Skip to content
Part 11 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ummu da Yusuf da yaya Azima suka haɗa kudi suka sayi ragon suna, ranar da na kwana biyar na tashi da ciwon nono ga zazzabi ya rufe ni, za muje kauyen dawo karɓo magani ganin yadda nake rawar sanyi Innarmu ta ce in kwanta bari ta je ita kaɗai.

Ina nan kwance na tattake a kuryar gado, maganar mata na ji sun shigo falo, ban ko motsa ba illa kara kashe kunne da nayi ina jin hirar da suke ɗaya daga cikin su tana cewa; To kwaɗayi yasa aka ja ma yarinya wahala,  ga shi nan ba’a samu abun duniyar da ake kwaɗayin samu ba an ja wa yarinya wahala sai ƴar da aka haifa, wacce marabar ta da shegiya kaɗan ne.

Gabana naji ya buga da karfi, ɗayar ta amshe, haka ne kuwa Asabe dan ko kare an ce bai leko ta fannin uban ya ce su ci kan su ba. Sallamar Baba Gambo yasa su yin shiru, ta ce “kuna ta jira ko ga shi har yanzu Innar su Salmar bata dawo ba sai dai ashe Shuhainar tana ciki ni ban ma san ba tare suka tafi ba.” “Eh tafiya ma za mu yi idan ta dawo ayi mata barka.”

Hankalina ya ɗaga kwarai da jin zancen su wunin ranar kuka nayi ta yi wanda Innarmu ta alakanta hakan da ciwon ne ke damuna. Sai ina tunanin ko meye dalilin Innarmu na kin sanar da iyayen Ahmad? Ranar suna da yayarmu za ta taho ta kawo min sabuwar Atamfa ta ɗinka, na ce; Da ba ki wahalar da kanki ba ina da kaya. Ta ce Ai duk me jego sabo take sawa ran suna.”
Na kada kai daidai Ummu ta na ɗaukar yar ta ce Allah ya raya mana Antynmu. Yaya Azima ta ce amin. Na cigaba da wanka da kula da yata wacce nake ce wa Anty har muka yi arba’in, yarinyar ba ƙaramar ƙiba tayi ba, ga ta fara sol ga suma baka sidik me lub- lib dan haka take da farin jini ko bari na da ita ba’a yi, wannan ya ɗauka wancan ya ɗauka har makota. Samun yarinyar a tare da ni sai ya dauke min hankalin tunani ba ni da aiki sai gyaran a ba ta, Innarmu ba ta bari na zuwa ko ina a cewar ta ai mijina ba cewa ya yi baya auren ba,  tafiya ya yi kuma ya ce idan ya dawo zai zo ya tafi da ni,  don haka bata ga dalilin yawon ba.  Ni dai ina jinta ne kawai sai in ga shi kam ya yada kwallon mangwaro ya huta da kuda.

