 2008 har yau ban gama ba. Kuma labarin duka yana kaina. Na yi masa dukkan abin da nake yi wa labari amma har yau na gagara kammala shi. Sai dai ina jin dadin rubutunsa duk lokacin da na waiwaye shi. Saboda ta dalilin rubutun littafin na san hanyoyin zuwa Kamaru da Chadi da Sudan har zuwa Bar Sudan gefen Bahar Maliya. A bi ta Kasala a isa Bar Sudan a haura bahar Maliya a je Jeddah ko Yemen. Na rike sunayen hanyoyi da dama duk da ban ta\u0253a zuwa nan haka ba. Ta dalilin littafin na tattauna da mazauna \u0199asashen nan da yawa musamman Hausawan Chadi da na Sudan da wasu \u0199alilan da ke Yemen da Saudiyya. Ina fatan dai na iya kammala shi da wuri kafin labarin ya gudu daga kaina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wani lokaci kan marubuci kan cushe har ya kasa rubuta komai. Shin ka ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Tabbas hakan na faruwa sau da dama kuwa. Na ta\u0253a halartar wani kwas dangane da dabarun rubutu. \u018aaya daga cikin abubuwan da na ji da\u0257in kwas \u0257in shi ne dabarun da aka koya mana lokacin da kana cikin rubutu sai ka ji \u0257if basirar ta \u0199are. Ka kakare. Babu gaba babu baya. Hanyoyin su ne, tun farko marubuci ya tsara abubuwan da zai yi mataki mataki watau <em>synopsis<\/em>. Sannan ya karkasa <em>synopsis <\/em>\u0257in nasa zuwa \u0253angarori. Kullum da abin da zai \u0257auka ya rubuta har ya \u0199are. Sannan a ware lokacin yin bincike da nazari da tambayoyi ga inda ya dace. Idan kana rubutu, sai ka ji basirar ta \u0199are, sai ka ajiye da zummar sake waiwayarsa. Ko ka tashi ka kama wani aikin, ko ma ka yi barci abinka. Da zarar \u0199wa\u0199walwarka ta huta, za ka ji basirar ta dawo. Amfanin yin gajerun rubutu ana ajiyewa watau <em>blocking <\/em>yana da yawa. Wani lokacin idan kana rubutu ka kakare, kana duba <em>synopsis <\/em>dinka ko <em>blocking <\/em>\u0257inka nan da nan sai ka tuna ka ci gaba.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large is-resized\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"569\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1-1024x569.jpeg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4065\" style=\"width:818px;height:auto\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1-1024x569.jpeg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1-300x167.jpeg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1-768x427.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1.jpeg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-2-1.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Madalla, yanzu lokaci ya canza, haka zalika al\u2019amura da dama na mutane su ma sun canza wanda na wasu yake zuwa a karkace, har ta kai ga yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira za ka yi wa irin wa\u0257annan marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Kamar yadda na fa\u0257a a baya, rubutu na zuwa ne gwargwadon wayewa da shekarun marubuci. Tun wuri ya kamata marubuci ya yiwa kansa fa\u0257a, ya rubuta abu mai ma&#8217;ana da ko ina aka tsayar da shi zai iya karantawa ba tare da taradaddi ba. Masu rubutun batsa da suke ganin burgewa ce ko wayewa, ba za su fahimci illar abin ba sai lokacin da ruwa ya karewa \u0257an kada. Kuma ma ni gani nake yi marubutan batsa basu da wata fasaha illa irin abin nan na ki\u0257anki na jiyo. Da za a bibiyi rubutun kusan duka abu \u0257aya ne a cikinsa. Babu wani abu sai yaudarar kai da \u0253ata lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da kake yi irin wa\u0257anda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin wa\u0257anda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin