{"id":435,"date":"2021-10-24T16:13:25","date_gmt":"2021-10-24T16:13:25","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?p=435"},"modified":"2022-07-13T01:36:01","modified_gmt":"2022-07-13T01:36:01","slug":"tsarin-murhun-girka-jigo-a-labari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-murhun-girka-jigo-a-labari\/","title":{"rendered":"Tsarin murhun girka jigo a labari"},"content":{"rendered":"\n<p>A ma\u0199alar da ta gabata, mun yi bayani sosai tare da misalai na&nbsp;<a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-yadda-ake-girka-jigo-ya-koma-labari\/\">yadda ake girka jigo ya koma labari<\/a>. A yau kuma insha Allahu ma\u0199alarmu za ta yi duba ne a kan irin tsarin murhun da ya kamata a girka jigon a kai. Shin ta wacce mahangar za mu kalli irin wannan hikimar mu samar da labari mai armashi?<\/p>\n\n\n\n<p>Irin yadda ake tanadar duwatsu uku domin ha\u0257a murhu, haka ake samar da \u0253angarori uku wajen gina labari. \u0181angarori ukun su ne:<\/p>\n\n\n\n<ul class=\"wp-block-list\"><li>Tsini (farkon labari)<\/li><li>Doro (tsakiyar labari)<\/li><li>Tushe (\u0199arshen labari)<\/li><\/ul>\n\n\n\n<p>Kamar yadda murhun \u0257ora tukunyar girki ba ya yiwuwa sai da duwatsu uku, haka ma babu wani labari da zai girku ya yi \u0257an\u0257ano ga masu karatu idan ba a \u0257ora shi a kan salon wa\u0257annan murahun ba. Kowanne labari dole ne marubucinsa ya tanadar masa farko, ya tanadar matsa tsakiya, sannan ya tanadar masa \u0199arshe. Sa\u0253anin haka kuwa wata matsalar za ta iya biyo baya, irin matsalar da wanda ya \u0257ora tukunya a kan duwatsu biyu zai samu don yana ta\u0199amar ya ri\u0199e tukunyar da hannunsa. Don kuwa da zarar tukunyar ta \u0257auki zafi ta yadda ba za ta ru\u0199u ba wata\u0199ila sai dai ya saketa ya yi asarar girkin tunda duwatsu biyun ba za su iya ri\u0199e tukunyar ta zauna ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Marubuta da yawa, musamman sababbin marubuta suna yi mini \u0199orafin cewa sai sun fara rubuta labari sun yi nisa, wata\u0199ila ma har sun je tsakiyarsa kawai kuma sai su kasa yin gaba ko su yi baya. To a inda matsalar take shi ne rashin \u0257ora labarin a wannan mizanin tun asalin lokacin da za a fara girka shi. Dayawa kawai fara yin rubutun suke yi ba tare da tsara masa doro da kuma tushe ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamar sikeleto ko \u0199warangwal na mutum, haka ake samar da sikeloto na labari mai \u0257auke da farkon labarin, tsakiyar labarin, da kuma \u0199arshen labarin. Wanda da zarar ka tashi za ka gina ainahin labarin shi sikeleto \u0257in kawai za ka kalla ka \u0257ora masa tsoka da fata ya dawo halitta.<\/p>\n\n\n\n<p>Yadda ake samar da sikeleto \u0257in shi ne, a cikin &#8216;yan ta\u0199aitattun kalmomi ka samar da yadda kake so farko da tsakiya da \u0199arshen labarin ya kasance, ta yadda idan ka zo za ka rubuta ainahin labarin sai dai ka yi ta fa\u0257a\u0257a ga\u0253o\u0253in kana \u0199ara musu armashi.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"misalin-sikeleton-labari-mu-nazarci-wannan\"><strong>Misalin sikeleton labari:&nbsp;<\/strong>Mu nazarci wannan<\/h2>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"\u0253addabami\"><strong><em>\u0181addabami<\/em><\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p><em>Labari ne a kan wani gari, duk girman garin otal \u0257in saukar ba\u0199i guda \u0257aya ne, wannan dalilin ya sa mai otal \u0257in yana yin cikini sosai. Kwatsam kuma sai ga wani shi ma ya zo ya gina sabon otal a garin. Sabontakar sabon otal \u0257in da aka gina, da kuma irin abubuwa na zamani da aka zuba a cikinsa sai ya kashe wa mai wancan tsohon otal \u0257in kasuwa mutane suka dena zuwa nasa, wanda wannan abin ne kuma ya fusata shi&nbsp; mai tsohon otal \u0257in ya ji lallai ya kamata ya \u0257auki matakin dur\u0199usar da sabon otal \u0257in.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Bayan dogon nazari, sai ya gane cewa idan ya shirya wani kisan kai a \u0253oye cikin sabon otal \u0257in, zai kashe wa otal \u0257in farinjinin mutane su ce babu tsaro a cikinsa tunda har za a iya bin wani a kashe shi a ciki. Wannan dalilin ne ya sa shi mai tsohon otal \u0257in ya biya wasu &#8216;yan ta&#8217;adda suka tsara masa wani kisan kai mai sar\u0199a\u0199iya, ta yadda har sai da aka rufe sabon otal \u0257in da sunan bincike, kuma aka kama mai otal \u0257in.