{"id":4857,"date":"2026-06-05T11:35:36","date_gmt":"2026-06-05T11:35:36","guid":{"rendered":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/?p=4857"},"modified":"2026-06-05T11:36:09","modified_gmt":"2026-06-05T11:36:09","slug":"sharhin-littafin-kishiyar-katsina-na-hadiza-isyaku","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-kishiyar-katsina-na-hadiza-isyaku\/","title":{"rendered":"Sharhin Littafin &#8216;Kishiyar Katsina&#8217; na Hadiza Isyaku"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Sunan Littafi: <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=kishiyar+katsina\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=kishiyar+katsina\">Kishiyar Katsina<\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Sunan Marubuciya: <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/khadjahishaq\/\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/khadjahishaq\/\">Hadiza Isyaku<\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Inda Aka Buga Littafi: <strong>Bakandamiya Hikaya<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Shekarar Bugu: <strong>2023<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Nau&#8217;in Labari: <strong>Soyayya\/Zamantakewar Aure<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Yawan Babi: <strong>21<\/strong><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Mai Sharhi: <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/haiman-raees\/\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/author\/haiman-raees\/\">Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)<\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Manufar Sharhi: <strong>Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba<\/strong><\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Gabatarwa<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hausawa kan ce &#8216;kishi kumallon mata&#8217;, wasu ma kan ce &#8216;duk macen da ba ta da kishi aura ce.&#8217; A gefe kuma, Hausawa kan yi wa Katsinawa kirari da cewa &#8216;kunya gare ku ba dai tsoro ba.&#8217; Ita kanta Katsinar ma akan yi mata kirari da &#8216;Ta Dikko \u0257akin kara.&#8217; Kishi dai kam an san kowace mace na da shi daidai misali, to amma me ke faruwa yayin da kishi, zargi, bin shawarwarin mugayen \u0199awaye ya ha\u0257u da tsantsar son zuciya? Wannan shi ne abin da wannan littafi na Kishiyar Katsina ya \u0199unsa a dun\u0199ule. Kishiyar Katsina labari ne wanda yake shiga zuciya ta hanyoyi masu yawa. Wasu lokuta ya baka dariya, wasu lokutan kuma ya sa ka zubar da hawaye, ba hawayen da suke fitowa a dalilin  ba\u0199in ciki kawai ba, har ma daga takaicin ganin mutumin da kake tunanin zai iya gyara kanshi, sai kuma ya \u0199ara lalacewa. <\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Tarihin Marubuciyar A Ta\u0199aice <\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An haifi Marubuciya Hadiza Isyaku ne a cikin garin Katsina a 1992. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini da na zamani ne tun tana \u0199arama kuma ta yi karatunta na Firamare da na Sakandare ne duk a garin Katsina. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kamar mafi yawancin marubuta, marubuciyar ita ma ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance \u0257aya daga cikin fitattun marubutan da sunansu ya fi yawo a online a wannan zamani domin abu ne mai wuya ka fa\u0257i sunanta a duniyar marubuta da makarantan wannan zamani ba a samu wanda ya santa ba. Zuwa yanzu marubuciyar ta rubuta jiggan litattafai guda hu\u0257u. Ga su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">1. Mai Awara<br> 2. <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=ko+ruwa\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=ko+ruwa\">Ko Ruwa Na Gama Ba Ki<\/a><br> 3. <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=kishiyar+katsina\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=kishiyar+katsina\">Kishiyar Katsina<\/a><br> 4. <a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=cikin+baure\" data-type=\"link\" data-id=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/?s=cikin+baure\">Cikin \u0181aure<\/a><\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sai kuma littafinta na biyar da ke kan hanya mai suna YUSRIYYAH.