wa\u0257anne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Nasarorin suna da \u0257umbin yawa da gaske. Rubutu ya sa na san mutane da yawa ciki da wajen \u0199asar nan. Haka nan na shiga gasar rubutu da yawa. Na yi nasara a cikinsu da dama. A\u0199alla na shiga gasanni da suka kai 10 kuma na yi fice a mafi yawancinsu. Misali, gasar Duniyar Marubuta a 2013. Na yi na \u0257aya a \u0253angaren Wasan Kwaikwayo. Gasar Gusau Institute na yi na biyu a 2018. Gasar Pleasant Library na yi na uku a 2020, da sauransu. Na samu kyaututtuka da dama ta silar rubutu. Sannan ina aiki da mutane da dama duk albarkacin rubutu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A harkar rubuce-rubuce, wa\u0257anne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>A rubutu suna da dama. Kusan duk wanda na karanta littafinsa ko wani rubutu nasa, na kan \u0257osani wani abu daga gare shi yadda zan kattaba nawa idan bu\u0199atar hakan ta taso. To amma manya daga ciki sun ha\u0257a da Farfesa Ibrahim Malumfashi, da Farfesa Yusuf Adamu da Bala Anas Babinlata da Ado Ahmad Gidan Dabino da Nazir Adam Salihi da Maimuna Idris Beli da kuma Rahama Abdulmajid. A fannin wa\u0199a da wasan kwaikwayo kuwa, Malam Nasiru G. Ahmad shi ne al\u0199ibla ta. Haka kuma, na kan yawaita aika masa rubuce-rubucena yana mini gyara musamman ta fuskar salo da sarrafa harshe da kuma \u0199a&#8217;idojin rubutu. Shi kuwa marigayi Abubakar Imam, na \u0257auke shi wata al\u0199ibla da nake waiwaya duk lokacin da zan yi rubutun gajeren labari. Misali, Tekun Labarai na ari wani salo daga Magana Jari Ce wajen \u0199ulla gajerun labaru cikin uwar labari ta yadda mai karatu zai yi ta shiga da fita cikin labarai ba tare da an \u0199ar\u0199are wanda aka fara tun farko ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ma sha Allah! Kasancewar rubutun novel da rubutun fim kamar \u0257anjuma ne da \u0257anjummai shin kana sha&#8217;awar rubutun fim? idan hakane me ya sa? idan ba haka ba ne saboda me?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>To, shi rubutun fim musamman wanda ba naka ba. Ma\u2019ana, kai ne marubucin kuma kai ne Furodusa kamar yadda Ado Gidan Dabino MON ya yi a <strong><em>Da\u0199i\u0199a Talatin<\/em><\/strong>. In dai ba haka ba, to wajibi ne ka sadaukar da lokacinka kacokam domin biya wa daraktoci da furodusoshi bu\u0199atunsu. A halin yanzu ni ba ni da cikakken lokacin rubuta fim musamman irin gaggawar da ake yi da azazazzalar masu rubutun da su yi su gama da gaggawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Kada ka manta. Ina aikin akawu, wanda shi ma yana jan lokaci, ga kuma aikin harha\u0257a manhajar kwanfuta watau \u2018programming\u2019.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da haka, wasu na zuwa wajena neman shawarwari ko gyara a wasu rubuce-rubucen na fim. Na kan bayar da gwargwadon gudummuwar da ta dace idan an bu\u0199aci haka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Mene ne babban burinka dangane da rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Ina da buri mai girma dangane da rubutu musamman cikin harshen Hausa. Ina fatan rubutun Hausa ya zama ya mamaye duniya ta kafafen intanet. Ya zamana an samar da manyan dandamalai kamar su Amazon KDP da su Watpad da Webnovel da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuma Alhamdulillahi, ya zuwa yanzu akwai yun\u0199uri a ciki da wajen \u0199asar Hausa dangane da wannan manufa. Ni kaina ina daga cikin wasu tafiyoyin da ake wannan shirin. \u018aaya daga ciki kuwa, wata babbar \u0199ungiya ce da ke \u0199o\u0199arin zamanantar da harsunan Afrika. Sun \u0257auki Hausa da Siwahili da kuma Zulu a matsayin wa\u0257anda za a fara da su.