*****

A harabar kasaitacciyar makarantar da ke cikin birnin Canada karkashin wata itaciya zaune a kan kujera Ahmad ne, a zahiri za’a ce hankalin shi na kan mutanen da ke shawagi a wurin sai dai a badini ba haka ba ne tunanin shi ya yi nisa kwarai a kan matarsa wadda yake ganin abin da ya yi mata bai kyauta ba. Abin ya zama masa kamar wani sihiri baya da ikon rufe idonsa surarta za ta rika ma sa gizo idan ya dawo daukar darasi ya kan fita harabar makarantar dan shan iska duk matan turawan da za su rika giftawa ta gabansa da fatan ko zai taya lumshe idanuwan sa yake yi cike da jin zafinsu sai ya ga duk ba wadda ta kama kafarta sai ya shiga tunanin rana guda da ya kasance tare da ita hakika yarinyar ta yi mace ce sosai, wadda za ta gamsar da namiji har ta sa shi mance sunan shi. A duk sanda ya tuna al’amarin da ya shiga tsakanin su lumshe idanuwansa yake ya fada cikin wani yanayi me wuyar fassara, ina ma bai yi karyar ya taho da ita ba da sai kawai yanzu yasa ayi mata biza a kawo mishi ita wani irin murmushi ya yi tuna ba karamin morewa zai yi ba. Daidai da Abdullahi bai fada ma gaskiyar lamarin ba, duk kiran da yake mishi ya na cewa Khausar ce ke son magana da Shuhaina,  sai ya ce baya kusa da ita. Watan Anty hudu wadda su Yusuf ke ce ma little ta iya zama ranar wata asabar ta tashi da zazzabi Yusuf da ya zo daga makaranta ya sawo mata magani amma zazzabin nan ya ki sauka cikin dare ta ce ga garinku nan.  Na shiga wani hali na rasuwar yarinyar, tuni na koma halin da na fita sanadin samun ta.  Kwananta biyar da rasuwa ina kwance a uwar daka kan karamin gado, littafin matanir risala ne a hannuna na Ibn Abi Zaidil Kairawani,  Innarmu tana falon ta tana yankan dinki.  Hayaniyar da na ji tsakar gidan ya dauka ne, ana maraba da gaisuwa na gane an yi baki, kofar dakinmu ake sallama muryar wadda na ji ta shigon ce ya ba ni mamaki sai dai ban motsa ba har suka gama gaisawa da innarmu tambayar ta na ji tana yi.

“Wai ina yar tawa ba ta zuwa ta gaishe ni? Ko nima laifin baba karamin ya shafe ni? Innarmu ko da ban ganta ba na san murmushi ta yi, “lamarin yayan zamani ne, dan dan fari ya mutu ka dauke shi wani tashin hankalin da za ka ki ci ka ki sha.” Cikin rashin fahimta a maganarta, ta ce, “Hala waye ya haihu? Innarmu ta bata labarin dawowar da nayi da ciki har zuwa haihuwata da rasuwar yar kwana biyar da suka wuce.  Sai ga momi tana hawaye Innarmu tana bata hakuri, ta ce, “Wannan wace irin cuta ce?” 

Ranar dai sai ga baban su Ahmad har dakinmu, da iyayena maza aka zauna suka bada hakuri iya iyawar su baban shi ya ce, “Yanzu zaman Shuhaina ya dawo karkashin kulawata zan sa ido dan ganin bai cutar da ita ba,  Idan kuma abin ya gagara wanda ba’a fata da kaina zan maido ta.”

Mahaifiyar shi ta karbe, “Tun bayan tafiyar su na fahimci akwai abin da Baba karami yake boyewa ko da yaushe muka yi waya na nemi ya bata wayar sai ya ce baya gida na tada hankali kan ina so in je in gano abin da yake boyewa sai Alh ya ce in hakura da cewar da nake sai na je a tura Najib dan wajen Amaryarmu. Da Tunau direba ya ga lallai tafiyar za’a yi ya ce zai fadi yanda aka yi amma dan Allah ka da sunan shi ya fito a wurin Baba Karami.

Ya ce, “Gaskiyar magana oga shi kadai ya kai airport, matarsa  gidan su ya sa ya kai ta,  ya ja kuma kunnan shi da kar ya fada wa kowa,  jiya aka yi maganar nan yau muka taho da Alh ku yi hakuri ku bamu Shuhaina kamar yanda Alh ya ce zamu kula da ita.  Zaunar da ni babannina suka yi ina kuka suka ce in tashi in hada kayana.

Ta ce, “Bar kayan, ki zo mu je Baba Karami zai gane kuskuran shi, da ni yake zancan.” Ta kama ni muka fito, Salma na biye da mu tana kuka. Mahaifin Ahmad da momi suna baya, ni na shiga gaba gefen direba na kudundune cikin hijab di ta.