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babban abin da marubuciyar ta fi so shi ne karatu da rubutu, sai kuma sana&#8217;ar \u0257inki da take ta\u0253awa. Baya ga wannan, marubuciyar ta kasance \u0257aya ce daga cikin membobin \u0199ungiyar marubuta mai suna Haza\u0199a Writers Association. Marubuciyar ta ta\u0253a shiga gasar HIKAYATA ta BBC Hausa sau uku amma ba ta yi nasara ba. Littafin da ta fi so a duk cikin litattafanta shi ne &#8216;Ko Ruwa Na Gama Ba Ki&#8217;. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hadiza Isyaku tana da aure, kuma yanzu haka tana zaune ne a Katsina da yaranta guda biyu. <\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Labarin A Ta\u0199aice<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Labari ne akan wani mutum mai suna Khamis (Abban Haneef) da matarsa Aisha wadda ta \u0257auki damuwa ta babu gaira babu dalili ta \u0257ora wa kanta saboda za a yi mata kishiya. Babban abin da ya tayar mata da hankali shi ne jin cewa kishiyar da za a yi mata &#8216;yar Katsina ce. A cewarta ai Katsinawa sun fiye yawan asiri. Tun daga nan fa ta shiga fa\u0257i-tashi wajen ganin ba ai auren ba amma abu ya faskara.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan an yi auren, duk irin kirkin da ke tattare da amaryar (Maryam) Aisha ba ta gani. Duk kuwa da cewa Maryam \u0257in ta \u0257auki yaranta Haneef da Haneef kamar ita ta haife su. Wannan ya sa Maryam ta samu shiga a wajen Khamis sosai, ita kuma Aisha sai ta yi tsammanin asirin ne dai take yi domin ta \u0199wace mata miji.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da wannan dama ce babbar \u0199awar Aisha wato Zuzee ta yi amfani wajen dulmiyar da ita cikin sa\u0253o da aikata shirka domin ta amshe mata ku\u0257a\u0257e. A haka har ta ha\u0257u da Jamsy wadda ta kai ta wurin bokan da ya yi musu asiri aka cusa wa Maryam tsoro da tsanar Khamis kuma aka kashe \u0257an da ke cikinta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A \u0199arshe dai asiri ya tonu cewa Aisha ce ta kitsa komai, kuma ashe Zuzee nema take ta aure mata miji ba tare da ta sani ba. Maryam na samun lafiya, Khamis na sakin Aisha. Jami&#8217;an tsaro kuma suka kama Jamsy, Zuzee da boka.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\"> Babban Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Babban jigon Kishiyar Katsina shi ne &#8216;Kishi a Matsayin Makamin Hallaka Kai. Ra&#8217;ayin cewa kishi idan ba a iya sarrafa shi ba, ba ma\u0199iyinka kawai yake hallakawa ba, face kai kanka. Wannan shi ne mafi mahimmancin sa\u0199on da labarin ke son mai karatu ya \u0199afa a ransa bayan ya rufe shafi na \u0199arshe.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wanda ya karanta wannan littafi zai ya lura da cewa Khamis bai cutar da Aisha ba. Maryam ma ba ta cutar ta ba. Ita ma Zuzee, duk da muguwar rawar da ta taka, ba ta halaka ta ba. Aisha ce ta hallaka kanta, ta hanyar za\u0253ukan da ta yi \u0257aya bayan \u0257aya, dukkansu a kan dalili na kishi wanda ya rufe mata idanuwanta daga ganin ha\u0199i\u0199anin gaskiyar al&#8217;amuran da ke faruwa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">\u0198ananan Jigo<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Bayan wannan babban jigo da na yi bayani, marubuciyar ta yi amfani da wasu \u0199ananun jigogi masu yawa wa\u0257anda su ne suka ha\u0257u suka goya wa labarin baya ta hanyar koyar da darussa da dama a cikin wannan labari. Ga wasu ka\u0257an daga cikin su kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Illar Mugayen \u0198awaye: Zuzee ita ce silar dukkan bala&#8217;in da ya samu Aisha. Babu wanda ya yi mata magana mai cutarwa ko bayyana mata wani abu da Khamis ya yi yi mata na rashin jin da\u0257i, amma Zuzee ta bi ta duk wata hanyar da za ta iya har sai da ta \u0257ora ta akan gadar mummunan tunanin cewa asiri ne hanyar da ta dace, maimakon hali mai kyau da nuna so da \u0199auna. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar ta bayyana wannan ta hanya mafi sau\u0199in fahimta da tasiri fiye da yadda yawancin labaran Hausa ke yi. Ba wai kawai cewa ta yi &#8220;Zuzee ce ta \u0253ata ta&#8221; ba, a&#8217;a ta nuna mana yadda Zuzee ke \u0253ata ta ne a aikace mataki-mataki.