<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>A \u0199arshe da \u0199yar wutar rikicin ta mutu bayan asiri ya tonu cewa kisan shirya shi mai tsohon otal \u0257in ya yi da gangan don ya \u0253ata wa mai sabon otal \u0257in suna. Bayan &#8216;yan jaridu sun baza labaran yadda abin ya faru sai sabon otal \u0257in ya sake dawowa da martabarsa irin ta farko<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p>Abin lura shi ne, ga\u0253a ta farko na rubutun ta \u0199unshi ainayin yadda za a tsara farkon labarin. Ga\u0253a ta biyu kuma sai ta nuna yadda matsalar, ko kuma ainahin rikicin da aka yi bayaninsa a ga\u0253a ta farko zai je \u0199ololuwa. Yayin da ga\u0253a ta \u0199arshe kuma nake bayyana irin yadda nake so \u0199arshen labarin&nbsp; ya kasance.<\/p>\n\n\n\n<p>Indai har marubuci zai ri\u0199a samar da sikeloto na labari irin wannan kafin ya fara, to zai yi wuya ace zai samu matsalar kakarewa a tsakiyar labari idan ya fara. Da zarar ya rubuta sikeleto irin wannan duk lokacin da ya zo zai fa\u0257a\u0257a labarin ba zai samu matsalar rashin makama ba.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan tsara sikeleton labari, abu na gaba da ya rage wa marubuci ya na\u0199alta shi ne ya san yadda zai fa\u0257a\u0257a ga\u0253o\u0253in labarin nasa, wanda kuma yanzu abin da za mu yi bayani kenan.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"ya-ake-so-farkon-labari-ya-kasance\"><strong>Ya ake so farkon labari ya kasance?<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Wannan ga\u0253ar tattaunawa ce mai matu\u0199ar muhimmanci, domin kuwa ga\u0253a ce wacce da ita ne makarancin labari yake yi wa labarin da ya \u0257auka hisabi, daga nan ne zai fahimci shin zai karanta ko ba zai karanta ba. Bincike ya nuna cikin kaso \u0257ari na manazarta, kaso saba&#8217;in zuwa tamanin suna iya jefar da muhimmin labari kuma mai da\u0257i idan aka samu akasi shi marubucin labarin bai iya tsara farkon labari irin yadda ya kamata a tsara shi ba. Sau tari wasu manazartan suna karanta irin wannan labarin ne bayan an samu ya\u0257uwar cewa labarin ya yi da\u0257i, ko ya yi ma&#8217;ana daga bakin \u0199alilan \u0257in mutanen da suka yi juriyar bibiyar labarin da karanta shi duk da rashin tsaruwar farkonsa.<\/p>\n\n\n\n<p>Shin ba ka kula ba cewa ko wajen masu sayar da littafi ka je za ka ga mutane suna \u0257aukan labari suna duba farkonsa ko za su karanto abin da zai iya jan hankalinsu a cikin littafin kafin su saya? Akwai maganar da na \u0257akko ta wasu shahararrun marubuta a waccan mu\u0199alar da ta gabata wadda maganar tana \u0199arfafar wannan zancen, inda nake ce wa:<\/p>\n\n\n\n<p><strong>Jodie Archer<\/strong>&nbsp;da&nbsp;<strong>Matthew L. Jockers<\/strong>&nbsp;sun ce jumlolin da fitattu kuma shahararrun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf kan yi amafani da su wurin bu\u0257e labaransu wato a farkon labarinsu, sukan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma \u0199asa da haka. Kenan dai suna amfani da hikima su bayyana jigon su a ciki ta\u0199aitattun kalmomi don kama zuciyar mai karatu, ya ji yana so ya karanta labarin. Shi ya sa za ka ga ko a bayan bangon littafi akan yi wani \u0257an ta\u0199aitaccen bayani game da labari, ta yadda koda farkon labari bai yi maka yadda kake so ba za a iya jan hankalinka da wannan \u0257an bayanin don ka sayi littafin.<\/p>\n\n\n\n<p>A ta\u0199aice dai ana so marubucin ya yi amfani da salon da zai yi matu\u0199ar jan hankali ya burge mai karatu a farkon labari ta yadda zai ji lallai ya kwa\u0257aitu da karanta labarin don ya ji me ya \u0199unsa.&nbsp;<strong>Jeffrey Archer<\/strong>&nbsp;ya ce a irin wannan ga\u0253ar marubuci ya tabbatar mai karatu ya juya shafi na gaba cike da shauki da son gano mai zai faru a cikin shafin da ya bu\u0257a \u0257in.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\" id=\"dabarun-gina-farkon-labari\"><strong>Dabarun gina farkon labari<\/strong><\/h2>\n\n\n\n<p>Ana gina farkon labari ta yadda zai ja hankalin duk wanda ya \u0257auka ta sigogi da dama wa\u0257anda za mu \u0257auki wasu daga muhimman ciki \u0257aya bayan \u0257aya mu tattauna tare da misali.