Skip to content
Part 16 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Bismillahir Rahmanir Rahim

Da hannu ɗaya ya bude ɗakin, wanda Farhan ya taɓa gaya min na shi ne tun yana saurayi. Ga mamakina kan luntsumemiyar katifar da ke yashe kan carpet ya wurga ni, ya naɗe hannuwansa akan kirjinsa ya kafeni da ido, “Ke ba ki jin magana ko? Taurin kunne ne da ke ko?” Ya yi kwafa.

“Daga yau idan na ce bana son abu ba za ki yi marmarin ƙara aikata shi ba.” Tuni jikina ya soma rawa har ban san sanda na soma fadar gaskiyar lamarinba. “Ka yi hakuri wallahi ga laffayata nan a jaka muna tafiya zan sa.” “Ok dama ni kenan ake so in ga kwalliyar, dama ai laifina ne da na sa miki ido shi yasa Momi ta ji daɗin riƙe min ke, da ta ga kina amai da zubar da yawu ai da ta bani ke ba gidan asibiti  ba,  ko a ɗakin patient ɗin nake kwana.”

Daga haka sai na ga ya fara cire kayan jikinsa, ya rage daga shi sai gajeren wando kallo ɗaya nayi ma katafaren kirjinsa  na rufe idona ina salati da tunanin yanda zan yi in tsere, cikin nutsuwar shi  ya shiga cire min kaya ina mishi  kuka, sai da ya min yanda ya ma kanshi abin da ya ga dama shi ya shiga yi dani, ba tare da na iya motsi ba ko ƙwace kaina, dogon lokaci ya ɗauka sai da ya gamsar da kanshi sannan ya tashi zaune, dafe kanshi ya yi da hannuwansa biyu, ni dai ina kwance kamar matatta ya gajiyar da ni hannunsa yasa ya jawo ni na faɗa kirjinsa, magana yake gaya min kamar yana raɗa, “Na riga nayi wa kaina alkawarin zan ta yin hakuri ba zan taɓa kusantarki ba sai ranar da Momi ta hakura ta bani ke, sai dai in yi abinda zan rage wa kaina zafi na kwaɗayin ki da ke azalzalata.”

Leka fuskata ya yi, “Me Momi ke ba ki ne komai naki ya ƙaru? kin kara girma da kyau, amma kina gani Momi tayi min adalci in tafi sama da shekara ba mata in dawo ta yi min horo irin wannan?” A raina na ce ka ji wata magana ko kafin ka tafin mene ne? ka san ma ka ajiye wata mace a gida.”

Kara sunne kaina nayi a kirjinsa dan ba zan iya hada ido da shi ba. Wani sha’anin ya shiga yi sai da ya gaji dan kanshi ya kyaleni ya fara maida min kayana, kuka na fara mishi yana tambayata mene ne? da kyar na ce “Ni yanzu ya zan yi in koma wurin momi ta gan ni.” Dan murmushi ya yi. “Fuska kawai za ki yi, ko in rakaki? Saurin goge idona nayi na mike, ban ko kara komawa ta kanshi ba nayi waje da na kasa shiga sashen Momi, sasan Anty Amarya na wuce, na sameta zaune ita da yan biyunta.

Na dade sashen har Farhan ya shigo neman Najib zai ba shi hand out, ya ce, “Anty na, nan kika sauka? Na daga mishi kai. Ni ce ban tafi ba har sai da Husna ta zo ta ce Momi na kirana, sai kuma da na je na ga Momi ma bata sashen. Washegari muka tafi sai dai Husna sauke ni kawai tayi ta wuce gidan yayar su Aunty Luba.  A Maitama take aure, ta aiko tana nemanta. Khausar din ce ta bude min da na yi knocking ta ce ” Ai wallahi nayi fushi.” da hannu na rika bata hakuri na ce “Kaina bisa wuyana Amarya “Tana murmushi ta bani hanya, na shige mamakin shigarta ya ishe ni kamar bame cikin wata bakwai ba duk da ya bi jikinta, wani damammen siket ne tasa sai bingilalliyar rigar da ta ka mata, kan nan ya sha gyara sai sheki yake. Na zauna muna gaisawa Abdullahi ya fito cikin shirin fita, gabanshi ta sha cikin wata kisinanniyar murya ta ce, ” Haba dear na ya zan shirya maka breakfast ka ce za ka tafi? Yana saka link din wuyan rigarshi yana fadin “Laifin wa? wa ya sani makara? ta karbi saka mashi link din, ya zauna cin abincin ya waiwayo inda nake.

