{"id":4285,"date":"2024-09-21T16:45:39","date_gmt":"2024-09-21T16:45:39","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4285"},"modified":"2024-09-21T16:45:44","modified_gmt":"2024-09-21T16:45:44","slug":"sharhin-littafin-na-sake-ta-na-mustapha-abbas-rijiyar-lemo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-na-sake-ta-na-mustapha-abbas-rijiyar-lemo\/","title":{"rendered":"Sharhin littafin &#8216;Na Sake Ta&#8217; na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo"},"content":{"rendered":"\n<p>Sunnan littafi: <strong><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/series\/na-sake-ta\/\">Na Sake Ta<\/a><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Marubuci: <strong><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/mustapha\/\">Mustapha Abbas Rijiyar Lemo<\/a><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Inda aka buga littafi: <strong>Hikaya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Shekarar wallafawa: <strong>2023<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p>Mai sharhi: <strong><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/baban_imam\/\">Abba Abubakar Yakubu<\/a><\/strong><\/p>\n\n\n\n<p><em>An gabatar da wannan sharhi da farko ne a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar Lahadi 30 ga watan Juni 2024, da karfe 9 zuwa 10 na dare.<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tarihin marubuci<\/h2>\n\n\n\n<p>Mustapha Abbas Rijiyar Lemo haifaffen unguwar Rijiyar Lemo ne da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano. Ya fara neman iliminsa da karatun Islamiyya, kafin daga bisani a saka shi a firamare a wata makaranta da ake kira \u2018Yammata Special Primary School. A shekara ta 2004 ya shiga \u0199aramar sakandire a J.S.S. Gogau, daga nan kuma sai ya kammala babbar sakandire a G.S.S. Kwachiri duk a cikin birnin Kano. Yanzu haka bayan rubutun labaran hikaya, Mustapha \u0257an kasuwa ne, kuma yana sana\u2019ar \u0199awata gine-gine. Ya fara rubutun adabi ne a shekarar 2008 lokacin yana aji uku na \u0199aramar sakandire da labarinsa mai taken <em>\u0198addarar Mutum,<\/em> wanda shi ne rubutun labari mafi tsayi da ya ta\u0253a yi kawo yanzu.&nbsp; Daga nan ya rubuta wasu gajerun \u0199agaggun labaran wato short stories, har guda 7, da suka ha\u0257a da wannan \u0199aramin littafin da ake rubuta wannan sharhi akansa, watau, <em>Na Sake Ta<\/em>. Sauran littattafan da marubucin ya rubuta sun ha\u0257a da <em>Halacci Ko Butulci?,<\/em> <em>Ranar Kuskure<\/em>, <em>Girman Al\u0199awari, Inuwar Sirri, Ku\u0257i Ko Rai da So Ko \u0198awance?<\/em><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Game da littafin<\/h2>\n\n\n\n<p>Littafin \u2018Na Sake Ta!\u2019 na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo Kano, \u0199aramin littafi ne da bai wuce shafi shida ba, da kalmomin da ka\u0257an suka haura dubu biyu da \u0257ari hu\u0257u. Gajeren labari ne wanda marubucin ya nuna cewa ya faru da gaske, sai dai \u2018yan sauye-sauye na hikimar marubuci da aka yi, domin \u0253atar da hankalin mai karatu daga sanin ha\u0199i\u0199anin mutanen da abin ya faru da su.