Skip to content
Part 7 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Faɗaɗa fara’ata na yi, “Sannu da zuwa” Cikin fara’ar ita ma ta amsa min. Jin muryar ta yasa nayi saurin cewa “Idan ban yi kuskure ba Ina ganin Khausar ce a gaba na.” Lallausan murmushi ta saki “Of course” Cikin zumudi na miƙe dan kawo mata abin motsa baki.
Hira sosai muka shiga yi, tare muka yi sallah, na kawo mana abinci, mun kammala ci ba ɗaɗewa ta ce, “To ni fa zan yi ta yan mota.” Ɓata rai na yi, “Ni ina ce wuni sosai za ki yi min.” Ta ce ,”Ki yi haƙuri ai zan dawo jibi, akwai wuraren da zan ziyarta yau da gobe, kasantuwar ba ɗaɗewa zan yi ba, Dear na bai fada maki next week ne ɗaurin aurenmu ba? na turo baki “Na sani, bayan ba tarewa za ki yi ba, yayana ya huta da zaman kadaici.”

Dariya ta yi, “Gara in kammala karatun shekara ce da yan watanni suka rage, Ban da ya kasa haƙuri da sai na kammala sai a ɗaura a tare gaba ɗaya.” Sai bayan tafiyarta na riƙa tunanin tarihinta da ta bani, mahaifinta babarbare ne mutumin borno. Mahaifiyarta shuwa Arab, Alh Muhammad Bulama, Sunan mahaifinta, ɗan boko ne wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi, Mahaifiyar ta Haj bilkisu Dr ce. Ita ce ta uku wurin iyayenta, Tana bin maza biyu, mata biyu na bin ta, Abdullahi ma a nan Abujan suka haɗu Saboda tana zuwa Wajen ƙanwar mahaifinta Anty Zara, Ƙanin mijin Anty zaran abokin Abdullahi ne, anan Abdullahi ya haɗu da ita. Shi kuma Abdullahi Ƙanin mahaifinshi neighbor ɗinsu Ahmad ne, Kasantuwar ba shi da ɗa namiji a lokacin, sai ya riƙa ɗauko Abdullahi, har ya samu ya rabo shi da katsina gaba ɗaya.

Tare suke da Ahmad tun primary har secondary, har tafiyarsu England Inda Ahmad ya zama kwararren likita Abdullahi kuma cikakken lauya. Tana karatun digiri ne a jami’ar maiduguri, Inda take karanta Business administration. Na yi murmushi na janyo ledar da ta kawo min tsaraba, irin turarukansu ne, Sai wasu kwalabe da ke ɗauke da wasu abubuwa kamar magani, Na buɗe drawer na saka.

*****

Washegari ne na tashi ina jin jikina ba daɗi kaina yana sarawa, tun ina daurewa har ta kai ni kwanciya a falo, wai ko zan ga Ahmad idan zai fita, in shaida masa ba ni da lafiya, Shiru har na fidda rai, da ƙyar na miƙe na leƙa window, Inda na hango Tonny yana ta aikin shi na kula da shukoki, na rasa yanda zan yi in kira shi ya ji ni ya zo ya sawo min magani kwanciya na ci gaba da yi kamar in kira wayar momi, ganin yin hakan zai iya janyo tashin tashi na ni kuma ba mai son in ta faɗar abinda ya dame ni bace Iamba ɗinshi na danna wadda na ɗauka a wayar Khausar har za ta soma ringing na katseta, kaina ya ci gaba da azalzala min, ga shi ban ci komai ba. Da dai na ga ba nayi, Sai na kira wayar ta shi har ta karaci ringing ta katse ba’a ɗaga ba, na ƙara kira ba’a ɗaga ba kuma, Sai na haƙura na ci gaba da kwanciyata, Sai zuwa Azahar ya ɗan lafa, Tea na haɗa na kukkurɓa sama sama, na watsa ruwa Sai nayi sallah na koma na kwanta, Zuciyata na gaya min yanzu ko mutuwa zan yi ƙarshenta kafin wani ya zo kaina, gawata ta sandare. Haka na ƙarasa wunin a wuya ce, cikin dare zazzaɓi ne ya rufe ni. Da safe har goma na ga bai shigo ba, sai na san yau ma ba shi da niyyar zuwa inda nake, Hawaye ke bin idona ɗaya bayan daya, Ina me tausaya wa kaina. Ƙaraurawa a ke taɓawa da ƙyar nayi maganar da aka jiyo ni, ta bayyana cikin falon Khausar ce, Turus! ta tsaya “Me ya same ki? A hankali na ce ba ni da lafiya ta ce, “Tun yaushe? na ce “Tun jiya da safe” “Kin sha magani? na girgiza kaina “Shi likita bokan turan bai sani bane? nan ma ɗaga kai na yi “Ya fita? na ce “E bai daɗe sosai ba, Waya ta ɗauko a jakarta tana ƙoƙarin neman lamba tana cewa, Ko jiya a wurina suka yi hira shi da dear. “Yawwa Dear ko za ka juyo sai mu shigar da Shuhaina cikin Hospital ɗiin nan? na same ta kwance ba lafiya”. Saurarawa ta yi “E” ta ce min bai ma sani ba, kuma bata sha magani ba.” Ta kashe wayar ta juyo gare ni, “Bari in haɗa maki ruwa, sai ki daure ki yi wanka dear zai wuce da mu cikin hospital ɗin.” Kaɗa kaina nayi, Ita kuma ta ajiye mayafin ta ta wuce cikin sauri. “Taso to.” Umarnin da ta bani kenan, Na miƙe ina dafe da kaina, mai kawai na murza na sa jallabiya da hijab, A gidan baya na kwanta, Abdullahi na ƙoƙarin barin wurin Yana tambayata abinda ke damuna? nai masa bayani ya yi min fatan samun sauƙi.

