{"id":4140,"date":"2024-01-20T06:37:50","date_gmt":"2024-01-20T06:37:50","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4140"},"modified":"2024-01-21T18:44:50","modified_gmt":"2024-01-21T18:44:50","slug":"sharhin-littafin-bakar-tafiya-na-amina-abubakar-yandoma","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-bakar-tafiya-na-amina-abubakar-yandoma\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Bakar Tafiya&#8217; na Amina Abubakar &#8216;Yandoma"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan Littafi: <strong>Bakar Tafiya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Sunan Marubuciya: <strong>Amina Abubakar &#8216;Yandoma<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka Buga Littafi: <strong>Hikaya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar Bugu: <strong>2023<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Yawan Babi: <strong>17<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai Sharhi: <strong>Hajara Ahmad Oum-Nass<\/strong><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tarihin marubuciyar a takaice<\/h2>\n\n\n\n<p>Aminatu Abubakar &#8216;Yandoma, an haife ta a garin Katsina, ta yi karatu a cikin garin katsina, ta fara rubutu bayan ta kammala makarantar secondary school a shekarar 2019, ta rubuta litattafai da dama wa\u0257anda suka ha\u0257a da na zamantakewa sai kuma na barkwanci da kuma na aljannu.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan shi ne tarihin marubuciyar a ta\u0199aice.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tsokaci kan littafin<\/h2>\n\n\n\n<p>Sanadi ko kuma ace sila wasu abubuwa ne da suke faruwa ga \u0257an adam, a wani lokacin ma sai mutum ya \u0199ir\u0199irarwa kansa faruwar abin daga baya ya ambace su a matsayin kalmar \u0199addara duk da shi ne ya \u0199ir\u0199irarwa da kansa faruwar su.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar dai yadda Rabson, Salma, Basma, suka zama silar wanzar da mummunan \u0199addara ga Jafar da Biba, wajen kwasar romon zunuban su.&nbsp;<\/p>\n\n\n\n<p>Na san da yawa za su ce \u0199addarar wani ba ta ta\u0253a shafar wani, amma kuma idan Allah ya so jarrabaka sai ya \u0257ora ma nauyin zunuban wani don ya gwada imaninka.&nbsp; Labarin zai fi kama da films \u0257in horaye da masu shan jini, ta wata fuskar kuma ya fi kama da na hatsabiban aljannu ko kuma fatalwa da aka saba gani a fina finan indiya. Sai dai duk da haka ya samar da kyakkyawan darasi na illar taurin kai ga mutane, da bijirewa umarnin miji da iyaye.<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice dai labari Ba\u0199ar Tafiya labari ne na wasu matasa guda biyar da suke da buri mabambanta na zuwa wani gari, kwatsam kuma suka yi karo da mummunan \u0199addara ta silar mutuwar Direbansu a tsakiyar jeji ba tare da sun san dalili ba. Hakan ya sa suka bazama suka nausa cikin jejin da tunanin hanyar dawowa gida suka nufa, ashe mahallakarsu suka tunkara.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abubuwan birgewa game da littafin<\/h2>\n\n\n\n<p>Akwai abubuwa masu yawa sosai na birgewa a cikinsa. ka\u0257an a ciki su ne Jigon da aka sa\u0199a labadin da yadda marubuciyar ta fito da illar bijirewa miji, da kuma rashin bin umar ni mahaifi.<\/p>\n\n\n\n<p>Tasirin addu:a ga musalmi a duk halin da ya tsinci kansa.<\/p>\n\n\n\n<p>Warwarewar labari bayan an nuna kamar ba za a rayu cikin sa ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Tasirin addu&#8217;ar Uwa ga yaranta.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigon littafin<\/h2>\n\n\n\n<p>An gina labarin ne akan Jigon kuskuren \u0199auracewa umarnin miji da kuma na iyaye, sai tasirin addu:a ga bawa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Zubi da tsari<\/h2>\n\n\n\n<p>Tun daga farko marubuciyar ta yi nasarar ri\u0199e mai karatu, ta yadda ta ja zaren labarin nata, ta sa\u0199a shi ta kuma kai shi \u0199ololuwa wajen wanzar da matsala, har kuma zuwa a \u0199arshe ta yi nasarar warware shi cikin salo mai armashi da gamsar wa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Halayen taurarin labarin<\/h2>\n\n\n\n<p><strong>Rabi&#8217;u (Rob son)<\/strong>: \u018aan gayu ne da ko a kalamansa da shigarsa yake bayyana \u0257abi&#8217;arsa ta irin guy \u0257in da ya yi wa makarantar arabi da ta zamani gudun famfala\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Jafar<\/strong>: Yaro mai ladabi da biyayya da nema wa mahaifansa mafita, mai tsananin ru\u0199o da addini da \u0199aunar iyayensa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Salma<\/strong>: Shagwa\u0253a\u0253\u0253iyar yarinya ce da mahaifiyarta ta sangarta ta, take kuma nuna mata cewar za ta iya komai saboda suna da ku\u0257i da wadata.