Skip to content
Part 2 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ni ma na bita. Tana mamutse da ita suka shiga ɗakin, murna yaya Azima take sosai.
Ita kuma ta faɗa kan Innarmu tana kuka. Mutanen gidan ma kan ka ce me, sun cika ɗakin.

Sai da aka natsa kowa ya kama gabansa sai mu kaɗai. Labari ake ta bata na bayan bata,
zuwa can sai ta zura min ido, “Wai Shuhainar Inna ce ta zama haka?”
Jawo ni ta yi, “Ba ki gane ni ba ko?

Na ce, “Da dai a hanya na haɗu da ke zan rinƙa tunanin ina na san ki, dan ko hotunanki da ke akwai ba haka kike ba.” Ƴar dariya ta yi.
Ni kuma mamakin irin kyan da ta ƙara nake, duk da dai dama mutane suna cewa ba me kyanta a ɗakinmu, gata doguwa ce ita, kuma bata da jiki, amma tsananin jin dadi yasa fatarta ta murje ta yi lukwi-lukwi. Kyan fuskarta kuwa ya isa. A ɗakin da Yusuf kaɗai na ga take kama, dan dai shi ba fari ba ne. Ita kuwa kalar jikinta wani yallow yallow ta koma dan tsananin kyan da tayi. Dakinmu kuwa tunda ta shigo tamkar kana a cikin birnin Paris tushen turaren saboda tsabar kamshin da yake.
Wani ƙanƙararren less ne jikinta wanda kallo ɗaya kai masa ya wadatar da kai gane ba na me ƙaramin karfi ba ne.

Yaya Azima ta dubi Yusuf, “Amma dai ɗan Ƙanina tafiyar nan ba yau ba ko?
Ya murmusa, “Ga fa sister ta iso wane tafiya, sai dai kuma lokaci yana kurewa.”
Amina ta nemi jin inda za su. Aka faɗa mata.
Ta ce, “Jiya bayan mun isa Kaduna, na tsaya na saya mata kayan daki.”
Yusuf ya ce, “Kaduna kuka sauka?
Ta girgiza kai, “Abuja muka sauka.” Mun samu mahaifinshi ya gyara ma shi ɗaya daga cikin gidajen shi.

Kwananmu biyu, jiya muka isa Kaduna ya ga wani dan uwan shi, ni kuma sai nayi sayayyar, anjima kaɗan kayan za su iso, har da kayan kitchen da na saya mata a Dubai. Dan sai da muka biya ta can, har da su kafet su zannuwan gado da labulayya duk an yi sayayyar su.
Yaya Azima ta ɗaga hannu sama Allah kai ne Almusawwiru Mun gode maka bisa ga wannan rufin asiri da kayi mana Allah ka ƙara rufa mana.
Innarmu kuwa sai dai muka ga ta faɗi tayi sujjada, kafin ta ɗago tayi ta sa mana
albarka.Ta dubi Anty Amina, “An tsinke da labari ba’a tanbaye ki mijin naki ba.”
Gyara zama tayi, “Tare muke sai dai ya ce ba zai shigo yanzu ba, wai yanda nake ɗokin nan suma mutanen gidan suna ɗokin ganina, sai dai idan sun dawo gidan abokin shi da muka zo tare.”
Abokin nasa ɗan katsina ne, sunan shi Abdullahi.”
Innarmu ta ce, “Na gane shi.”

Daidai nan amarya ummu ta shigo da gudu, sai wurga ido take inda za ta ga Aminan
A guje ta faɗa mata Innarmu ta rike haɓa, “Ke kam yau sai jikin ki ya yi ciwo.” Muka yi dariya.

Amina ta ce, “Yayanmu Ina yaran ki? Na san kin tara su da yawa, wai Yusuf ya ce min uku ne.” Ummu ta yi karaf ta ce, “Haka ne, Khadija ce babba mai sunan mahaifiyarsa,
sai Yakub, sai na bayanta Khalid.” Ta karbe shi a hannuna tana ma shi wasa
“Anjima Salma ta dauko min su in gan su, amma na sha sun kai hudu.”

