Skip to content
Part 12 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Oh! Na ce cikin raina, Allah sarkin dadi in ji barawon zuma, cikin satin da ya gabata, idan an ce zan tsinci kaina cikin farin cikin da na samu kaina yanzu zan ce ah ah, amma da yake Allah babu ruwan shi baya dawwama ka a bakin ciki haka kishiyar shi. Sai ga shi wuni guda ya jefani cikin dadin da nake ji tun da na ke duniya ban taba tsintar kaina cikin sa ba. Motsin Momi da na ji ya katse min tunani, na ce “Innarmu, zan ba.” Na shiga yi mata godiya.

Da daddare na je nayi ma Abba godiya da Haj Babba.
Ranar sai dai barci da yake shi barawo ne ya samu nasarar sace ni. Momi da kanta tayi wa innarmu waya ta shaida mata zancan tafiya sauke farali. Ranar da na cika sati guda da dawowa sai ga Abdullahi, Ya zo gaida Momi. Kallon mamaki ya yi min da ya ganni ke kuma mutanen waccan kasar saukar yaushe? ba ko labari.

“Saurin fara gaishe shi na yi. Momi ta fito, ya shiga nutsuwar shi ya soma gaisheta. Ta ce “Anya na amsa gaisuwar nan taka Abdullahi? Dan na san duk tsiyar da abokin ka ya tsula ba zaka rasa sani ba.” Cikin nutsuwa ya ce, “Momi me muka yi?” Ta ce, “Kana nufin ba kasan abinda Baba karami ya yi wa matarsa ba? Nan ya shiga rantse rantsen bai da masaniyar komai. Na mike na shiga kitchen na hada mishi abun motsa baki, sanin shi din gwauro ne, sai na koma hada ma shi abinci. Na dawo momi na ba shi labari, zan shige ciki ta kirani, “Zo ki yi zaman ki” har zufa ya rika yi “Wallahi momi ban san Ahmad ya yi haka ba, ina dai shan jinin jikina akwai abinda yake boye min, sai dai duk tunanina na kasa gano komai.” Nan ya shiga bata hakuri a madadin Ahmad suna neman afuwar ta, na bata masu da aka yi.

Sun dan jima suna tattauna maganar daga bisani ta tashi ta shiga ciki. Juyowa yayi yana fuskantata. Hakuri yake bani murmushi kawai nayi amma zuciyata cike take fal da kunci, Sai na sunkuyar da kaina a hankali na ce mishi ” Ina Khausar? “Tana gidan su” ya bani amsa. “Yaushe ne tarewar? Ya ce “Za su je aikin hajji da mamanta idan suka dawo za’a sanya rana. Na fadi “Allah ya nuna mana” Ya dubi hoton little Amina da momi ta kawo mishi “Allah sarki mun yi rashin beautiful baby wallahi Allah ya kawo masu albarka? Shiru na mishi ya kammala cin abincin kudi ya ajiye min “Ki kara hakuri, in sha Allah ribar shi tana tafe. gyada mishi kai na yi sannan na mishi godiya. Ya yi ma momi sallama ya wuce.

Na kira khausar a waya, ranar ban yi hirar dare ba, duk da dama in Momi na wuri ban iya sakewa. Mun sha hira na gaya mata halin da na shiga bayan rabuwarmu. Daga muryar ta na gane ta shiga damuwa kwarai. Ita ma hakurin tayi ta bani. Da safe ne Ahmad ya kira Momi a waya ta amsa radam kamar bata da wata mas’ala da shi. da ta bar falon ne Farhan ya ce “Humm lumbu lumbu Momi ta mishi, sai ya dawo zai sha masifa.”

