Skip to content
Part 21 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Bismillahir Rahmanir Rahim

Na koma wurin Haj na zauna muna gaisawa, ina tambayarta mutanen gida.  Na ce “Sam bai faɗa min zai ɗauko min ke ba hasalima ba muyi da shi zai biya Malumfashi ba.” Ta ce “Kuma kwanaki ya je garin sai ya yi wa uwar taku maganar zai zo ya tafi da ni dan in kula da ke, sosai Rakiya ta so zuwa tunda ta ji zancan, uwar ta ku kuma ta ce in barta ta zo duk da ta san zaki fi jin dadin ganina kusa da ke, to jiya ya biya ya ce idan ya dawo yau zamu wuto, to an yi rashin sa’a Rakiya tun jiya ta tafi Kankara gaisuwar ƴar aminiyarta da ta rasu sai yau din za su dawo.

Yar dariya na yi “Wai ki ce mita na can yau idan Gwoggo ta dawo.” Muna ta labarummu har dare, sai na kaita dakin da za ta zauna dan ta samu ta kwanta ta huta. Kwarai na ji dadin zuwanta, ko ta ina ji da ni ake ga ta ga Baba Kulu, Momi ma kullun sai ta yi waya ta kan zo daga lokaci zuwa lokaci ballantana kuma ogan da ban san yanda zan misalta kular da ya ke bani ba, ya kan gaya min rasa yanda zan yi da ke nake Shuhaina idan na tuna kin taba dawainiyar ciki wanda nawa ne ni ke da shi ke kadai ba tare da na taimaka maki ba.

Wata safiyar talata na tashi da ciwon kai tunanina zai bari dan haka ban shaida wa ogan ba har ya fita da kyar na daure nayi wanka na ji bai bari ba, sai na kira Dr sa’a ta ce in hanzarta in zo dan tana cikin aiki ne da sai ta zo gidan. Na ce bari in nemo Dr a waya ta ce bai shaida maki zai shiga meeting ba? na ce “Na manta gani nan zuwa ” Na fada masu Haj zan tafi asibiti har suna hada baki ita da baba kulu wajen tanbayata lafiya na ce “Ba komai kaina kawai ke ciwo” Haj ta ce “Ko in zo muje tare” na ce A’a zan je ni kadai Dr tayi min tanbayoyi game da yanda nake ji tayi min duk abinda ya dace da na gama zan wuce ta ce “Dr ya fito ba za ki je ki fada masa abinda kenan ba? na ce “Haka ne fa bari in karasa.”

Na wuce tinkis tinkis sanin wace ce ni stander bata tsaya yi min iso ba, ta dai gaisheni na murda handle din na shiga, me zan gani Ahmad ne zaune ya ma bar kan kujerar shi ta likita ya zauna kan kujerar me ganin likita kujerun guda biyu ne dayar wata ce zaune suna fuskantar juna, kallo daya na yi mata na shaida ko wace ce budurwar da muka taba haduwa da ita a office dinshi lokacin da Abdullahi ya kawoni shi kuma ya wulakantani gabanta. Lokaci guda na ji faduwar gaba dama har yanzu suna tare? na tambayi kaina kare masu kallo na yi sai na juya na fice idona da kyar na ke gani sai na ji ciwon kan ya dawo min sabo.

Na isa inda Malam Isa ke jirana na fada motar ya ja sai muka bar Asibitin muna tafe ina waiwaye ko zan ga Ahmad ya biyoni to ko me kama da shi ban gani ba. Sadadawa na yi kamar barauniya na shige dakina, zama na yi dirshan a tsakiyar gadona na dafe goshina da hannayena tunanin makomata a gidan Ahmad nake yi, ba zan manta ba ko in zolayi kaina da maganar da Abdullahi ya taba yi Ahmad ya yi wa budurwar tashi alkawarin aure da zarar ya kammala ginin gidanshi, ga shi kuma na gansu tare shaidar cewa suna tare, anya kuwa idan ta shigo ba zan raina kaina ba? Ita da ya gani da kanshi yana so da ni da aka fi karfinshi aka ba shi. na dade cikin tunani da na rasa mafita sai na kama hawaye turo kofar da aka yi bai sa na dago ido ba har sai da ya janyo kujerar madubi ya zauna gabana muna fuskantar juna, hannu biyu yasa ya tallafi habarshi ya zura min ido magana ya ke min a hankali, “Yi hakuri ki daina kukan meye abin tashin hankali dan kin gan ni da mace alhali kin fi kowa sanin irin aikina, wannan da ki ka gani yar’uwarta ce ke labour. na dago idanuwana da ke ta faman zubar hawaye na ce, “Meye abun boyon hadaddiya me class wadda ba bagidajiya ba yar bokon karshen zamani da za ka aura, ai dama babban goro sai magogin karfe nima dama ai karanbanin akuya ne gaida kura, amma ai bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne, kawai ina kukan tausayawa kaina ne idan matan so suka shigo matar tushe kashinta ya bushe.