Azima ta ce, “Haba dai sai ka ce duk shekara ake haihuwar duka auren shekaru shida ke ba ga shi ko daya ba ki haiho mana kin taho mana da shi ba.”
Murmushi ta yi, “Karatu na ke, amma na yi ta ɓari.”
Ummu ta ce, “Amma ba yanzu za ku koma ba ko?”
“Mun dawo kenan ai mun sha Turai.”
Ta kamo hannuna, “Me za ki dafa mana da rana? Na san innarmu indai tana da budurwa to ta kan horar da ita aikin gida.”

Na dubi Yusuf, “Ga mai gidan nan, bai riga ya bada kuɗaɗen cefanen ba.”
Tana ɗan murmushi ta dube shi, “Ran maigida ya daɗe, me za’a yi mana ne”?
Yana ƴar dariya ya ce, “Ai baƙin ne sun fi ƙarfin aljihuna,”
Yanda ya yi maganar shi ya ba kowa dariya. Jakarta ta hannu ta jawo,
Bandir ne na yan ɗari biyu wanda ban yi tunanin an zari wasu masu yawa ba ta miƙa masa, “Ayo mana cefane.”
Ya karba yana, “Yawwa ko ke fa.”

Na mika hannu, “To bani tunda dama kowa ya san ni kake ba in lissafa sai in sawo.”
Tsaye ya mike, “A’a wannan ya fi ƙarfin ki, da kaina zan sawo.”
Yayammu ta murmusa, “Yusuf ho indai kudi ne.”
Bai saurari komai ba ya fice.

“Anty Amina ta ci gaba da tanbayar abinda za’a buƙata na fannin bikin yayarmu na gaya mata.

Sha ɗaya Yusuf har ya kawo mun dora. Ni da ummu dan har zabi ya sawo, muka shirya ma baƙi lafiyayyar miya.

Zuwa sha biyu kayan amarya suka iso, dama tun kan isowarsu, an gaya wa mutanen gidan su shirya.

A Area za su zauna mijin ma’aikaci ne. Kaf mutanen gidan sun tafi, Yayanmu ma ta tafi, sai yara, mun gama girki, muka dauko kulolin ummu da take tarawa, muka zazzuba abincin mijin Anty Amina da abokin shi. Muna sallar azahar, muka ji sallamarsu. Amina ce a falon dan ta idar, Innar mu ta fara fita suka gaisa, tayi waje. kamar jira yake ta fita, sai cewa ya yi, “Ke kuma fa lafiya kike kwance kasa? Tace, ” sanyin kasan daɗi yake min.”

Yace” Tohm ban yarda ba tashi.” ta tashi, ta shirya masu abincin a gaban su, abokin shi na mata tsiya, wai har yanzu gajiyar ce bata wartsake ba. Suna fira Ummu ta fara fita ta gaishe su, tayi waje.

Ni ma ban tsaya cire hijabin ba, na fito na gaishe su, na fita. Ina mamakin kyau na mijin Anty Amina.
Dogo ne fari, dirarren namiji mai cikar halitta, ga sajen shi wani irin dogon hanci gare shi da wasu kyawawan idanuwa masu jan hankali, farin yadi yasa bashi da nauyi sosai da farar hular da su kai matuƙar tona asirin kyansa.
Da na fito na ce ma innarmu bari in je in ce ma kawata Hafsat ta kusa da gidanmu, ba zan samu zuwa makaranta da yamma ba.

Inna ta ce, “Anya Shuhaina, ba fa kije da safe ba, yanzun ma ki ce ba za ki ba?” Nace, “Kin san dai innarmu bana fashi, Allah ban gaji da ganin aunty Amina ba.”
Na fice.

Da yamma bayan yaya Azima ta dawo. Amina ta umarce ni in ta jawo jakunkunan da ta zo dasu, nayi kamar yanda ta ce. Jakar farko amsa sunan innarmu, dan haka ita ta aje mawa. Sai taba Azima tata daya, ta yaranta daya. Sai ummu wadda Yusuf ya ce, “Kawai kin kama sawo ma wannan yarinyar kaya, ba ki ga akwatunan da aka dankaro mata bane?”