<br>\nDubi wannan kalamin da Zuzee ta furta lokacin da Aisha ta fara damuwa bayan mutuwar \u0257an Maryam:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;To meye na damuwa tunda ba ke kika kashe shi ba.&#8221; (Babi na 15)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wace irin \u0199awa ce ke kwantar da hankalinki ta hanyar \u0253ata miki tunani da yaudara? Marubuciyar ta nuna mana cewa irin wannan magana ce  mafi ha\u0257ari a tsakanin \u0199awaye, domin tana saka mai laifi ya ji cewa bai da laifin komai. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Kissa a Matsayin Mafarkin Mace Na Gaskiya: Maryam, kishiyar da kowace mai karatu za ta tsana a farkon labarin, a zahiri ita ce mafi muhimmancin darasin labarin. Ba ta yi asiri ba. Ba ta je gidan boka ba. Ba ta ya\u0257a sirrinta a kafar sada zumunta ba. Amma ta iya kissa. Ta yi biyayya. Ta ri\u0199e tsaftar jiki. Ta koyar da yaran Aisha halaye da mahaifiyarsu ta kasa koya musu. Kuma ta ci nasara ne ba don wani taimako na waje ba, sai don halayyarta ta sha bambam da ta kishiyarta.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar ta nuna wannan bambancin ta hanyar nunawa, ba ta hanyar fa\u0257i ba:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Ni naki nake so.&#8221; Khamis ya fa\u0257a wa Maryam, a daidai lokacin da Aisha ke cikin nta \u0257akin tana sanya wa \u0199ofar makulli saboda fushi. (Babi na Shida)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Mutuwar Yaro: An nuna mana yadda mutuwar \u0257an Maryam ta ta\u0253a kowane tauraron labarin ta hanya ta daban. Khamis ya yi kukan zuci wanda ba ya iya bayyanuwa a waje. Maryam ta kar\u0253i \u0199addararta, kuma tsaya tsayin daka domin ganin ta samu damar sarrafa zuciyar mijinta, damar sarrafawar da asiri da tsoratarwa ba za su ta\u0253a ba ta ba. Aisha kuwa ta ji cewa ita ce ta jawo wannan bala&#8217;i da hannunta, nadamar wannan laifin ya fi sukarta wahala fiye da duk wani hukunci da wani zai iya yi mata.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Nadama a Matsayin Makaranta: Aisha ba ta mutu ba. Ba ta zama mace wadda aka ci zarafinta ba. Ta zauna ne tare da zunubinta. Ta yi istighfari. Ta yi nafilfili. Ta ga yadda duniya ke horo mai tsauri ga mutum bisa sakamakon ayyukansa. Sannan ta koma ga Allah, ta dawo cikin hayyacinta tare da wata irin sabuwar fahimtar rayuwa wadda irin wannan hali da ta shiga ne ka\u0257ai ke koyar da mutum irinta. Wannan shi ne yanayin nadama ta gaskiya wanda adabin Hausa ke bu\u0199atar nuna shi fiye da yadda ake nunawa a labaran zamani.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Sakamakon \u0198addara: Zuzee, mace mai son hallaka \u0199awarta domin ta aure mata miji, ta \u0199are ta auri wani Alhajin \u0199auye, kuma da ma da matanshi na jira a gida. Wannan ba horo ne irin na almara domin nishadantarwa ba kawai, shi ne irin sakamakon da mafi yawancin mata irinsu ke fuskanta a zahiri, kuma shi ne irin abin da ya fi dacewa da mutumin da ya \u0257auki rayuwarsa da nufin aikata mugunta ga wasu.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Salo da Sarrafa Harshe<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar ta nuna basira sosai wajen ba da wannan labarin. Domin ta yi amfani da salo iri daban-daban kuma duk masu burgewa wajen isar da sa\u0199on labarin a sau\u0199a\u0199e. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Misali:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">I. Salon Koyarwa<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar ba ta yi wa&#8217;azi kai tsaye ba. Ta koyar ne ta hanyar nuna sakamakon yanke-hukunci. Kowane za\u0253in da Aisha ta yi ya zo mata da irin nashi sakamakon wanda ba a bu\u0199atar mai sharhi sai ya ya fayyace, domin sakamakon ya bayyana kansa a fili. Wannan shi ne mafi ingancin hanyar koyarwa a rubutu, kuma Hadiza Isyaku ta yi amfani da shi da \u0199warewa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Misalin da ya fi fice shine lokacin da Khamis ya ce wa abokinsa K.B:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Oh ni Muhammadu Khamis, wai me ke damun mata ne da suke hana junansu zaman lafiya? Ko da yake wani lokaci har da laifinmu maza.