{"id":4432,"date":"2025-12-25T12:32:01","date_gmt":"2025-12-25T12:32:01","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4432"},"modified":"2025-12-25T12:32:38","modified_gmt":"2025-12-25T12:32:38","slug":"babban-kalubalen-da-na-samu-a-rubutu-shi-ne-rashin-iya-daidaitacciyar-hausa-nana-aicha-hamissou","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/babban-kalubalen-da-na-samu-a-rubutu-shi-ne-rashin-iya-daidaitacciyar-hausa-nana-aicha-hamissou\/","title":{"rendered":"Babban Kalubalen da na samu a rubutu shi ne rashin iya daidaitacciyar Hausa – Nana Aicha Hamissou"},"content":{"rendered":"\n
Filin tattaunawa da fitattun marubuta na Hikaya a yau ya samu yin tattaki har \u0199asar Niger inda muka za\u0199ulo muku matashiyar marubuciyar nan kuma hazika, Nana Aicha Hamissou. Ga yadda hirar ta kasance:<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Da farko muna son jin ta\u0199aitaccen tarihin ba\u0199uwar tamu.<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Sunana Nana Aicha Hamissou Abdoulaye, an haife ni a ranar Laraba ashirin da bakwai ( 27) ga watan Yuli na shekarar dubu \u0257aya da \u0257ari tara da casi’in da hu\u0257u (27\/07\/1994) a unguwar sabon gari ta jihar Mara\u0257i, Jamhuriyar Nijar. Na fara karatu a \u0253angaren addini a Madarassatul Hizibur Rahim da ke unguwar Zaria ta 2 a nan garin Mara\u0257i. A lokacin da na cika shekara shida a duniya aka saka ni a makaratar boko a shekarar 2000 a wata primary mai suna Ecole sabon gari a nan garin Mara\u0257i, na gama a shekarar 2006 inda kai tsaye na \u0257ora karatuna a wata \u0199aramar Sakandire mai sunan CEG Rauda, bayan na gama na wuce babbar sakandare mai suna Lyc\u00e9e \u018aan Baskore. A lokacin ne kuma Allah Ya albarce ni da saukar Alkur’ani a shekarar 2013.<\/p>\n\n\n\n
Bayan na gama Sakandire na samu gurbin karatu a jami’ar Gwamanti mai suna Universit\u00e9 DanDicko DanKoulodo de Maradi (UDDM) a shekarar 2015. Sakamakon yajin aiki ban gama ba sai a watan Yulin 2020 inda na samu kwalin digiri a fannin Etude d’Impact Environnemental (Nazarin Tasirin Muhalli). A \u0199arshen watan Disambar shekarar na \u0257ora master a jami’ar Abubakar Ibrahim International University a \u0253angaren Gestion de L’environnement (Yadda za a kula da Muhalli). Wani uzuri mai girma ya \u0257an tsayar da ni, da tun bara na gama Master \u0257ita. A ta\u0199aice dai da izinin Ubangiji na kusa gama digiri ta biyu in Sha Allahu.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Me ya ja hankalinki har kika fara rubutu?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ban taba zaton zan zama marubuciya ba! Abu guda na sani, ina karance-karance duk da ban yi karatun littaffai ba na takarda amma na yi karatun littafai online wanda in na ce zan \u0199irga su to zan yi \u0199arya don ban san adadinsu ba. Kwatsam wata rana ina zaune sai na fara wani rubutu mai kama da \u0257an\u0257ano sai na tura a wasu group biyu da nake ciki na Rahma Kabir da Asma Baffa. Sai mutane suka yi ta ce mini in ci gaba ai littafin zai yi da\u0257i har Rahma Kabir ita ma ta ba ni \u0199warin gwiwar farawa a akwatin sirri. Na ce mata ba zan iya ba saboda ban iya Hausar Nijeriya ba. Sai ta ce mini zan iya, in yi typing in turo mata za ta gyara min. Babu \u0199yashi babu hassada na turo mata shafi na farko ta gyara mini ha\u0257e da fitar mini da gyararrankina, sannan kuma na sake wani shafin ta sake gyara mini. Daga nan na fara typing na yi wa kaina editing ina turawa. Wannan shi ne mafarin zamana marubuciya.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ki ka ta\u0253a karantawa da ya fi burge ki?<\/p>\n\n\n\n
Amsa: <\/strong>Suna da yawa ga wasu daga ciki:
