Skip to content
Part 22 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Bismillahir Rahmanir Rahim

Na kashe datar na ajiye wayar, na gyara kwanciya. Haj tuni tayi nisa cikin barcin ta. Babyn ba shi da rigima da zarar an mashi wanka to ya shiga barci kenan.  Hasken da na gani a wayata yasa ni ɗauko ta, saƙon Ahmad ya shigo zolayata yake in zo in taya shi kwana ni kaɗai yake jira, ɗan murmushi na yi na rufe wayar na ja bargo na rufe rabin jikina.

Da safe cikin nishad’i me yawa na tashi, saboda yau zan ga ƴan uwana a daki.  Isowar la’asar suka yi, motoci biyu suka zo.  Masu aikin girki aka ɗauka bayan haka Aunty Kubra da Khausar na tsaye kan kula da komai, an karramasu da abinci da na sha nau’i nau’i, ƴan garin su Ahmad su ma sun zo suna gidan su Ahmad.

Sai dare muka kebe da ƴan uwana suka bani abin da suka kawo min na amsa ina ta jin dadi, har da  yajin jego Innarmu ta dako min me dadi, suka ce Yusuf na min barka ya ce yana nan zuwa ganin yaron.  Mun raba dare muna hira.

Da safe yaro ya amsa sunansa Muhammad Khabir sunan yayan mahaifinsa. Ahmad ya shirya walima inda jama’a da dama suka halarta musamman abokansa da abokan aikin shi, aka ci aka sha sai aka tashi, zuwa goma na safe kamar ba a yi komai ba sai masu aiki da ke ta ƙoƙarin gyara wajen da aka bata.   Na fito cikin kwalliya, atamfa nasa wacce ta ji kayataccen ɗinkin da ya karbe ni, wuyana da kunnuwa da hannu ko ina sheki yake dan an kayatasu. Dakin mai gidan na nufa, a hankali na tura kofar cikin siririyar sallama ya amsa yana zaune a bakin gadonshi, da dogon wando a jikinshi na ainahin shaddar da yasa da safe, rigar na rataye sai singlet fara a jikinshi. Kallo ya bi ni da shi kafin ya mike ya ruko ni muka koma bisa gado ya dora ni saman kafafunshi ya zagayo da hannayenshi kan cikina ya dora kanshi kan kafadata, magana yake gaya min kamar me rada.

“A yau na kara godewa Allah bisa baiwar da yayi min ya bani ke, na so in yi wa kaina, amma Allah da ya soni da rahma sai ya bani iyaye nagari suka tsaya min ban rasa ki ba, yayi maki baiwa da sirruka wa’anda duk namijin da aka baiwa ke, sai dai ya nemi lahira dan duniya kam ta samu, kamun kanki na daga abinda ya kara jefani cikin mayen sanki, a yau an wayi gari kin haifa min da me zan maki ne in kara nuna irin san da nike maki?”

A hankali na ce, “Ka ci gaba da sona, dan nasan halinku maza baku da tabbas, masu dauka da ajewa ne, yau ke ce gobe kuka kyallo wata kin zama bola, idan aka wayi gari ka juya min baya, ban san irin halin da zan tsinci kaina ba. Da gama fadin haka sai na juyo na kankameshi dan idanuwana na ji za su fidda ruwa, shi kuma dama me kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ai sai kawai na tsinci kaina tsakiyar gadon, nan fa idon me jego ya raina fata, na shiga rokonshi da magiyar ya kyale ni, sai da na kwaci kaina na koma gefe guda ina kallonshi.

Rigingine ya yi ya tada kanshi da hannayenshi shima kallona yake ya ce “Ba ki san wani abu da aka yi gabana ba, na ziyarci wani abokina Dr Mu’azu a Kano, ina tare da shi a office dinshi, yana duba marasa lafiya, wasu mata da miji suka shigo da yaronsu jariri, result din da suka karbo na gwajin jini suka kawo ya duba ya rubuta masu magunguna hada waanda za su ba jaririnsu, mijin ya nemi sanin meye lalurar matarshi, likitan ya ce Juna biyu ne da ita na kimanin watanni uku, sai matar ta fasa kuka likita na ta magana amma yin shirunta ya gagara da kyar ta ce yaronta ma watan shi uku, ita yanzu ta bani idan maganar cikin ta fito a kauyensu, daga karshe dai mijin wanda yayi zugum kamar ruwa ya ci shi ya ce ‘Shi wallahi ranar suna ne tayi kwalliya (kinsan mutanen kauye ba wai kwalliya ta dame su bane, sai dai ayi ta zama haka, to wannan kwalliya ita ta dauke shi suka aikata abinda suka yi har rabo ya shiga mutanen sun zo ne daga wani kauyen jihar Kano.”