Yar harara na ba shi, “Momin ce zata yi masifar? Saurin marin bakin shi ya yi “Au Allah na tuba fada, zai sha fada.” Ni dai bin shi nayi da ido ina kara jinjina shakiyancin shi.  Daga bita zuwa duk wani abin da ya danganci mahajjaci ya yi tare da Momi muke zuwa, dan tare zamu je. Dan duk shekara, Abba na tafiya da daya daga cikin matanshi, To wannan zuwan na Momi ne, An hada Innammu da wanda zai taimaka mata Illa dai idan tashin ya zo za’a dauko ta mu tashi tare. Kwanci tashi lokacin ya zo, kwana daya Innammu tayi aka kira mu aiki me dadi muka yi, tunda tafiya ce da masu abun, na dukufa gayawa Allah Allah matsalolina idan aurena da Ahmad shi ne alheri Allah ya saukaka min al’amarin, idan kuma babu alheri Allah ya yi min canji da abinda ya fi alheri. Mun kammala aikin mu, mun yi tsaraba sosai dan duk wanda ya dace in saya ma wa na saya ma shi Momi ta saya min English wears masu yawa, wanda saboda yawansu da tsadar su sai nayi tunanin yar ta budurwa ta saya mawa, Nan na kara yaba tsantsar alherinta a raina. Sai da muka kwana biyu da dawowa aka sa direba ya mayar da Innar mu gida. Sai ga Abdullahi ya zo mana sannu da zuwa cikin kayan hannuna na ba shi hadaddiyar jallabiya da agogo na maza.

Yana dariya ya ce, “Ina na abokina? gane ba zan tanka ba ya ce Na ma manta shi na shi special ne. Ni mantawa ma nake ina da wani miji in ba maganar shi aka yi ba dan Momi ta yi kokarin ganin ta mantar da ni duk wata damuwata ta hanyar alherinta da karamcinta, kuma na san ban da Momi ta hana shi da tuni ya guntsa ma Ahmad.

Wani hantsi ina shirya ma Momi kayan ta da me guga ya kawo, ta kirani na amsa sai na fito na same ta, a zaune take da takarda a hannunta na ce, “Gani” Miko min takardar tayi foam ne na wata computer school da ke nan bayan mu ki cike sai ki fara zuwa ko diploma kya samu kafin mu ga abinda Allah zai yi, zuwan zai rage maki zaman kadaici idan wannan uban shiriritar baya nan.”

Na dubi gefen da Farhan yake yana bata rai ina ma shi murmushin zolaya na fadi, “Na gode Momi Allah ya kara girma Ba’a dade ba na fara zuwa, gaskiyar Momi ne fitar yana sani nishadi da kafa nake zuwa na dawo a kafa. Waya muke da Khausar nake ce mata, “Wai ku sai yaushe za ku tare” Ta ce, “Sha kuruminki an kusa, yanzu Dubai zamu ni da mommy na da Anty Rabi muna dawowa haka nan daddy zai hakura ya mika ni.

“Ina jinjina kai kamar tana kallona na ce “Ah lallai ya ta rika” dariya ta yi na ce ina son zuwa bikin tarewar nan taku, amma ba zan iya tunkarar Momi in tanbaye ta dan ba kasafai take barina fita ba imma zan fita sai tare da ita yawanci ma wajen gyaran jiki ne.”

Ta ce, “Iyee ki ce har an fara shirye shiryen taran sweet heart din? dan tsaki nayi, “Ji ki da wata magana, kawai ta ce tana so in dawo da kyau na kamar da, wai ba karamar yamutsewa nayi ba. cike da zolaya ta ce, “To kin yi kyan ko? ba tare da na fahimci in da ta dosa ba, na ce, “Sosai ma kuwa.”

Dariyar ta kara “To ai shi kenan, amma ina ganin tunda ogan na bisa hanya dan ya kammala abinda ya kai shi, yana kuma san halartar bikin mu, kin ga kuwa ba zai bar abar shi ba. Tsaki na kuma ja “Kan ki ake ji biki daurin aure sama da shekara a kudunduno ki a kawo kawai, ba sai an ba yayana wata wahala ba.” Wata irin dariya tayi me nuna abinda ba zai yuwu ba kenan. Mun dade har credit dinta ya kare sai na kira ta muka kare maganar.