<\/p>\n\n\n\n<p>Aikin da ake yi yanzu haka, sun ce zai \u0257auki kimanin shekara guda ana yi. Ina fatan yadda aka fara da ni za a kammala da ni cikin nasara<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A naka ra\u2019ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi ma\u2019ana da tsari?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Hanyar isar da sa\u0199on rubutu ko littafi na da yawa. A da can ana saka marubuci ne a gaba, ya bu\u0257e ya yi ta karantawa mutane. Aka samu lokacin da ake \u0257aukar nauyin buga masa littafin ana sayarwa, shi kuma ana ba shi kamasho watau royalty. Da tafiya ta tafi, sai marubutan suka ri\u0199a buga littatafan da kansu a cikin samfurin \u0257auki sandarka. Wannan ta samar da ambaliyar marubuta har ake wa rubutun take da <strong><em>Adabin Kasuwar Kano<\/em><\/strong>. Sannu a hankali kuma aka samu gidajen rediyo na karanta labaran ga \u0257umbin masu sauraro. Sai kuma yanzu da ake sakin rubutun a intanet walau kyauta ko da ku\u0257i. Su ake kira marubuta online. A nawa ra&#8217;ayin, babu wanda ya fi wani martaba ko daraja ko \u0257aukaka a tsakanin masu wallafa littafi a Adabin Kasuwar Kano da masu saki online. Wanda ya fi wani kurum shi ne wanda rubutunsa yake da inganci wajen kyautata rubutu da gamsassun bayanai da kuma kwarewa a salo. A dukkan wa\u0257annan \u0253angarori akwai kwararru akwai &#8216;yan dagaji. Akwai hazi\u0199ai akwai &#8216;yan kwamacala. Don haka rubutu dai rubutu ne, babu wanda ya fi wani sai wanda ya iya tsara labari tare da salon isar da sa\u0199o mai armashi.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3-768x1024.jpeg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4066\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3-768x1024.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3-225x300.jpeg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Danladi-Haruna-3.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu yake jawowa sai \u0253ata tarbiyya. Shin wacce shawara yakamata a dinga ba irin wa\u0257an nan mutanen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Kowanne rubutu ya danganta da irin manufar marubucin da kuma al\u2019ummar da ya samu kansa tare da wa\u0257anda yake rubutun domin su. Kenan za mu iya cewa rubutu a karan kansa ba ya \u0253ata tarbiyya sai dai idan marubucin ne lalatacce ya gamu da makaranta \u2018yan amshin shata. An samu za ni ta tarar da mu je mu. Sai a yi ta yi. Marubuta da dama suna rubutu ne gwargwadon zarafin shekarunsu, a lokacin da marubuci ke tashen \u0199uruciya mafi yawa rubuce rubucensa akan soyayya da rayuwa da holewa da nisha\u0257i ne da kuma rigima da zungurin sama da kara. Yayin da shekarun hankali suka hau shi yana iya canja akalar rubutunsa zuwa nazarin rayuwa da fa\u0257i tashi da kiri da muzu da sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p>Makaranta su ne alkalai, idan sun ga rubutun na cike da batsa da lalata da sakin baki, nan take za su iya bijirewa ko waye su tilasta masa yin ritaya matu\u0199ar ba zai gyara ba. Idan kuma ba a iya samun haka ba, ba zai zama adalci a ce wake \u0257aya na \u0253ata gari ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin ya kake ganin tafiyar Adabin Hausa? Ma\u2019ana, irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Adabin Hausa na samun cigaba amma galibi irin na mai ha\u0199ar rijiya ne. Ana samun \u0199aruwar marubuta da makaranta amma yawanci da\u0253en kwalo ake yi. Ka ga rubutu a cukurku\u0257e kamar ana caku\u0257a \u0257an wake. Rubutu babu ma&#8217;ana