Skip to content
Part 19 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Ranar da na cika kwana talatin da biyar sati biyar kenan, muna kwance da daddare, kaina ya shafa “Har kin yi barci ne? Na ce “A’a” “Akwai aikin da zan je yi ibadan ina sa ran zan yi sati biyu.” Dan shiru na yi, jin ban ce komai ba.

Ya ce, “Ba ki yi magana ba? Maimakon maganar sai na kama mishi  kuka, rarrashi ya shiga yi ya ce, “Kin fi san in tafi da ke? Ba halin hakan ne, wadda Momi ta samo maki za ta iso gobe kin ga za ta debe maki kewar zama ke kadai.” “To” Na ce mishi, na dade barci bai dauke ni ba ina tunanin yanda zan kwashe tsawon sati biyu ban gan shi ba.

Da safe ina hada mashi kayan tafiya jikina duk ba kwari jawo ni ya yi muka zauna bakin gado, kalamai masu dadi yake gaya min, sannan ya mike tare da ni, ina rike da brief case din shi zuwa mota, mun dade cikin motar kafin ya sallameni ya wuce. na tsaya ina goge yar kwallar da ta taho min duk da ya ce Isa direba yana dawowa ya kaini gidan Momi.

Baba Kulu bata iso ba sai la’asar, a yanda na gan ta za ta yi sa’ar mahaifiyata, sai da ta huta sai muka tafi, dan sau biyu Ahmad na kirana yana tambayar na koma gida? da na ce, “A’a” sai ya kama min fada.

Kwana biyu da tafiyar ina kwance ina barcin safe, wayata da ke aje ta hau rurin neman agaji, cikin barcin da ke idona na kai mata wawura, ina mamakin wanda ke kirana a safiyar nan, dan Ahmad tunda ya tafi da asuba yake kirana ya ji na tashi. Na kai idona kan fuskar wayar sunan Khausar ke yawo kan screen din wayar, da sauri na tashi zaune “Kin juye ne? Na tambayeta cikin zumudi.

“Kamar kina wajen” ta amsa min. Cikin murna na ce “Me muka samu? Baby boy ne ga shi nan kwance.” Ta kashe wayar ta bar ni ina ta murnatasai da na gama shiri na tuna to wa na tambaya? Kira daya ya daga na gaya mashi haihuwar da son da nake in tafi, ya ce, “A’a, ke da fita sai Allah ya dawo dani.” Rokonshi na shiga yi kamar Zan yi kuka,sai da ya gama ja min rai ya ce a dawo Lafiya.

Dakin Baba kulu na wuce na sameta tana jan carbinta, na zauna muna gaisawa na gaya mata zancen haihuwar da akayi na ce mata zan wuce, agogo ta kalla  “Yan nan karfe tara za a bar gida? Ni ma na bi agogon da kallo “Ba damuwa Baba abokin Ahmad ne na kud da kud sun ma zama kamar yan’uwa.” Ta ce “Amma kya tsaya ki karya dan na taya wannan yarinya mun yi abun karyawa.” na ce “Sannu Baba, Ma’u ma akwai san aiki bata ko gajiya amma ni ku ci kawai zan karya a can. Rike baki tayi “Kai wannan zumudi da yawa yake, sai kin dawo nima idan za ki koma zan bi ki muje in yi barka ki gaida masu jegon. na mike ina fadin “Za su ji Baba”

Na leka dakin Ma’u muka gaisa na shaida mata zan fita.  Na samu me jego sumul kalau ita da yaronta da aka shigo mata da farfesun kaza wanda ya dahu lugub yana fitar da kamshi, daga ji an sa daddawa sai na ji miyauna ya tsinke, na ce “Me kuke da shi a gidan ban ko tsaya karyawa ba.”