*****

Bayan kara rabo ni da gidan mu a karo na biyu ba tare da sallama da yan’uwana ba. A mota ina kudundune ina sharbe ina sauraren su,  Daddy na bayyana tsananin bacin ransa da abin da Ahmad ya yi,

har muka shiga Abuja zancen suke. Momi dai na rike da hoton Amina (little) wanda ke cikin frame Yusuf ya bata,  album guda ya cika da hotunan yarinyar. Mun isa gidan su Ahmad ana sallar magrib Abba shi da Direba alwala kawai suka yi suka nufi masallacin da ke cikin harabar gidan, Mu ma muna shiga sashen mommy Alwalar muka yi muka bada farali, Yan aikin gidan suna ta shigowa mana barka da dawowa Haj Babba ta shigo da Anty Amarya Suna ta maida maganar ina sauraren su. Momi dai duk wanda ya shigo cikin yaran gidan sai ta nuna masu pictures din little su kuma sai ka ji sun ce “wooow! Fine baby.”

Da kuma ta ce, “Ai ta rasu” Sai su yi ta cizon yatsa sun jima suna maida maganar daga bisani sun bar sashen suna fadin Allah shi kyauta. Suna fita momi ta dube ni “Sauko ki ci abinci.” da yake an shirya abinci a ledar cin abinci da ta ga na zuba ina ta juya cokali, ta ce,”Ina nan fa har sai kin ci kin koshi ko kya dawo yanda kike da gwanin ban sha’awa.”

Da safe momi ta ba danta daya daga cikin hotunan Little ta ce ya kai a yo lamination. Farhan ya dawo ya ce, “Na kai momi, Yacson din ya ce sai Friday in koma in karba.” Ta ce “Allah ya kaimu.” Sai ta shige bedroom dinta, wayar ta da ke kusa da in da ta tashi ta shiga ruri Farhan ya kai hannu ya duba da ganin sunan ya yi saurin mikewa da karfi ya ce,

“Momi yaya Ahmad a waya.” Daga ciki ta ce, “Kar ma ka karaso ce ma shi ina gaishe shi.” Farhan ya yi turus da waya a hannu cikin sanyin jiki ya daga ya gaishe shi ko ya tambayi ina momi ne ya ce, “Ban san dalili ba ta ce ba sai na bata ba wai tana gaisheka.” Kome yake gaya mashi Farhan ya yi tsuru tsuru, daga karshe ya kashe yana share zufa kallona ya yi yana tabe baki.

Ni bamma je farautar ba ballantana ma in kashe zomon ko a kashe a bani rataya. Ya kara da cewa daga fadar sako sai ya zama laifi? Dan murmushi nayi ban yi magana ba dai dai nan momi ta fito ta miko ma shi makullan motar ta, “Ku je Farhan ka rakata gidan ta ta kwaso kayan amfanin ta kafin in samu lokaci sai muje kasuwa.” Ya amsa hada makullan gidan ta hada masa. Na mike na shiga dakin da momi ta ware min na dauko abaya muka fito yana gaya min, “Momi bata bani motar ta wai kar in je in buga ma wani sai yau, dama ai an ce albarkacin kaza kadangare kan sha ruwa a kasko.” Murmushi nayi dan na lura yana da san raha motar samfurin vibe kalarta ruwan sararin samaniya sai walkiya take Muna tafe yana gaya min.

“Wai saboda Allah ban isa mallakar mota ba? Kallon shi na yi “Haba dai in ji wa? Abba mana ya hanani mota, Na lura kuma hada momi ke zuga shi daga fa na taba buga ma wata mota sau daya wai sai na shekara ashirin da daya” Na ce, “Suna da gaskiya ka ga sannan ka kara hankali sosai.”

Kwafa ya yi, “Har fa sai nan da shekara biyu.” Na ce, ” To meye? ba dai an sa lokaci ba? Kar ka damu zai zo.” Dan gajeren tsaki ya ja, “Sai dai in za ni school in yi wani ‘kwam direba na ja na ko kuma in wani ya ji kaina ya bani aro.” Maganar shi dariya ta bani dana auna sai na ga shi din sa’ana ne yana karatun Engineering a jami’ar Abuja.

Dai dai nan muka shiga asibitin ya shiga gidajen ma’aikata zuciyata cike da tunanin abubuwan da suka shude a gidan. A raina ina cewa ko ina Tonny? A falo ya jira ni na shiga Bedroom komai na nan yadda na bar shi sai dai kura na hada kayan na fito Ya dube ni, “Aunty kinga wata waya.”

