{"id":4259,"date":"2024-07-05T15:43:07","date_gmt":"2024-07-05T15:43:07","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4259"},"modified":"2025-05-02T05:29:51","modified_gmt":"2025-05-02T05:29:51","slug":"rubutun-batsa-koma-baya-ne-ga-dukkan-marubuci-mai-kima-haiman-raees","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/rubutun-batsa-koma-baya-ne-ga-dukkan-marubuci-mai-kima-haiman-raees\/","title":{"rendered":"Rubutun batsa koma-baya ne ga dukkan marubuci mai kima &#8211; Haiman Raees"},"content":{"rendered":"\n<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya Hikaya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi yi tattaki mun za\u0199ulo muku da fitacce kuma shahararren marubucin wake, da yake fassara wakokin Indiyawa gami da dan taba rubutun zube kansa, wato dai sha kundum a kowanne fanni, Jamilu Abdurrahman (Haiman Raees). Marubucin kuma mawakin ya bayyana irin gwagwarmayar da ya sha a harkar, dama sauran abubuwa da suka danganci rayuwarsa. Ku kasance damu domin jin ko wane ne Haiman Raees.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Malam Jamilu da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>To, Assalamu Alaikum warahamatullah wa barakatuhu. Cikakken sunana shi ne Jamilu Abdulrahman, amma an fi sani na da Haiman Raees. An haife ni a ranar uku ga watan Maris shekara ta alif dubu \u0257aya da \u0257ari tara da casa\u2019in da uku (3rd March, 1993) a garin Gadan Gayan, wanda ke gundumar Fanshanu, \u0199aramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a Najeriya. Na fara karatuna na boko da kuma na addini duk a garin Gadan Gayan ne kafin daga baya na dawo cikin garin Kaduna inda na ci gaba, kuma har yanzu dai ina ci gaba da karatun ne. Ina da aure kuma yanzu haka ina zaune ne a cikin garin Kaduna. Baya ga haka, ni marubuci ne, manazarci kuma mai sharhin litattafai da fina-finai tare kuma da fassarar wa\u0199o\u0199in fina-finan Indiya.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A wacce shekara ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinka har ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya na da\u0257e da fara rubutu, domin tun ina aji hu\u0257u a firamare na fara rubuta labarai, kuma har yanzu duk suna nan. Sai dai ban fara fitar da su a matsayin littafi ba sai a tsakanin 2022-23. Gaskiya tun ina yaro ni mutum ne mai son yawan karance-karance, domin tun ina aji uku a firamare na fara iya karatu kuma daga nan na dasa har yanzu. Shekera guda daga nan na fahimci cewa ina da labaran da zan iya bayarwa. To tun daga nan ne na fara rubuta labarai ina ajiyewa. In lokaci ya ja sai in kwafe su a cikin sabon littafi, ina kuma rubuta wasu sababbi. Baya ga rubutun zube, ina rubuta wa\u0199o\u0199i, wasan kwaikwayo da kuma mu\u0199aloli. Sannan ina rubutu da harshen Hausa da kuma Turanci.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1-1024x809.jpg?strip=all\" alt=\"Hira da Haiman Raees 1\" class=\"wp-image-4261\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1-1024x809.jpg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1-300x237.jpg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1-768x607.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1.jpg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-1.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuci Haiman Raees<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne irin \u0199alubale ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Babban \u0199alubalen da na fuskanta a baya dai shi ne rashin damar fara fitar da labaraina duniya ta san da zaman su. Hanyar da na bi wajen magance matsalar kuwa ita ce ha\u0199uri tare da ci gaba da rubutun ba tare da sagewar gwiwa ba. A yanzu kuma, babban \u0199alubalena shi ne \u0199arancin lokacin yin rubutu, domin ina da labarai masu tarin yawa da nake so in bayar amma babu isasshen lokacin bayar da su. Sai kawai in yi ha\u0199uri da \u0257an abin da ya samu kuma in yi abin da zan iya yi da shi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya na rubuta littattafai da dama, za su kai guda goma sha \u0257aya. Ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/fasaha-haimaniyya-1\/\">Fasaha Haimaniyya<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/fatalwar-sinu-1\/\">Fatalwar Sinu<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/birnin-sahara-1\/\">Birnin Sahara<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/voice-of-love-1\/\">Voice Of Love<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/baindiya-1\/\">Ba\u2019indiya<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/malam-jatau-1\/\">Malam Jatau<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/bakar-kaddara-1\/\">Ba\u0199ar \u0198addara<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/warwara-1\/\">Warwara<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/falsafa-1\/\">Falsafa<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/tambaya-1\/\">Tambaya<\/a><\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/mysterious-pen-1\/\">Mysterious Pen<\/a><\/em><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p>Amma Falsafa da kuma Mysterious Pen ba ni ka\u0257ai na rubuta ba, ha\u0257aka ce muka yi ni da Mujahid Nuhu Yusuf (Matashi)<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne littafi ka fi so a duk cikin littattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya na fi son littafin Birnin Sahara, saboda shi ne tubalin ginin duniyar labaraina na Duniyar Labaran Haiman (DLH).