{"id":4184,"date":"2024-05-17T11:48:44","date_gmt":"2024-05-17T11:48:44","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4184"},"modified":"2024-05-29T11:39:28","modified_gmt":"2024-05-29T11:39:28","slug":"sharhin-littafin-hoton-mijina-na-nana-aicha-hamissou","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-hoton-mijina-na-nana-aicha-hamissou\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Hoton Mijina&#8217; na Nana Aicha Hamissou"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunan littafi: <strong>Hoton Mijina<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubuciya: <strong>Nana Aicha Hamissou<\/strong> <strong>Abdoulaye<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka buga littafi: <strong>Hikaya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar bugawa: <strong>2022<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai sharhi: <strong>Hasssana Labaran \u018aanlarabawa<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>An gabatar da wannan sharhi ne da farko a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar 31 ga watan Junairu na 2024.<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tarihin marubuciya<\/h2>\n\n\n\n<p>An haife Nana Aicha Hamissou Abdoulaye a ranar Laraba ashirin da bakwai ( 27) ga watan Yuli na shekarar dubu \u0257aya da \u0257ari tara da casi&#8217;in da hu\u0257u (27\/07\/1994) a unguwar sabon gari ta jihar Mara\u0257i jamhuriyar Nijar. <\/p>\n\n\n\n<p>Ta fara karatu a \u0253angaren addini a madarassatul Hizibur Rahim da ke unguwar Zaria ta 2 a nan garin Mara\u0257i. A lokacin da ta cika shekara shida a duniya aka saka ta a makaratar boko a shekarar 2000 a wata primary mai suna Ecole sabon gari a nan garin Mara\u0257i. Ta gama primary a shekarar 2006 inda kai tsaye ta \u0257ora karatunta a wata \u0199aramar Sakandire mai sunan CEG Rauda. Bayan ta gama wannan ne ta wuce babbar sakandare mai suna Lyc\u00e9e \u018aan Baskore. A lokacin ne kuma Allah Ya albarce ta da saukar Alkur&#8217;ani a shekarar 2013.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan ta gama Sakandire ta samu gurbin karatu a jami&#8217;ar Gwamanti mai suna Universit\u00e9 DanDicko DanKoulodo de Maradi (UDDM) a shekarar 2015. Sakamakon yajin aiki ba ta gama ba sai a watan Yulin 2020 inda ta samu kwalin digiri a fannin Etude d&#8217;Impact Environnemental (Nazarin Tasirin Muhalli). A \u0199arshen watan Disambar shekarar ta \u0257ora master a jami&#8217;ar Abubakar Ibrahim International University a \u0253angaren Gestion de L&#8217;environnement (Yadda za a kula da Muhalli). Wani uzuri mai girma ya \u0257an tsayar da ita, da tun a bara za ta gama Master \u0257inta. A ta\u0199aice dai da izinin Ubangiji ta kusa gama digiri ta biyu in Sha Allahu.<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0253angaren addini ma har yanzu tana neman ilmi, inda a halin yanzu tana karatu a madarassatul Imamul kisa&#8217;i, Al&#8217;islamiyatul Tahfizul Qur&#8217;an da take nan garin Mara\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta fara rubutu a yanar gizo a shekarar 2019. Ta yi rubuce-rubuce da dama a kafafen sadarwa, a halin yanzu tana da labarai fiye ashirin daga dogwayen labarai zuwa gajerun labarai.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Game da labari<\/h2>\n\n\n\n<p>&#8216;Hoton Mijina&#8217; Labarin wata mace ce mai kishin tsiya da \u0257aukar wa kai Dala babu gammo, wadda duk kusancin ta da \u0199awaye bai sa ko sau \u0257aya an ta\u0253a ganin mijin da za ta aura ba saboda kishin masoyin nata da take yi. Da\u0257in da\u0257awa da ma ba garinsu \u0257aya ba, sai abin ya zo mata a daidai wai mai ido \u0257aya ya le\u0199a shantu.<\/p>\n\n\n\n<p>Tauraruwar mai suna Rashida, ba ta tsaya a nan ba, ta yi ta girba wa \u0199awayenta da aminiyarta Aisha \u0199aryar mijin da za ta aura Kabir ustazu ne, shi ya sa bai yarda ta nuna hotonsa ba. A haka aka binne zancen, aka kuma ci biki aka su\u0257e ba tare da \u0257aya daga cikin \u0199awayenta ta yi arba da mijin ba.