“Kanwata ke ce yau a gidan namu ai sam ban ganki ba.” Na ce “Kasan an ce hankali ke gani.” A raina kuma na ce ” Ina fa za ka ganni ana maka wannan kwarkwasar? da hanzari ya kammala ya mike, “Ai kanwata kina nan har in dawo ko? na ce “Anya ban dai sani ba.” Ya ce “Haba ko shi Ahmad din ya zo ki ce na ce ya bar ki sai na dawo Lagos za ni.” Na ce “Allah ya kiyaye hanya.” Ya fadi amin suka fita tare da Khausar, da ta dawo ta canza kayan jikinta cikin doguwar riga me fadi, nayi yar dariya.

“Ban da dama rigima shigar da ta dace da ke a yanzu kenan.” Kallona tayi “In ji wa? Mazan nan da kike gani sai da haka dan ga matan nan birjik a titi jira suke ki koro mijinki ya iskesu, meye ki koroshi da zarar bai samu yanda yake so ba a wurinki kina mashi abinda zai dauke ma shi hankali daga kansu.” Tana gama fadar haka ta ce “Cire hijab din nan mu shiga kitchen.”Nna ce “To” Sai da muka fara kintsa wurin kafin muka sarrafa abinci daban daban muna fira, da muka gama ta jani bedroom dinta.

Ahmad ya yi min waya in jira shi zai zo ya dauke ni a raina na ce ko ina Momi da ya samu wannan damar? ina gidan har magrib har wanka na yi, horn din mota mukaji ta ce, “Ga mijinki nan.” Shiru bai shigo ba ashe Abdullahi ne daga falo yake cewa yau ba’a tarata ta mike tana barin dakin sorry please my dear.”

Sai da na basu lokaci kafin na fito dan in gaishe shi yana kan kujera ita kuma tana kan cinyarshi ganina sai ya ce dagani dama kanwata na ciki? Kinsa naji kunya, Ahmad bai shigo ba?. Kai na daga mashi ina ma shi ya hanya, ba a kara minti goma ba wayar Ahmad ta shigo ya ce yana jirana a waje. na shaida wa Khausar ita kuma ta fada wa Abdullahi ya goge bakinshi da tissue sai ya mike ya rigamu fita, mun jero da Khausar ta ce, “Yau gidan nawa ma ba za’a shigo ba?

Ya ce “Yi hakuri amarya Momi na jiran yarta kar in shigo in dade. ” ya bude motar na shiga, Khausar ta ce “Ki yi min godiya wurin Momi kafin in shigo.” Na ce “Za ta ji” Abdullahi ya ajiye min kudi kan kafa nayi godiya ya ja motar muka bar wurin, hannu daya ya rike sitiyari dayan yana cikin rigata, ni dai sai innalillahi nake fadi a raina mutumin da ke tuki me ya hada shi da wannan akin? Allah dai ya rufa mana asiri yasa muka sauka lafiya bayan ya tsaya wani Mr bigs ya min sayayya, da ya tsaya da motar na ce ba za ka shigo ba? Kallona ya yi har sai da na sunkuyar da kaina, saboda irin kallon da yake min “Ke kinga ya dace in shiga a irin wannan yanayin da nake ciki?

Ni kaina na gasgatashi, wani shaanin ya shiga kafin ya hakura ya sallame ni ya wuce. Ina ta tunanin yanda zan shiga ciki, sam barka Momi ita ke da Abba bata ma sashen, ajiye masu ledojin nayi na shige ciki dan yin shafa’i da wuturi. Mun kwanta ya kira wayata sai da ya yi ta magiyar ko ba zan ce komai ba kada in kashe in saurareshi, sai da na ce ina jin barci ya kyaleni, na kashe wayar gaba daya na gyara kwanciya, “Har an gama soyewa? Husna ta ce min tana murmushin shegantaka, ba tare da na dubeta ba na ce “Waye yake soyayyar?