Ta ce “Ki isa kitchen din akwai kunun gyada Yagana ta dama nasan mutuminki ne, idan kuma tea za ki sha akwai ruwan zafi.” Na isa kitchen din muka gaisa da Yagana yar’uwar babanta, me aikinta ta gaisheni, na koma dakin ina cikin ci zuciyata ta fara tashi na ce, “Ba ku da wani abu me dan daci da zan shashe baki” ta ce “Me ya faru? Na yamutsa fuska. “Zuciyata ke tashi” murmushi ta yi, “Lallai Dr ko har ya cika aiki.” Harara na bata, “Haba daga dawowata duka kwana nawa? Ta ce “Na sani ko dan gidan Momi ne? Banza na mata, ta ci gaba “Dama tun shigowarki na ga canji a jikinki sosai nayi zaton haka.”

Na mike ina cewa ” Kya karaci sharrinki kin sani ma likita kika karanta karshen bin diddiki” na barta tana dariya na yi waje.

Kullun direba ke kaini gidan masu jego, ranar da akayi kwana hudu da haihuwar na samu wayar Ahmad ya ce “In samu Najib ko Farhan wani cikinsu ya yi min rakiya zuwa kasuwa in yi ma me jego da baby sayayya, akwai kudaden da zai turo in biya banki dan ATM dina na da matsala in cire sai mu shiga kasuwar amma in kula da shigar da zan yi. Godiya na mishi dan haka a washegarin ranar da na gama abinda zan yi na fito na sallami Ma’u da Baba Kulu, direba ya saman ya ce ba isashshen mai a motar na ba shi kudi ya je ya nufi shan man.

Kujerun da ke harabar gidan na zauna jiran dawowar direba da zuwan Farhan, na ciro wayata Yusuf na kira muka gaisa na tambayi mutanen gidan ya ce kowa lfy sai dai innarmu da tayi fama da mura na ce ” Har yanzu Murar? Ya ce A’a ta samu sauki”. Na ce ya karatun? Ya ce “Karatu yana nan muna bugawa” na ce “Ya shagon fa? Ya ce “Yana nan amma kin san yau da gobe karatuna da abinda za mu ci duk shi muka zurawa ido.”

Na ce “Allah ya rufa asiri” Ya ce Amin” na ce “Account no dinka nake so ka turo min ” Yar dariya ya yi “Haba zancen yaushe Shuhaina ai an rufe shi, me to zan kai bankin.” Na ce “To ba na wani da za ka turo min? Ya ce “Akwai ta abokina Mahammadu Sani zan turo maki.” Na ce “To ka hanzarta ina jiranka dan zan fita yanzu sai in turo maka idan ka cire sai ku karawa shagon kaya sauran ku sayi abinci, ka gaida innammu kwana biyu ban samunta a waya. ya ce “Wayarta ta lalace amma na kai mata wurin gyara.”

Na ce ” Ka saya mata waya” ya ce “An gama ke dai godiya muke.” Na kashe wayar Farhan ya karaso “Ke Hajiyata ina ta nemanki ashe kina nan.” Na ce “E” muka jera ina tanbayar shi su Momi, mun samu isa direba jikin motar ya dawo, Farhan ya karbi key a hannunsa, mun bar gidan ina tambayar shi, “A me ka zo? Ya ce “Acaba na hau.” Na dan rike baki.

“Kamar ka  babban yaro kana hawa acaba ba girmanka bane, duk ina motocin gidan?” Ya ce “Ba direba ko daya duk sun fice da motocin ai yaya Ahmad ba karamin gwangwajeki ya yi da wannan motar ai ta shiga tsara ce. Ni ne dai har na fidda rai, sai idan na gama karatuna sai ki ga na saya idan Allah ya taimakeni dan ba zan kara cewa a saya min ba.”

Ta wutsiyar ido na dubeshi, “Kenan fushi ka yi? kada kafadu ya yi “Kawai dai na ga sa ran da zaman jiran sai ammaka ba mafita bane, gara kayi fatan samun naka.” Na ce “Haka ne, kaima dan dai kana son motar da yawa ne ai ba cewa akayi ba za a saya maka ba, wani lokaci aka diba kuma idan muna raye zai zo, amma Abba mota nawa ya aje saboda ku? muna firar har muka isa bankin sai da na cire kudaden masu yawa ya turo dan haka da na shiga kasuwa sayayya sosai na yi.