Gyaɗa kai nayi na ce Allah ya kyauta, ni kam nan da wasu shekaru ma ban fatar shi.” Zaune ya tashi ya ce, “Me kika ce?. Ai kam cikin sauri na nufi kofa dan na lura so yake ya kuma cafkoni, na koma dakina na samu ana nemana baby ya tashi. Haka na wuni cikin jama’a yan suna, wasu da yawa ma a ranar na soma ganinsu, na samu alheri me yawa daga kudi zuwa kaya abun ba magana.

Mutanen gidanmu washegarin suna suka koma amma yayarmu da Ummu sun kara min kwana biyu su kwana hudu suka yi, na sallame su da shatara ta arziki. 

Khausar ta dawo wanda ni na nemi ta dawo, muka hada uban kayan da na samu ta bani shawarar rage kayan dan sun yi yawa, kuma tana so ta fada min ko zamu hada hannu mu jaraba saro kaya sai mu bude shago, mu nemi wanda zai zauna mana. Na ce “To zan shawarci Ahmad amma sai an kwana biyu. ta ce “Hakan ma yana da kyau dan gaugawa daga shedan take.”

Farhan na kira na ba shi kudaden da na samu ya kai min banki. Na ci gaba da wanka da kula da junior kamar yanda ilahirin family babansa suke kiran shi, kafin arbain mun yi bulbul gwanin ban sha’awa, sannan Haj ta fara maganar ita fa in gayawa me gidan tana son komawa gida, na ce “Kai Haj ni na sha zamammu za mu yi ki taya ni zama” kallona tayi sosai “E lallai ke naki rashin hankalin babba ne, zaman auren zan taya ki? ai da ni da ke sai a rasa wa yafi rashin hankali.” Na marairaice “Allah har fargabar ranar da za ki tafi nake.” ta ce “Allah ko? to dama kin daina dan ina ganin nayi abinda ya kawo ni, zaman me zan yi in ta takurawa yaro” Jin zancenta sai nayi shiru illa dai na fada mashi.

Sati ta kara bayan nan har muka je gidansu Momi muka yi musu wuni.  Ranar da za ta wuce bani ba ma, Ahmad ma alheri me yawa ya mata yasa direba ya mayar da ita gida, mun yi kewarta sosai ni da Baba Kulu. Sai da nayi sallar la’asar na shiga kitchen, Ma’u na gefe tana taimaka min, kafin in haihu na maigidan kawai nake yi, Ma’u da Baba su yi na gida duka, yau sai na hada nayi duk gaba daya, na kuma dage nayi nau’i nau’i masu gamsarwa. Baba ta karaso kitchen din tana cewa “Hala me jego yau ta shiga kitchen? ina daga zaune nake ta jin gidan ya kauraye da kamshi. dan murmushi na yi ta samu wuri ta zauna muna hira ina aikina, sai da na kammala na bar Ma’u tana gyara wurin.

Daki na koma na sheka kwalliya cikin wani yadi me two color riga da wando rigar karama ce dai dai jikina, ina son mu’amala da kananan dinki matsatstsu dan na lura ba kadan ba suke dauke hankalin me gidan. Na fito cikin daddadan kamshin da ko’ina na jikina ke fitarwa, inda nake jin maganar Ma’u Junior ta kawo min, dan tun yamma yake bayan baba ta goya shi, na karbe shi muka nufi falon da ya raba wurina da na Ahmad, na kwantar da shi dan barci yake, Remote na dauka na kunna TV ina kallo sama sama ina tunanin abinda ya hana Ahmad dawowa har lokacin dan da ya sallami Haj Niger state ya wuce, kuma ya ce min in sha Allah zuwa magrib ya shigo, ban gama tunanin ba na ji sallamar shi cikin natsatstsiyar muryarshi, na mike ina amsawa yana sabe da Junior muka nufi wurin shi , sai da yayi wanka na gabatar mashi da abinci ya ce “Ba zan hau tebur din nan ba,  kawo min nan kawai. Na shimfida ledar cin abinci kafin na jera mashi, na zuba mashi nima na zuba muna ci yana kallona, maganar da na ji ya yi ta sa ni dago ido ina duban shi.