Murmushin ta kara “Miji da mata man, uhum dama abinda kesa maza suke more mana rauninmu, kinga yanzu har kin manta abinda yaya Ahmad ya yi maki kin yafe ma shi.” ta yi kwafa “Maza masu gari suna sha’aninsu.” Tunanin da na shiga ne yasa ban ce mata komai ba sai na lumshe idanuwana. Ranar wata juma’a da misalin karfe hudu da minti biyar na rana ni da Husna ne a kitchen, Momi ta sa ni hada mata salad, Husna zaune take kan wata kujera ina aikin muna fira, dukkanmu cikin kwalliya muke ta wani material da Momi ta bamu a safiyar ta ce muyi kwalliyar juma’a dinkin doguwar riga ne kowaccenmu ya zauna mata das a jiki, na Husna fari ne nawa pink kaina kitso ne guda biyu Husna ta kama min jelar ta sauka kan wuyana, sai na daura dankwalin.

Daga falo Momi take kiran sunan Husna ta amsa gami da mikewa, bata jima ba ta dawo ” Momi ta ce “Ki hada salad din hada ya Ahmad, ashe shi ne ya shigo ni sam ban ma dauki murya ba.” “Uhm” kawai na ce mata dan ni tun shigowar shi na gane muryarshi.

Na ce ” Ke wai tsakaninki da Allah ba za ki rika girki ba? Ko har idan kinyi auren ba za ki rika girkin ba? yamutsa fuska tayi “Idan ya rage three month aurena kawai sai in dauko kwararrun masu girke girke su koya min, idan momi ta ki koya min dan yanzu ma nasan fushi tayi ta daina kirana idan kuna yi, ko da yake gani ma da kwararrar ketchener a hannu kawai ma na huta da dauko kowa tunda ina da ke.”

Shiru dukkanmu muka yi muna sauraron firar Momi da danta. Shi ne ya ce ” Momi gida fa ya kamala.” Ta ce “Ma sha Allah, Allah ya sanya albarka yasa yawan rai aka yi mawa.” Sai tayi shiru ya ce “To Momi Shuhaina idan zakuje ganin gidan sai ku tafi da kayanta ko? ta ce wane kayan? ya ce “Na sawar ta mana.”

“Kayan da har goyon ciki tayi da su tayi goyo ai sun tsufa.” Ya ce ” Sai mu fita ko yanzu, idan ta shirya ta fito muje.” Ta ce “Yawwa ana gama dinkasu sai ku yi ta tafiya.” Ta kara da cewa “Ba ki kammala bane Shuhaina? na ce na gama na dauko na Momi Husna ta biyoni da na Ahmad, zan shige ciki Momi ta ce ” In ya kammala zaku fita, kema Husna dauko naki lullubin.”

Dukkanmu muka ce to. Sai da muka jira ya gama ya fita Husna ta ce wa Momi “So kike dai ya Ahmad ya hada sabon lefe.” Bata yi magana ba ta soma amsa waya. Cikin abaya na fito ya bude kofar gaba na shige, Husna ta shiga baya karatun Al-kur’ani kira’ar Abba zaria ke kwarara cikin motar, yana burgeni saboda san sauraron karatun Al-kur’aninshi, dan kallona ya yi “Gimbiya yaushe za ki fara gaisheni? Gyara zama nayi ban yi magana ba.” “To ai ni sai in kwashi gaisuwar kin wuni lafiya.”

A yangace na motsa labbana “lafiya” bai hakura ba ya kuma cewa “Ko ke yanzu ba ki ga kin fi kyau ba da kika suturta jikinki? duban kaina nayi ban tanka mashi ba, haka muka kasance yana ja na da zance ina basarwa, har muka tsaya wani tankamemen wuri, gyara parking ya yi ya ce, “Ku shiga Husna ta tayaki zabe, me wurin abokina ne duk abinda kuka dauka zan ji a wurinshi.” Daga mashi kai nayi, muna shiga wanda ke zaune wurin biyan kudin na farkon shiga ya taso da sauri ya taremu da faraarsa muka gaisa.