<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne littafi ne da ka ta\u0253a karantawa kuma ya fi burge ka?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya na karanta littattafai da dama wa\u0257anda suka burge ni matu\u0199a. A litattafan gida Nijeriya dai akwai <em><a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/magana-jari-ce\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Magana Jari Ce<\/a>, <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/uwar-gulma\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Uwar Gulma<\/a>, Fasaha A\u0199iliya, <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/kundin-tsatsuba\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Kundin Tsatsuba<\/a>, <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/things-fall-apart\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Things Fall Apart<\/a>, <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/a-man-of-the-people\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">A Man Of The People<\/a><\/em> da kuma From <em>Fatika With Love<\/em>. A litattafan \u0199asashen waje kuma akwai <em><a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/wizards-first-rule-novel\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Wizard\u2019s First Rule<\/a>, <a href=\"https:\/\/bakandamiya.com\/origin-novel\/\" target=\"_blank\" rel=\"noreferrer noopener\">Origin<\/a>, Twilight, A Game Of Thrones<\/em> da kuma <em>Harry Potter<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye ka ke farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya sau tari sai na tsara tukunna nake farawa. Amma akan samu lokacin da kawai farawa nake yi in ya so daga baya sai in gyara abubuwan da suka kamata.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Rubutawa nake yi a gefe saboda gudun mantuwa, in na samu nutsuwa sai in dawo in duba. To amma da yake yawancin labaraina suna da ala\u0199a da juna, irin wannan sabon tunani na iya zama wani littafin daban ko kuma wani labarin da zai fito ta wata siga ta daban.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka ta\u0253a rubutawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Birnin Sahara, saboda shi ne tubalin ginin Duniyar Labaran Haiman (DLH). Baya ga haka kuma, littafi ne da ke \u0257auke da sa\u0199onni masu yawa da ke bu\u0199atar bincike mai zurfi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wani lokaci kan marubuci kan cushe har ya kasa rubuta komai. Shin ka ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Eh, gaskiya ina tsintar kaina a irin wannan yanayi a lokuta da dama. Kuma sau tari da zarar irin hakan ta faru bacci nake zuwa in yi. Ko kuma in kama wani abu can daban har sai na samu nutsuwa tukunna sai in ci gaba.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2-768x1024.jpg?strip=all\" alt=\"Hira da Haiman Raees 2\" class=\"wp-image-4262\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2-768x1024.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2-225x300.jpg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-2.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuci Haiman Raees<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Yanzu lokaci ya canza, haka zalika al\u2019amura da dama na mutane su ma sun canza wanda na wasu yake zuwa a karkace, har ta kai ga yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira za ka yi wa irin wa\u0257annan marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Rubutun batsa koma-baya ne ga dukkan marubuci mai \u0199ima. Domin kuwa, shi marubuci tamkar malami ne da ke koyar da tarbiyya, to idan kuwa aka wayi gari shi ya koma aikata \u0253arna ai ya ci baya kenan. Kiran da zan yi ga masu rubutun batsa kuma shi ne, su guji rubuta abinda zai zamo musu bala\u2019i duniya da lahira, su mayar da hankali wajen rubuta abinda zai amfane su da sauran jama\u2019a duniya da lahira.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da kake yi irin wa\u0257anda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin wa\u0257anda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin wa\u0257anne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Babbar nasarar da na samu a harkar rubutu ita ce damar yin rubutun da mutane ke so, suke karantawa har ma su amfana. Nasara ta biyu kuma ita ce sanayya da na samu a wurin jama\u2019a masu tarin yawa wa\u0257anda ban san iyakar su ba. Sannan na samu lambobin yabo daga wurare da dama kuma na samu kyautuka na ku\u0257i da ban san adadinsu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>A naka ra\u2019ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi ma\u2019ana da tsari?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Rubutun bugu na hannu ya fi, saboda ana tsayawa a bashi ha\u0199\u0199o\u0199insa yadda ya kamata. To sai dai shi ma rubutun online yana da irin nashi muhimmancin, musamman duba da irin yadda zamani ya canza. Kuma duk da haka, a kan samu jajirtattun mutane da ke tsayawa kai da fata wajen ganin sun inganta shi. Wata\u0199ila hakan na daga cikin dalilan da ke sa yake ta \u0199ara samun kar\u0253uwa a wurin masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu yake jawowa sai \u0253ata tarbiyya. Shin wacce shawara yakamata a dinga ba irin wa\u0257an nan mutanen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Wannan magana ba gaskiya bace, rubutu babbar hanya ce ta isar da muhimman sa\u0199onni ga al\u2019umma ta hanya mai sau\u0199i da za su iya fahimta kuma su \u0257auka. Dalili na farko da zai tabbatar miki da haka kuwa shi ne, kaso casa\u2019in da biyar da \u0257igo biyar duk za ka samu mutanen kirki ne, in banda wa\u0257ansu \u2018yan tsirarun da suka fan\u0257are. Kin ga kenan ba daidai ba ne a yi jam\u2019in aiyukansu waje guda. Matasa da yawa a wannan zamani daga maza har mata suna amfana daga rubutun da ake wajen fahimtar al\u2019amuran zamantakewa, kai har ma da na addini a wasu lokutan.