“Wata yarinya tana son kasancewa da mijinta ta ma tsohuwa wayau ta koreta.” Baki bude na ci gaba da kallon shi “Abin da  za ka ce min kenan? Shi kenan ni da kai za a ga wanda ya matsu.” Murmushi ya yi ya mike da junior a kafadarsa dan ya kammala,  ni ma na kwashe komai sai na bi bayan shi . Yaron yake kallo dan ya bude idanu, na karbe shi nasa mashi nono sai da ya koshi ya karbe shi ya kwantar bisa gadonsa, ya dawo kusa da ni magana yake rada min, wadda ta sa ni runtse idona, halin da na ga ya shiga yasa na yi amfani da hakan na roke shi abin da na so tuntuni nake kuma tunanin sanar da shi cikin sanyin murya na ce “Dan Allah so nake ka bar ni in ci gaba da karatu.”

Bai tanka min ba ci gaba ya yi da abin da yake yi, shudewar lokaci ya tsallake ni zuwa bathroom sanda ya fito har barci ya fara daukata, hada ni ya yi da jikinsa  sai ya rufe mu. “Me na ji dazu kina cewa? faduwar gaba na ji ta same ni da kyar na maimaita mashi abin da na ce ajiyar zuciya ya yi “Ba zan iya ba Shuhaina, ban taba kishin wani abu a rayuwata yanda nake kishinki, ke wata aba ce me daraja a wurina, ba zan taba nutsuwa ba duk da ba wai ban yarda da ke ba ne, na san na so Amina amma ban taba jin irin kishin da nake maki a kanta ba, in kina san jari zan ba ki amma makarantar nan a hakura. jin haka sai nayi amfani da damar na fada mashi yanda muka yi da Khausar ya ce “Ba matsala, amma ni kam ba inda za ki wani yawon kasuwanci, idan za ta rika zuwa maku ko za ku nemi me maku duk daya.”

Na yi mashi godiya. Da asuba da nayi sallah komawa nayi na kwanta saboda yanda nake cikin gajiya, sai da na farka na lalubi Junior na ga wayam na san baban shi ne ya dauke shi, dakina na koma nayi wanka na fito cikin less baki da akayi wa ado da flower ruwan goro sai aka ratsa fararen duwatsu. Ahmad na samu zaune yana duba wasu takardu, gaban shi na zauna na ce, “Ina kwana?” “Ya gajiya? ya ce yana duban cikin idona, na sunkuyar da kaina “Ina junior? ya ce “Na kai shi wurin Baba, tuni ta mashi wanka ta goya shi.”

Dafe goshi nayi “Shi kenan sai ta san abinda kenan, ni yanda ma zan hada ido da ita nake tunani.” Kada kafadunshi ya yi “So what dan ta san abinda akayi, ai ko ita shaida ce kan hakurin da na yi, infact fa an yi two month, sai dai idan an dan saci jiki a dan yi min yan dabaru ana min korafin kada su Haj su gane.” Na ce “Dama office ka tashi ka tafi kar kayi latti patient na can na jiranka.”

Kallo ya bi ni da shi “Ai yau ba inda zan fita, ko kin manta ango nake, yau?   Ai ke ce likitar, in ba gama duba ni ki ka yi ba ba inda zan iya zuwa.” Ban samu amsar ba shi ba muka ji sallama, Ma’u ce Junior ta kawo na tashi na fita na amso shi ta ce Baba ta ce a ba shi nono sai a dawo da shi na koma falon na zauna ina ba shi nono, Ahmad ya ce “Idan kin gama da Junior ina jiranki.” Ya tashi ya shiga ciki. Sai bayan fitar shi na kira Khausar na fada mata yanda muka yi da Ahmad, ta ce, “Maganar ba ta waya ba ce kamata ya yi mu samu lokaci mu hadu, kodayake ba ma ki zo min yawon arba’in ba.”

Na ce “Ki yi hakuri kinsan ogan wai amarci muke, ko zan fita sai mun gama.” Shewa ta yi, “Yana da kyau hakan.” Na ce “Amma daga gidanki ne nasan ba zai hana zan yi kokarin fitowa sai muyi maganar. Da na tambayeshi bai hana ba kamar yanda nayi zato, shi yama sauke ni da zai wuce wurin aiki, bayan mun tsaya ya sayawa Al’amin kayan wasa da carton na madarar da yake sha, mun sameta zaune, Al’amin na wasa a cikin kekenshi na dauke shi kamar yanda ta karbi Junior tana fadin irin girman da ta ga ya yi mata, na zauna ina tambayar Abdullahi. Tace ya yi tafiya zuwa Calabar.