<\/p>\n\n\n\n<p>Labarin wani mutum ne da aka sa wa suna Kamal, kodayake ba a kwatanta yanayinsa ko shekarunsa ba a cikin labarin, amma hasashena na manazarci ya nuna matashi ne da ba zai wuce shekaru 25 zuwa 30 ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamal talaka ne da ke neman ku\u0257i ido rufe, yana da mata Hajir, wacce ta kasance salihar mace ce, mai biyayyar aure, kuma sun yi aure ne na soyayya. Sai dai duk da soyayyar da ke tsakanin ma\u2019auratan nan biyu, sai da wani tsohon saurayinta Usman, wanda ya kasance mai tashen arzi\u0199i kuma abokin mijinta ya yi amfani da shegen son ku\u0257in mijinta Kamal ya raba su, ta hanyar yi masa tayin ku\u0257i har Naira Miliyan 5. Tayin da Kamal ya kasa \u0257auke kwa\u0257ayinsa a kai, sanin cewa ko dubu biyar ba a ta\u0253a sawa a asusun ajiyarsa na banki ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Son zuciya da rashin daraja soyayyar da matarsa Hajir ke nuna masa, sun rufewa Kamal idanu har ya amince da bu\u0199atar da Usman ya gabatar masa, duk kuwa da kasancewar hakan ya girgiza shi. Amma ha\u0257amar son abin duniya sun rufe masa idanu har ya sallamar da aurensa da farincikin matarsa, saboda rashin samun abokin shawara nagari. Kamal ya kasance matsiyaci ne mai masifar son ku\u0257i, wanda har i\u0199irari yake yi cewa zai iya yin komai saboda ku\u0257i.<\/p>\n\n\n\n<p>A \u0199arshe, bayan Kamal ya samu arzi\u0199in da yake burin yi, samun kwanciyar hankali ya gagare shi. Ya yi nadamar abin da ya aikata, musamman ganin duk aure-auren da ya yi har bakwai, amma ya kasa samun salihar mata kamar Hajir. Sakamakon irin halayen da matan da yake aura suke nuna masa, sa\u0253anin na salihar tsohuwar matarsa. Kamar yadda ya bayyana cikin takaici da nadama.<\/p>\n\n\n\n<p>\u2018Na gane babu abinda ya kai matar \u0199warai irin Hajir wuyar samu a wannan zamanin, ku\u0257i ba sa iya samar da ita, kai yanzu na gane ma ba komai ne ku\u0257i ke iya saye ba.\u2019<\/p>\n\n\n\n<p>Labarin \u2018Na Sake Ta\u2019 ya tuna min da wani fim \u0257in turanci da na kalla, mai suna \u2018Indecent Proposal\u2019 inda shi ma wani attajiri ya yi wa wani mutum, talaka kuma malamin makaranta, tayin ma\u0199udan ku\u0257a\u0257e don ya bashi dama ya kwanta da matarsa, wacce suke cikin tsananin soyayya da juna, amma talauci ya zama musu \u0199arfen \u0199afa. Don haka suka yanke shawarar su kar\u0253i tayin da aka yi musu, duk da ba haka ransu ya so ba. Matakin da daga baya ya zama sanadiyyar lalacewar aurensu, da samun kansu cikin wani mawuyacin hali.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Kamar yadda na yi bayani a baya, jigon wannan labari shi ne illar fifita ku\u0257i a kan farincikin rayuwa. A ta\u0199aice dai za a iya cewa, \u2018Kwa\u0257ayi Mabu\u0257in Wahala\u2019. Mun ga yadda son zuciya ya sa Kamal sadaukar da soyayyar da ke tsakaninsa da matarsa Hajir, saboda ku\u0257i, a \u0199arshe kuma ya kasa samun farinciki da jinda\u0257in da yake hasashen samu. Saboda yadda ya kasa zaman aure da duk mata bakwan da ya aura, wa\u0257anda ya aure su cikin dukiya da walwala. Alhalin ita Hajir da ta aure shi ne saboda soyayya, ta kawar da kai daga talaucin da yake ciki, ta guji duk manemanta da suke da arzi\u0199i, saboda shi. Amma a \u0199arshe, mutumin da ta guji aurensa ta bi soyayya, shi ne ya biya mijin da ta aura, shi kuma ya sake masa ita ya aura.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Darussan dake cikin labarin<\/h2>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\">\n<li>Illar biyewa son zuciya: Mun ga yadda kwa\u0257ayi da son abin duniya ya jefa Kamal&nbsp; cikin danasani, inda ta kai ga ya yi nadamar cin amanar da ya yi wa matarsa Hajir.<\/li>\n\n\n\n<li>Illar rashin samun abokin shawara nagari: Mun lura da yadda Mansur abokin Kamal ya ri\u0199a zuga shi da angiza shi ya \u0257auki mataki kan bu\u0199atar da Usman ya gabatar masa, ba tare da ya ba shi shawarar abin da ya dace ba. Amma a fakaice yana nuna masa ya kar\u0253i ku\u0257in ya fi masa zaman soyayya da Hajir cikin talauci.