{"id":4194,"date":"2022-07-14T09:56:00","date_gmt":"2022-07-14T09:56:00","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4194"},"modified":"2024-05-20T10:09:53","modified_gmt":"2024-05-20T10:09:53","slug":"amfani-da-darsau-wajen-kayata-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/amfani-da-darsau-wajen-kayata-labari\/","title":{"rendered":"Amfani da darsau wajen kayata labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan\u00a0<a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/hadakar-salo-sama-da-daya-wajen-samar-da-labari\/\">ha\u0257akar salo sama da \u0257aya wajen samar da labari<\/a>. Mun bayyana yadda ake sa\u0199a salo mabambanta su \u0199ara armashi a cikin labari, mun kuma fa\u0257i muhimmanci ko amfanin yin hakan. Yau insha Allahu za mu tattauna ne a kan \u018aarsau.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Me \u0257arsau ke nufi?<\/h2>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na labari<\/strong>:- Cikakkiyar kalmar ita ce \u0257arsawa. A rubutu na Adabi marubuci yana amfani da ita ne wurin yi wa masu nazarin shi sa\u0199a, ko nune ta yadda zai sanya musu irin tunanin da yake so su yi a zukatansu. Idan yana so su yi mamaki sai ya \u0257arsa musu wasu kalamai cikin hikima su fara mamaki, idan yana so su yi al&#8217;ajabi, ko su ji tsoro, ko su fara wata tantama, ko kuma ya sanya musu tausayi ko farinciki duk akwai hikimar da ake yi ta hanyar amfani da \u0257arsau a \u0257arsa musu wa\u0257annan tunanin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Ya ya ake yin \u0257arsau?<\/h2>\n\n\n\n<p>Hikimomin yin \u0257arsau&nbsp; su za mu tattauna a wannan ma\u0199ala insha Allah. Za mu ri\u0199a \u0257aukar kowacce ga\u0253a ta \u0257arsau \u0257aya bayan \u0257aya muna tattauna ta da misalanta. Kamar kullum yau ma zan so na yi amfani da wani tsagi na labari wurin ba da misalan don a fi fahimta. A don haka, zan yi amfani da labarina na&nbsp;<em>Da ma Sun Fa\u0257a Mini<\/em>&nbsp;don fito mana da misalan tarin \u0257arsau \u0257in da ke cikinsa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na al&#8217;ajabi<\/strong>:- Wannan shi ne \u0257arsau na farko da aka fara sa\u0199a labarin da shi. A labarin an nuna cewa Zainab ta yi mafarki da &#8216;yan \u0199ungiyar asiri sun ce za su shanye jinin jaririn da za ta Haifa. Bayan ta farka daga mafarkin a firgice kuma ga abin da ya biyo baya:<\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Mene ne? Me ya faru?&#8221; Ya shiga tambayarta a ki\u0257ime kamar yadda ita ma take ba shi amsar a ki\u0257ime tana waige-waige.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Bi . .. bi . . . biyo ni suka yi za su kashe ni.&#8221; Jin haka ya \u0199ara jawo firgitacciyar matar tashi jikinsa bayan ya fahimci mafarki ta yi. Don haka sai ya fara yi mata addu&#8217;o&#8217;i yana tofa mata yayin da ita kuma take ma\u0199ale da shi kamar za ta shige jikinsa, fuskarta ta ha\u0257a gumi sharkaf kamar sabuwar kuturwa a rana. Bai daina addu&#8217;ar yana shafa bayanta ba har sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ta dawo cikin hayyacinta ta nutsu sosai sannan ya tambayeta abin da ya faru.&nbsp; Nan take ta kwashe labarin mafarkin nata gaba \u0257aya na ganin dodonnin mutanen da ta yi da kuma ce mata da suka yi wai sai ta ba su \u0257an cikinta sun sha jinin shi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Jin haka ya yi shiru alamun damuwa suka bayyana \u0199arara a kan majigin fuskar shi, tuni ma ya saki matar tashi ya mi\u0199e tsaye ya fara safa da marwa a cikin yalwataccen \u0257akin nasu mai dishi-dishin hasken lantarki na bacci.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Murad.! Me ya faru?&#8221; Zainab ta tambaye shi tana mai \u0199ara yin nazarin shi ganin yadda a cikin \u0199an\u0199anin lokaci yanayinsa ya sauya. &#8220;Da ma sun fa\u0257a mini.