Ranar ban samu zuwa gidan masu jegon ba.  yaron ya ci suna Al’amin ranar suna shagali me kayatarwa akayi an tashi kuma lafiya. Zama na da Baba Kulu ya debe min kewar zaman kadaici, mace ce me hikima da sanin ya kamata, idan muka zauna za ta yi ta bani labarurruka daban daban kwarai nake amfanuwa. Ranar da Ahmad zai dawo tun da safe ya yo min waya ya ce goma za su shiga meeting suna fitowa zai wuce airport.

Tun da  na tashi nake yan gyare gyare sai da na ji ko ina ya dauki kamshi me dadi, na sanya kira’ar Abba zaria wanda ni ma  saboda zama da Ahmad ba karamin so nake wa karatun nashi ba. na shiga kitchen nayi girke girke masu dadi sai da na adana komai a warmers ma’u ta gyara wurin, dakina na koma nayi sallah sai na dauko wata koriyar atamfa shar tana da dan ratsin fari, riga da siket ne waanda suka zauna min dam, sarka da yankunne fashion ne na burgewa. Ina feshe jikina da turare kala kala ina kara kallon kaina a madubi, na sa takalmi sai na isa kitchen na debi abinci, dakin baba na wuce na sameta tana lazumi yawan ibadarta kan tuna min Innarmu, sai da ta kammala sai muka gaisa ina cin abinci muna fira.

Rabin hankalina na kan firar rabi yana kan agogo Ina tunanin Ahmad, shiru har akayi la’asar, daki na koma nayi sallar na gyara fuskata sai na dawo zamana ba dadewa sallama kawai muka ji a kofar dakin, na dubi kofar wani irin dadi ya rufe ni samun wuri ya yi ya zauna suna gaisawa da Baba Kulu da kyar na ce sannu da zuwa saboda kunyar kallon da yake bina da shi ga shi ba mu kadai ba. Mikewa ya yi “Bari in je in dan huta Baba.”

Ta ce “Kwarai ai ya kamata.” ya fice nayi dan jim ina jin nauyin bin shi, ta ce “Oh wane sakarci kenan? mijinki ya dawo tafiya ba za ki yi hanzarin isa wajenshi ki ba shi kulawa, maza mike ki gani.” Na tashi na bi bayanshi, a dakinshi na sameshi yana cire kaya miskilallen kallon shi ya watso min “Sannu da zuwa ya hanya? Na fadi ina kare fuskata da hannayena. dan murmushi ya yi “Bari in yi wanka sai in zo in ga irin sannu da zuwan da zan samu.”

Wucewa nayi na hada mashi ruwan sai ya shiga, da ya fito ya kintsa kanshi zai cafkoni na fara rokonshi ya bari ya ci abinci a wurin cin abincin ma yana ci idan shi na kaina ya ga na rufe fuskata murmushi ya yi me fidda sauti, da ya kammala muka wuce dakinshi, a ranar dai Baba Kulu bata ji motsina ba sai dare na fito na gasa mana kaza. Da safe yake gaya min kudadenshi da suke hadin gwiwa da mijin Aunty Kubra na shigo da ingantattun magunguna sun fito, dan haka in fada mishi abinda zai mini, da na rasa abun cewa sai na ce “Ka sayawa Farhan mota.” Na ki na ce bana Farhan ba.”

“Ai idan kayi mani alfarma ka saya mashi kamar ka yi min ne.” Dubana ya yi saboda me? Na ce “Dan yanda nake son yan’uwana haka nake jin naka ma nawa ne, yaron yana son mota, kuma yana da nutsuwa ba wani yawo yake zuwa ba.” Bai ce min komai ba ya tashi ya fita. Bayan sati dayin maganar sai ga Farhan ya zo yana murna Aunty fito ki ga motata da yaya Ahmad ya saya min.” A baya nake biye da shi har inda ya ajiye motar na girgiza kai.