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"> II. Salo Mai Armashi<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wasu wuraren a labarin sun faye da armashi da yawa, har ma su ke sa mai karatu ya bu\u0257e baki ko ya yi murmushi ko da yake ya san labarin na da nauyi. Misali, lokacin da Khamis ya zauna tare da Maryam a kitchen yana ta faman firar kabewa, sai Aisha ta doso ta gans su, ta ce a ranta:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Shanyayyen banza.&#8221; (Babi na 05)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ba dariya ce za ta kufce maka irin ta \u0199aryar labarin ba, dariya ce da ke nuna cewa a cikin rashin nutsuwar Aisha akwai wani \u0253angare na \u0257an&#8217;adam wanda ya kasa ganin abin da ke gaba da bayansa saboda wani abu ya kange masa ganinsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">III. Salon Hoton Zuci<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar ta nuna irin wannan yanayi ta hanyar zurfafa bayani wanda ke sa mai karatu ya ji kamar yana wurin abin ke faruwa, ba wanda ke kallo daga waje ba. Misali, lokacin da Maryam ta zo gaban Khamis cikin maternity gown bayan dawowarsa gida:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8216;A falo ta samu Khamis, sosai ta lura da yadda yake kallonta, musamman cikinta da kuma fararen \u0199afafunta da ke waje. \u018aan russunawa ta yi sannan ta ce &#8216;Girki na jiranka&#8217;.&#8221; (Babi na 18)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ba wani dogon bayani bane da ke bu\u0199ata dogon yabo ba, amma kana iya ganin hoton abin da ya faru a cikin zuciyarka. <\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Zubi da Tsari<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">1. Hange<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An fara Kishiyar Katsina daidai tsakiyar rikicin labarin, Aisha a dur\u0199use a gaban Khamis, idanunta cike da \u0199walla, tana kuka. Ba a yi wata gabatarwa mai tsawo ba, ba a gaya wa mai karatu &#8220;Aisha mace ce mai kyau ko mugun hali ba,&#8221; sai dai ana riga an shiga cikin zuciyar matsalar ne. Wannan za\u0253i abin burgewa ne, domin kai tsaye mai karatu ya shiga duniyar labarin ba tare da ya \u0253ata lokaci ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">2. Waiwaye<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">An yi amfani da waiwaye a wurare da dama domin fayyace asalin yadda wasu al&#8217;amura suka fara, musamman game da tarihin ha\u0257uwar Khamis da Maryam, da kuma yadda Zuzee ta shiga ala\u0199a da Khamis ta waya a \u0253oye, ta \u0253oye kanta a matsayin &#8220;Aydah.&#8221; Wa\u0257annan waiwaye sun ba labarin \u0257imbin bayani ba tare da sun da\u0199ile zagayowar labarin ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">3. Ba\u0257oki na Gaske<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Akwai ba\u0257oki na gaske da ya shafi shigowar Maryam gidan Khamis, wannan ya faru ne a babi na biyu. Tun daga nan mai karatu zai iya gane cewa kalaman Aisha na nuna cewa ba za a samu zaman lafiya a gidanba, ba yau ba, ba gobe ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">4. Ba\u0257oki na Giri<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ana tsaka da wannan labarin sai kuma marubuciyar ta nuna labarin Auwal, babban abokin Khamis shi da da Hafsat suna \u0199ullawa Irin soyayyar. Wannan ala\u0199a mai sau\u0199i da \u0257an\u0257ano ta kawo \u0257an numfashi a cikin labarin mai cike da rikici, kuma mai karatu ya samu hannunka mai sanda da cewa rayuwa na ci gaba da wanzuwa a tsakanin matsaloli.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">5. \u018aarsau na Tsoro<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Lokacin da Zuzee ta fallasa duk asirin Aisha a tsakiyar falo, a gaban Khamis da Abdul da dukkan dangi:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">*&#8221;Ke da Anty Jamsy kuka je wurin boka aka baki maganin da kika ha\u0257a da jinin al&#8217;adarki kika ba mijinki ya sha, tun daga wannan rana bai sake neman matarshi ba, har yun\u0199urin zubar ma Maryam da ciki kika yi, Allah bai nufa ba, amma da yake kwanan \u0257an da aka haifa ya \u0199are sai da boka ya sa aljanu suka kashe shi.&#8221;* (Babi na Ashirin Da \u018aaya)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Sallallami duk wanda ke wurin ya shiga yi.