Na karba ina dubawa, sai na ga ainahin wayata ce wadda Aunty Amina ta bani da Ahmad zai tafi ya karbe. Dadi ya kama ni har Farhan ya gane farin cikina. Ya ce “Haba dai Aunty ba girmanki bane kina matar Dr Ahmad ki rike wannan wayar ni dai murmushi na yi. Da yamnacin ranar tare da momi muka shiga kitchen dan girka abincin dare na lura da kanta ta kan yi girki matukar ita ke da me gidan duk da tarin maaikatan da ke gidan. tunda kowace tana girkin ta a sasanta da masu aikinta Saboda girman gidan da kuma sashen kowa daban sai kai sati ba ka ga mutum ba matukar ba kafarka ta kai ka in da yake ba. Ina lura da yanda take sarrafa komai aikina ta kan bani umarni miko min wannan, yadda wannan. Kafin magrib mun shirya abinci kala kala waanda suka cika sashen da kamshi.

Da daddare hada autan momi Abakar me shekaru sha uku muka hau dinning dan cin abinci Momi tana sasan Abba. Da safe ma ina gefenta ta gama shirya komai dagowar hantsi muka fito, ina rike da jakar kayana waanda ba’a dinka ba Farhan ya dube ta, “Momi in zo muje?” Ta girgiza kai, “Na hutar da kai.” “Amma momi dan kin samu Aunty Shuhaina ne ko?”

Ta ce, “Yi zaman ka, idan lokacin shigar ka lecture ya yi sai kayi tafiyar ka.” Gyada kan shi ya yi ya maida kan shi ya cigaba da kallon da yake a TV. Muka fito Ta burgeni kwarai da bani sha’awa yanda take jan motar. Muna tafe ina satar kallonta har muka shiga harabar wani katafaren waje Me hawa biyu, Faka motar tayi wurin motor park din wajen muka fito ta kulle kofofin ina biye da ita.

Wani kanti ta shiga a hawa na daya yanda maaikatan wurin ke gaisheta cikin girmamawa na gane ba zuwanta na farko kenan ba. Wurin zama aka bamu wata cikin su wadda alamu suka gwada ita ce shugabar su ta ce, Wannan yarinyar za ku gyara min.”

Yar dariya tayi, “Haj zaku aurar da ita ne?” Ba tayi magana ba murmushin su na manya tayi matar ta bani umarnin in biyo ta gyara sosai aka yi min cikin awanni tun daga gashin kaina har jikina da kafa da hannu. na fito ina ta sheki, ko ina nawa na fidda daddadan kamshi Na samu momi in da na bar ta na yi mata sannu aka bata list na kudaden gyaran ta biya muka bar wurin. Wani wurin muka shiga in da ake sayar da kayan kwalliya, ta ce in zabi wa’anda nake amfani da su nauyinta yasa na kasa daukar komai sai ita ta zabar min ban tsinke ba sai da na ji yawan kudaden su da aka caje ta shagon masu dinki muka shiga sun karba da alkawarin yin waanda zasu burge. Mun fito ta dube ni “Na gaji Shuhaina bari muje gida na so saya maki English wear sai dai idan mun dawo.” Sanda muka koma gida an yi la’asar.

Farhan ne ya shigo Mummy kina da labarin zuwan babban yaya? Duban shi ta yi, “Kabir ya shigo kenan?” Ya daga mata kai tayi fara’a. “Ban sani ba dan bamu dade da shigowa ba, kai baka wuce school din ba? Sosa keyar shi ya shiga yi, “Akwai sauran time, muhimmin abu kuma ina so yaya kabir ya ganni.” Dan tsaki ta ja “Allah kuwa ya kyauta maka. Ni ban san sanda ka baci da shegen san kudi ba. To me ka nema da ba’a shigo maka da shi an ajiye maka ba? Dan kada kan shi ya yi, “Wai ma momi, ai su kudi da sa nishadi suke ka juya ka ji aljihunka cike ba abinda ya fi shi farin ciki amma ina amfanin ka zauna duhu na dukan duhu bakin wando ba kwabo.” Duban shi kawai ta yi bata sake magana ba. Kabir dan wajen Haj Babba ne shi ne da na farko a gidan, Matanshi biyu da yara biyar daga uwargidan shi. Amaryar an ce banufiya ce bata haihu da shi ba. Sallama aka yi a kofar falon ya shigo mutum me dinbin fara’a da sakin fuska Momi ta amsa cikin jin dadi. Tana fadin “maraba da mutanen Ikko.”