Mun taba hira  har muka gangaro kan maganar da ta kawo ni. Ta ce akwai wani yaron gidansu tun yana karami yake wa mamanta aike almajiranci aka kawo shi daga wani kauyen Kano, ya zama dan gida a gidanmu ba ki ganin shi ma yanzu ki ce ba dan gidan bane yana da amana ko sare saren Momina da yawan lokaci shi ta kan aika, to shi nake so musa ke kuma daga bangarenki sai ki samo mutum daya sai mu hada su, shi Idris yasan hanya ya kuma san takan komai, me kike gani ya kamata mu sa? Na dan yi tunani na ce “Ina ga mu sa kayan mata zasu fi karbuwa.”

Ta ce “Allah ya shige mana gaba.” Ta wuce kitchen ta dubo girki ta dawo ta zauna “Ke ban fesa maki ba”. Na ce “Ina jinki” ta ce “Ashe wannan kanwar mijin taki yar rainin wayo da kika ce kin rasa ubanda kika kashe mata ta raina maki kura ashe budurwar Ahmad Zubaida kawarta ce.” Tabe baki na yi. “Ke wa ya gaya maki? ta ce “Shi yanzu nake son ba ki labari na ce Ina jinki dama sunanta Zubaida? daga kai ta yi. “Babbar yarinyar Aunty Zahra sun je bikin wata course mate dinta ita take bani labari a wurin dinner sun zauna kusa da wasu kawaye biyu firar da suka ji suna yi yasa su saurarensu, dayar tana fadin shawarar da ta yanke na rabuwa da Ahmad Tafida, kawar ta ce Ahmad Sulaiman Ahmad Tafida kika samu za ki yi wasarere har damar da kika samu ta subuce, gayan fa ya hadu karshe sosai yake burgeni ina maki kwadayin samun sa dan akwai aji ita kuma marairaicewa ta yi.

“Banda yanda zan yi ne, duk wata dabarata ta kare in ma na ci gaba da nacin bin shi sai dai in ta yaudarar kaina, dan farkon dawowarshi bayan rasuwar matar shi sosai yake saurarona, har ma ya ce in ba shi lokaci zai aure ni idan ya kammala ginin gidan da ya fara, duk da na razana da jin auren shi da kanwar matar ta shi, ya ce min kar wannan ya daman, Rufaida kuma ta ce min bai san yarinyar cusa mashi ita aka yi, kuma na yarda dan na je wajenshi muna tare a office dinshi abokinshi ya kawota bata da lafiya a gabana ya wulakantata sai na biyu a sunan Rufaida nan ma ina zaune ta kira shi ya zo ya tafi da ita nan take ya yi halin nashi, na samu kwanciyar hankali a wannan lokacin ina ganin na ma samu Ahmad na gama, duk da zuciyata na tuno min yarinyar natural kyau ne da ita duk hassada banga inda za a kusheta ba, ina ganin wata rana za ta shawo kansa daga mace take tana kuma da abinda ake so, amma Rufaida take danneni “Wai wannan gajar yar talakawa ce fa ta daina bani tsoro, to kwanaki mun kuma haduwa a office dinshi kin san me na gani? Da tsohon ciki na gan ta, kuma kallonmu kawai ta yi ta juya tunda ta fita kuma hankalin shi ya bar kaina, bai samu sukuni ba sai da ya tashi ya bar asibitin, tun daga ranar bai kuma bi ta kaina ba wai ni na yi fushi ban sake neman shi ba, to ko ta waya bai nemeni ba.

Sumayya ta ce suna zuwa nan ko sun fahimci muna sauraronsu sai suka tashi suka bar wurin. “Tabe baki na kuma yi “Hala recording ta yo maki? Yar karamar dariya ta yi “Dadina da ke kishinki baya buya” na ce “Ai ni wannan Rufaidar matsala za ta zame min matukar Ahmad na tare da wannan.” Ta ce “Ai ba ki bari na kai maki karshe ba dear na ke gaya min Dr ya ce zuwan da kika yi kika same su ba karamin taimako ya yi mashi ba, dan dama neman hanyar rabuwa da ita cikin salama yake baya san su yi rabuwar baran baran dan saboda kaunar da ta nuna mashi baya san wulakantata.” Ajiyar zuciya na fidda sannan muka ci gaba da maida zancen, wuni zungur muka yi mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 21Canjin Bazata 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×