{"id":4587,"date":"2026-01-14T13:37:21","date_gmt":"2026-01-14T13:37:21","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4587"},"modified":"2026-01-14T13:41:06","modified_gmt":"2026-01-14T13:41:06","slug":"manyan-kura-kurai-10-da-marubuta-ke-yi-da-yadda-za-su-kauce-musu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/manyan-kura-kurai-10-da-marubuta-ke-yi-da-yadda-za-su-kauce-musu\/","title":{"rendered":"Manyan Kura-Kurai 10 da marubuta ke yi da yadda za su kauce musu"},"content":{"rendered":"\n<p>Kamar kowacce irin sana&#8217;a, rubutu yana da wasu matakai ko tsari da lallai ne mutum yana bu\u0199atar ya bi su kuma ya \u0199ware akansu matu\u0199ar yana son ya isar da sa\u0199onsa ga wa\u0257anda suka dace. Bai yiwuwa haka kawai mutum ta fara rubutu ba tare da sanin abubuwan da rubutun ya \u0199unsa ba kuma ya sa ran cewa zai ci nasara. Ba ma wannan ka\u0257ai ba, hatta wa\u0257anda suka ci nasara ko suka yi shura a harkar rubutu ba su fi \u0199arfin su yi kuskure ba. Ballantana kuma wanda shi yanzu ma zai fara. To, ko da kai sabon marubuci ne ko kuma wanda ya da\u0257e yana yi, tabbas ya wajaba akanka ka kiyaye wa\u0257annan kura-kuran wa\u0257anda aikata su na iya rage kimar rubutunka. Fahimtar matsala rabin maganin matsala ce. Sanin kura-kuran da ya kamata ka kiyaye tare da fahimtar hanyoyin kauce musu na iya taimakawa sosai wajen ingantanwa tare da ha\u0253aka naka rubutun. Manufar wannan ma\u0199ala ita ce ta fahimtar da kai wa\u0257annan kurakurai tare da kawo mafita.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">1. Kuskure: Rashin Tsari<\/h2>\n\n\n\n<p>\u018aaya daga cikin manyan kura-kuran da mafi yawancin marubuta ke aikatawa shi ne rashin tsari. Sau da dama sai ga ka marubuci ya hau rubutu haka kawai kai tsaye ba tare da ya yi wani tsari na yin wannan rubutun ba, ba kuma tare da takamaiman bigire da yake son kaiwa gare shi da rubutun ba. Sau da dama irin wa\u0257annan marubutan su ne wa\u0257anda sai sun yi nisa sai su kasa motsawa daga inda suka tsaya. Saboda dama can basu da wata tsayayyar manufa game da rubutun, kawai dai suna yi ne. Misali, mutum ne zai rubuta labari, amma bai san farko, tsakiya da kuma \u0199arshen labarin ba. Don haka sai ya yi ta \u0257anwaken zagaye yana neman yadda zai kamo bakin zaren labarin amma ya kasa. Daga \u0199arshe ya \u0253ata wa kansa da masu rubutu lokaci, kuma da kasu sharhi za su caccake shi sai ya fara cewa hassada suke yi mishi.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Ka \u0257auki lokaci ka bi aikinka a hankali ka tsara shi yadda ya kamata. Ka zana jadawalin yadda al&#8217;amura za su tafi a cikin labarin naka. Daga mataki kaza sai kaza, daga nan sai can. Daga wannan babi sai wancan. Tauraro kaza yana da ala\u0199a da tauraro kaza. \u0181angare kaza na labarin shi zai ha\u0257e da \u0253angare kaza domin fitar da asalin jigon labarin. Idan ka yi irin wannan tsarin, shi ne zai taimaka maka ko da ka ma\u0199ale a hanya ka san ina ya kamata ka bi. Kuma masu yin irin wannan tsarin aikinsu ya fi kyau kuma ya fi fita musu cikin sau\u0199i.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">2. Kuskure: Zuzutawa<\/h2>\n\n\n\n<p>Zuzutawa kan faru ne yayin da marubuci ya \u0199u\u0199e wurin fa\u0257a\u0257a bayani game da wani abu fiye da \u0199a&#8217;ida, ko kuma ta hanyar maimaita magana \u0257aya ko kuma kawo wasu bayanai na babu-gaita-babu-dalili a cikin labarinsa. Irin wannan kuskure ne ke sa masu karatu su kasa yarda da labarinsa ko ma su ji ya fitar musu a ka. Sau da dama ma sai ka ji wasu na cewa &#8216;ai marubuci wane \u0199aryarsa ta shahara.