“Kara zuba min ido ya yi kamar me nazarin wani abu “Duk wannan jerin maganganu naki wai me suke nufi? Ni dai na cigaba da kukana ina share hawaye shi dai rarrashina ya ke yana fadin in duba cikin jikina in kyale wannan soki burutsun ni dai nayi kunnen uwar shegu da shi. Da ya ga bani da niyyar shirun ya ce, “In dai ba so kike in hawo gadon nan ba to ki yi shiru, dan tausayinki yasa ban hawo ba, dan garin lallashin zan iya sauya babi.

Maganar Haj muka rika jiyowa na yi saurin sauka bisa gadon ina share hawaye sai na bude kofar ganin na fito sai ta zauna. “Ke kuma haka ake sai ki dawo ba sanarwa mu kin barmu da tunanin ko yaya.” Kafin in kai ga magana ta zuba min ido “Me kuma ya samu fuskarki? ko duk ciwon kan ne? Kai na daga mata ta ce “To Allah ya sawake da haka sai ka ga an rabu, sun ba ki magani ko? Kan na kuma daga mata sai a sannan ma na tuna da magungunan, Baba kulu ta shigo itama sannu tayi min sai suka fita tare. Ahmad ya fito “Yaya kin hakura ko?  Ni za ni in yi sallah.” baki na tura banyi magana ba.
Da daddare ko da muka zo kwanciya juya mashi baya nayi nasa kaina wurin kafafuwansa  sai ya dauko pillow yasa bayana ya rungumoni ta baya yana rada min “Kin kuwa san hukuncin macen da ke juyawa mijinta baya? Matukar ba ta nemi iznin shi ba amma ni na yafe maki daga nasan kina fama da kanki ne. Haka muka tashi da safe tunda na gaisheshi ban kuma magana ba kujera na koma na zauna ya zo ya zauna kusa da ni “Yaya dai madam akwai damuwa ne? na girgiza kaina ya ruko kafaduna “Tunda na yi lallashin kin ki na baki to mu je dakina.” Saurin girgiza kaina na yi “Ni ya wuce tuni.”

Ya rage murya “Daga ganina da budurwa wannan irin bori haka ranar da zan kara aure fa sai yaya? idanuwa na watsa mishi ya mike “Bari in yi shirin office muje ki tayani.” Na mike na bi bayanshi. daga nan aka bar maganar budurwar duk da dai da na tuna sai in ji kamar in ta kwarma ihu, sai in ta ganin har kamar ma ya aurota inda nake jin sauki daya ne idan na tuna ginin gidan na mace daya ne sai dai abinda na manta namiji sai dai idan baisa ma kanshi jarabar son kara aure ba, dan akan idona da wayauna cikin kannen babana akwai wanda ya saida dawar da ya noma suke ci da iyalansa ya biya sadakin wata bazawara.

Kwana biyar tsakani na tashi da nakuda wadda ban bari Ahmad ya sani ba dan bai matsa mun ba sai bayan fitar shi, Haj da baba kulu suna tare da ni.  Baba ta ce “Ko za a kira mijinta ne? na ce “Yi hakuri baba mu kara gani tukuna ni a tunanina waccan a gida nayi. Wucewar awa uku Allah ya taimakeni ya saukeni lafiya na samu namiji mahaifar na fadowa Baba Kulu ta kira wayar Ahmad bata shiga ba na karba na nuna mata na ce ta kira min sister Rabi ai kam ban tashi daga inda nake ba ta iso ta karbi yaron a hannun Haj bayan ta kwashe min jini tayi min allura muka wuce Bathroom da Haj ta taimaka min dan jin da nake kamar iska zata daukeni saboda nauyin da cikin ya yi min yanzu kuma babu shi, ta fita ta dawo min da bagaruwa cikin wata container da ke jike da ruwan zafi sai da na gama na zuba a roba na zauna ciki na dade a ciki sannan ta kamoni na fito.

