{"id":4199,"date":"2024-05-29T16:52:46","date_gmt":"2024-05-29T16:52:46","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4199"},"modified":"2024-05-29T16:53:59","modified_gmt":"2024-05-29T16:53:59","slug":"marubuta-haske-ne-kuma-idaniya-ne-ga-rayuwar-alumma-sanah-matazu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/marubuta-haske-ne-kuma-idaniya-ne-ga-rayuwar-alumma-sanah-matazu\/","title":{"rendered":"Marubuta haske ne, kuma idaniya ne ga rayuwar al&#8217;umma &#8211; Sanah Matazu"},"content":{"rendered":"\n<p>A ci gaba da tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon mun tattauna da marubuciya Sanah Matazu inda ta haska mana abubuwa da dama da suka shafi rubutu da kuma rayuwarta. Ga yadda hirar ta kasance:<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarki.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Cikakken Sunana shi ne Hassana Sulaiman Isma&#8217;il. An haife ni a shekarar 1993. Ni haifafiyar jihar Kano ce, \u0199aramar hukumar Gwale a unguwar Goron Dutse. Ina da aure da yarinya guda \u0257aya. Ina zaune ne a unguwar Northwest ta wurin Kabuga. Matakin karatu kuma ina karantar Hausa Education a Jami&#8217;ar Bayero.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A wace shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na soma rubutu ne a shekarar 2015, sai dai \u0257aukar niyyar fara rubutuna ta \u0257okantu ne a raina tun ina aji shida na \u0199aramar makarantar primary. Abubuwa da dama sun ja hankalina game da rubutu, sai dai babban abin da ya mayar da ni marubuciya shi ne yawaitar karance-karance mabambanta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.<\/p>\n\n\n\n<p>Litattafaina sun kai guda 22 wasu sun \u0253ata ina neman su wasu kuma na buga su, wasu kuma suna kan manhajoji mabambanta, yayinda wa\u0257ansu daga ciki suke \u0253u\u0199atar gyare-gyare. Ga su daki-daki:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Shi Ne Burina<\/li>\n\n\n\n<li>Rabi&#8217;atul Adawiyya<\/li>\n\n\n\n<li>Sanadin Bodin<\/li>\n\n\n\n<li>Yanar Gizo<\/li>\n\n\n\n<li>Gimbiya Zajlat<\/li>\n\n\n\n<li>&#8216;Yar Kurma<\/li>\n\n\n\n<li>&#8216;Yar Mafiya<\/li>\n\n\n\n<li>\u0198iyayya Ce Ko Son Zuciya?<\/li>\n\n\n\n<li>Mahaifiya Ce!<\/li>\n\n\n\n<li>Matar Saddik<\/li>\n\n\n\n<li><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/fitsarin-fako-1\/\">Fitsarin Fako<\/a><\/li>\n\n\n\n<li>Sarkakiya (Labarin Rayuwar Najwa)<\/li>\n\n\n\n<li>Kurman Dutse<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Sai kuma wa\u0257anda nake kan gyara labaran da \u0199a&#8217;idojin rubutun cikin su, ga su kamar:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Kaidinsu<\/li>\n\n\n\n<li>Yarda Ce Sila<\/li>\n\n\n\n<li>&#8216;\u01b3ar Fulani Ce<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Sai wa\u0257anda nake son bugawa, su ne kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Wata Mace<\/li>\n\n\n\n<li>Idan Ka Daka Ta Bado<\/li>\n\n\n\n<li><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/kuskuren-wasu-1\/\">Kuskuren Wasu<\/a><\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p>Akwai kuma gajeru, su ne kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Lefan Aro<\/li>\n\n\n\n<li>Nadamar Rayuwata<\/li>\n\n\n\n<li>Hannunka Mai Sanda<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na fi son Rayuwar Najwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Saboda wahalar da na sha wurin rubuta shi, kasancewar labarin ya shafu jinnu har tsorata ni aka soma yi akan rubutun.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1-1024x809.jpeg?strip=all\" alt=\"Hira da Sanah Matazu 1 - Bakandamiya Hikaya\" class=\"wp-image-4200\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1-1024x809.jpeg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1-300x237.jpeg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1-768x607.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1.jpeg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-1.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Sanah Matazu (a dama) ke karbar shaidar girmamawa a madadin kungiyar Fikra Writers&#8217; Association daga hannun Fatima Ibrahim Dan Borno (a hagu) a taron muhawarar kungiyar GAMJIK na shekarar 2022 <\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ba ni da ko \u0257aya, sai dai zan iya cewa akwai wa\u0257anda nake \u0199o\u0199arin koyo daga garesu ta fannin abin da ya shige mini duhu. Kamar Mutta\u0199a A Hassan da kuma Jibrin Adamu Rano.