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\" id=\"i-dun\u0199ule-abin-da-labari-ya-\u0199unsa-a-ta\u0199aitattun-kalmomi\"><strong>i &#8211; Dun\u0199ule abin da labari ya \u0199unsa a ta\u0199aitattun kalmomi<\/strong><\/h3>\n\n\n\n<p>Wannan dabarar ita za mu fara dubawa, dabara ce wacce ake yin ta ta fuska biyu ita ma,&nbsp; ya danganta da irin salo da yanayin da marubucin yake so ya \u0257auka. Ko dai ya bayyana abin da labarin ya kunsa&nbsp;<em>ta sigar bayani<\/em>, ko kuma ya bayyana&nbsp;<em>cikin hikima a labari<\/em>.<\/p>\n\n\n\n<p>Bari mu fara da bayar da misalin yadda marubuci zai bayyana abin da labari ya \u0199unsa ta sigar bayani a cikin ta\u0199aitattun kalmomi. Mu \u0257auki labarina DA MA SUN FA\u018aA MINI, ga masu littafin a hannu su duba shafin farko na littafin, ga bayanin da shafin ya \u0199unsa kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p><em>MABU\u018aI<\/em><\/p>\n\n\n\n<p><em>Kalmar sila&nbsp; wata kalma ce da Bahaushe yake amfani da ita don nuna sanadi ko dalilin samuwar wani abu. A wasu ararrun kalmomin na shi, yana iya cewa ma\u0199asudi ko musabbabi, wanda duk suna nufin abu \u0257aya ne da sila. Sila takan zamo ta fuska-fuska, kamar yadda silar samuwar labarin &#8216;Dama sun fa\u0257a min&#8217; ta zamana dalilin zaman majalisa irin na al&#8217;ada ta matasa, wanda kuma taurarin cikinsa ba wasu&nbsp; ba ne face \u0199ungiyar asirin da suke yi wa amaryar wata takwas Zainab barazanar hallaka duk abin da zata haifa, Zainab wacce take zargin mijinta Aliyu da zama \u0257an \u0199ungiyar asirin da ya bayar da abin da zata haifa ga \u0199ungiyar tasu, Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba \u0257an \u0199ungiyar asiri ba ne, sai iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa &#8216;yarsu ba zata zauna da \u0257an shan jini ba, da kuma Al\u0199ali da mu\u0199arrabansa da mu kanmu &#8216;yan kallo wanda da mu aka kawo \u0199arshen tirka-tirkar&#8230;&#8221;<\/em><\/p>\n\n\n\n<p>Idan muka kalli wannan misali, shi ne abin da marubuci&nbsp;<strong>Jodie Archer&nbsp;<\/strong>yake nufi da &#8216; a dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma \u0199asa da haka.&#8217; Da iya \u0257an wannan bayani ka haska wa makaranci duk abin da labarin ya \u0199unsa, duk da dai kuma ba zai iya gane komai yadda ya kamata ba har sai ya karanta labarin. Amma dai ko babu komai za ka lasa masa zumar son jin yadda aka haihu a ragaya.<\/p>\n\n\n\n<p>Akwai misalai iri-iri daga labarai kala-kala, sai dai za mu dakata a nan. Ku kanta&nbsp;<a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/yadda-ake-sanya-tsakure-taba-ka-lashe-da-somin-tabi-a-labari\/\">ma\u0199ala ta gaba<\/a>&nbsp;inda na \u0257ora da misalin yadda ake bayyana labari ta hikima ba tare da mai karatu ya fahimci bayyana masa aka yi ba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ma\u0199alar da ta gabata, mun yi bayani sosai tare da misalai na&nbsp;yadda ake girka jigo ya koma labari. A yau kuma insha Allahu ma\u0199alarmu za ta yi duba ne a kan irin tsarin murhun da ya kamata a girka jigon a kai. Shin ta wacce mahangar za mu kalli irin wannan hikimar mu samar&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/tsarin-murhun-girka-jigo-a-labari\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Tsarin murhun girka jigo a labari<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3338,"comment_status":"open","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[58,2],"tags":[3,11,5,8,9],"class_list":["post-435","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","category-writing-tips","tag-dabarun-rubutu","tag-girka-jigo","tag-jigon-labari","tag-rubutun-labari","tag-samar-da-jigo"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2021\/10\/Murhun-girka-jigo.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/435","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=435"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/435\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3338"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=435"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=435"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=435"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}