babu wa\u0199afi babu aya. Kuma wai marubuci ne. A da gwamnati na taimakawa harkar adabi da yaren Hausa, amma yanzu kusan ci da \u0199arfi ake yi. A wasu makarantun sakandare \u0257in ma an daina koyar da Hausa wai saboda ci baya ne. Kenan ba za a iya samun ingantaccen rubutun Hausa ba tunda a kasuwa ake tsinta. A wajen batun bun\u0199asar harshen babu laifi, domin kuwa har ana ta samun kafafen ya\u0257a labarai na gargajiya da na zamani, na intanet da na satilayit suna ta ya\u0257a shi sosai da gaske. Amma ta fuskar rubutu kuwa, babu wani abin yabawa saboda hatta gidajen jaridu yawanci suna tafka kura-kurai a rubutun nasu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wacce Karin Magana ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Na fi son karin magana mai \u0257auke da azanci ko haibaici ko gugar zana. Saboda irin wa\u0257annan sun fi da\u0257in isar da sa\u0199o yayin da ake son a yi nuni cikin nisha\u0257i. Misali karin magana irin su, makaho bai san ana ganinsa ba, sai ya ji an zungure shi, Mu gani A kasa, an ce da kare ana biki a gidansu, na munafukinka tabarmarka, zancen banza, zakara ya taka wuka da dai sauransu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin ko akwai wani labarin da ka ke rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Littatafin Tekun Labarai na uku da na hu\u0257u nake son fitarwa ba da jimawa ba. Tuni na \u0199ulla zaruruwan labaran na kuma samar musu da take. Abin da ya rage kurum shi ne samun zama na rubuta su yadda ya dace. Wa\u0257annan littatafai, ci gaban gajerun labaran Littafi na \u0257aya da biyu ne. Kowanne littafi akwai irin salon da ke cikinsa. Littafi na \u0257aya \u0257an sarki ne ke ba wa Sarki labari, littafi na biyu Waziran Sarki ne ke ba wa Sarki. Littafi na uku kuwa mutanen gari ne ke ba wa Sarki labari. Littafi na hu\u0257u kuma mutanen gari ne ke ba wa junansu labari.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan Tekun Labarai na uku da hu\u0257u kuma akwai wani littafi mai suna <strong><em>Hanyar Jidda. <\/em><\/strong>Labari ne akan wata \u0199ir\u0199irarriyar tafiya daga tashar motar Unguwa Uku zuwa Jidda da ke Saudi Arabiya wadda tauraron labarin ya yi cikin shekaru takwas. Labarin na \u0199unshe da abubuwan mamaki da tarihi da al\u2019adu da soyayya da sauransu. Na rubuta labarin ne a bisa abin da ya faru a Sudan a shekarar 2006 tsakanin gwamnatin Sudan da \u2018yan Janjawid a yankin Darfur. In sha Allahu ba da jimawa ba za su fito.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Duk wanda zai yi rubutu ya tabbata ya \u0257aura aniya ta \u0199warai a ransa ba domin ganin kitson wance ba. A yi rubutu mai tsabta da ma&#8217;ana, ba rubutun tir da shiririta ba. A guji rubutun \u0253atanci ko batsa da cin zarafin juna. Abu ne mai amfani marubuta su ri\u0199a ba wa junansu labaran da suka rubuta suna yi wa<\/p>\n\n\n\n<p>kansu gyara. Wannan shi ne hadafin da \u0199ungiyar ANA take kai kuma ta wannan hanyar an yi wa marubuta da yawa gyara mai ma&#8217;ana kuma sun amfana sosai ciki kuwa har da ni. Duk mai sha&#8217;awar soma rubutu ya yi azama da gaske kuma ya kyautata niyya tare da zurfafa bincike. A guji rubutu mai salon daga buhu sai tukunya saboda gudun butaci.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta &#8216;yan uwanka da kuma al&#8217;umma masu karanta littattafanka?