&#8217; Ka ga batun ma labarin ya yi tasiri a zukatansu ko ma ya kai ga wanzar da canji bai taso ba. Mafi yawancin irin wannan kuskuren na faruwa ne a tsakanin sabbin marubuta wa\u0257anda ke ganin kamar yawan labari ko girman littafi shi ne iya rubutu.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>A Koyi yadda ake ta\u0199aita magana a yayin rubutu. A kuma tabbatar an tace rubutu sosai tare da rage duk wani bayanin da bai da wani muhimmanci a cikin rubutun ta yadda za a \u0257aure labarin zam ya zamana ya ri\u0199e tunanin mai karatu. Ka tambayi kanka, shin wannan jumlar tana da wani muhimmanci a cikin wannan labarin? In har ba ta da shi, to cire ta kawai. Sannan karanta rubutunka kafin ka fitar da shi zai taimaka \u0199warai waje ba ka damar rage abubuwan da suka kamata a cire.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">3. Kuskure: Nuna halin ko in kula ga masu karatu<\/h2>\n\n\n\n<p>Yin rubutu haka kawai ba tare da halarto da wa\u0257anda ka ke yin rubutun domin su a daidai lokacin da ka ke yin rubutun ba na iya sa wa sa\u0199on da ka ke son isarwa ya kasa zuwa inda ya kamata ya je. Misali: yin amfani da kalmomi masu tsauri ko kuma manya-manyan karin magana a cikin littafin da ka rubuta domin yara, ko kuma nuna son iyawa da gwanintar iya sarrafa harshe a cikin littafin da aka rubuta domin &#8216;yan makaranta na iya sa masu karatu su \u0199auracewa rubutunka gaba \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:.<\/h3>\n\n\n\n<p>Kafin ka fara rubutu, ka san su wa kake yin rubutun domin su. Idan ka fahimci wannan, sai ka yi rubutun a harshe, da sauti, da murya irin wadda za su iya fahimta. Ka kuma yi amfani da jigo da salo irin wanda ya dace da su.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">4. Kuskure: \u0198in tace rubutu<\/h2>\n\n\n\n<p>Marbut da dama suna aikata wannan kuskuren. Wasu da sun yi rubutu haka kawai za su tura wa masu karatu ba tare da sun sake bibiyar wannan rubutu sun duba ko akwai gyaran da ya kamata su yi ba. Rashin komawa a duba aiki yadda ya kamata ke sa kai ta ganin kurakurai a cikin rubutun da sha\u0253a iri-iri a cikin littafin.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Komai ka gani yana son gyara sai dai in bai samu ba. Ba gazawa bace ba rauni bane kuma ba rashin iya bane ke sa mutum ya koma ya duba aikinsa ko kuma ya ba wani ya duba mishi. Face sai don son ganin an fitar da aiki managarci. Ka duba aikinka da kyau ka yi gyaran da dace ya fi akan a ce sai ya fita tukunna a yi ta surutu game da gyaran da bai taka kara ya karya ba.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">5. Kuskure: Tsaron rashin nasara<\/h2>\n\n\n\n<p>Tsoron rashin nasara na iya jawo cutar farfa\u0257iya ta kama al\u0199alamin marubuci. Hakan ke sa wasu marubutan su ma kasa rubuta labarin ko kuma su kasa kammala wanda suka fara. Sau da dama irin wannan tsoron kan samo asali ne daga rashin yarda da kai, tunanin sai an yi abu tsaf-tsaf ko kuma takura wa kai wajen ganin an cimma wani gaci na tsammani.