2. Tamanin da tara na Abdullahi Hassan Yarima
Tambaya:<\/strong> Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ya danganta daga yanayin rubutun, idan dogon labari ne nakan yi \u0199warangwal kafin na \u0257ora al\u0199alamina. Idan kuma gajere ne ina iya tsara shi a \u0199wanyata na \u0257ora al\u0199alami ko kuma shi \u0257in ma nakan yi masa \u0199warangwal wani lokacin. Ya dai danganta daga yanayin labarin.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Ya kike yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ka san ba a yi wa rubutu hawan \u0199awara, idan har wani tunani ya zo mini daban nakan nemi takarda na rubuta abin da labarin ya \u0199unsa. Alabarshi sai na ci gaba da wanda nake yi gudun rikita kaina da kuma masu bibiya ta.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Ki kan \u0257auki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan \u0257auke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ya danganta daga yanayin labarin da kuma inda za a yi bincike. Kawai dai nakan sa a raina abin da zan yi mai muhimmanci ne don haka ina mayar da hankali ga abin da na sa gaba. A da can ina wata uku ko biyu in gama labari guda, amma yanzu gaskiya ina \u0257aukar lokaci har shekara guda sukutum.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ko a hanya na ga wani abu da ya ba ni mamaki, birgewa ko haushi nakan yi sa\u0199e-sa\u0199e a raina yadda zan iya rubutu a kansa da tunanin zama darasi ga mutane. Ni abu ka\u0257an zan gani ya busa mini ruhin rubutu, samun jigo bai ba ni wahala. Matsala guda ce rashin mayar da hankali da nake da shi wurin rubutu.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Idan na yi \u0199warangwal, nakan samu feji guda na rubuta sunayen taurarin labari tare da matsayin kowane da kuma irin rawar da zai taka.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Shin ko kin ta\u0253a amfani da wani \u0253angare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ko sau \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka ta\u0253a rubutawa?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Kundin Bincikena.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne irin \u0199alubale kika fuskanta a bangaren rubutu?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> \u0198alubalen da na fuskanta a lokacin da na fara rubutu ba su da yawa gaskiya. Zan iya cewa ba su wuce na rashin iya daidaitattaciyar Hausa ba.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya: <\/strong>Litattafai nawa kika rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Na rubuta littafi bakwai ni ka\u0257ai:
1. ‘Yar Aikin Gidana
2. Da Wa Na Dace?
3. Rayuwarmu Ce Haka
4. Soyayyar Gaskiya
5. Laila Hafsat
7. Kundin Bincikena.<\/p>\n\n\n\n
Sannan na yi rubutun ha\u0257aka sau uku: na farko shi ne Sai Na \u018aauki Fansa tare da \u0199awata Aisha Abubakar Mrs Bb da kuma ‘yar’uwata Maryam Nasir (Manab ‘Yar Baba), sai rubutu na biyu tare da marubutan kungiyarmu ta Kainuwa mai suna Hannu \u018aaya Ba Ya \u018aaukar Jinka, sai na uku shi bai fita ba wanda muke sa ran bugawa in sha Allah mai suna Da Jininsa A Jikina tare da fasihan marubuta guda goma.<\/p>\n\n\n\n
A Sanadin Mijinta<\/li>\n\n\n\n
Wani Jinkiri…<\/li>\n\n\n\n
Kuskuren Da Na Tafka<\/li>\n\n\n\n
Na Yi Nadama<\/li>\n\n\n\n
Rai da \u0198addara<\/li>\n\n\n\n
Kala Biyar<\/li>\n\n\n\n
Butulci<\/li>\n\n\n\n
Wanda Bai Ji Bari Bari Ba<\/li>\n\n\n\n
Ramin Mugunta<\/li>\n\n\n\n
Sanadin Bikin Salla<\/li>\n\n\n\n
Wata Rayuwa<\/li>\n\n\n\n
An \u0198i Cin Biri…<\/li>\n\n\n\n
Akwai Bambanci<\/li>\n\n\n\n
