Skip to content
Part 15 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ni dai da na samu na kai kaina dakin da aka sauke mu da kafafuwana da nake jin kamar ba za su dauke ni ba, na fada kan gadon ajiyar zuciya nake fiddawa tare da nadamar shigar da na yi, ni kaina nasan ba tayi ba, istigfari na shiga yi. Ina nan kwance Husna ta shigo kamar an biyo ta, na ce “Lafiya.”

Ta ce “Kin tafi kin bar ni da fargaba boyewa nayi tayi kar yaya Ahmad ya gan ni, dan ban san yanda zai yi da ni ba karshenta ma ya ce ni na koya maki daga ya san ba ki yi.” Na ce “Allah dai ya kyauta gaba amma ai ba karamin da na sani nayi ba.” Husna ta ce, “Kai yau na ga kishi.” Na ce “Wurin wa?. Kallona tayi mijinki mana.” Na ce “Haba dai kawai ya dai ga shigar bata dace ba.” Ta murmusa shi ma din ai ya yi kasuwa a wurin, wasu taron yammatan amaryar da na boye a bayansu na ji suna ta maganar shi ba ki ji yanda suke kuranta shi ba kamar ba sauran maza.

Wani abu na ji ya tsaya min dan haka ban kara magana ba, mikewa tayi ta soma cire kayan jikinta ta mayar da na barci, ni kuma nayo alwala nayi shafa’i da wuturi, sako aka kawo mana ledoji biyu cike da kayan kwalama daga Ahmad. Da muka kwanta na dade barci bai dauke ni ba yammatan amarya sai wajen daya suka shigo, hayaniyar da suke ta kara temakawa soyewar idona.

Da safe shirin wucewa da Amarya kawai ake, na shirya cikin farar super riga da zane da dankwali, Husna da ta gama shiryawa tana murza daurin dankwali ta dube ni “Yau antyna ba matsewa? Na kama baki “Allah ya tsaran haihuwa daya horon mahaifa.” Ahmad ya kira ni mu fito ana jiranmu, a natse muka fito a wajen gidan inda motoci suke tsaye suna jiran masu tafiya, hango su  muka yi Abdullahi yana kan bonet din motar Ahmad,  shi kuma yana tsaye da wani abokinsu yawancin abokan nasu duk suna cikin motocinsu, Abdullahi ne ya fara magana kafin ma mu gaishesu, “Ran amaryarmu ya dade.” A raina na ce “Kai kam dan dai ba mutumin da zan ba amsa bane da sai in ce duk zumudin angoncin ne ya ruda ka ko kuma dan ka san tsiyar da ka tsula shi yasa ba ka cewa matarka amarya ba, sai ni za ka turo wa amarci.” Dan murmushi nayi muka gaishesu.

Husna ta koma dauko trolley din ta da ta manta. Ahmad ya ce Airport za ka kai min su. Dariyar shegantaka abokin ya yi, “Ba za ta iya zaman mota ba? amsar da Ahmad ya ba shi ta sani jin faduwar gaba” Ai nima yau amarcin nan zan yi idan na bari mota ta gajiyar da ita ai ka ga ba kanta.” Dariya suka yi shi da Abdullahi shi kuma ya yi kamar ba shi ya fadi maganar ba, ni dai na sunkuyar da kaina.

Husna ta dawo abokin ya shiga ya tada motar, Ahmad ya leka inda yake “Kai dan iska nasan irin tukinka to ka ja min mata a hankali.” Ya ce, “Allah sarki dadin abun ma matar nan nima ina da ita da yau haushi ya kashe ni.”