Ya gyara parking a wurin adana motoci Khausar ta ɗan rike ni, Muna biye bayan shi wata ya tambaya da alama stander ce Doctor Ahmad na ciki? Ta ba shi amsa “E Yana ciki, amma yana da baƙuwa.” Ji na yi gabana ya faɗi kai tsaye ya murda ƙofar ya danna kai ciki, muna biye da shi, Office ɗin ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, ga wani ƙamshi da ya haɗu da sanyin A.C ya bada wata ni’ima ta musamman, zaune yake kan kujerar shi teburin gaban shi ya yi ma shi shamaki da matashiyar budurwar da suke fuskantar juna, Mikewa ya yi tsaye, “Ran barrister ya daɗe”. Ya miƙo ma Abdullahin hannu, Shi bai miƙa ma shi ba Maimakon haka mur ya sha, ganin su waye a bayan Abdullahin ya sa shima ya sha mur, illa dai sun gaisa da Khausar, Abdullahi ya ce “Dama ba wani abu muka zo yi ba, matarka ce, bata da lafiya.”

Ƙara tamke fuskar shi ya yi, “Dan bata da lafiya kuma sai an biyo ni da ita? Waya ya ɗaga stander ya kira, ta shigo cikin hanzari. Ya ce, “Ki je da su wurin Dr sa’a, In ji ni tayi treatment ɗin ta.” Ta amsa ta kuma juya, muka rufa mata baya. Doctor Sa’a ta duba ni ta rubuta min magunguna sai da tasa aka kawo magungunan hada allura ta min da kanta ta ce ba jimawa zan samu barci. Mun nufi wurin motar, Khausar na dafe da ni, Sakamakon jirin da na ce mata ina gani, Ahmad idona ya nuna min tsaye gaban wata Hommer jeep, Yarinyar da muka gani a office ɗin shi, Ita ma tana jingine jikin motar suna magana, Duk da ciwon da ke damuna sai da na ji wani kullutu ya tsaya min, ya tokare ƙirjina. Khausar na bude min bayan motar sai na kwanta, Abdullahi ya ce yana zuwa, Riƙe da ledoji hannu bi biyu ya dawo, Sama sama na ke jin maganar da suke da Khausar, Idanuna a lumshe suke ina maida numfashi a hankali, “Ka ga har ta samu barci.” Na ji muryar ta sama sama.