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Rashin nasara ba ba\u0199on abu bane a wurin kowa. Ba lallai ne don kayi nasara yau ya zama kullum kuma kai mai nasara bane. Kamar yadda rashin nasara a yau baya nufin rashinta har abada. Ita rashin nasara ma wani \u0253angare ne na \u0199ara girma da samun damar gyara abubuwa da dama a gaba. Manyan marubuta irin su J. K Rowling da Stephen King ma sun fuskanci \u0199alubale iri-iri amma hakan bai hana su zama abinda suka zama ba a duniyar rubutu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">6. Dogaro da gana-garin magana\/jigo<\/h2>\n\n\n\n<p>Amfani da gama-garin magana, karin magana, jigo ko yankin magana na iya sa masu karatu su ji ai sun saba jin ire-iren su. Don haka sai su kasa \u0257aukar marubuci da muhimmanci. Misali; kiran tauraron labari da &#8216;\u0199a\u0199\u0199arfa kamar zaki&#8217; ba ba\u0199on abu bane, kuma ba zai wani burge masu karatu ba.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Amma ko da za ka \u0257auki jigo wanda yake gama-gari ne, to sai ka canza salo. Yi \u0199o\u0199ari ka \u0199ir\u0199iro wani abu sabo maimakon ka dogara da gama-garin abin da mafi yawancin mutane ke amfani da shi. Ka nemo sabbin hanyoyin da za ka iya bayyana abinda ke ranka ta hanyar amfani da salo na daban a rubutunka. Misali: maimakon ka ce &#8216;lokaci na gudu&#8217; kana iya cewa &#8216;kamar da wasa haka awoyi daga cikin ranakun rayuwarmu ke wucewa ta tsakankanin yatsunmu amma ba mu ankara ba&#8217; da dai sauransu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">7. Kuskure: Rashin gina taurari yadda ya dace<\/h2>\n\n\n\n<p>Taurari su ne zuciyar kowane labari. Amma duk da haka wasu marubutan ba sa maida hankali wajen ganin sun \u0199ir\u0199iro taurarin da za su shiga zukatan masu karatu. Sai ka ga tauraro da \u0257abi&#8217;a iri kaza a babi kaza, ana shiga wani babin kuma ka ganshi da wata. Sannan wasu taurarin ba a basu lokacin da ya dace balle su girma daga inda suke tun a farkon labarin har zuwa \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Kana iya fitar wa da taurarin labarinka jadawali na musamman mai \u0257auke da bayanan duk da suka dace game da su. Yin hakan zai ba ka damar komawa kana dubawa akai-akai saboda kar ka sauka daga kan layi. Misali; abu ne mai wahala ace ga tauraro mai kunya da \u0199arancin magana ya tashi ya yi wani abu gatsal haka irin wanda bai saba ba sai dai in wani abu ne ya faru da shi da har ya sauya daga inda ya ke. To in ba ka bayyana wannan abin da ya kawo canjin ba masu karatu sai su gundura da irin wannan hawan-\u0199awarar da ake yi musu kuma su kasa yarda da labarin naka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">8. Kuskure: Sauri ko nawa<\/h2>\n\n\n\n<p>Wasu marubutan saboda gaggawar ganin sun gama rubuta labari sai su yanke wani \u0253angare na labarin kawai su dira a wani. Wannan ba \u0199aramin kuskure bane. Domin yana hana mai karatu jin cewa lallai abinda ya faru a \u0199arshen labarin ya dace da ya faru. Akwai wadu kuma da ke jan labari su yi ta ya\u0199wan\u0199wana shi haka kawai suna ja wa masu karatu rai fiye da kima har ta kai ga suna tsallake shafuka zuwa shafi na gaba. Dukkan wa\u0257annan kuskure ne da bai kamata a samu marubucin \u0199warai na aikata su ba.