<\/li>\n\n\n\n<li>Illar talauci: Idan talauci ya ha\u0257u da son zuciya, ana samun babbar matsala. Saboda yadda idanun mutum ke rufewa ya ri\u0199a aikata abin da idan da ya yi ha\u0199uri kuma ya yi aiki da hankali ba zai aikata abin da daga baya zai yi danasani ba. Mun ga yadda talauci ya angiza Kamal ya cefanar da soyayyarsa, saboda hangen daular da zai samu daga ku\u0257a\u0257en da aka bashi, amma duk da haka sai da ya yi nadamar abin da ya aikata.<\/li>\n\n\n\n<li>Ku\u0257i na iya sayen soyayyar da ba ta ginu a kan tushe mai \u0199arfi ba. Abin takaici ne yadda Kamal ya yi watsi da soyayyar da Hajir ta nuna masa da sadaukarwarta gareshi, yadda ta fifita son da take yi masa, ta aure shi duk da talaucin da yake ciki, ta \u0199i auren Usman duk da arzi\u0199insa. Amma saboda tasirin ku\u0257i da nacin da Usman ya nuna ko ta halin \u0199a\u0199a sai ya auri Hajir. A \u0199arshe ku\u0257insa ya yi masa rana, don ya sayi soyayyarta daga wajen mijinta, wanda ta \u0199i aurensa saboda \u0199aunar da take masa.<\/li>\n<\/ul>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abin lura<\/h2>\n\n\n\n<p>Mustapha Abbas Rijiyar Lemo, marubucin wannan labari na \u2018Na Sake Ta\u2019, na daga cikin matasan marubuta na onlayin da suke \u0199o\u0199arin fitar da rubuce-rubuce masu ma\u2019ana da kuma tsafta. Ko a salon yadda ya rubuta labarin za ka fahimci ya san abin da yake yi, musamman wajen kiyaye \u0199a\u2019idojin rubutu, da zubin labari mai jan hankalin mai karatu. Sai dai duk da haka, an ce mutum tara yake bai cika goma ba. Duk da kasancewar ya rubuta wasu littattafai da gajerun labarai sun kai 10, a nazarin da na yi wa labarin \u2018Na Sake Ta\u2019, na lura da wasu \u2018yan kurakurai na tuntu\u0253en rubutu, kamar yadda ake gani a mafi akasarin littattafan onlayin, akwai matsalar rashin kiyaye \u0199a\u2019idojin rubutu a wasu wurare. Amma ba zan yi magana a kan kowanne kuskure na \u0199a\u2019idar rubutu da idona ya gani ba, saboda wani darasi ne mai zaman kansa. Sai dai ina fatan marubutan mu za su \u0199ara neman sani kan \u0199a\u2019idojin rubutu wajen ha\u0257awa da raba kalmomi. Kuma a ri\u0199a bai wa wasu da aka san suna da ilimi a \u0253angaren su ri\u0199a dubawa, suna ba da shawarwari.<\/p>\n\n\n\n<p>Na lura da yadda aka samu kuskuren rubutu a wasu wuraren, kamar misali, a sakin layi na farkon labarin an rubuta \u2018dai-dai\u2019, a maimakon \u2018daidai\u2019, wato an sa karan\u0257ori a inda bai dace ba. Haka kuma an rubuta \u2018\u0257an kasuwa\u2019, a maimakon \u2018\u0257ankasuwa\u2019.<\/p>\n\n\n\n<p>A wasu wuraren an yi amfani da sunayen wasu abubuwa da turanci a maimakon a ambaci sunayensu na Hausa ko kuma yadda ake kwatanta su. Misali, an rubuta \u2018Taxi\u2019 maimakon \u2018Tasi\u2019, an kuma&nbsp; rubuta \u2018Juice\u2019 a maimakon \u2018tataccen ruwan \u2018ya\u2019yan itatuwa\u2019. An sa kofin \u2018glass\u2019 maimakon \u2018gilashi\u2019.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan an rubuta \u2018Katsam!\u2019 a maimakon \u2018Kwatsam!