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ki ka ta\u0253a karantawa da ya fi burge ki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Suna da dama gaskiya. Na marubuta yanar gizo da kuma masu bugawa, amma zan iya bugar \u0199irji in ce duk litattafan Belli suna burge ni.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kin ta\u0253a shiga wata gasa? Idan eh ne amsar, shin ko kin ta\u0253a yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na ta\u0253a shiga gassani ba gasa \u0257aya ba. Alhamdullilah a duniyar rubutu na taka nasarori da dama wa\u0257anda har gobe ina alfahari da su a rayuwata. Babban nasarata ta farko ita zamana marubuciyar kanta. Domin burina ne.<\/p>\n\n\n\n<p>Nasarorin da na samu kuwa ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar Tsangayar Marubuta ta ranar 30\/12\/2018. Gasa ta farko dana soma ci kenan a duniyar rubutu wadda aka karramani a gidan Hisbah na Kano. Wadda na kar\u0253i kambun na uku.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar Marubuta Group Chat 4\/4\/2019. Gasa ta biyu dana sake ci a duniyar rubutu ita ma ta uku na zo. Na samu kyautar ku\u0257i naira 5000.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar Mujjalar Zauren Marubuta 18\/8\/2019. Gasa ta uku da na ci ita ce ta Mujallar Zauren Marubuta wadda na zo ta hu\u0257u. Na sami kyautar ku\u0257i 3000.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar Gusau Institute 1\/12\/2021. Sai gasa ta hu\u0257u da na ci ita ce kuma mafi \u0199ololuwar daraja wato gasar Gusau. Inda na samu zama zakara\/kaza na lashe ku\u0257i naira dubu \u0257ari biyu da hamsin da bugaggen littafi guda goma na labarin dana rubuta wanda aka buga. Ina alfahari da gasar saboda a kaina mata suka soma kar\u0253o kambun na \u0257aya a gasar tsawon shekara biyar da soma gudanar da gasar.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 B.B.C Hausa: Sai kuma gasar da ta biyo bayan ta Gusau wato BBC Hikayata wadda na samu shiga goman farko a shekarar 2020.<\/p>\n\n\n\n<p>Shiga ashirin da biyar \u0257in farko ma babbar nasara ce ballantana kuma goman farko, wannan babbar nasara ce a gare ni tabbas domin har gida aka aiko min certificate daga Abuja.<\/p>\n\n\n\n<p>Sau uku ina shiga sahun marubuta 25 na BBC Hausa, sau uku ina shiga Top 10 na BBC Hausa. Ina fatan kuma na shiga cikin ukun da suke da nasara idan rai ya kai mu da kuma rabo.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 The Nigeria Prize: Ita ma gasa ce da ake yi da bugaggen littafi, na samu zama ta uku a tsakanin jihohin da suka shiga gasar karon farko. Sai dai kuma su na \u0257aya ka\u0257ai suke ba wa kyauta. Shekarar da ta gabata ma na shiga ban kai matakin da suke muradi ba. Na sake komawa a 2024 shi ma dai haka. A ta\u0199aice dai,<\/p>\n\n\n\n<p>2021 na zo ta uku<\/p>\n\n\n\n<p>2022 na zo ta uku<\/p>\n\n\n\n<p>2023 na zo ta biyu.<\/p>\n\n\n\n<p>Ina fatan a 2024 na haye sira\u0257in nasarar wannam gasar. Domin har yanzu ban kai matakin da suke so ba saboda su na \u0257aya ka\u0257ai suke \u0257auka su ba shi kyauta. Sai dai na ji sun ce za su gyara nan gaba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Exquisite Competition 6\/3\/2022. Gasa ce &#8216;yar \u0199arama da na samu hayewa matakin ta uku.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar ya\u0199i ta Maya\u0199iya 2022. Na samu zuwa ta biyu a gasar rubutun.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2022 Gasar Kyauta Fundation ta Ilkima 2023. Na zo ta biyu a gasar.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2-768x1024.jpeg?strip=all\" alt=\"Hira da Sanah Matazu 2 - Bakandamiya Hikaya\" class=\"wp-image-4202\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2-768x1024.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2-225x300.jpeg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-2.