Da sauran su.<\/li>\n<\/ol>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne littafi ne Bakandamiyarki, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Shin kema kin amshi sauyin da zamani ya zo da shi na rubutu a waya?<\/p>\n\n\n\n
Amsa: Eh na amshi wannan sauyin saboda ana saurin isar da sa\u0199o cikin wayar. Ba tare da ko sisi ba ka karanta littafi ka \u0199aru da darasin ciki. Don akwai wa\u0257anda suke karanta littafi ba tare da sun siya data ba, a facebook wato freemode.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> A duk cikin Taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Fatima ta cikin labarin Butulci wanda na yi nasara a gasar BBC da shi. Dalilin za\u0253enta a matsayin wacce na fi so saboda yadda ta ku\u0253utar da kanta daga masu garkuwa da mutane ta hanyar amfani da hikimarta.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya: <\/strong>Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin ta\u0253a shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ban ta\u0253a shiga ba. Abin da na sani shi ne ina tsintar kaina a gajiye idan na jima ina rubutu ko na so takura wa kaina. Abin da nake yi shi ne ajiye al\u0199alami na fita hanyar rubutun sai an kwana ko a wuni ban bibiyi labarin ba.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ya zamana idan ina karanta labari in ji tamkar gaske ne abin da yake faruwa da taurarin labarin da nake karantawa ko nake kallo ko saurare.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Abubuwa da yawa:
Karatu
Shiru tare da nazari
Hira da masoyana ds.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Mai ha\u0199uri yakan dafa dutse ya sha romo. Saboda duk wanda ya yi ha\u0199uri a rayuwa zai yi nasara da \u0199arfin ikon Allah..<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Da rubutun online da na littafi wanne ya fi ma’ana da saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Duka suna da ma’ana gaskiya kuma suna saurin isar da sa\u0199o yadda ya kamata. Amma a ganina littafan takarda sun fi ma’ana saboda babu tarkace a cikin su, duk da online ma akwai \u0199wararrun marubuta wa\u0257anda littafansu suke da da\u0257i da ma’ana. Sannan littafan waya sun fi saurin isar da sa\u0199o saboda da waya kana iya karatu ba tare da ka biya ko sisinka ba ko kuma ka fita waje siye. In har za ka karanta littafi mai ma’ana na online to ya fi na takarda saurin isar da sa\u0199o.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Marubuci mutum ne mai isar wa al’umma sa\u0199o, mai warware masu matsalolinsu ba tare da ya yi tozali da su ba, ta hanyar \u0199ir\u0199irar wata duniya ya \u0199awata ta da wasu mutane masu \u0257auke da irin matsalolin mutanen zahiri ko makamancin haka. Ko iya haka na tsaya na san za ku fahimci girman tasirin marubuci a cikin al’umma. Yana yin rubutu saboda abubuwa da dama kamar : Samar wa al’umma mafita, wa’azantarwa, adana tarihi, wayar da kai, Yada ilmi, nisa\u0257antarwa, sanar da halin da duniya take ciki, ds.<\/p>\n\n\n\n
Wa’azantarwa : Yana rubutu domin yin wa’azi ga mutane, wani lokaci ma sai ka ga an yi wa mutum wa’azi ya \u0199i \u0257auka amma sai a yi rubutu ya jijjiga shi silar iftila’i ko wani abu da ya faru da taurarin labari.<\/p>\n\n\n\n
Ya\u0257a ilmi: marubuci yana yin rubutu domin ya\u0257a ilmi a cikin al’umma. Kamar misalin littafin gwanata Hauwa Shehu na Harin Gajimare. A hikimance ta ya\u0257a ilmin cybercriminal kuma ta isar da sa\u0199onta cikin sau\u0199i ta hanyar rubutu.<\/p>\n\n\n\n
Adana tarihi : marubuci yana bayyana ainihin yadda rayuwar alumma take ciki, marubuta. suna yin rubuce-rubuce su fa\u0257i hali da lokacin da ake ciki.<\/p>\n\n\n\n
Wayar da kai : Marubuta suna wayar da kan al’umma. Kamar misali a hikimance marubuta suke yin rubutu a kan illolin auren dole, ko kuma shaye-shaye, kula da lafiya ds.<\/p>\n\n\n\n