Na samu har su Haj Babba sun iso da Aunty  amarya da yaran Haj Babba su biyu Aunty  luba da Aunty zainab, Khausar ma ta iso na wuce suna min sannu na zauna bakin gado, Khausar ta miko min kayan shafa ina murza mai tana min sannu “Kin yi kokari wannan uban boxing baby da ki ka sullubo mana ai dole ki rika tafiya da kyar.” Na ce “Zabo min zane da riga na atamfa me dinki me saukin sakawa.” Na sanya bayan na mutsutstsuke jikina da wata hadaddiyar Humra, ta ce “Mutuniyar har fa kin fito nan da nan karfa ki sa angon karnin kyasawa idan ya iso.”

Na ce lokacin da nake kwanciya, “Allah ya kyauta maki kina min wannan maganar tun ban gama dawowa hayyacina ba.” ta miko min cup da ta hada min tea na fara sha, Aunty Luba ta shigo da kwanonin abinci a hannunta “Maza shanye ki ci abinci mai jego.” Na ce “Na gode Aunty Luba.” Ta fita sai da aka dan jima na ci abincin tuwon semo ne da miyar kubewa danya, duk yadda naso yin barci bai samu ba saboda jama’ar da ke shigowa.

Ahmad ya iso mutanen da ke dakin suka yi mashi barka suka fita, zama ya yi kusa da kafafuwana ni kuma ina kwance “Sannu da kokari, amma ya ba ki bari an sanar dani na zo munje hospital? A hankali na ce “Kayi hakuri na ga abun da sauki ne a fada maka a daga maka hankali kana cikin aikinka.” Ya ce “Sister ta yi maki komai ko?” Kai na daga mashi.

“To tashi ki sha magani.” Ya shiga bude magungunan da shi ne ya shigo da su, na yunkura ya tallafoni na tashi zaune yana miko min magani ina sha yana bani ruwa da na gama sai na gyara kwanciya ina kallonshi yana tofe yaron da Addu’a ya ba shi zamzam ya gama kallonshi ya kwantar da shi kusa da ni.” Bari in barki mata nasan shigowa ki ci abinci sosai zan gayawa Khausar abinda za a dafa maki da za a barki ma da barci kika yi ki huta sosai. Sallama muka ji ya amsa nima na amsa a hankali Rufaida ce ta shigo ta gaisheshi ina mata maraba. Ya ce “Ku koma falo ku barta ta samu ta huta.” Dan bata rai ta yi ta dauki jaririn ta fita, shima ya fita ya ja kofar.

Washegari Aunty Amarya ta dauki baby ta kaiwa Abba ya yi mashi huduba. Ranar da muka yi kwana uku da daddare muna zaune mu uku ni da Haj da Baba Kulu, yaron yana barci cikin gadonshi Baba ke cewa, “Banda abin yayan zamani komai aka yi su ce canfi ai da an daura wa yaron nan maganin baki kowa ya zo sai ya tanka” Haj ta ce “Yaron ne tubarkalla har ya fi iyayen kyau” na dan tura baki “Amma dai banda ni ni kam bai fi ni kyau ba” Ta ce “Ke tafi can mijin naki ma bai fi ki kyau ba? na ce “lala ke da kika ce sanda aka haifeni saboda kyauna da ban sha’awa idan kika yi min wanka kasa ajiyeni kike sai ki ji kamar ki saceni” ta kama baki “Ka ji ni da Ja’ira yaushe kuma na ce har kamar in saceki? Ta jehoni da pillow muka sa dariya ni da baba, na ja abun rufa na ce, “Ni dai na kwanta Allah ya bamu alheri.”