Ta ce, “Nasa daban, nawa daban, matsayin shi daban, na wa daban.”
Ummu ta fara masa gwalo, ya ce, “Allah zan make ki.”
Innarmu ta ce, “Ka rufa min asiri, ke kuma ki bari.” Ta ce “To.”

Shima Jaka guda aka ba shi wadda ya ja ta zai waje da ita. Azima ta riƙe. Ta ce, “Allah yadda kaga na kowa, sai an ga naka.”

Dolensa ya bude, yadiddika ne na maza masu matuƙar kya da tsada, sai shaddodi da takalma da agoguna har da su turare. Salma ma Jakarta daban, aka ba innarmu, jakar innarmu atomfofi ne masu asalin tsada hada mai golding da kuma lesussuka da hijabai
da takalma flat, haka na Azima. Na ummu kayan barci ne dasu turaren wuta.
Nawa riguna ne dogaye da kuma riga da sket da takalma da hijabai (jilbab), ta dube ni. “Yusuf yace min ba ki sa gyale.” Na gyada kai, Yusuf ya ce, “Ai kin daɓa a ƙas! Wannan da ki ke gani, ya nunani da hannu, “Da ni kika ba su da sunyi min rana,
dan kalarsu zan nema.”

Amma kin ga wannan yadda kika ganta haka da hijabin nan, to kullum a haka take.”
Azima Ta ce, “Allah dai wadaran babban kwabo.” Yusuf dai sai ya ja jakar shi ya yi waje.

Ta cire sarƙa da dan-kunnen dake jikinta. Ta miƙa wa Yayanmu, dan tun zuwan ta Yayanmu ta yaba kyansu. Saura jakunkuna uku, ta tura ma innarmu,
“Ga shi nan abinda ya kama mutanen gidan nan zuwa abokan arzikinki ki ba kowa,
na hajiya ma suna nan ciki.”

Nan muka yi ta godiya. Innarmu wadda tunda aka fara buɗe kayan take kame da baki,
ta ce, “Hala dai tun randa ku ka sauka garin, kika fara sayen waɗannan uban kaya?
tayi ƴar dariya, “Haba dai na jima tukuna.”
Ummu ta ce, “Uhm!”

Anty Amina ta ta dube ta,  “Yi maganarki.”

“Ta ce naga kin ba Yayanmu takalma da agogo da turare, kince na Babansu Khaleed ne, shi ne… Sai kuma ta ƙara shiru.

Ta ce, “Da kin je direct!
Yusuf ya harare ta, “Mara kunya, ita nufin ta ba’a ba nata mijin ba.” Ai kuwa a guje ta bar dakin. Da daddare sallar isha’i kawai nayi na hau gado. Aunty Amina ta ce, “Ba dai barci za kiyi ba?”

Na ce “Hutawa zanyi, idan kuma barcin ya zo tom duk daya.”
Ta ce, “Ke baki da saurayi ne?”

Ummu da ke ta kwalliyar tafiya wajen angonta, ta taɓe baki, “Wannan, ai ta dai yi aikin gida, amma duk wanda ya zo, ya ma gaji ya kama kansa, bata sauraron kowa.
innarmu tana ganin ta fara kuka, idan aka aiko kiranta,
za ta ce a rabu da ita akwai sauran time.”
Amina ta yi ‘yar dariya, kuma ta fice.

Innarmu tana tsakar gida inda mutanen gidan ke shan iska. Aminar ma ta fita tsakar gida, shigowar ta naji tana magana.

“Ina ka bar Abdullahin?”
Ya ce, “Zan zo wajen matata kuma sai na ɗakko shi?” Daidai yana zama wata carpet data shimfida masa,
ta ce, “Amma dai gari ya gari ka dauko shi?”

Ya ce, “kin manta jihar shi ce nan, yanzu haka ya isa Katsina.”
Ta ce, “Ka hana in maka girki, to me kaci? Ledar dake hannunsa ya miƙa mata. “Cire wa su mama leda guda, ki aje mana guda.” Suna ci tana jan shi da fira,
wanda dama magana bata dame shi ba, ban san lokacin da suka tashi ba
na dai farka naga innarmu da Amina suna ta fira, ba alamar barci,
Aunty ummu ce kusa da ni, itama barcin take.