<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0253angaren aminiyar amarya Aisha kuwa, ta fi son sai ta yi karatu mai zurfi kafin ta yi aure. Wannan ne ya zamo shamaki tsakanin ta da Rashida, bayan ta cale \u0199asar Moroko karatu.<\/p>\n\n\n\n<p>Kwatsam, babu zato babu tsammani bayan wasu shekaru, Rashida ta yi karo da fuskar Aisha a matsayin matar da Kabir ya auro mata. Sanadin hakan ta gigice har da suma, a \u0199arshe bayan ta dawo hayyacinta ta warware musu zare da abawa, kan yadda ta yi ta kaffa-kaffa da hoton mijinta, sai ga shi a rashin sani aminiyarta ta aure shi. Dole babu yadda ta iya, ta na\u0257a gammon ha\u0199uri, ta rungumi mijinta da kishiyarta, duk da aminiyar tata ta so rabuwa da mijin gudun a ce ta ci amana. Amma Rashida ta \u0199i hakan ta nuna komai ya wuce za su ci gaba da zama a tare a matsayin kishiyarta cikin aminci.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Taken labari<\/h2>\n\n\n\n<p>A ha\u0199i\u0199anin gaskiya take\/sunan da aka ba wa labarin ya ja hankali \u0199warai da gaske. Aka kuma da\u0257a yin katari ya zamo asin-da-asin da abin da labarin ya \u0199unsa. Dole a jinjina wa marubuciyar labarin, domin tun daga kan taken ta \u0257arsa wa mai karatu tunane-tunanen abin da zai riska dangane da taken labarin &#8216;Hoton Mijina&#8217;, haka nan, wata \u0199warewa ce ga marubuci a ce sunan labarinsa yana da ala\u0199abda labarin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Babban jigon wannan labarin shi ne kishi, sai kuma \u0199ananan jiguna kamar nuna \u0199arfin \u0199addara. Wadda duk yadda bawa ya kai ga dabara da kauce-kauce, bai hana abin da Allah Ya hukunta tabbatuwa. Kuma jigo ne mai \u0199arfi kasancewar abin da ya fi damun mata kenan wato lamarin kishi, wanda yake warware karin maganar malam Bahaushe ta ciwon &#8216;ya mace na &#8216;yw mace ne.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Warwarar Jigo<\/h3>\n\n\n\n<p>Marubuciyar ta yi \u0199o\u0199ari wurin isar da sa\u0199on da jigonta ya \u0199unsa. Daga farkon labarin har zuwa \u0199arshensa inda ta samar da mafita a \u0199arshen labarin, hakan kuma \u0199warewa ce sosai ga marubuci.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Zubi da tsari<\/h3>\n\n\n\n<p>Ha\u0199i\u0199a marubuciyar ta tsara labarin da zubi mai kyau da jan hankali. Ta tsara labarin daga tsakiya, farko sai kuma \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abubuwan birgewa<\/h2>\n\n\n\n<p>Labari ne da farkonsa yake da jan hankali matu\u0199a, ta yadda marubuciyar ta bayyana mafarkin da tauraruwar labarin ta yi da \u0199awarta, wadda aljanu suka zo a siffar \u0199awar tata har suke tsorata ta da abin da ta fi tsana wato kishiya.<\/p>\n\n\n\n<p>Duk da dai marubuciyar ba ta fito kai tsaye a farkon labarin ta bayyana cewa matsalar a kan kishi ba ne, sai dai ta yi \u0199o\u0199ari wajen \u0257arsa wa mai karatu batun da zai ta kai-kawo a zuciyarsa a farkon labarin, a inda ta ce.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Babban abin tashin hankalin shi ne yadda aljanu suka yi siffar \u0199awata a mafarki har suke tsorata ni a mafi munin abin da na fi tsana a rayuwata.&#8221; (Abin da ta fi tsana a rayuwarta kishiya)<\/p>\n\n\n\n<p>Iya wannan sa\u0257arar ta isa haska wa makaranci\/manazarci cewa abin da ta tsana a rayuwarta shi ne jigon labarin da aka gina labarin a kai; wato kishi ko kishiya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kura-kuran da ke ciki<\/h2>\n\n\n\n<p>Duk \u0257an&#8217;adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba, don haka ba zai yiwu a ce komai da yake cikin labarin nan daidai ba ne, akwai wasu kura-kurai da suke cikin labarin wanda ya kamata a ce an fito da su domin marubuciyar labarin ta nazarce su ta yadda a gaba za ta kaucewa faruwar hakan a yayin da za ta rubuta wani labarin ko wasu labaran. Don haka ga kura-kuran nan kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Cushe<\/h3>\n\n\n\n<p>Rubuta kalmomin da suka zamo taken labarin da manyan ba\u0199a\u0199e, cushe ne kai tsaye ake yi wa mai karatu na lallai ana so a ankarar da shi cewa ga sunan labarin fa, kuma hakan ragon salo ne tun da dai tun farko mai karatu ya san sunan labarin to babu bu\u0199atar a yi ta rubuta shi cikin labarin kuma da manyan ba\u0199i. Haka nan, an ta rubuta su a mabambantan wurare ba sau \u0257aya ba ba sau biyu ba. Misali.