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan \u0257arsau na tsoro ya fi kowanne yanayin tsoro da ake sawa a labaran soyayya na Hausa, ba na wuta bane ko na \u0199arfin jiki ba, face na tonon silili na mummunan aikin da mutum ya aikata da hannunsa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">6. \u018aarsau na Al&#8217;ajabi<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Maryam, wadda aka yi wa dukkan wannan mugunta, tun daga asiri, banka\u0257a a ciki, mutuwar \u0257anta, amma ita ce wadda ta ce lokacin da za a \u0257aure Aisha bisa zargin laifi:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">*&#8221;Ba inda za ta je, ni ce uwar \u0257an da aka kashe, kuma na yafe mata.&#8221;* (Babi na Ashirin Da \u018aaya)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan abu ya \u0199unshi al&#8217;ajabi na gaskiya kuma mai ban mamaki. Domin wannan ba yafiya ce irin ta tatsuniya ba, yafiyar mace ce da ta san cewa Allah ne ka\u0257ai zai yi wa zalunci da azzalumai hisabi, ba ita ba. Kuma ta san cewa \u0257aukar takobin fansa yana lalata hannun wanda ya \u0257auke shi fiye da wanda ake bugawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">7. \u018aarsau na Mamaki<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Lokacin da Aisha ta gano cewa sunan da ke a cikin wayar Zuzee a matsayin &#8220;Fiance&#8221; shi ne lambar Khamis, kuma a daidai lokacin tana nan tana ganin Khamis yana wayar a gaban Zuzee:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">*&#8221;Princess Aydah, ko kuma na ce Zuzee.&#8221;* (Babi na Ashirin Da \u018aaya)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Wannan bu\u0257e wa&#8217;adi ne wanda marubuciyar ta ri\u0199e sosai tsawon labarin kafin ta \u0253alle shi a mafi dacewar lokaci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">8. \u018aarsau na Murna<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A ranar Idin \u0199aramar sallah, Khamis ya je gidansu Aisha, ya yi mata albishirin komawa \u0257akinta, amma tare da babbar shara\u0257i:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Wannan shi ne last chance \u0257inki, saura igiyarmu \u0257aya, idan kin yi ri\u0199o da ita bisa ga tsoron Allah, to mutuwa ce za ta raba ki da \u0257akinki, idan kuma kika yi wasa da ita, toh wallahi tsaf za ki dawo gida.&#8221; (Kusa da \u0199arshen labarin)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Tabbas wannan abin murna ne, amma murna ce mai nauyyi da ke \u0257a\u0257e zuciya. Kuma haka irin wannan farin ciki ke kasancewa a rayuwa ta gaskiya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">9. Hoton Zuci<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Marubuciyar tana iya zana yanayi da \u0199warewa ta yadda mai karatu ke iya ganin tamkar abun yana faruwa ne a gabansa. Dubi wannan:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Jiki ba \u0199wari ta mi\u0199e tare da kama hannun amaryar da ke ta mazurai a cikin lifaya ta ce, &#8216;Mu je Maryam.'&#8221; (Babi na Biyu)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da kuma yadda ta bayyana Khamis a daren da ya dawo ba tare da bacci ya so ba:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">&#8220;Kishingi\u0257a ya yi akan sofar bayan ya \u0257auke wayarta da ta manta a nan. Sosai ya yi nisa cikin tunanin Maryam wanda yake sa shi kukan zuci, musamman idan ya tuna da rasa \u0257anta da ta yi&#8230;&#8221; ( tsakiyar labarin)<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Halayen Taurarin Labari<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Aisha: Ita ce tauraruwar da labarin ya ginu a kansa. Ba tauraruwa ce mai tsarki da nagarta can ba, mace ce mai kishi wadda ta ha\u0257u da muguwar \u0199awa, ga ta da \u0199arancin ilimin sarrafa rai, dukkansu sai suka tattaru suka jefa ta cikin hallaka. Wannan shi ne ya sa labarin ya fita daga tsarin &#8220;jarumar kirki ta \u0199arshe ta yi nasara akan muguwar kishiya&#8221; wanda yawancin labaran Hausa ke faruwa a kai. Bayyana Aisha a matsayin &#8216;yar&#8217;adam mai rauni, ni&#8217;ima da sauran abubuwan da ake iya ala\u0199antuwa da su shi ne babbar gagarumar nasarar da marubuciyar ta samu a wannan labari.