{"id":4317,"date":"2025-02-01T12:49:57","date_gmt":"2025-02-01T12:49:57","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4317"},"modified":"2025-02-01T13:13:21","modified_gmt":"2025-02-01T13:13:21","slug":"alkalamin-marubuta-na-iya-canja-abinda-ba-zai-yiwu-ba-ya-koma-wanda-zai-yiwu-fareeda-abdallah","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/alkalamin-marubuta-na-iya-canja-abinda-ba-zai-yiwu-ba-ya-koma-wanda-zai-yiwu-fareeda-abdallah\/","title":{"rendered":"Alkalamin marubuta na iya canja abinda ba zai yiwu ba ya koma wanda zai yiwu &#8211; Fareeda Abdallah"},"content":{"rendered":"\n<p>Hikaya ta tattauna da hazi\u0199ar marubuciya Fareeda Abdallah game da rayuwa, rubutu da kuma irin ra&#8217;ayinta game da rubutu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:\u00a0<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarki in ba za ki damu ba.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Sunana Fareeda Abdallah. Haifaffiyar garin Kaduna. Na yi Firamare da Sakandare duk a garin Kaduna, yanzu haka ina aure a garin Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na fara rubutu a shekarar 2012. Yawan karanta littattafai na marubuta daban-daban shi ya ja hankalina na fara rubutu. Sannu a hankali ina matsayin makaranciya har na kai matakin da nake ga ni ni ma fa kamar ina da baiwar da zan iya isar da sa\u0199o ga al&#8217;umma ta hanyar al\u0199alami.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na rubuta littattafai guda goma sha biyu.<\/p>\n\n\n\n<ol class=\"wp-block-list\">\n<li><em>A Dalilin \u018aa Namiji<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Duniya Sabuwa<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Inuwar Mutuwata<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Bara A Kufai<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Bihakki<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Sanadiyya<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Tsakanina Da Mutuwa<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Tubalin Toka<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/rabon-a-yi-1\/\"><em>Rabon A Yi<\/em><\/a><\/li>\n\n\n\n<li><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/lokaci-1\/\"><em>Lokaci<\/em><\/a><\/li>\n\n\n\n<li><em>Kasaitacciyar Mace<\/em><\/li>\n\n\n\n<li><em>Bayan Tiya<\/em><\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Duk littattafan da na rubuta ina matu\u0199ar son su. Amma a zahirin gaskiya na fi son littafin <em>Rabon A Yi<\/em> saboda a cikin labarin ne na ta\u0253o wani \u0253angare daga cikin halayena da wani \u0253angare na tarihin rayuwata.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Akwai marubuta da yawa daga cikin manyan marubuta da \u0199anana wa\u0257anda nake kallon yanayin rubutunsu a matsayin madubin dubawa kafin tsara nawa rubutun.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1-768x1024.jpg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4334\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1-768x1024.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1-225x300.jpg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-1.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuciya Fareeda Abdallah<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ki ka ta\u0253a karantawa da ya fi burge ki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya littattafan suna da yawa, kawai dai duk wani littafi da marubuciya ko marubucin ya zurfafa bincike gurin rubutawa, kuma aka hasko matsalolin da muke fama da su aka yi bayanin hanyoyin warware matsalar wannan littafi abin burgewa ne a gare ni.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin kin ta\u0253a shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin ta\u0253a yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Eh! Na ta\u0253a shiga gasar Hikayata ta BBC. Sau biyu labarina ya ta\u0253a fitowa a fitattun labaran da suka tsallake matakin farko. Na kuma ta\u0253a shiga gasar Gusau Institude labarina ya tsallake matakin farko sau \u0257aya. Na samu nasarori da yawa sanadiyyar rubutu. Ka\u0257an daga ciki su ne, bayan alkhairan da nake samu daga wurin mabanbantan mutane, na ha\u0257u da manyan mutanen da ban ta\u0253a tsammanin zan ha\u0257u da su ba a rayuwata, amma sanadiyyar rubutu yanzu ala\u0199a ta girmamawa da mutunci ce tsakanina da su. Alhamdulillah!<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina tsara matakin farko na labarin, tsakiya, \u0199arshe. Amma kuma idan tafiya tayi tafiya wasu abubuwan suna canjawa daga cikin wanda na tsara.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina rubuta muhimman abubuwa ne daga cikin sabon tunanin da ya zo min. Sai in cigaba da asalin wanda nake yi, bayan na gama sai in \u0257auko wancan sabon tunanin da yazo min in fara bincike a kanshi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Ki kan \u0257auki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan \u0257auke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Eh to tsawon lokacin da nake \u0257auka wajen bincike ya danganta da irin jigon da nake so inyi rubutu a kai. Wani jigon bincikenshi mai sau\u0199i ne, wani kuma mai wahala ne. Da wannan dalilin ya sa bazan iya yanke takamaimai lokacin da nake \u0257auka wajen bincike ba. Ina \u0257aukan watanni biyu, uku, hu\u0257u kafin in kammala rubutun littafi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Rayuwarmu nake kalla a matsayin madubi, sannu a hankali sai in za\u0199ulo \u0257aya daga cikin manya ko \u0199ananun matsalolin da suke addabarmu in yi rubutu akai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina kallon mutanen da ke kewaye da ni ne da irin kyawawa da munanan halayensu, sai in fitar da halayen taurarin labarina sannan in za\u0253a musu sunayen da ya dace da su.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko kin ta\u0253a amfani da wani \u0253angare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Eh! Na ta\u0253a yi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka ta\u0253a rubutawa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Littafina na <em>A Dalilin \u018aa Namiji<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne irin \u0199alubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake \u0199alubalen?