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Sanah Matazu yayin da take zantawa da baturiyar dake kula da library na Gusau Institute a taron Gasar Gusau Institute na shekarar 2020<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> To idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> A baya bana tsara rubutu gaskiya, kawai idan rubutu ya zo mini ina somawa ko da ban gano \u0199arshen sa ba. Sai dai yanzu yadda muke \u0199ara tsunduma a harkar rubutu muna \u0199ara mu&#8217;amalantar Adabi da kuma masana. Na kan tsara \u0257in idan damar hakan ta samu ko da ban sama masa \u0199arshe ba. Domin wani labarin shi yake yin \u0199arshensa da kansa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Bana wannan gangancin ina dai rubuta tunanin na sakaya shi zuwa lokacin da zan bu\u0199aci aiwatar da shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ki kan \u0257auki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan \u0257auke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiyar magana a baya ma ni bana soma sakin littafi a yanar gizo sai na kammalashi gaba \u0257aya, saboda bana so na ga ana nema. Kuma har yanzu na fi rinjaye akan wannan tsarin, sai dai yanzu duba da yanayi da sauye-sauyen hidimar rayuwa, hidimar gida da karatu ga kuma matsalar wutar Nepa ba zan iya cewa kai tsaye ina kammala rubutu a lokaci kaza ba. Amma ina \u0199o\u0199ari matu\u0199a wurin ganin ban \u0199ure ha\u0199urin mabiyana ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Batun bincike kuma abu ne da ya zama wajibi ga duk marubucin da yake son rubuta abin da yake fatan ko da bayan ransa a \u0257aga a yaba, duk rubutun da babu bincike shirme ne. Ina \u0199o\u0199ari matu\u0199a wurin ganin na binciki matsalar da na \u0257ora al\u0199alami a kanta kafin fitar da ita ga masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Jigo a rubutu kawai zuwa yake yi, domin wani jigon ma kana tafe a hanya kake samunsa. Wani kuma wata hira ce za ta \u0257auki hankalinka har ka sa\u0199a zaren labari ka samar da jigon da kake jin ya zauna maka. Wani kuma wani ne zai zo maka da matsalarsa da bu\u0199atar ka yi rubutu akai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Tunani tare da nazari wurin tantance \u0257abi&#8217;ar da ta kamaci a saka\u0257a a jikin sunan wane. Domin akwai sunayen da suke da \u0199imar da ba kowace \u0257abi&#8217;a ake manna musu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko kin ta\u0253a amfani da wani \u0253angare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na ta\u0253a.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka ta\u0253a rubutawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> <em>Rayuwar Najwa<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne irin \u0199alubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake \u0199alubalen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> \u0198alubale kam babu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Taurarin da nake so gaskiya ba \u0257aya ba ne,<\/p>\n\n\n\n<p>Shukuriyya ta cikin labarin <em>Yarda Ce Sila<\/em>, saboda gwagwarmayar rayuwarta a matsayinta na &#8216;yar gudun hijira.<\/p>\n\n\n\n<p>Najwa saboda wahalhalun da ta fuskanta domin ita labarinta kusan gaba \u0257aya ma gaskiya ne. Sai kuma Halimatu ta cikin labarin Fitsarin Fa\u0199o.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya ban ta\u0253a ba, amma na kan ga masu irin matsalar nan na tambayar masana. Sai dai na kan ware na zomaye ne na kwashi rumbun ilmin da ake ba su domin na san zai yi mini amfani tunda yau gareka ne gobe ga \u0257an uwanka.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> \u018aebe kewa tare da fa\u0257a\u0257a tunani da kuma sauya tunanin shi kansa daga wani bigire zuwa wani bigiren da ba ma rayuwata ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na kan yi karatu. Na kan yi gyaran labarai na da suke bu\u0199atar gyara.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ba kowa ne yake gane \u0257ingishin kwa\u0257o ba. Sai kuma Kiki makaka zakara mai neman suna ba da hatsi ka ci tsakuwa. Saboda suna ba ni nisha\u0257i tare da bayyana ma&#8217;anarsu a bigiren da na ajiye su.<\/p>\n\n\n\n<figure class=\"wp-block-image size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3-768x1024.jpeg?strip=all\" alt=\"Hira da Sanah Matazu 3 - Bakandamiya Hikaya\" class=\"wp-image-4203\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3-768x1024.jpeg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3-225x300.jpeg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3.jpeg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3.jpeg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3.jpeg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Sanah-Matazu-3.jpeg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Sanah Matazu yayin da take hoto da Maigirma Sarkin Zazzau Bamalli tare da Maigirma General Muhammad Aliyu Gusau<\/em><\/figcaption><\/figure>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A naki ra&#8217;ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Kowanne da amfaninsa, kowanne kuma da lokacinsa. Buga littafi na ba marubuci \u0199imar zama cikakken marubucin da wasu ke hasasshen bai kai ba. Sai dai kuma rubutu a yanar gizo abu ne da yake tafiya da zamani. Allah kuma shi ne zamani, don haka dole \u0199anwar na\u0199i a amshi zamani yadda ya zo matu\u0199ar ba zai ta\u0253a mutuntaka ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al&#8217;umma?