\u2019<\/p>\n\n\n\n<p>Na lura, marubucin bai yi wa labarin tsarin babi-babi ko kashi-kashi ba, kamar dai yadda akasarin marubutan onlayin suke suke rubutu, inda suke zuba shi kawai ratata. Sai dai shi a nashi salon ya \u0257an sha bamban da wasu, domin ya yi amfani da tsarin sanya lokacin da wasu abubuwa ke faruwa a cikin labarin. Ko kuma ya sanya take kan wasu ga\u0253o\u0253i na labarin, kamar yadda a farko ya bu\u0257e da \u2018Asabar 7:30 pm\u2019 (a maimakon a sa 7:30 na maraice). A wani wajen kuma ya sanya kanu, kamar \u2018Ta Faru Ta \u0198are\u2019, bayan sakin layi da basu wuce shida ba kuma sai ya sake sa, \u2018Sauyi\u2019. Haka dai labarin ya ri\u0199a tafiya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Arashi<\/h2>\n\n\n\n<p>Na lura a maimakon a sa wa littafin sunan, \u2018Soyayyata Da Ku\u0257i\u2019 ko \u2018Na Yi Biyu Babu\u2019 da makamantansu, marubucin ya za\u0253i ya sa sunan \u2018Na Sake Ta!\u2019 don ya ja hankalin mai karatu, yadda zai damu ya san mene ne dalilin da ya sa aka yi sakin, wanda shi ma wani \u0253angare ne na labarin.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya yi amfani da adon harshe da ya ban sha\u2019awa, a inda yake bayyana cewa, \u2018Sai da na tattaro dukkan jarumtata kafin na iya mi\u0199awa Hajir mummunan sa\u0199on da na shafe tsawon dare ina tunanin ta yadda zan fara rubuta shi kamar ba\u0199on marubuci a fagen rubuta \u0199agaggen labari.\u2019<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Shawara<\/h2>\n\n\n\n<p>Yana da kyau marubuta su ri\u0199a mayar da hankali ga rubutun da suke yi, kuma su daina gaggawar sai sun fitar da labari a lokacin da suke son fitarwa, yadda za su samu zarafin yin gyare-gyare da sake canza wasu abubuwa, wanda a baya tunaninsu bai kai wurin ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan su sani, yin rubutu mai inganci yana da muhimmanci, saboda ba ka san hannun wanda zai shiga ba, ko idanun wanda zai karanta ba. Kiyaye \u0199a\u2019idoji da dabarun yin rubutu mai jan hankali, kamar kwalliya ce ga rubutu, domin abin da wani yake kallo kenan kafin ya bu\u0257e littafi ya karanta.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">A karshe<\/h2>\n\n\n\n<p>Ina mai jinjinawa marubucin wannan labari game da tunaninsa, da \u0199o\u0199arinsa na isar da sa\u0199on hannunka mai sanda ga masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p>Allah Ya \u0199ara basira da \u0257aukaka. Amin<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunnan littafi: Na Sake Ta Marubuci: Mustapha Abbas Rijiyar Lemo Inda aka buga littafi: Hikaya Shekarar wallafawa: 2023 Mai sharhi: Abba Abubakar Yakubu An gabatar da wannan sharhi da farko ne a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar Lahadi 30 ga watan Juni 2024, da karfe 9 zuwa 10 na dare. Tarihin marubuci&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-na-sake-ta-na-mustapha-abbas-rijiyar-lemo\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin littafin &#8216;Na Sake Ta&#8217; na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":4290,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[28],"tags":[29,41],"class_list":["post-4285","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-reviews","tag-book-review","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/Sharhin-littafin-Na-Sake-Ta-na-Mustapha-Abbas.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4285","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4285"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4285\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4290"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4285"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4285"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4285"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}