“Ran amarya ya dade yanzu oga ya sanar dani za ku shigo.” Dubansa nayi ina tunanin inda ya sanni sai na gane wanda Ahmad ya taba aike ne ya kawo min waya. Mun shiga zagayawa, ganin na ki daukar abin kirki Husna ta ce “Naki wasa ne ko in tayaki zabe ne? na ce zan kuwa so haka dan ke din gwanar dressing ce.” Ta soma jidar lesussuka na karshen da shaddodi atanfofi, na rike hannunta “Wai ke malama ba ki tunanin kudin?” Wani sakaran murmushi ta saki, “Aunty kenan kina tausayin yaya Ahmad ne?” Na marairice “Ba ki ji ranar nan yana gayawa Momi kudaden da gidan nan ya lashe, kuma ga shi an sakashi hada kaya, in dan tani wallahi da an barsu.” humm kawaita ce “Aunty Shuhaina idan banza ta fadi kawai ki bi ta da yakushi ki tsaya kina tausaya wa namiji.” Ta koma kan takalmi da jaka nan kam da gaske na riketa.” Indai ba fahari abin zai zama ba duk waanda ya kawo min a kuma kara wasu? ke to ba ki dauki komai ba?”

Noke kafadarta tayi “No bani da matsala na ma kusa barin kasar karshenta ma in rigaki wucewa.” Na ce ” Haba dai ki yi hakuri in tafi in ba ki sasan fadi zai min.” Muka koma wurin jakunkuna muka yi ta ruwan ido muka rasa na dauka. Cikin masu kula da wurin wani ya ce “Haj ko za ku duba wasu sabbin shigowa satin da ya wuce aka shigo dasu sai dai tsada” gabadaya muka kai idanunmu wajen tabbas sun hade, Mun fito ma’aikatan suka biyomu da kayan, wani wurin da ake siyar da kayan ball na shiga Husna ta biyoni tana tanbayata “Me kuma za ki yi a wurin saida kayan ball? Abakar zan saya mawa? Ina dubawa nake bata amsa, Jc jc na dibar mashi sai kwallon na hada hada takalmin training, na bude jaka zan biya Husna ta ce “Ki bari in karbo kudi a wurin ya Ahmad”. Na ce “Ah ah zan biya ai ba shi ya sani ba.”

Ta ce “Haka ne sarkin tausayin miji.” Muka fito muka shiga motar, dai dai wani wuri da aka rubuta Shawarma spot ya tsaya “Ko za ku ci shawarma?” Ya tanbayemu Husna ta karba da sauri, “E” ya bata kudi ta fita zuwa amsowa A raina na ce kila dan ba kasan kiran ruwan da muka yi maka bane sai ka ji bill din Husna ta dawo muka wuce wurin dinki. Sati daya bayan nan ya kawo dinkunan momi tana dagawa tana cewa lallai telolin nan naka ba kadan suka kware ba ga shi cikin sati har sun kammala, anjima za muje ganin gidan. Sati me zuwa sai ka zo ka dauki matarka.” Godiya ya yi mata ya tashi ya tafi. 

Ta umarcemu mu shirya, duka mutanen gidan muka tafi hada Haj Babba da Aunty Amarya, gidan yana cikin unguwar gwarumfa gidan farin gini ne da aka yi mishi tsarin bature ya yi matukar tsaruwa a tsakiyar gidan aka yi ainahin ginin an yi shuke shuke masu ban sha’awa, har Gymnasium akwai, mun shiga ciki inda yaji kayan alatu komai an jereshi a tsare inda ya dace, da muka shiga bangaren da aka ce nawa ne dan wani kayataccen falo ne ya raba sashina da nashi ai kusan rudewa nayi sai na shiga tasbihi a raina a zuciyata ina fadin anya kana cikin wannan gidan za ka rika tunawa da mutuwa?