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Babbar magana. Tasirin marubuta a cikin al&#8217;umma abu ne da za mu iya kwana muna magana akai ba mu gama ba, sai dai a ta\u0199aice zan iya cewa marubuta haske ne, kuma idaniya ne ga rayuwar al&#8217;umma.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Tabbasa akwai shi &#8211; <em>Kundin Sanah<\/em>. Wani kundi ne mai \u0257auke da wasu muhimman abubuwa guda 30 wanda nake fatan ya dinga fita duk shekara da izinin Allah. Na kammala.shi har da cover \u0257insa bayar da aikin sa ne ya rage. Sai kuma <em>Turken Jaki<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wane ne tauraronki a cikin marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Tauraro na shi ne mai \u0199o\u0199arin samar da ci gaba a rayuwar marubuta kowaye shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Fim.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Su ji tsoro Allah. Su kyautata al\u0199alamin su. Su kaifafa tunaninsu. Tare da cire ganda waurin yin bincike kafin gudanar da rubutu. Uwa uba fa\u0257a\u0257a saninsu kan Adabi da mu&#8217;amalantar masanan da suka dace.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne burinki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Samar da ci gaba tsakanin marubuta ta fuskar warware duk matsalolin da za su taso mana a iya kanmu. Wala ta fanin rayuwa ko kuma fannin rubutu. A ta\u0199aice ina da buri kan gina wata gidauniya da za ta zamo madogara ga \u0257aukacin marubuta musamman marubuta Online irina.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me za ki iya cewa game da Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Bakandamiya! Sha kundum kenan. Sha gwagarmaya, zan iya cewa ban ta\u0253a ganin manhaja mai \u0199o\u0199arinta ba. Musamman wurin gudanar da aiyukanta cike da \u0199arfin gwiwa ba tare da ginshira ba. Gaskiya ina jinjina musu matu\u0199a da gaske. Aiyuka cikin inganci tare da za\u0199wa\u0199uran ma&#8217;aikata masu sanin ya kamata.<\/p>\n\n\n\n<p>Wani abu mai jan hankali shi ne yadda suke \u0199o\u0199arin bu\u0257e account a kowa ce kafar sadarwa domin duniya ta dama da su, gaskiya ba kowa zai iya wannan ba duba da cewar aikin aiki ne na gaske. Muna fatan Allah Ya ci gaba da dafa musu tare da \u0199arfafa musu gwiwar gudanar da duk wani abu da ya kamata.<\/p>\n\n\n\n<p>Amin. Mun gode sosai.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi wannan hira da Sanah Matazu ne a ranar 19 ga watan Maris, 2024.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa:<\/strong> Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ci gaba da tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon mun tattauna da marubuciya Sanah Matazu inda ta haska mana abubuwa da dama da suka shafi rubutu da kuma rayuwarta. Ga yadda hirar ta kasance: Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarki.&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/marubuta-haske-ne-kuma-idaniya-ne-ga-rayuwar-alumma-sanah-matazu\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Marubuta haske ne, kuma idaniya ne ga rayuwar al&#8217;umma &#8211; Sanah Matazu<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4208,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[78],"tags":[79,81,103],"class_list":["post-4199","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-interviews","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews","tag-sana-matazu"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Hira-da-Sanah-Matazu.jpeg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4199","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4199"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4199\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4208"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4199"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4199"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4199"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}