Abokin nasu shi ya kaimu airport sai da ya ga tashin jirgin kafin ya juya, su Ahmad sai da suka ga tafiyar kowa kafin suka biyo jirgi. A falon Momi muka baje su Farhan na cin kayan bikin da aka lodo mana, Ahmad bai leko gidan ba sai washegari da yamma, suna gaisawa da Momi ni kuma ina kitchen ina girki su Husna da Farhan sun fita shan Ice cream, ta kira sunana da na amsa ta ce in kawo wa pepper chicken din da na yi, ina shirya mashi a babban tire ina tunanin kaina ba dankwali calabar ce kaina Husna tayi min da rana ta kwanta kan kafadata, riga da siket ne jikina na atamfa dinkin cif jikina, na dai yi karfin halin sunkutar tiren na jawo ina gogewa dukawar da nayi gabanshi ashe rigata ta rabu da jikina tayi kasa ga shi bansa komai a kasa ba ashe na kunnan tashar shi, sai dai na ji maganar shi  cikin kaina, “Momi yaushe za ki bani yar taki ne?”

Dan murmushi ta yi, “Harka shirya ne?” Ya ce “Ai tun ban dawo ba Momi an gyara gidan dama kuma Abdullahi na sawa a gyara.” Ta ce “Ba damuwa amma ya ta ba za ta koma wannan gidan naka na asibiti ba.” Saurin dubanta ya yi ni kuma na gama jere ma shi na koma kitchen ina saurarensu, da sanyin murya ya ce “Saboda me momi? Sai da ta dan jima kamar ba za tayi magana ba sai ta ce, “Saboda dalilai da dama ina sane da dalilin kai Shuhaina wannan gidan, ko ba dan bata kai mace ba a wurinka? Idan ka gama tsararren gidan naka sai ka auro masoyiyarka wayayya kyankyasar inji?”

Ba Ahmad ba ko ni na sha mamakin yadda aka yi tasan haka, ya ce “Momi yin maganar nan yana nufin har yanzun ba ki yafe min ba.” Ta ce “Ko daya so nake dai ta tare a sabon gidan da kake yi wanda na ga har yan’uwanka suna tayaka san shi suna ganin ya fi karfin Shuhaina.” Namma mamaki na kara sha dan na gano abinda take nufi, dan kafin Ahmad ya dawo ina zaune yayan gidan mata masu aure suka zo wuni suna ta maganar ginin na shi, Sumayya yar wajen Haj Babba ta ce ” Mun je ni da Alh mun gano ginin yaya Ahmad, wow gidan ya hadu.”

Rufaida ta amshe “Eh Wallahi kamar ace ba wannan local din zai sa a ciki ba, ya samu diyar wata don ita ke dai dai da wannan gida.” Suka sa dariya. Ban san Momi ta ji ba. ya ce “Dama na bar aikin hannun wani abokina a nayi a hankali, yanzu kudina da muka hada hannu da Dr kasim muna turo magunguna sun fito mun samu alheri yanda ba ki tunani.” Ta ce “Allah ya sanya albarka” Ya ce ” Amin” ta ce “Kai na ga fa Alert na makudan kudade na meye? Ahmad ya ce ” Irin kudaden ne Momi ki sa albarka.”

Ta ce “Allah ya yi Albarka.” Ya ce “Komai na gidan ya kusa kammala har ma na yi order kayan furniture’s din da za’a sa.” Ta ce “Allah ya taimaka” Ban ji motsin yaran nan ba ina suka shiga? Ta ce “Kasan sarakan shan zaki ne sun fita shan ice cream.” ya ce ” Ita yar taki bata sha?” Da gatse ta ce “Bata da kudi kuma kasan ba za su bata kyauta ba.” Ya ce “Kai Momi tana tare da ke ne bata da kudi?” Ta ce kudina daban naka daban ko tunda ka dawo ka bata nairarka?”

Ya ce, “Ayi hakuri Momi, na tambayi Husna abinda za’a yi mata kan ta tafi ta ce min canjin mota take so gobe za’a zo a tafi da tata sai a kawo wadda take son,. Nan ma Momi addua tayi, suna ta firarsu ni dai da na samu na kammala daki na shige, ruwa na watsa, ina zaune kan mirrow ina murza mai na ji turo kofa tunanina Husna ce dan haka ban damu da in waiwaya ba, ta madubi na ganshi yana kare min kallo kamar ranar ya fara ganina rasa yanda zan yi na yi dan daga ni sai guntun tawul takowa ya yi ya tsaya bayyana, ban aune ba sai dai na ji ya balle tawul din ratsa hannuwansa ya yi jikina abubuwan da yake yi ne yasa jikina daukar rawa, ya ja ni zuwa gado na rasa yanda zan yi da kyar na iya furta “Ka da Husna ta shigo.”