Mun fita harabar gidan babu abinda ya fi burgeni irin daga kofar sashena ta baya aka dasa kujeru da tukwanen fulawa. Muryar Rufaida na tsinkaya cikin kunkuni da yake sun zo ita da sauran yan gidan na ma’aura. “Shi ya Ahmad nufinshi duk wannan gidan ginin mace daya zai mashi, dama matar tashi ma yar babban gida ce shi kenan am.. waiwayowar Ahmad wanda bai dade ba da zuwa ba suna tsaye shi da wani abokinshi suna magana kusa da inda muke, cikin daurewar murya ya ce “Ke me kike cewa?

Saurin ja da baya tayi tayi tsuru kamar ruwa ya ci ta. Nayi kamar zan sa wannan cin fuska da ta yi min a raina sai na ga dan me to? Domin ni kam ina ganin kina mace kuma kina san cin mutuncin mace yar’uwarki to ki ta kanki dan ba ki yi komai ba, tunda ba ki tara sanin ke kuma abinda zai sameki ba. Kowa ya yi addu’ar fatan alheri a kayi ciye ciye da shaye shaye dab da za a tashi Khausar ta zo ta ce, baki tayi daga Maiduguri shi ya hanata zuwa tun dazu. A daren ranar ina zaune kan gado na riga na gama shirin kwanciya, Husna ta shiga bathroom tana wanka Momi ta shigo na kara shiga nutsuwata cup ta miko min “Karbi shanye wannan na amsa na shanye na mika mata wata yar karamar buta ta miko min “Ki rinka kama ruwa da ita idan ya kare sai ki zuba wani to na ce mata.” Tun kuma daga ranar kullun da abinda za ta bani wanda na tabbatar ko ita ta haifeni iya gatan da za ta min kenan, hakan yasa na kara ganin girmanta da kimarta.

Akwai matar da ke zuwa kullun tana min gyaran jiki, ranar alhamis ana gobe zan tafi gidan Ahmad muka ziyarci sallon Husna tayi tayi dani a gyara min kai kawai ni kuma na kafe na ce kitso nake so su min, an kuwa yarfa min shi abinka da gwanaye dan da nan fuskata tayi fayau, aka gyara wa Husna gashi. Mun koma muka iske wasu tsadaddun lesuka a kan gadonmu, Husna ce ta tafi tambayo Momi na waye ta ce Baba karami ya kawo su na Shuhaina ne” Husna ta dawo tana ce min “To kin gani? ke kina mitar kayan da na zabo sunyi yawa, to ga shi nan ya karo maki wasu.” Ni dai na jinjina kai.

Mun zo kwanciya na saka lalle lallabe a kafata da yan yatsun hannuna, Husna tana mitar, “Kin ki yadda a yi miki kunshin zamani kin wani tsaya yin wannan ordinary kunshin.” Na ce “Ni ban ga wani abin daukar dumi ba sai ka ce wata amaryar gaske har fa haihuwa nayi.” Wani malalacin murmushi ta saki “To haihuwa idan ba fadi kika yi ba wa ya san kin yita? da ba ki yi amarci ba dole yanzu ki ke Amarya, me kika karas da in ba ciwon zuciya ba?. Ban magana ba na ci gaba da kunshina.

Da safe da na wanke ba karamin kyau ya yi ba hatta Husnar sai da ta yaba. Tunani na shiga yi,  zuciyata na kara jaddada min kudirina abin da nake ganin ya dace in sulale in tafiyata Malumfashi su shafa su ji bani, wani sashen na zugani Ahmad bai taba zuwa gidanmu ba tunda aka ba shi aurena bai je ya gaida uwata ba da Babannina ba ire iren tsegunguman da mutanan gidanmu suka yi tayi a zaman gidan da nayi dan haka na duro daga gadon na fada bathroom da sauri nayi wanka na fito na shirya cikin atamfa riga da zane na daura after dress takalmi flat nayi amfani da shi na dauki jakar da na sawa kaya kala biyu sannu kan hankali na tura kofar a harabar gidan ma ba kowa farin ciki na ji ya baibayeni hango get babu maigadi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 15Canjin Bazata 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×