“Wace ce yarinyar da ke tare da Ahmad? Dan tsaki ya ja “Wai ita yake son ya aura” Gabana na ji ya yi wani irin bugu, Tsaki ta ja “Duka yaushe ya yi wannan auren, har yake neman rakito wata? Ya ce “Sun daɗe tare, tun muna karatu a England, Ita kuma a lokacin dadynta Ambassadan Nigeria ne a can, ta nace masa. Shi kuma bai damu da ita ba a lokacin, wai sai yanzun kawai na gan su tare, shi ne yake faɗa min aurenta zai yi, amma sai ya kammala ginin shi da ya fara, na filin da ya saya, bayan dawowarmu”. Taɓe baki tayi “Lallai sai ta shirya zama, ko ba gidan da na ji kuna magana ba? Yana cewa daga turai ya zo da tsarin gininshi, yana son shi cikin nutsuwa, dan ayi mashi kamar yadda yake so. Dai dai nan muka isa, Da sauri ta ɓalle murfin motar, ta zagayo baya Sai da ta taɓani sai na buɗe ido “Za ki iya takawa In riƙeki? na ɗaga mata kai Ta riƙeni muna takawa a sannu zuwa ciki, kafin ta koma ta karɓo sayayyar da Abdullahi ya yo, kamar jira sai barci ya ɗauke ni.
Na farka ne na ga Khausar kan sallaya ta idar da sallah. Ta ce “Kin tashi? Na ɗaga mata kai cikin sauri ta miƙe ta fita, sai ga ta ta dawo ɗauke da tray a hannunta, “Ɗan daure ki wanko bakinki” na yi kamar yanda ta ce, “Ya kike jin kan? na ce, “Kamar an sauke min kaya ya yi wasai”. “Zazzaɓin fa? Na sharo zufar da ke kan goshina, “Ba ki ga yanda nake gumi ba?. “Okey to ɗan daure ki cinye abincin nan, ko kya yi saurin wartsakewa. Ta miƙe ta ƙaro karfin A.C ban san yi mata musu dan ko banza ta yi min abinda ƴan’uwana za su yi min, ga wanda na ke zaman shi ma indan shi sai dai in mutu. ɗan tsakura nayi sai na cire hannu, Mug ta miƙo min cike da kunun gyaɗa, “Ɗan daure ki sha.” Na sha shi fiye da zatona, sannan na yi sallah, a inda nake ina Addu’a Na ji hawaye masu ɗumi suna sauka bisa fuskata, ban san Khausar na lura da ni ba sai da ta kira sunana, na yi maza na share hawayen, na amsa a sanyaye.

Ta ce “Ko da ba ki gaya min aurenku yana da matsala ba, ni na san haka, gabana ya ɗan faɗi na dai yi zugum, Ina sauraronta. Ta ci gaba “Kin san dai tsakanin Abdullahi da Ahmad Sai Allah ko? Na ce “Haka ne? ta ce, “To amma saboda wai hankali na da dear ya ce yana yabawa shiyasa ya gaya min halin da kuke ciki, kuma abinda ya tsara tuni yake so in zo garin nan, a ganin shi ke yarinya ce, ba zan rasa shawarwarin da zan taimaka maki da su ba.” ta ja numfashi “Amma ke tun zuwanki wace hikima kika yi irin tamu ta mata dan ganin kin taimaki kanki? na watsa mata idanuwana, nuna alamar ban fahimci abinda take nufi ba, “Nufina wane ƙoƙari kika yi, dan ganin kin taka masa birki?”

Dan langabe kaina nayi maimakon magana sai hawaye, Ban ko damu da share su ba, ta dafa ni,”Ki yi haƙuri Shuhaina, ba nufina in sa ki kuka ba, Kuma ba wai ina son sai na ji sirrin zaman ki bane, illa dai na san daga sanda Abdullahi ya faɗa min matsalarki na san ina tausaya maki, daga sanda na haɗu da ke, Sai na ji zuciyata tana maki so tamkar ni da ke mun haɗa jini, Ina sonki da zuciya ɗaya.” Na share hawayen, “Ban taɓa sha’awar bayyana ma wani damuwata ba, Ina dai gayawa Allah ya yi min zaɓin abinda ya fi alheri, dan Ahmad na haƙura da shi, ɗiyar tsohon Ambassador ya ke son ya auro ya haɗa da ni, Ni da ba yar kowan kowa ba ga shi ganina da ita na farko ya fara nuna min iyakata a gabanta. Dama yana sona ne da ɗan dama dama. Sai da nayi kuka me isa ta, sannan na ji zuciya ta ta Aminta in bata labarin ko ni wace ce, A kalla ko bata yi min maganin matsala ta ba Zuciyata za ta yi sanyi. Nan na gaya mata tarihina, har zuwa yau. maimakon kamar yanda nayi zato za ta tausaya min, Saɓanin haka wani kallo take bi na da shi, kamar za ta falla min mari.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 6Canjin Bazata 8 >>

1 thought on “Canjin Bazata 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×