Baba ta mike “Mu kwana lafiya bakon duniya.” Ta fadi tana leka gadonshi, dama Haj tare muke kwana tunda na haihu. Ana jibi suna Aunty kubra ta iso wanda ban yi tsammanin zuwanta ba sam, kayanta kawai ta ajiye ta iso gidana, ba ta zo da yaranta ba wata dandatsetsiyar sarka da ke ta sheki ta bani wai gift dina kenan na haiho masu baby na yi mata godiya ta bani na yaranta kowa da nashi wai aba abokin danbensu har da na mijinta, na Husna ribbons ne kala kala sai mayukan gyaran gashi sai set set na kayan yaro masu matukar tsada sai turaruka designers, na ce “Kin gama Aunty dazu yaya Kabir ya zo shi da Aunty Aisha (uwargidanshi) shi ya koma ita ta wuce gidansu na nan sai anyi suna akwati biyu suka kawo shima Abdullahi da zu Khausar ta kawo nasu akwatuna, haka abokananshi duk wanda zai zo bai zuwa haka na kare da cewa ni kayayyakin sunyi yawa har firgitani sukayi” yar dariya tayi “Wa ya ce maki sun yi yawa? ai dadin haihuwar kenan ba ki ji kirarinta ba ta kurya me gumin alheri? Sai ma ranar sunan dan kila ba ki san waye mijin naki ba, shi dai barshi da miskilancinshi amma mutum ne me alheri ko cikin yan’uwa za ki ga kamar bai san me kake ciki ba, amma da zarar abu ya sameka shi ne mutum na farko da zai fara kawo maka dauki, har a cikin gidanmu ba shi da banbanci, wajen aikinshi ma suna yabonshi na tsare hakkin aikinshi, sannan yana kyautatawa na kasa da shi.

Na ce “Haka ne” duk da dai ba komai na sani na halayen nashi ba, ta katse min tunanina ta hanyar cewa “Haka ya kabir ya taso kafin ya kwaso auren wata Kabila ta raba shi da kowa, yanzu ma al’amuran sun yi sauki shi ne har ya kan yi alheri, uwargidan ta shi ma dan tsaye take.” Haka muke rufe firar ta barni cike da tunanin waye mijina? dan a gaskiya ko ni a farkon zamana da shi kallon da nake mashi Irin na yayan masu da shi dinnan masu bakin girman kai da rashin ganin kimar jama’a, sai da muka daidaita na fahimci da yawa cikin zatona ba haka bane, mutum ne mara san hayaniya miskili ne dan miskili ko ma’aikatan gidan ina yawan ganin yana masu alheri ba sai albashinsu ba. Me yawan kusanta kanshi da Allah ne ta hanyar istigfari ga yawan sauraron karatun Al-kur’ani dan ban taba jinshi yana sauraron kida ba, har mamakin dadewar da ya yi a Turai nake yake kuma da wannan kyawawan dabi’un, yanayin aikinsu kowa yasan ko wane irin lokaci za a iya bukatarsu to haka zai tsallakeni komai dare koda kuma me yake yi a lokacin ban taba jin ya yi korafi ba, mutum ne me kwazo kwarai akan aikinshi. Kakkarfar ajiyar zuciya na fidda da kara ganin girmanshi a raina. Na mike maimakon in kwanta wayata na janyo data na kunna na shiga WhatsApp Husna nake son tura wa sako sai na gan ta online dan haka na tura mata.

“Barka da jin dadi yanmata.” Ba a jima ba sakonta ya shigo Barka dai Auntynmu to ya babynmu? ya Ahmad ya turo min pics din babyn, kwarai na yaba da kyautar da ubangiji ya yi mana na wannan tsalelen yaron Allah ya raya mana shi kyakykyawar rayuwa.” Na tura mata “Amin ina godiya mutuniyar na ga sayayyar taki ta manya ce, mayyar ribbon hada ribbons ɗin naki.”

Turo min ta yi “Ba ki da labari mutumniyar  na tsinci dami a kala na ke gaya maki,  wani dan canji na samu ba ki gan shi ba handsome wallahi ya mutu kaina duk da nima sosai na fada san shi, a wani boutique muka hadu a birnin na Mumbai. Na tura mata “Dan ina ne? dan na yi tunanin ba’indiye za ki dauko mana.”

Ta turo “Kai haba dan garinmu ne Bauci, amma ya fi zama lagos.” Me mata ne ko single ne? Matar yayanmu yar jarida dama Yayanmu ya barki kiyo karatun mass com shi ne dai dai da ke, yana da mata shekaru biyu kenan da aurensu suna da yaro guda, ganina ya ruda shi kamar yanda nima kaunar shi ta sa ni janye kudirina na kin auren me mata. Sunansa Sagir Ningi, ina fata za ki tayani addu’ar Allah ya yi min zabi na alheri? Na tura “Na taya ki murna,  Allah yasa Alheri.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.9 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 20Canjin Bazata 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×