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Kira ga gwamnatoci shi ne, kada a manta mafari. Marubuta su ne mafarin cigaban adabi. Yadda ake yi musu shakulatin \u0253angaro a wannan lokaci daidai yake da an ci moriyar ganga an jefar da kwaurenta. Ya kamata a \u0253ullo da sababbin hanyoyin \u0199arfafa gwiwar marubuta yadda haza\u0199arsu za ta cigaba da kaifafa su ri\u0199a za\u0199ulo hanyoyin da za a warware matsalolin Arewaci da ma \u0199asar Nijeriya baki \u0257aya. Haka kuma gwamnatoci na iya kai wa marubuta \u0257auki wajen tallafa musu da duk abin da ya dace domin su wallafa rubuce-rubucensu kuma su ci riba. Ba kamar yanzu ba da marubuta ke ta fa\u0257i tashi suna aiki kan jiki kan \u0199arfi amma ha\u0199a ya kasa cimma ruwa ta fuskar kasuwancilittattafanka Marubuta &#8216;yanuwana kuwa, ha\u0257in kai wajibi ne. Ha\u0257in kai shi ne tushen nasara da isuwa ga biyan bu\u0199ata. Manyan marubuta su ci gaba da ha\u0199urin tarbiyyantar da mu \u0199anana ta hanyar shawarwarin da \u0199arfafa gwiwa. Mu kuwa \u0199ananan marubuta, wajibi ne mu kasance masu ladabi da biyayya da girmama na gaba. Ta haka ne burin da muke da shi na sauya al\u0199iblar rubutu zuwa na zamani zai kai ga gaci.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Daga \u0199arshe, me za ka iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Bakandamiya gida ne kuma zaure ne mai hidima \u0199warai ga harshen Hausa da Adabi. Zan iya cewa babu wani dandalin intanet da yake tiri-tiri da marubutan Hausa kamar sa. Abubuwan da na sani ya yi wa marubuta ba za su \u0199idayu ba, musamman fa aka shirya bita ga marubuta domin sanin dabarun rubutun shiga gasa. Kuma daga wa\u0257anda suka bibiyi shirin an samu wadda ta yi nasara da kuma wa\u0257anda labarunsu suka samu jinjina musamman a gasar BBC ta marubuta mata. Haka kuma Bakandamiya ta shirya gasa ta musamman ga kungiyoyin marubuta da aka shafe watanni ana fafatawa daga karshe aka shirya wani gagarumin biki aka karrama \u0199ungiyoyin da suka yi nasara. Ga kuma hidimar da ake yi wa marubuta wajen tallata su gami da ayyukansu. Babu abin da za mu ce sai godiya da fatan Allah ya \u0257aukaki wannan kamfani ya sa ya zama tambari a duk duniya a ji \u0257uriyarsa. Amin summa amin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsarawa da gabatarwa:<\/strong> Asma&#8217;u Abdallah (Fulani Bingel)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A yau hirarmu da marubuta ta yi babbar kamu, inda ta yi kacibis da hazikin marubuci, manazarci, kuma akawu, Danladi Haruna. Ga yadda hirar tamu ta kasance. Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba. Amsa: Assalamu Alaikum. Sunana dai Zakariyya Haruna&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/rubutu-dai-rubutu-ne-babu-wanda-ya-fi-wani-sai-wanda-ya-iya-tsara-labari-tare-da-salon-isar-da-sako-mai-armashi-danladi-haruna\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Rubutu dai rubutu ne, babu wanda ya fi wani sai wanda ya iya tsara labari tare da salon isar da sako mai armashi &#8211; Danladi Haruna<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4062,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[78],"tags":[96,95,79],"class_list":["post-4060","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-interviews","tag-danladi-haruna","tag-hira-da-danladi-haruna","tag-hira-da-marubuta"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2023\/12\/Hira-da-Danladi-Haruna.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4060","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4060"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4060\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4062"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4060"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4060"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4060"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}