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Maryam: Ita ce tauraruwar labarin a zahiri. Ba mai son hayaniya ba ce, ba mai neman fa\u0257a ba, mace ce da ta san yadda ake mallakar zuciyar miji ba ta hanyar asiri ba, sai ta hanyar kissa, tsaftar jiki, da koyar da yaransa abubuwan da mahaifiyarsu ba ta iya koya musu. Marubuciyar ta nuna cewa wanda ya fi nasara ba shi ne wanda ya fi \u0199arfi ba, face sai wanda ya fi juriya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Khamis: Mutum ne \u0257aya da rabi, yana \u0199aunar Aisha da gaske, yana \u0199aunar Maryam da gaske, yana \u0199o\u0199arin yin adalci a tsakaninsu, kuma yana da hankali fiye da yadda matansa ke \u0257aukarsa. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Zuzee: Ita ce mafi ban mamaki a taurarin labarin. Ta wuce yanayin &#8220;muguwar \u0199awa&#8221; da a iya yin bayani cikin sau\u0199i, ta zama hoton cikakken nau&#8217;in irin \u0199awayen da ke cin amana a \u0253oye, tana tsegumin kishiyar \u0199awarta a zahir, tana kuma neman zuciyar mijin \u0199awar tata a ba\u0257ini. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Mommy (Umman Khamis): Mahaifiya a wajen Khamis kenan, ita ce tauraruwar da ba a ba isasshen sarari ba a cikin labarin. Dukkan kalaman da ta furta a labarin suna nuna hikima, tsauri, da gaskiya wanda ba ta \u0253oye ba. Dubi wannan:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">*&#8221;Gashi da kanki kin ce ba ta da lafiya, kuma duk abin da kika yi mata kema lokaci zai zo da za ta yi miki, don haka kada ki sake cewa ma kin gaji.&#8221;* (Babi na tsakiyar labarin)<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Labari mai fa\u0257i irin wannan ya cancanci a \u0199ara wa irin wannan tauraruwar sarari da lokaci.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kurakurai<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Mutum tara yake bai cika goma ba. Kuma marubuciyar ta yi namijin \u0199o\u0199ari wajen rubuta wannan littafi, amma duk da haka akwai wasu kura-kurai da aka samu kamar haka:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Yawan Kalmomin Turanci a Cikin Tattaunawar Taurari: Wannan shi ne babban raunin da ya fi bayyana a cikin littafin. An yi amfani da kalmomin Turanci kamar &#8220;okay&#8221;, &#8220;baby&#8221;, &#8220;darling&#8221;, &#8220;fiance&#8221;, &#8220;bedroom&#8221;, &#8220;wardrobe&#8221;, &#8220;last chance&#8221;, &#8220;control&#8221; da sauransu da yawan gaske. Ko da yake yanayin taurarin, matasa ne na birni masu ilimi yana ba da dalili, yawan wa\u0257annan kalmomin ya rage \u0199arfin isar da sa\u0199o ga duk masu karatu, musamman wa\u0257anda ba su saba da Turanci ba. Hausa mai \u0199arfi tana iya isar da kowanne yanayin rayuwar zamani ba tare da bu\u0199atar aro daga wani harshe ba. Yahaya da sauransu (1992) sun yi bayani a sarari kan muhimmancin tsarkin harshe wajen sarrafa rubutu mai inganci.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Wasu Sa\u0253anin Bayani Tsakanin Babi-Babi: A wasu wuraren, abin da aka bayyana a wani babi ya sa\u0253a da yadda aka bayyana batun a babi na gaba. Wannan alama ce cewa ana bu\u0199atar duba da gyara (editing) mai zurfin gaske kafin wallafa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Fallasan Zuzee Ya Yi Sau\u0199in Fita: Ko da yake fallasan asirin Zuzee a matsayin &#8220;Aydah&#8221; yana \u0257aya daga cikin mafi kyawun lokutan labarin, yadda SP Ameer ya ganota ta hanyar bibiyar lambar waya ya zo da sauri maras isasshen fayyacewa. \u018aan \u0199arin bayani da ya kai ga wannan ganowa zai \u0199arfafa wannan lokaci mai muhimmanci a cikin  labarin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Jerin Nadamar Aisha Ya Yi Gaggawa: Duk labarin yana gudana ne hankali, hakan ya sa masa \u0257an\u0257ano mai da\u0257i, amma a \u0253angaren dawowa da gyaran Aisha sai aka tattara tuba da sauyawar hali a cikin &#8216;yan shafuka wa\u0257anda ba su yi daidai da girman nauyyin da ta \u0257auka ba. Domin mai karatu ya gaskata gyarawa ta gaske, dole ne a ba shi isasshen lokacin zai ga canji yana faruwa a hankali-hankali.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u2022 Code-Switching a Lokutan Rikici: Musamman a lokutan da ake cikin zafin rikici, kamar lokacin tonon asirin Zuzee a gaban jama&#8217;a, shigo da kalmomin Turanci yana ragewa \u0257arsau dmotsin rai da ya dace ya kasance cikakke a wannan mawuyacin halin.