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>A yi \u0199o\u0199arin daidaita aiki da kuma sakamakon aikin. A yi amfani da rubutun sauri wajen da ya dace, a kuma tafi a hankali a wurin da ya dace. Hanya mafi sau\u0199i da za a iya gane wane irin salo masu karatu suka fi so shi ne ta hanyar jin ra&#8217;ayin masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">9. Kuskure: \u0198in \u0257aukar shawara<\/h2>\n\n\n\n<p>Wasu marubutan sam ba sa \u0257aukar shawara. Musamman idan masu karanta labarin nasu ne. Sau da yawa sukan yi tunanin cewa ai aikinsu ya fi \u0199arfin kuskure ko kuma sun fi \u0199arfin a yi musu gyara. Irin wannan halin ke sa marubuci ya kasa ci gaba.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Kamata ya yi marubuci ya kasance mai sauraron \u0199orafin masu karatu tare da \u0257aukar shawararsu. Haka kuma marubuci ya kasance mai kar\u0253ar \u0199orafi ko suka da bu\u0257a\u0257\u0257iyar zuciya. Hakan shi zai ba ka damar sanin inda ya kamata a yi gyara.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">10. Kuskure: saurin karaya<\/h2>\n\n\n\n<p>Rubutu \u0199alubale ne mai zaman kansa, kuma sau da dama rubutu na bu\u0199atar ka\u0257aici. Wannan dalili ne ke sa wasu marubutan ke karaya har ma su ajiye wani aikin nasu tun kafin ya ginu saboda rashin samun \u0199warin gwiwa, fushi ko kuma tsoron fa\u0257uwa.<\/p>\n\n\n\n<h3 class=\"wp-block-heading\">Mafita:<\/h3>\n\n\n\n<p>Marubuci ya zama mai ha\u0199uri da juriya tare da kafewa akan muradunsa. Ka zagaye kanka da mutanen da kuke da ra&#8217;ayi iri \u0257aya wa\u0257anda za su ke \u0199arfafa maka gwiwa. Idan kuma in ka tashi yin wani abu mai muhimmanci, to ka fara da abubuwa masu sau\u0199i na \u0199asa kafin ka je ga manya na sama.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi rubutu wata irin tafiya ce wadda ke cike da \u0199alubale iri-iri. To amma duk da haka, kauce wa irin wa\u0257annan kurakuran na taimakawa wajen tsallake irin wa\u0257annan \u0199alubalen. Musamman tsara aikinka kafin ka fara da kuma komawa ka duba inda gyara ka yi.<\/p>\n\n\n\n<p><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kamar kowacce irin sana&#8217;a, rubutu yana da wasu matakai ko tsari da lallai ne mutum yana bu\u0199atar ya bi su kuma ya \u0199ware akansu matu\u0199ar yana son ya isar da sa\u0199onsa ga wa\u0257anda suka dace. Bai yiwuwa haka kawai mutum ta fara rubutu ba tare da sanin abubuwan da rubutun ya \u0199unsa ba kuma ya&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/manyan-kura-kurai-10-da-marubuta-ke-yi-da-yadda-za-su-kauce-musu\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Manyan Kura-Kurai 10 da marubuta ke yi da yadda za su kauce musu<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":4589,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[104,58,1,2],"tags":[149,132,148,146,138,147],"class_list":["post-4587","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-book-matters","category-hausa","category-uncategorized","category-writing-tips","tag-bincike","tag-hausa","tag-inganta-rubutu","tag-kura-kurai-10","tag-nazari","tag-rubutu"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/kurakurai-10.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4587","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4587"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4587\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4589"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4587"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4587"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4587"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}