<\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ina tunanin hanyar da zan bi ki ga HOTON MIJINA&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Da ire-iren wa\u0257annan wurare, wanda kai tsaye hakan ke nuna cushe ga mai karatu, a wata mahangar ma ana ganin yin irin hakan kamar raina basirar mai karatu ne.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Kufcewar salo<\/h3>\n\n\n\n<p>Labarin tauraro fagen ciki ne, amma akwai wurin da aka samu kufcewar salo ya zama tauraro fagen waje. A maimakon a rubuta hana ni sai aka rubuta hana ki.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Ha\u0257ewa da rabewa<\/h3>\n\n\n\n<p>A \u0253angaren nahawu cikin rubutun Hausa mun sani akwai \u0253angaren ha\u0257e kalmomi da rabawa, a cikin wannan labari duk da marubuciyar ta yi \u0199o\u0199ari sosai wurin kiyaye ha\u0257e kalmomi da rabawa, sai dai akwai wuraren da marubuciyar ta ha\u0257e alhali rabewa ne, fito da su zai sa marubuciyar ta nazarce su domin gujewa faruwar hakan a rubutunta na gaba. Don haka ga su kamar haka.<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li><em>sarawa kaina ya yi &#8211; sara wa kaina&nbsp; ya yi (Jakada wa)<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>akan &#8211; a kan<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>bana &#8211; ba na<\/em><\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Harufa masu \u0199ugiya<\/h3>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Watakila &#8211; Wata\u0199ila<\/li>\n\n\n\n<li>Karaji &#8211; \u0198araji<\/li>\n\n\n\n<li>Kasarsu &#8211; \u0198asarsu<\/li>\n\n\n\n<li>roko &#8211; ro\u0199o<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Zamiyar al\u0199alami<\/h3>\n\n\n\n<p>Duk da cewa marubuciyar ta yi namijin \u0199o\u0199ari wajen rubuta kowace kalma yadda take bisa \u0199a&#8217;ida, sai dai akwai wasu &#8216;yan wurare da na ci karo da su da ke tabbatar mini da zamiyar al\u0199alami ne. Fito da su zai sa marubuciyar ta ankara a rubutu na gaba domin kiyayewa, tare da sake bin rubutun ta duba kafin ta fitar da shi. Akwai wuraren da marubuciyar ta rubuta suffa, wasu wuraren kuma ta rubuta siffa, Shin wanne ne daidai?<\/p>\n\n\n\n<p>Mumunnar &#8211; Mummunan<\/p>\n\n\n\n<p>Marako \u2013 Maroko<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Rashin azanci da karin magana&nbsp;<\/h3>\n\n\n\n<p>Ha\u0199i\u0199a rashin azanci ya tauye darajar wannan labarin sosai, domin kamar miya ce da ba ta ji kayan \u0257an\u0257ano sosai ba, kenan dai ba za ta yi da\u0257in \u0257an\u0257ano a kan harshe kamar wadda ta ji kayan \u0257an\u0257ano sosai ba. To kamar haka ne a rubutun labari, da labarin da ya ji azanci da karin magana da labarin da bai samu wannan tagomashi ba babu ha\u0257i. Don haka wannan labari ya samu na\u0199asu ta fuskar karin magana da azancin da zai \u0199ara masa gar\u0257i har mai karatu ya ji yana shau\u0199i da mararin karatu.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">\u0198a&#8217;idojin rubutu<\/h3>\n\n\n\n<p>Dole a jinjina wa marubuciyar kasancewar ta kiyaye \u0199a&#8217;idojin rubutu sosai a rubutunta, ba kamar sauran rubutu ba ne da za a gan shi ta-ci-barkatai babu saka alamomin rubutu a ciki, wannan kam an \u0199awata shi sosai da \u0199a&#8217;idoji sai \u0257an abin da ba za a rasa ba na ajizanci ko mantuwa. Na ci karo da wuraren da marubuciyar ta saka alamar motsin rai a wuraren da ba muhallin ta ba, misali wurin da Rashida take tambayar mijinta shin shi ma ya yi mafarki ne? Sai ya ce, &#8220;Mafarki!