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Basma<\/strong>: Marar ha\u0199uri da fatali da duk wasu sharu\u0257\u0257a na zaman aure, bijirarriya a wurin miji mai girmama al&#8217;amarin \u0199awayenta sama da na mijinta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Biba<\/strong>: Mai sanyi hali da dogaro da kai ta \u0257auki kalmar babu maraya sai rago ta du\u0199ufa wajen gina rayuwar \u0199annainta don su yi karatu, tana kuma girmama al&#8217;amarin mahaifiyarta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Garba Kisa, Audu Gwarama, Nura Shila<\/strong>: Su dukansu &#8216;yan fashi ne, manyan \u0199wauraye masu haddasa ruguntsumi da fa\u0257an banga a siyasa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">\u018aarsau<\/h2>\n\n\n\n<p>Akwai \u018aarsau da yawa a labarin, wanda ya ha\u0257a da na addini, tausayi, al&#8217;ajabi, tawakkali, da sadaukarwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau Na Addini<\/strong>: A shafi na 30 in da Jafar ya ke cewa Biba &#8220;Biba yanzu ba lokacin kuka ba ne, mu sa mu mafita, ni fa gani nake mu ha\u0199ura da dajin nan mu zauna cikin gidan nan kawai in Allah ya yi za mu fita shi zai kawo mana \u0257auki da kan shi, saboda fa\u0257ar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam da ya ce &#8220;Idan annoba ta samu gari to na ciki su zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau Na Sadaukarwa<\/strong>: Lokacin da Biba ta fara magana, &#8220;Sanin ha\u0257arin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani bala&#8217;i ya samu \u0257an uwanmu kada wanda ya \u0199ara \u0199o\u0199arin guduwa ya rabu da sauran.&#8221; Anan duk sun amince da shawarar Biba na su rayu tare su mutu a tare.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na Tawakkali<\/strong>: A shafi na 47 Jafar ya fa\u0257a musu &#8220;A halin da muke ciki yanzu ba mu da mafita face mu dogara da Allah mu yi Basmala muci abubuwan da muka samu, Waman ya tawakkalu Alallah, Fahuwa hasbuhu.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na Nadama<\/strong>: A shafi na 39 Basma kuka take tana sambato ita ka\u0257ai, &#8220;Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, da na bi shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin ta gaban goshi, Allah ya isa tsakanina dake ta gaban goshi ke ki kai ta tura ni, ina ma Habib rashin mutunci, yanzu ga shi nan na baro \u0257ana, mijina yana fushi da ni na san mutuwa zan yi.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aaursau na Imani ga Allah<\/strong>: A&nbsp; Shafi na 41 muryar Aljana ta bayyana tana mai yi musu garga\u0257i &#8220;Kun yi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya \u0199are, a sannu zaku ba\u0199unci lahira.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Jafar yayi \u0199arfin halin fara magana.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;\u0198arya kike ya ke wannan la&#8217;anannar halitta, ke baki isa ki kashe mu ba sai dai in kwanan mu ya \u0199are, Ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma ba dai ke ba.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau Na Shawara<\/strong>: Tasirin Addu&#8217;a ga bawa a shafi na 52 in da wani dattijon aljani yake ba su shawara da su ri\u0199e addu&#8217;ar LA&#8217;ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN, domin ita ka\u0257ai ce za ta cece ku.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Darsau Na Tsoratarwa<\/strong>: Lokacin da direbansu ya mutu muryar Aljana ta bayyana &#8220;Kun yi kuskuren&nbsp; shigowa DAJIN KAI KAZO!! Ku masu taurin kai Dukkan ku babu wanda zai fita da rayuwar shi. Za mu ri\u0199a yi muku \u0257auki \u0257ai-\u0257ai har sai mun \u0199arar da ku&#8221; Hahahaha.