Nisha\u0257antarwa: Marubuta suna rubutu domin nisha\u0257antarwa, kamar misalin fim \u0257in Gidan Badamasi, a zahiri labarin nisha\u0257i ne amma idan aka natsu za a fahimci tarin darussan da suke \u0199unshe cikin shi.<\/p>\n\n\n\n
Sanar da halin da duniya ke ciki: marubuta suna rubutu domin sanar da duniya halin da ake ciki. Kamar misalin labarin Rai da Cuta na Maryam Umar da ya lashe gasar BBC a 2020. Duk wanda ya karanta shi komai nisan shekaru idan bai san cutar Corona ba to zai yi tambaya game cutar a fa\u0257a masa.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?<\/p>\n\n\n\n
Amsa: Na’am. Har ma na gama shi, za a buga shi in Sha Allahu. Sunansa Kundin Bincikena.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wane ne tauraronki a cikin marubuta?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Muntasir Shehu.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da sa\u0199o?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Ban sani ba gaskiya don ban cika kallon fim ba. Na jima ma ban kalle shi ba.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya: <\/strong>Wanne kira za ki yi wa masu rubutu na kauce hanya?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Kira na farko a gare su shi ne su ji tsoron Allah, su ji tsoron Allah, su ji tsoron Allah.
Kira na biyu da zan yi masu shi ne su sani rubutun batsa ba abu ne mai kyau ba, in har suna yin shi ne don su samu mabiya ko su zama celebrity to wallahi tun wuri su farka da mumunnan mafarkin da suke yi. Masu rubuta abin alkairi ma ba kowa ne yake tunawa da su ba in suka daina rubutu ko kuma suka je hutu, wata \u0257aya wata biyu an gama yayin mutum an kama wani.
Kira na uku a gare su da su zubar da makamansu na rubutun batsa don ni dai ban ga wata fadakarwa da yake ba su kama rubutun da zai amfani al’umma musamman a wannan lokacin da muke ciki wanda cin hanci da rashawa ya yi yawa, matsalar tsaro ta yawaita, bangar siyasa ta zama ruwan dare gama duniya, media ta zama dandalin musayar ra’ayi, harkar ilmi ta ta\u0253ar\u0253are. Akwai jigogin labarai da yawa da ya kamata a ce an yi magana a kansu amma a banza sai shirme kawai suke ya\u0257awa.
Duk wata marubuciya mai rubutun batsa ina yi mata addua’a Allah Ya shirya ta shiri na addinin Musulunci.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wa\u0257anne nasarori kika samu a rubutu<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Nasara ta farko da na fara samu ita ce ha\u0257uwa da mutane na gari wa\u0257anda suka zame min ‘yan’uwa har nake alfahari da su, wa\u0257anda nake jin su tamkar ‘yan’uwan da muka fito jini daya da su.
Nasara ta biyu kuma ita ce alkairi, na samu alkairi mai yawa sosai. Kullum cikin samun alkairan marubuta nake yi. Ga girmamawar da nake samu daga wasu mutane. Ina matu\u0199ar son girmamawa shi ya sa duk wanda ya girmama ni ina jin da\u0257in hakan a raina. Wannan ma yana cikin nasarar da na samu.
Na uku na koyi rubutu, na fara gane rubutu, ina kan gane rubutu, ina fatan na ci gana da gane rubutu. Wannan ma wata nasara ce da na samu.<\/p>\n\n\n\n
Bayan su na samu wasu nasorori da suka ha\u0257a da:<\/p>\n\n\n\n
1: A shekarar 2021 na yi nasarar zama gwarzuwa ta biyu a gasar Hikayata ta BBC. Silar wancan nasarar na samu wasu nasarori kamar haka:
A. Nasarar karramawa daga \u0199ungiyarmu ta Madubi.
B. Nasarar karramawa daga mamallakin jami’armu Dr Muhammad Abubakar Ibrahim, inda aka shirya taro na musamman a karrama ni, a wurin taron aka yafe mini ku\u0257in karatun shekara biyu Masters ta 1&2 wa\u0257anda za su kusa kimanin miliyan guda na sefa.