Sai ma na lura bai san ina yi ba, da kyar nayi kokarin kwace kaina na dauki tawul din na daura na bar ma shi gadon, na koma neman rigar da zan sa. Na bar shi cikin wani yanayi da ni kaina ban ji dadin barinshi a hakan ba, to amma a ina za’a yi abinda yake nufin? Cikin lumshewar ido ya ce “Ki fadi abinda zan saya maki” shiru na ma shi kara maimaita min ya yi ya ce ” Idan kuma ba ki yi magana ba tabbas zan tafi da ke sai kin kwana wajena.” Sauri nayi na furta laptop tashi ya yi ya bar dakin bayan ya ajiye min bandir na yan dari biyar, na dade zaune ina maida numfashi sannan na shige bathroom tsarki na sake da alwala na fito na tada sallah, da na idar sai na fito falo Husna ta ce, “Mun dawo ba motsinki ga ice cream dinki yana fridge na ce,”Na gode.”

Baba mai gadi ya yi sallama daga kofa ya ce, “Haj Shuhaina na da bako a waje” Farhan ya ce “Waye? Ya ce “Na tambaye shi ya ce Babangida ke da aiken.” Tashi na yi na fita na samu mutumin mun gaisa ya miko min laptop da kwalin waya ya ce in ji Dr Ahmad. Ina shiga na mika ma Farhan laptop din murna yake iya karfin shi “Wa ya bani? ya tambaya bayan ya tsagaita da murnar na ce “Yayanka” ya ce “Amma da na ce mishi ya ban kudi zan saya wa abokina laptop fada ya yi ta yi min.”

Momi tayi dariyarsu ta manya “Ba ka gane ba Farhan ita ta fada mashi sai ya saya maka” Kallona ya yi “Ko dai ya take anty na gode, Allah ya bar ki da yayanmu ke kadai, ya rufe idanshi kar ya hango wata.” dariya Husna ke ma shi, shi kam ko a jikinshi sai ma barin falon da ya yi yana kiran abokin na shi a waya. Husna ta bude wayar sanfurin IPhone ce. Kwana biyar tsakani muna zaune dariya muke na labarin da Farhan ke bamu wai kakar abokin shi ta basu labari wai a da idan an yi mutuwa a kauyensu tsofaffin da ke kwana wurin gawa kwana suke suna fadin ta tafi kenan ta tafi kenan sai wasu su amsa da mulumundu, mulumundu.”

A haka Ahmad ya shigo ya same mu, “Kai lafiya duk kun cika waje da surutu.” tsit mukayi “Ina Momi? Ya tanbaya “Tana dakinta yaya” Farhan ne ya amsa mishi ta wayarsa  ya sanar da ita zuwan shi ta fito ta zauna cikin shiri take da alama fita za ta yi ta ce “Sai ina haka ko zancan za ka? Sai da na ji faduwar gaba jin maganar dan gaskiya ya hade cikin wani rantsatstsen farin boyel sai sheki yake hula da takalmin da ya sa sun shiga da juna kamshinsa na ko yaushe na tare da shi, ya ce “Haba Momi ba’a kada gizo ba ai ba’a cewa koki taso.” Murmushinta me kyau tayi “Daga Asibiti nake ina da patient sai na dubata, yanzu zamu tafi da yar ki ne a bude account din daga nan mu wuce ta ga tsarin gidan.”Girgiza kai tayi “Na hada ta da Farhan an je an bude a baka account no din? Daga ni dauriya me yawa ya yi wajen cewa “E to Momi ganin gidan fa?.