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aarsau na Barkwanci. : A shafi na 53 bayan \u0253acewar Aljani Rabson, ya ma\u0199al\u0199ale Basma dake kusa da shi.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ba ka da hankali? Ina matar aure za ka rin\u0199a shige mini?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ke da auren na ha\u0257a ku a turmi na \u0198ul\u0199ule. Kina matar aure tsabar gantali me ya fito da ke wannan tafiyar?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Da dai sauransu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kurakurai<\/h2>\n\n\n\n<p>A tashin farko marubuciyar ta datse ala\u0199ar \u0199auna tsakanin mai karatu da jarumanta, ta yadda sakin layi ya yi yawa matu\u0199a. Misalin farkon labarin an fara hasko gidan Basma, da yadda take ta musayya da mijinta. Kafin mai karatu ya fahimci wainar da ta toya aka yi tsalle aka fa\u0257a gidan su salma. A haka dai aka yi ta sakin layi har aka sada mu da jaruman da ba mu ji mun sha\u0199u ba har sai da tafiya ta mi\u0199e. Ko me ya sa haka?<\/p>\n\n\n\n<p>Tun daga farkon labarin har zuwa \u0199arshensa marubuciyar ta yi watsi da \u0199a&#8217;idojin rubutu. kamar yadda aka ha\u0257e kalmomi masu yawa wa\u0257anda ya kamata a ce a rabe suke, kamar su :<\/p>\n\n\n\n<p>Baka madadin BA KA<\/p>\n\n\n\n<p>Isaba madadin ISA BA<\/p>\n\n\n\n<p>Dani madadin DA NI<\/p>\n\n\n\n<p>inje &#8212;- In je<\/p>\n\n\n\n<p>yayi &#8212;&#8211; ya yi<\/p>\n\n\n\n<p>bada &#8212; ba da<\/p>\n\n\n\n<p>abinda &#8212; abin da<\/p>\n\n\n\n<p>dani &#8212; da ni<\/p>\n\n\n\n<p>nayi, banga, jeki, zaki, kinyi, zani, barshi, yimashi, zakaje&#8230;&#8230;<\/p>\n\n\n\n<p>Da sauran su dai. Ko me yasa haka?<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai Hausar baka sosai a labarin kamar su : Mani, madadin mini, fah madadin fa.<\/p>\n\n\n\n<p>hajara madadin Hajara.<\/p>\n\n\n\n<p>&nbsp;Shin marubuciyar ta manta ana sanya farkon suna da babban harafi ne?<\/p>\n\n\n\n<p>Abubuwan da suka faru a jejen da matsalolin da suka haddasu ga jaruman ba su yi kama da abubuwan da ke faruwa a gaske ba. Amma ban sani ba ko marubuciyar ta shiga jejin ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Shin labarin na gaske ne, ko kuma dai almara ne?<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0199arshe ina jinjina da fatan alkhairi ga fasihiya &#8216;yar baiwa Allah ya \u0199ara basira da fikra.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko ban fa\u0257a muku ba kun san; Labarin ya cancanta ta kowacce kusurwa idan aka yi duba da shi ne Bakandamiyar marubuciyar, wanda mutane da dama sun so shi har kuma a gobe suna kan \u0199aunarsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Kuna iya karanta <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/bakar-tafiya-1\/\">littafin Bakar Tafiya<\/a> a Hikaya kyauta.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan Littafi: Bakar Tafiya Sunan Marubuciya: Amina Abubakar &#8216;Yandoma Inda aka Buga Littafi: Hikaya Shekarar Bugu: 2023 Yawan Babi: 17 Mai Sharhi: Hajara Ahmad Oum-Nass Tarihin marubuciyar a takaice Aminatu Abubakar &#8216;Yandoma, an haife ta a garin Katsina, ta yi karatu a cikin garin katsina, ta fara rubutu bayan ta kammala makarantar secondary school a&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-bakar-tafiya-na-amina-abubakar-yandoma\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Bakar Tafiya&#8217; na Amina Abubakar &#8216;Yandoma<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":4142,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28,58],"tags":[98,29,41],"class_list":["post-4140","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","category-hausa","tag-bakar-tafiya","tag-book-review","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/Sharhin-littafin-Bakar-Tafiya-na-Amina-Abubakar-Yandoma.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4140","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4140"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4140\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4142"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4140"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4140"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4140"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}