Da asuba tunda na yi sallah na kwanta, ina karanta addu’oi’n da ke cikin Hisnul Muslim, sai da 7:00 tayi, na dora koko. Yusuf ya kawo kosai enough har da bread.

Innarmu ce ta dubi Amina data shigo lokacin tayo brush, ta ce, “Zaki iya shan kokon kuwa?” Dan murmushi ta yi, “Ka ji innarmu, ke ki ka sha, ‘yan’uwana suka sha, sai ni ce ba zan iya ba, Shuhaina zubo min.”

Na ce, “To.”

Sallamar da aka yi a bakin kofa ne ya samu saurarawa. Na san ba ni kadai na shiga mamaki ba, kuma ba sallamar na ke mamaki ba, me muryar, watau, Baba Ya’u,
kanin mahaifinmu wanda ke bi masa. Dan sanin da nayi masa baya hulda da mahaifiyarmu, tun auren su Azima daya kawo wani tsohon mai kudi, ta ce bata san shi, sai ya ce innarmu ke zuga ta, tun daga nan bai kuma sake bi takan mu ba,
balle abinda ya shafe mu. Wai tunda an nuna masa iyakar shi, alhali lokacin da babanmu ke raye, yana cikin wadanda suka fi kowa cin moriyar shi. Wai yau shi ne har dakinmu.
Fakare na yi, in ji da wadda ya zo. Bayan sun gama gaisawa da innarmu, muka gaishe shi.

“Ashe Amina kin zo?
Ta ce, “Eh Baba.”
Ya ce, “Ai jiya ban shigo gidan da wuri ba, don na je mani. Da na dawo kuma na tsaya hira a layin barankaci.”
Ta ce, “Mun same ku lafiya?”
“Lafiya kalau, ya mai gidan da iyayen shi?
“Ta ce “Duk suna Lafiya, tare ma muka zo.”
To to madallah, ai ladi ta bani tsaraba, har da ita dani da yara duka.
“Ta ce, “Ai ba komai Baba.”
Ta sa, ummu ta miko mata jakarta ta hannu, ta amsa ta zaro bandir ɗin ƴan dari biyu
ta miƙa ma baba, “Ga shi ba yawa baba, ayi cefane.”

Godiya ya shiga yi, har yana ƴar ƙwalla, wai ya tuna dan-uwan shi mahaifinmu.
Ni ko dariya nake a zuciyata, ina cewa, “kuɗi masu gidan rana, ba wuya sun ruɗa mutum. Allah ya dora mu kan kudi. Kowa san su yake kamar me.” Dan idan baka da su, sai kaga karan rogo ma ya fi ka amfani.
Sai na tuna wani malaminmu da ke mana karatun tauhidi a islamiya inda yake ce mana yana daga cikin hikimar Allah Ta’ala da ya turo kowane manzo zuwa ga mutanen sa da mu’ujiza ga abinda manzon ya zo da shi. Kuma mu’ujizar manzon
tayi dai-dai da abinda mutanen sa suke akai, dan mutanen su gaskata mu’ujizarsa.
Dan bijiro da imaninsu da cewa lallai wannan daga Allah Ta’ala yake. Kamar Annabi musa (A.S) mafi yawanci a zamaninsa sihiri ne, kuma suna gasgata masu sihiri. Sai Allah ya aiko shi da mu’ujizar data ruɗa duk masu sihiri. Kamar kuma Annabi Isa (A. S). Allah ya aiko shi ne a zamanin likitanci da ma’abota ilimin ɗabi’a, sai ya zo masu da mu’ujizar data dace da wannan, ya kasance yana warkar da makafi da kutare da tayar da matattu da izinin Allah. Amma manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W) an aiko shi a lokacin fasaha da balaga ta magana, sai ya zo masu da mu’ujiza dawwamamma, ita ce Al-kur’ani. Sai malamin namu ya ce, “Da ace a yanzu za’a sake turo Annabi, da me kudi za’a turo, dan mutanen yanzu ba abinda suka fi ganin kimar shi irin naira…

To haka dai Baba ya gama matse-matsen shi, ya tafi. Ni kuma na tashi na gyara dakin. Ummu ta kwashe wanke wanke za tayi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 1Canjin Bazata 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×