Na mike zan shiga ciki bayan na gaishe shi. Ta ce “Hado ma yayanku abinci.” Na wuce yana cewa kamar ko kin san Momi ban samu lokacin cin abinci ba saboda jama’a.” Sai da ya fara cin abincin suka shiga gaisawa tana tambayar shi iyalin shi da wajen aikin shi, Ina ciki yake cewa, “Momi ina kika samo yarinya me hankali?”

 Ta ce “Surukar ka ce.” Baki ya dan rike, “Amma Ahmad bai kyauta min ba, ko a hanya na ganta ai ban santa ba.” Ta ce Lallai kam, “Bai kyauta ba, sai dai idan ya dawo sai ya kai maku ita.” Ya ce, “Allah ya dawo mana da shi lafiya dan ko jiya mun yi waya da shi akwai sauran kujeru biyu da suka rage a wurina, ina ga aba surukar tawa daya ai an kyauta ko?” Ta ce Kwarai sosai aka yi halin girma, Allah ya kara zumunci.

Yana kurbar lemo yana fadin “Amin” A dokance Farhan ya iske ni, “Babban yaya ya baki kujerar zuwa Saudiya.” Cike da jin nauyi na leko na yi ma shi godiya. Ya ce “Ba komai suka ci gaba da firar su da ya tashi tafiya bai yarda ya tafi haka nan ba kudade ya bamu ya ce mu raba ni da Farhan da Abakar. Farhan ya ce, “Ki fito kudi sun zo ko in wuce school sai na dawo a yi kasafi?”

Momi ta ce, “Ah ah dawo ka bata kudinta.” Na fito na zauna ina sauraren su, Ya ce “Wai momi ina kika kai yar taki? Sai sheki take tunda kuka dawo?” Ta harareshi “Ina ruwanka ko kawarka ce?” Ya ce, “Allah ya bada hakuri” Sai ya koma zancen kudi rafa guda ya miko min. Karbi naki in ji Babban Yaya dan shi ba karanta a lamarin shi, Sai dai kuma ni ina namiji nawa ba su kai nata ba, ke kina ma tare da Momi me za ki yi da kudi? Momi ta rike baki.

“Ni Hadiza wannan yaro kamar ya yi modi da sarki, zance sai ka ce dan kama ina laifi karan ka ya kamo?”  Ya ce “Kuma haka ne, ana yi da kai ya fi ba’a yi da kai an cire ka daga sarki an baka mai unguwa.”

Na ce ” Wai kai me za ka yi da kudi ne,? ga hausa bakin ka kamar jakin kano, dama hausa,  ka karanta.” Ya ce  “Aboki gare ni bakatsine, kin san ku din in dai hausa ce karshe ne ba shi da kowa sai tsohuwar kakar shi, duk fadi tashin nan shi nake temaka mawa.  Na na zari dubu goma cikin nawa na kara mishi, sai da ya dubi idan momi ya karba. Ta ce “Maza bata kudin ta.” Na ce “Bar mishi Momi na albishir din da ya yi min ne.” Ya fita yana cewa “Kar ya makara.  Momi ta dube ni” Ai ke da goshin ki kika dawo, jiya Alh ya ce Ya yi wa Husna booking din kujera ga shi basu samu hutu ba har lokaci zai kure, ya ce a bar miki kujerar ban kai ga gaya maki ba sai ga wata, sai ki yi shawara wa za ki ba wa dayar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 10Canjin Bazata 12 >>

3 thoughts on “Canjin Bazata 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×