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Gaskiya Alhamdulillah! Har zuwa yanzu kasancewata \u0199arama a cikin marubuta babu wani gagarumin \u0199alubale da na ta\u0253a fuskanta wanda har ya zame mini \u0199a\u0199a-nikayi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Na fi son Fareeda ta cikin labarin <em>Rabon A Yi<\/em>. Ina son ta sabida wasu daga cikin halayena na kalla na samar da halayenta.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Eh! Na ta\u0253a shiga. Rubutun nake ajiyewa gaba \u0257aya in koma makaranciya. Sannu a hankali idan na karanta littattafai da dama masu ma&#8217;ana da marasa ma&#8217;ana sai \u0199wa\u0199walwata ta bu\u0257e.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina son rubutu saboda sassau\u0199ar hanya ce ta isar da sa\u0199o ga al&#8217;ummarmu cikin \u0199an\u0199anin lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Tunanin abinda zan yi rubutu akai.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ina son karin maganar Babu maraya sai rago. Saboda a aikace nake amfana da karin maganar.<\/p>\n\n\n<div class=\"wp-block-image\">\n<figure class=\"aligncenter size-large\"><img decoding=\"async\" width=\"768\" height=\"1024\" src=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2-768x1024.jpg?strip=all\" alt=\"\" class=\"wp-image-4335\" srcset=\"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2-768x1024.jpg?strip=all 768w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2-225x300.jpg?strip=all 225w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2.jpg?strip=all 1080w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2.jpg?strip=all&amp;w=432 432w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2.jpg?strip=all&amp;w=648 648w, https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Fareeda-Abdallah-2.jpg?strip=all&amp;w=864 864w\" sizes=\"(max-width: 768px) 100vw, 768px\" \/><figcaption class=\"wp-element-caption\"><em>Marubuciya Fareeda Abdallah<\/em><\/figcaption><\/figure>\n<\/div>\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> A naki ra&#8217;ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Ko wanne yana da amfani da kuma muhimmancinsa. Amma a halin yanzu gaskiya rubutu online ya fi rubutun takarda. Saboda kaso takwas cikin goma na makaranta sun fi samun sararin karatu online.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al&#8217;umma?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Marubuta suna da tasiri mai matu\u0199ar yawa a cikin al&#8217;umma. Domin kaifin al\u0199alami ya fi na takobi. al\u0199alamin marubuta na iya canja abinda ba zai yiwu ba ya koma wanda zai yiwu. Shi yasa a kullum ake \u0199ara tunasar da marubuta su ji tsoron Allah su tsarkake al\u0199alumansu, ba don komai ba sai don saboda yadda sa\u0199onsu mai kyau ko mare kyau ke saurin isa ga al&#8217;umma.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Eh! Akwai labarai guda biyu. \u0198asaitacciyar Mace da kuma Bayan Tiya akwai wata caca.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wane ne tauraronki a cikin marubuta?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Duk wani marubuci da yake wasa \u0199wa\u0199walwarsa gurin yin rubutu mai cike da ma&#8217;ana taurarona ne.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Littafi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Su ji tsoron Allah su tsarkake al\u0199alaminsu. Kar rububin neman fans ya sa su dinga rubutun batsa ko munanan rubutun da zai taka rawa gurin \u0199ara ta\u0253ar\u0253arewar al&#8217;umma. Su dinga yin bincike kafin rubutu. Sannan su dinga \u0199o\u0199arin ba da rubutunsu ga manyan marubuta suna duba musu kafin sakin ko wane feji na labari ga masu karatu. Domin wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Mene ne burinki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Burina in zama \u0257aya daga cikin marubutan da ake kwatance da su wurin yin rubutu mai cike da ma&#8217;ana da fa\u0257akarwa.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tambaya:<\/strong> Me za ki iya cewa game da Hikaya?<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Amsa:<\/strong> Hikaya manhaja ce mai muhimmanci da ya zo da tsare-tsare masu kyau don tallafawa marubuta. A iya sanina, nan kusa dai ban ga wata manhaja da ke tafiya kafa\u0257a da kafa\u0257a da marubuta ba kamar Hikaya. Ako wane shirye-shirye da tsare-tsare na bakandamiya za ka samu marubuta a ciki. Kuma wani abin burgewa shi ne sun san darajar rubutu da marubuta. Babu abinda zan ce da Bakandamiya sai fatan alkhairi, da addu&#8217;ar Ubangiji Allah ya \u0199ara musu \u0257aukaka.<\/p>\n\n\n\n<p>An yi wannan hira da Fareeda Abdallah ne a ranar 22 ga watan Maris, 2024.<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Tsara tambayoyi da gabatarwa:<\/strong> Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hikaya ta tattauna da hazi\u0199ar marubuciya Fareeda Abdallah game da rayuwa, rubutu da kuma irin ra&#8217;ayinta game da rubutu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:\u00a0 Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma ta\u0199aitaccen tarihin rayuwarki in ba za ki damu ba. Amsa: Sunana Fareeda Abdallah. Haifaffiyar garin Kaduna. Na yi Firamare&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/alkalamin-marubuta-na-iya-canja-abinda-ba-zai-yiwu-ba-ya-koma-wanda-zai-yiwu-fareeda-abdallah\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Alkalamin marubuta na iya canja abinda ba zai yiwu ba ya koma wanda zai yiwu &#8211; Fareeda Abdallah<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":14,"featured_media":4339,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,78],"tags":[118,79,81],"class_list":["post-4317","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-interviews","tag-fareeda-abdallah","tag-hira-da-marubuta","tag-interviews"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/Hira-da-Fareeda-Abdallah.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4317","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/14"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4317"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4317\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4339"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4317"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4317"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4317"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}