C. Kafin karrama ni sai da ya kai ni wurin magajin gari shi ma dai ya \u0257an zura hannu a aljihu ha\u0257e da ba ni wani abu.
D. Watarana ina zaune na ga kira da wata ba\u0199uwar lamba. Bayan na \u0257aga mutumin yake ce mini Shugaban Alliance Fran\u00e7aise ne, ya kira ni yake shaida mini taro ne za su shirya a ranar Francophony, ya sa a nema masa marubuta biyu daga Nijeriya su karanta masu gajeran labari sai ake sanar da shi ai akwai wata ‘yar Nijar ma ‘yar ma Mara\u0257i da ta ci gasar BBC shi ne ya samu lambata ya kira ni.
2. Na zo ta 10 a gasar \u018aangiwa2022.
Tambaya:<\/strong> Wacce shawara za ki bawa sabon marubuci ko marubuciya?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Zan ba su shawarar da su je su koya, ko kuma su fara siyen littafan \u0199a’idojin rubutu da karin magana. Sannan su nemi masana su fara koyar da su. Abin da yake da amfani sosai wanda in aka bar shi an bar da\u0257in labari shi ne \u0199a’idojin rubutu. Daga rubutu ya caku\u0257e to fa zai fara gundarar mai karatu Musamman in wa\u0257anda suka san sirrin \u0199a’idojin rubutu ne.
Bayan sun fara koyon \u0199a’idojin rubutu sai su fara tuntu\u0253ar wani ya koyar da su yadda za su fara rubutu. Zan yi masu nasihar su nemi jigon labari mai ma’ana su fara yi da shi. Sannan bayan sun fara su kasance masu ha\u0199uri da juriya don dole in har kana son ka cigaba ko kuma ka zama wani to dole sai ka ha\u0257a da hakuri. Zan ba su shawarar su kasance marasa \u0199orafi game da makaranta. Zan yi masu fatan alkairi daga karshe.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne kira za ki yiwa mutane masu kallon rubutu a matsayin hanya ce ta \u0253ata tarbiyya?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Kafin in amsa tambayar bari in ce wani abu a kai. Ni fa in har wata ta ce mini ta lalace sanadin karatun littafin kuma marubuciya ce silar lalacewarta, ra’ayina ita ce babbar mai laifi.
Me ya kai ta karantawa? Dole aka yi mata?
Shafin farko da za ki karanta in bai yi maki ba sai ki aje shi ki nemi tsari a wajen Allah ya hane ki da son \u0199ara karantawa.
Shawarar da zan ba su ita ce, kai tsaye zan ce \u0199arya ne bai \u0253ata tarbiya sai wacce ta so ta lalace.
Sannan kuma zan ce masu akwai marubuta wa\u0257anda suka amsa sunansu masu ilmi da fasaha wa\u0257anda in har ka karanta littafansu za ka ji da\u0257in karantawa har ba ka son a zo \u0199arshen labarin. Kuma zan ce masu da yawan masu karatu in sun karanta littafansu har suke gyara matsalarsu. Saboda wata rayuwa ta littafi exactly wani zai ce rayuwarsa ce, wani zai ce da shi ake ma. Kenan ta wannan hanyar ma wani yana iya gyara wata matsalarsa. Don haka kai tsaye zan ce ba gaskiya ba ne.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Wanne irin cigaba harkar rubutu ta ke samu a yanzu?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Gaskiya an samu cigaba sosai ta fuskar bun\u0199asa shi ma yadda marubuta suke sarrrafa basirarsu cike da \u0199warewa suna rubutu.<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Shin wanene ubangidanki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n
Tambaya:<\/strong> Mene ne burinki a harkar rubutu?<\/p>\n\n\n\n
Amsa:<\/strong> Sa\u0199on da na isar ya amfanar da al’umma.<\/p>\n\n\n\n
An yi wannan hira da Nana Aicha Hamissou ne a ranar Talata, 13 ga 10 Oktoba 2020 kai tsaye. An kuma tace tare da sabunta tambayoyin a ranar 27 ga watan Mayu 2024.<\/p>\n\n\n\n
Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad.<\/p>\n\n\n\n
Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"