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Abin Yabawa<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko da yake na san cewa akwai wuraren da ke bu\u0199atar gyara, zan iya fa\u0257i da zuciya \u0257aya cewa *Kishiyar Katsina* labari ne da ke \u0257aukaka adabin Hausa zuwa wani matakin da ya cancanci yabawa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Da farko, halayyar Aisha ya sha bambam da yawancin &#8220;uwargidoji&#8221; da ake nuna su a labaran soyayya na Hausa. Maimakon ta zama tauraruwa mai muni gaba \u0257aya wadda mai karatu ke \u0199yamarta tun daga babin farko, tana da halayyar \u0257an&#8217;adam ta gaskiya, tana \u0199aunar Khamis, tana \u0199aunar yaranta, tana fama da kishi kamar yadda kowace mace za ta iya fama. Laifinta kawai shi ne ba wannan kishi damar cin galaba akanta. Kamar yadda Furniss (1996) ya lura a nazarinsa kan labaran Hausa, taurarin da ke \u0257auke da nauyin mutuntaka su ne suka fi da\u0257a\u0257a a rayuwar masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na biyu, yadda labarin ya nuna a sarari cewa asiri ba waraka ba ne , ya yi babban hani cikin hikima. Masu tsoratar da wasu da auren kishiyar Katsina ko na wani wuri daban saboda za su yi musu asiri sukan ci amanar mazajen da ke son su da gaske saboda tsoron wani abu da ba lallai ya zama gaskiya ba. <\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na uku, zan \u0199ara yaba mata, musamman yadda marubuciyar ta zana ala\u0199ar Maryam da yaran Aisha, Haneef da Haneefa. Wannan \u0253angare ne wanda ya fi ta\u0253a ni a cikin dukkan labarin. Mace mai \u0199aunar yaran kishiyarta kamar nata, kuma ba don cimma wani burin waje ba, sai don halayyar ta, ita ce mafi ingancin tabbatarwar jigon labarin. <\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Shawarwari<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ina ba marubuciyar wa\u0257annan shawarwari:<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na farko**, ta rage amfani da Turanci a cikin tattaunawar taurari. Hausa mai \u0199arfi da tsarki tana iya isar da kowanne yanayin rayuwar zamani. Yahaya da \u018aangambo (1986) sun nuna a sarari cewa tsarkin amfani da harshe shi ne ginin adabin da zai da\u0257e.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na biyu, ta ba jerin nadamar Aisha isasshen sararin labari domin mai karatu ya gaskata sauyawar hali ba tare da ya ji kamar an hanzarta ya \u0199arewa ba.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na uku, ta yi tacewa mai zurfi kafin wallafa kowanne labari a nan gaba, gano sa\u0253anin bayani tsakanin babi-babi abu ne da ake iya kauce masa da kyau kafin a tura aiki ga jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Na hu\u0257u, ta ci gaba da rubutu. Basirar da ta nuna a wannan littafi ta fi yadda za a bata a lokaci \u0257aya. Kuma adabin Hausa yana bu\u0199atarsa.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Kammalawa<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ban tsammanin wanda ya karanta *Kishiyar Katsina* zai iya cewa bai \u0257auki komai daga ciki ba. Labarin ya koyar da darussa da yawa, darasin aminci, darasin abota, darasin kissa, darasin nadama, amma ya koyar da su ta hanyar labari, ba ta hanyar wa&#8217;azi ba. Kuma wannan shi ne bambancin da ke tsakanin littafi na gaskiya da takarda ta nasiha kawai.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ko ki tsani Aisha ko ki \u0199aunace ta, ko ki so Maryam ko ki ji wani \u0253angare na kishi a ranki game da ta, duk labarin dai ya ri\u0199e ki. Wannan ne alamar labari mai tasiri.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hadiza Isyaku ta nuna a Kishiyar Katsina cewa tana da gagarumar ikon gina labari wanda ke ta\u0253a zuciya tare da koyar da darasi. Ina ro\u0199on Allah ya \u0199ara mata ilimi da basira, kuma ina fatan litattafanta na gaba su ci gaba da ha\u0253aka daga wannan tushe mai \u0199arfi da ta riga ta gina.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kuna iya karanta littafin Kishiyar Katsina a Bakandamiya Hikaya.