&#8221; Ya ambata hakan daidai lokacin da ya goya hannayensa a baya da alamar \u0199ololuwar damuwa a tare da shi.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Dama sun fada maka?&#8221; Zainab ta maimaita furucin na shi \u0199asa-\u0199asa.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Su waye suka fa\u0257a maka? Kuma me suka fa\u0257a maka?&#8221; Ta yi masa tambayar da ta dawo da shi hayyacinsa ya yi firgigit kamar ya tashi daga bacci, sai a sannan ya fahimci ya yi su\u0253utar baki zancen zuci ya fito fili, kamar yadda ita ma Zainab \u0257in sai a lokacin ta gane cewa bai san lokacin da ya ce &#8216;Da ma sun fa\u0257a mini&#8217; \u0257in ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan muka yi nazarin wannan misalin, daga lokacin da Aliyu ya ce&nbsp;<em>da ma sun fa\u0257a mini<\/em>, marubucin ya \u0257arsa wa masu karatu al&#8217;ajabi da tunanin yadda aka yi aka haihu a ragaya. Su waye suka fa\u0257a masa? kuma a ina ya san su da suka fa\u0257a masa? Wa\u0257annan su ne tambayoyin da za su mamaye zuciya cike da al&#8217;ajabi gami da son sanin amsoshin su. Da ire-iren wannan hikimar ake so marubuci ya ri\u0199a \u0257arsa wa masu nazarin shi al&#8217;ajabi ta yadda zai ri\u0199e su su kasa ajiye labarin sai sun ga \u0199wal-uwar-daka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na zargi<\/strong>:- Bayan mijin nata ya \u0199i ya fa\u0257a mata su waye suka fa\u0257a masa, kuma me suka fa\u0257a masa, ga hikimar da marubucin ya yi amfani da ita wajen \u0257arsa wa masu karatu zargin shi:<\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Ba . . . ba . . . babu komai . . . Ai ban san su ba&#8221; Zainab ta tuno a yadda ya ba ta amsar sai ka ce wanda wani ya ce masa ya san su. &#8216;To amma kuma idan babu rami me ya kawo zancen a kula da rami?&#8217; Zuciyarta ta fara tuhumar shi, lokaci guda kuma Shai\u0257an shi ma ya zage da aiki tu\u0199uru wajen yi mata aringizon hujjoji da za su tabbatar mata da cewa Aliyunta \u0257an mafiya ne.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kin ga fa Aliyun ki yaro ne matashi da ba zai haura shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba, amma idan ana lissafa masu hannu da shuni na unguwarnan idan bai zo na \u0257aya ba to ba zai ta\u0253a wuce na biyu ba, ko dama a inda ya samu na shi ku\u0257in kenan \u0199ungiyar asiri?&#8221; Tuhuma ta farko daga she\u0257an.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Kin ga dama su biyu ne wa\u0257anda duniyarsu ke haskawa a unguwar nan, da shi da wannan ma\u0199ocin naku Alhaji Suma&#8217;ila dilan manfetur. Kuma kin san batun tsayawa fasalta kyan gidajenku, ko kuma \u0199iyasta abin da aka kashe wajen gina su \u0253ata lokaci ne, abu \u0257aya dai da mutum zai saka a ransa shi ne ba \u0199ananun ku\u0257a\u0257e aka narkar wajen gina su ba, to abin tambaya shi ne mece ce sana&#8217;ar mijinki da har zai iya gina gida irin wannan?<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Shi dama Alhaji Suma&#8217;ila dilan man fetur ne wanda yake da gidajen mai, don haka idan ya gina nasa gidan babu mamaki tunda dama da mai kama ake yin \u0199ota. Duba da yadda aka ce harkar man fetur na garawa. To amma Aliyunki fa wanda ba komai ba ce sana&#8217;arsa face sayar da goro? Shin ko shi ma goron ana samun ku\u0257i da shi ne kamar fetur? To amma babu mamaki saka zaren makaho a allura.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Ba ma wannan ba! Ko kin manta da wannan \u0257akin da yake cikin gidan nan naku wanda tunda kike ba ki ta\u0253a shiga ciki ba kamar yadda ba ki ta\u0253a ganin Aliyu shi ma ya shiga ba? To ko dai a cikinsa Aliyunki yake cin mushensa? Kinga fa kusan shekara \u0257aya kenan da \u0257aura aurenku da Aliyu, amma sau \u0257aya kika ta\u0253a le\u0199a \u0257akin, shi ma kuma duhu bai bari kin iya ganin komai a cikin shi ba Aliyu ya fito ya ja hannunki kuka koma falo.