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin ya kake ganin tafiyar adabin Hausa? Ma\u2019ana, irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Gaskiya adabin Hausa na samun gagarumar nasara, musamman adabin zamani. Saboda yanzu zamani ne na ilimi da ci gaban zamani, hakan ya sa ilimi ya yawaita kuma kullum manazarta, marubuta da sauran masu sha\u2019awar adabin \u0199aruwa suke yi ba raguwa ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wacce Karin Magana ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>\u2018Jiki Magayi, duka da \u0257anyar kara.\u201d Saboda ka \u0199i jin gyara da baki, jikinka ya gaya maka. Sa\u0199o ne a bu\u0257e.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin ka na da wani maigida da yake nuna maka harkokin rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Tabbas ina da shi, ba ma mutum \u0257aya kawai ba. Da farko dai akwai Malam Mujaheed Abdullahi Kudan, wanda Malami ne a Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna na Jami\u2019ar Jihar Kaduna. Kuma ya ta\u0253a kasancewa Mai Taimaka wa Shugaban Karamar Hukumar Kudan a Kan Bincike da Sadarwa ta Zamani (Technical Assistant, Research, Documentation and Social Media). Shi ne mutum na farko da ya fara yin nazarin rubutuna. Sannan akwai Jamilu Adamu \u018aanwayye, da Lawan \u018aalha, da Abubakar Sadik da ma sauran wasu da dama.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"1024\" height=\"809\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3-1024x809.jpg?strip=all\" alt=\"Hira da Haiman Raees 3\" class=\"wp-image-4263\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3-1024x809.jpg?strip=all 1024w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3-300x237.jpg?strip=all 300w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3-768x607.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3.jpg?strip=all&amp;w=216 216w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees-3.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 1024px) 100vw, 1024px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuci Haiman Raees<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Shin ko akwai wani labarin da ka ke rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Akwai litattafaina guda hu\u0257u da nake sa ran duk za su fita a cikin wannan shekarar in Allah ya yarda. Su ne kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li><em>Dandi \u0198aho<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Tsibirin Al\u2019ajabi<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Kiahiyar Kwali<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Keken \u0181era<\/em><\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>To duk da dai ni ma sabon marubuci ne, ina ba su shawara da su zamo masu kyakkyawar manufa a cikin harkar rutbutunsu, kada su ke yin abubuwa ba tare da tsari ba. Yawancin abubuwa marasa tsari ba sa tasiri.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya: <\/strong>Daga \u0199arshe, me za ka iya cewa game da Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa: <\/strong>Hikaya ta zamo tamkar gida ne a wurina. Babu ranar da ba na shiga saboda irin amfanuwa da nake yi da ita ta fuskoki da dama. Ina fata wata rana Hikaya ta zarce kamfanin Amazon wajen samar da litattafai ga masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa:<\/strong> Asma\u2019u Abdallah (Fulani Bingel)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya Hikaya ke yi da marubuta na wannan zamani, a yau mun yi yi tattaki mun za\u0199ulo muku da fitacce kuma shahararren marubucin wake, da yake fassara wakokin Indiyawa gami da dan taba rubutun zube kansa, wato dai sha kundum a kowanne fanni, Jamilu Abdurrahman (Haiman Raees). Marubucin kuma&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/rubutun-batsa-koma-baya-ne-ga-dukkan-marubuci-mai-kima-haiman-raees\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Rubutun batsa koma-baya ne ga dukkan marubuci mai kima &#8211; Haiman Raees<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4260,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,78],"tags":[108,79,81],"class_list":["post-4259","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-interviews","tag-haiman-raees","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/07\/Hira-da-Haiman-Raees.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4259","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4259"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4259\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4260"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4259"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4259"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4259"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}