A kicin aiki ya kacame na abincin taron yayan Momi da za su zo daga India, babbar yar ta ita Ahmad ke bi ma wa Anty Kubra wadda take aure a can, da kuma Husna wadda ke zaune wurinta tana karatu, kanwar shi ce ita ke bin shi, amma a yadda Farhan ya bani labari tazarar shekaru me yawa ce a tsakanin su da Ahmad din. Sai da na ga kammaluwar komai, sannan na wuce nayi wanka da kwalliya cikin shadda riga da zane wadda aka kayatata da hadadden dinkin zamani sai na dora after dress.

Na fito falo in da Farhan ke jirana, dubana ya yi “Wannan kwalliya sai ka ce zamu taran yayanmu harara na bi shi dan ita dan Momi na wurin sai ban magana ba. Zaman kimanin minti talatin muka yi kafin saukar jirgin, mutanen da suka fito basu da yawa, sannan suka fito, kallo daya na yi masu na shaida su, dan duk na ga hotunan su wurin Farhan Husna ce gaba wadda take doguwa suna fizgen kama da Ahmad dan dai ta dan dara shi gaske, wanda na san shi mahaifin shi ne sak, Anty Kubra na biye da ita ita kuma kamar an tsaga kara da Momi matsakaicin tsawo da jiki gareta ga ta fara sol ga fara’a taro su muka yi da taimakon mu suka saka kayansu a boot Mun yi nisa da tafiya Anty kubra ta ce wa Farhan “Ina ka samo yar kyakykyawar budurwa? da mamaki ya dan saki sitiyarin ya dube ni cikin murmushi “Surukar ki ce” cikin mamaki ta ce “Dan Allah ? ashe da an yi abin kunya.”

Da muka isa ba karamar murna Momi tayi ba na ganin yayanta Husna dai bata cika magana ba, sai da suka gaido mutanen gidan aka zauna cin abinci, da aka kammala nayo ma yaran anty kubra wanka mata biyu namiji daya namijin take goyo tubarkalla kato da shi sai ganin shi ya rika tuna min little Amina, daukar shi na yi muka shiga daki ina yi ma shi wasa yaron me suna Zayyad. Tunda na ji Momi ta fara ba Anty kubra labarin watsa masu kasar da Ahmad ya yi, Husna na kwance shame shame saman sopa tana wasa da wayar ta, daga Farhan har Abakar ba wanda ya shigo wai ball ake yi suna kallo a dakinsu.

Daki daya muka kwana da Husna da yaran Anty kubra, Momi kuma ta kwana da yar farinta. Washegari da da yan aikin Momi muka hada abin karyawa sannan na taya yaran suka yi wanka suka shirya, na sha mamaki da na ji Husna ta gaishe ni musamman kalmar Anty da tayi amfani da ita wurin gaisuwar. Anty kubra kuwa sai sannu take min da aka hadu wurin karyawar, na dauki Zayyad wanda ya tashi a lokacin na cire mishi pampers nayi mishi wanka na ba shi abincin shi ina mishi wasa yana dariya.

Naso tafiya da shi wurin computer Momi ta hana ta ce, “Haka nan ki je da shi ya hana ki abin da ya kai ki sauke mata danta ki yi tafiyar ki.” Da na dawo na sha mamakin tsarabar da Anty kubra ta bani riguna ne da wando da lullubinsu irin na mutanen can masu daraja., Husna ta bani abin hannu sirara na silver farare da ribbom na kama kai kala daban daban. Na yi masu godiya. sati guda da zuwansu, ba karamin sabo muka yi ba.

Husna bata da saurin sabo amma kuma tana sabawa da kai mu’amala me dadi zakuyi. Duk in da za su ziyara tare muke zuwa sai dai idan na je makaranta, har Bauci muka je muka kwana daya, Satin Anty kubra uku ta koma Husna dai ce zata jima dan hutun nata dogo ne. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 11Canjin Bazata 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×