Ta ce “Su shirya sai ku je” tana fadin haka Husna tayi tsalam ta mike ta shige ciki, Farhan ya ce “Yaya na gode da laptop A… kafin ya gama jero kalmomin godiyar da zai yi ya katse shi da cewa “Waye ya baka laptop” cikin dan tsoro ya ce Anty Shuhaina” ya ce “Ai bata gaya min kai zata ba ba da ban saya ba dan nasan wata shiriritar za ka yi da ita daga ta ka na nan”. Momi ta ce min “Tashi kema ki shirya ba ki ga yar’uwarki ta tafi ba” Mikewa ya yi “Su yi zamansu.” Momi tayi dariya ta tashi ta bar falon, Husna ta fito farhan na son yi mata dariya yana tsoron masifar da za ta yi mashi, sai ya boye fuskarshi yana yi kasa kasa, ni kaina ta bani dariya ganin yanda ta sha kwalliya. Abakar dai babu ruwanshi sam yaron ba shi da hayaniya in dai ya samu ball shi kenan.

Haka suka yi ta drama da Momi duk yanda yaso kebewa da ni sai ta san yanda tayi ta toshe, misali sau daya ya iske ni wurin computer sai muka dawo tare to tun daga nan bata kara barina na tafi ni daya ba sai ta hada ni da Husna kome take sai ta bari mun tafi, shi kuma sai sai ya tare gidan ko da yaushe in dai ba shi wurin aiki to yana gidan, ya kuma takura wa yayanta suna wasan ludo ya karba ya fasa idan yana zaune babu me kara tari ko kallo baya barinsu sai dai yasa masu waazi. Muna waya da amarya Khausar ta ce, “Ba ki da kirki” na ce “Amarci kuke a zo karshe a takura maku, shi yasa na daga kafa ko da yake na mance amaryar ta zama kaya.” “Haba in ji wa? babu abinda za’a fasa ki zo ki yi course.” Na ce “Ah ah ni ko na gani ba ruwana.” Ta ce “Sai ki tsaya kallon ruwa kwado ya rike kafar.”

Mun shirya zuwa mata wuni ni da Husna, na gama shirina zan nade jikina da laffaya, Husna ta cire kanta jikin window ta dube ni. “Anty Shuhaina ga mutuminki can jikin motarsa,  ya dai zame wa Momi dan zane na lura ita ma ya ishe ta,  karfin hali ne irin nata tayi mishi  abin da  yake so ko ta huta.”

Na ce “Me kenan kike nufi?” Ta ce “Ina nufin ta sallame shi ta hanyar ba shi matarsa.” “Uhum” kawai na ce ta fara kwalliya tana cewa “Dan Allah cire laffayar nan Aunty Shuhaina mu zolayi yaya Ahmad.”  Na ce “Me zan yi” Ki sa cikin gyaluluwana me shara shara mu fita a haka.” Ido na zaro “Kin ga kar ki ja min fitina ranar nan har fitsari na kusa saki saboda razana ki kuma jaza min.”

Husna bata bar ni ba sai da ta hilace ni tsaf na cire laffayar riga da siket ne jikina na material rigar karama ce ta kamani siket din ma ya min dam daga mazaunai dama ga shi da abun, dankunne da sarka fashion ne, kaina ya sha gyara, dan Momi bata taba gajiya ba da tura ni gyaran jiki da kai dauri me kyau nayi. Husna shadda tasa dinkin yan Mali ta kafe daurin dankwalinta ga gyalenta ta jefa shi a wuya ga kamshi na musamman muna yi kwas kwas sautin da takalmanmu ke fiddawa kenan wurin Husna na koyi saka takalmi me tsini. Muka nufi wurin motar Husna waya yake yana kan motarsa ya juyo ya bi mu da kallo mun shiga cikin motar har tayi mata key sai dai muka gan shi gabanmu, daga mata hannu kawai ya yi ta kashe motar ya zagayo inda nake ya bude motar ya janyo ni ba shiri yana rike da hannuna ya yi sashen mazan gidan da ni.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 14Canjin Bazata 16 >>

1 thought on “Canjin Bazata 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×