&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A nan alamar tambaya ce za ta zo tun da tambayar ta ya yi, bai kamata alamar motsin rai ta zo a wurin ba.<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Mafarki! &#8211; Mafarki?<\/li>\n\n\n\n<li>Me ya sa na ce! &#8211; Me ya sa na ce?<\/li>\n\n\n\n<li>Ba yanzu ba! &#8211; Ba yanzu ba (Aya za ta iya zuwa, ko wa\u0199afi)<\/li>\n\n\n\n<li>Ko \u0257aya kam! &#8211; Ko \u0257aya kam,<\/li>\n\n\n\n<li>Raba mu da ustazunki da ya hana mu ganin shi! &#8211; Raba mu da ustazunki da ya hana mu ganin shi (Aya za ta iya zuwa ko wa\u0199afi)<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Sakin layi<\/h3>\n\n\n\n<p>A \u0199a&#8217;idar gajeren labari ba a amfani da sakin layi mai nuna alama, misali:<\/p>\n\n\n\n<p>*****<\/p>\n\n\n\n<p>Amma marubuciyar ta yi amfani da shi a lokacin ta tauraruwar za ta yi tunanin rayuwar baya, wanda hakan ragon salo ne, an fi so gajeren labari ya kasance a numfashi \u0257aya ba sai an tsittsinka shi ba, ya fi birge mai karatu ko mai nazari.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Tsinkaye<\/h3>\n\n\n\n<p>Anya kuwa mace mai kishi irin Rashida wadda ko hoton mijinta ba ta bari a gani za ta yi saurin zubar da makamanta ba tare da taratsi da kai ruwa rana ba? Duk da \u0199awarta da mijin nata ba su da laifi, amma abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa, a ce a lokaci guda kishin ya kau har ta kar\u0253i kishiyar da hannu bibiyu, a yadda mata suke da \u0257an karen kishi zai fi a ce an \u0257an turza kafin ta gane shayi ruwa ne ta dawo kan hanya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jinjina<\/h2>\n\n\n\n<p>Dole ne a jinjina wa wannan marubuciya, domin ta yi namijin \u0199o\u0199ari wajen girka labarin da ya ji \u0257an\u0257ano mai da\u0257i, ga fa\u0257akarwa da wa&#8217;azantarwa. Sannan ta \u0199ware a wurin gina gajeren labari wanda ba kowace marubuciya ce za ta iya ba. Haka nan, yadda ta bi matakai da kiyaye \u0199a&#8217;idoji abin a jinjina mata ne, domin ba don karatun nazari na yi wa labarin ba da ba lallai ma na hango kura-kuran ciki ba saboda da\u0257in labarin. Don haka ina yi mata jinjinar ban-girma da addu&#8217;a da fatan Allah Ya \u0199ara haza\u0199a da basira da kuma fikra. Allah Ya sa a da\u0257e ana yi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ku karanta littafin <em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/hoton-mijina\/\">Hoton Mijina<\/a><\/em> a Hikaya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunan littafi: Hoton Mijina Marubuciya: Nana Aicha Hamissou Abdoulaye Inda aka buga littafi: Hikaya Shekarar bugawa: 2022 Mai sharhi: Hasssana Labaran \u018aanlarabawa An gabatar da wannan sharhi ne da farko a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar 31 ga watan Junairu na 2024. Tarihin marubuciya An haife Nana Aicha Hamissou Abdoulaye a ranar&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-hoton-mijina-na-nana-aicha-hamissou\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Hoton Mijina&#8217; na Nana Aicha Hamissou<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":19,"featured_media":4189,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28],"tags":[29,101,41],"class_list":["post-4184","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","tag-book-review","tag-hoton-mijina","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sharhin-littafin-Hoton-Mijina.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4184","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/19"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4184"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4184\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4189"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4184"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4184"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4184"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}