&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>A daidai wannan ga\u0253ar za ku tarar duk mai nazarin an \u0257arsa masa zargin Aliyu, duba da irin abubuwa da suka sa\u0253a da tunani na cikin ga\u0253ar labarin, don haka mai nazari zai fara zuba kadarar mujiyarsa don ganin rashin gaskiyar ta Aliyu a gaba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>\u018aarsau na tantama<\/strong>:- Ita kuma a wannan ga\u0253ar marubucin yana so ya ki\u0257ima masu nazari su kasa gane cewa Aliyu yana da laifi ko ba shi da laifi ne. Don haka sai ya sake yin amfani da \u0257arsau wajen \u0257arsa musu tantamar wancan zargin nasu na sama.<\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;Anya kuwa Aliyunki zai aikata abu irin wannan? ko kin manta yadda ya kasance mutum mai matu\u0199ar ibada ko ka\u0257an salla&nbsp; ba ta wuce shi a jam&#8217;i, kar ki manta fa duk abin da Aliyu yake yi ana kiran salla to kuwa ya ha\u0199ura har sai an idar. Sallar nafila kuwa dare da rana cikin yin ta yake, ga shi kuma ba ya rabo da azumin nafila, haka kuma akwai shi da kyakkyawar mu&#8217;amala ta yadda babu yadda za a yi ka zauna da Aliyu bai shiga ranka ba.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Aliyu yana da tsananin tausayi da yawan kyauta. To wai anya kuwa a samu \u0199uma a jikin kifi?&nbsp; Anya kuwa mutum mai irin wannan halayyar zai yi abin da ki ke zargin shi?&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>&#8220;To amma idan ban zarge shi ba ta yaya wanda bai \u0257an\u0257ana fura ba zai ce sikari bai ji ba?&nbsp;&nbsp; Su waye suka fa\u0257a masa kuma me suka fa\u0257a masa?&#8221; Duk ta jera wa kanta jerin gwanon wa\u0257annan tambayoyin da amsarsu ba zasu samu ba a gareta.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Da zarar mai nazari ya zo ga\u0253ar nan, zai fara yarda a ransa cewa tabbas bai kamata mutum mai kyawun hali ya zama \u0257an mafiya ba, don haka gaba \u0257aya za a iya \u0257arsa masa tantama ya kasa gane al\u0199iblar labarin.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Abin lura<\/strong>: \u018aarsau ba shi da wata iyaka, ana iya \u0257arsa wa mai nazari duk abin da aka ga dama a cikin ransa don a cimma wata manufa ko a ribaci zuciyarsa. Ana iya \u0257arsa masa farin ciki, ko ba\u0199in ciki da duk wani abu mai kama da hakan.<\/p>\n\n\n\n<p>Za mu dakata a nan sai a ma\u0199ala ta gaba insha Allah. Kafin sannan kada ku manta \u0199ofar gyara, sharhi, tsokaci, \u0199arin bayani ko shawara a bu\u0257e take.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan\u00a0ha\u0257akar salo sama da \u0257aya wajen samar da labari. Mun bayyana yadda ake sa\u0199a salo mabambanta su \u0199ara armashi a cikin labari, mun kuma fa\u0257i muhimmanci ko amfanin yin hakan. Yau insha Allahu za mu tattauna ne a kan \u018aarsau.&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/amfani-da-darsau-wajen-kayata-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Amfani da darsau wajen kayata labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4195,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,102,19],"class_list":["post-4194","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-darsau","tag-writing-tips"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Amfani-da-darsau-wajen-kayata-labari.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4194","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4194"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4194\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4195"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4194"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4194"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4194"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}