<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">Manazarta<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u018aangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">\u018aangambo, A. (1990) Gadon Fe\u0257e Adabin Hausa (Ba a Buga ba). Kano<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Furniss, G. (1996) Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. Edinburgh: Edinburgh University Press<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Galadanci, M. K. M. (1976) An Introduction to Hausa Grammar. Lagos: Longman Nigeria Limited<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gusau, S. M. (2009) Mawa\u0199a da Mawa\u0199arsu a \u0198asar Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Junaidu, I. da &#8216;Yar&#8217;Aduwa, T. M. (2002) Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Newman, P. (2000) The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. New Haven: Yale University Press<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Skinner, N. (1980) An Anthology of Hausa Literature. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Umar, M. B. (1984) Dangantakar Adabin Baka da Al&#8217;adun Gargajiya na Hausa. Kano: Triumph Publishing Company<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yahaya, I. Y. da \u018aangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Yahaya, I. Y., Zaria, M. S., Gusau, M. S. da &#8216;Yar&#8217;Aduwa, T. M. (1992) Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press Plc<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Zarru\u0199, R. M., Kafin Hausa, A. A. da Alhassan, B. S. Y. (1987) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don \u0198ananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. Ibadan: University Press Plc<\/p>\n\n\n\n<h2 class=\"wp-block-heading\">A Karshe<\/h2>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ina mai jinjinawa marubucin wannan labari game da tunaninsa, da \u0199o\u0199arinsa na isar da sa\u0199on hannunka mai sanda ga masu karatu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Allah Ya \u0199ara basira da \u0257aukaka. Amin<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u2022 Sunan Littafi: Kishiyar Katsina \u2022 Sunan Marubuciya: Hadiza Isyaku \u2022 Inda Aka Buga Littafi: Bakandamiya Hikaya \u2022 Shekarar Bugu: 2023 \u2022 Nau&#8217;in Labari: Soyayya\/Zamantakewar Aure \u2022 Yawan Babi: 21 \u2022 Mai Sharhi: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees) \u2022 Manufar Sharhi: Bun\u0199asa Harshen Hausa da ciyar da adabi gaba Gabatarwa Hausawa kan ce &#8216;kishi kumallon mata&#8217;,&hellip;&nbsp;<\/p>\n<div class=\"read-more-wrapper\"><a href=\"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/sharhin-littafin-kishiyar-katsina-na-hadiza-isyaku\/\" class=\"button button-secondary\" rel=\"bookmark\">Read More &raquo;<span class=\"screen-reader-text\">Sharhin Littafin &#8216;Kishiyar Katsina&#8217; na Hadiza Isyaku<\/span><\/a><\/div>\n","protected":false},"author":6,"featured_media":4859,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"neve_meta_sidebar":"","neve_meta_container":"","neve_meta_enable_content_width":"","neve_meta_content_width":0,"neve_meta_title_alignment":"","neve_meta_author_avatar":"","neve_post_elements_order":"","neve_meta_disable_header":"","neve_meta_disable_footer":"","neve_meta_disable_title":"","neve_meta_reading_time":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[119,104,28,58],"tags":[29,181,180,41],"class_list":["post-4857","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-analysis","category-book-matters","category-book-reviews","category-hausa","tag-book-review","tag-hausa-novel","tag-kishiyar-katsina","tag-sharhin-littafi"],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/efd8kbkoisy.exactdn.com\/blog\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/Sharhin-littafi-.jpg?strip=all","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4857","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/users\/6"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4857"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4857\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4860,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4857\/revisions\/4860"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4859"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4857"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4857"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/hikaya.bakandamiya.com\/blog\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4857"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}