“Lallai yayan nan ya burgeka, sai ka kula banda tukin ganganci. Allah ya tsare.” Ya ce “Ai da kyar Abba ya yarda aka bani key.

Ni da kaina na fahimci ina da shigar ciki, amma ban gayawa likita bokan turan ba, ban ma yi tunanin ya sani ba sai da cikin ya shiga wata na uku, dan bana laulayi komai ci nake. Ranar wata Monday ya dawo aiki zaune yake yana aiki a laptop din shi, ina kwance kan cushion tashar mbc nake kallo wani film suke haskawa me suna Blede Trinity Kira na ji ya shigo wayata na daukota na daga yayarmu Azima ce sai da muka gama gaisawa ta ce suna asibiti ummu ta haihu an sami budurwa.

Cikin murna na ce bani ummun ta ce “Ai basu kaiga fitowa da ita ba. Na ce zan kira anjima idan an fito da ita. Kammala wayarmu da na rasa abinda zan yi in tabbatar da jin dadina sai na kama tsalle kamar wata yarinya, ni nama manta da mutum a falon. Daga kanshi ya yi, “Lafiya meye haka? A sannan na maida hankalina kanshi na shiga nutsuwata, daure fuskarshi ya yi “Wace irin wauta ce haka? Kina ba ke kadai ba kina tsalle, so kike ki illata abinda ke cikinki?”

Cikin tsananin mamakinshi na shiga ba shi hakuri a raina na ce miskili ashe yasan da cikin kuma yana san shi amma bai taba nuna min yasani da shi ba. Tashi ya yi ya shige dakinshi ya barni zaune na rasa abinyi, ko wajen cin abinci ma kin sakar min fuska ya yi kuma ki ci kanki bai ce min ba, da ya kammala kwashe wayoyinshi ya yi sai ya bar gidan.

Sai goma ya shigo na yi ta sauraron ko zai nemeni jin shirun sai ya sani sake saken ko in bi shi ko kuma nima in share shi in ga iyakar gudun ruwanshi, tunda ban ga abinda na yi ya yi zafin daukar dimi haka ba. Har na gama shirin kwanciyata zan hau gado amma na gaza barcin, har dai zuciyar da ke karfafani in je in same shi ko ba komai ni ce kasa da shi a karkashin ikonshi nake ta yi rinjaye, na mike na sabule rigar da ke jikina na maida wata sakaryar rigar barci wadda da ita da babu duk daya, na fito na ratsa falonshi, na murda kofar dakin barcinshi wanda ya yi karara da sanyin AC fitilar dakin bata da wadataccen haske amma na hangeshi kwance saman gadonshi daga shi sai gajeren farin wando, ido ya dago duba daya ya min ya maida idon shi ya runtse na dan dade tsaye sannan na karasa na hau gadon na kwanta bayanshi sai na kankameshi, mun dauki wani lokaci kafin ya juyo ya rufeni da jikinshi sassauta muryata nayi na ce. “Kayi hakuri ba zan kara ba.” Da safe nake gaya mashi haihuwar Ummu da san da nake ya barni in je suna, ya barni amma da sharadin kwana uku zan yi godiya na mashi, ana saura kwana biyu suna su Tonny suka rika shigowa da kwalaye wanda nayi ta bin su da ido, sai da suka gama jidesu suka ce aiken oga ne shi kuma da ya dawo aka shigo da wasu masu dauke da zannuwa, sai da safe yake ce min tsarabata ce da safe ma Momi ta aiko da alheri me yawa ta ce in kaiwa Innarmu da me jego, a tsanake na rika shiryawa duk da murnar da ke cike da cikina dan na lura sai bi na yake da ido ya ga na nuna zumudi, ina dakina ya sameni kudade ya ajiye min.

“Ki rike kuma ki kula da kanki bana son wauta zuwan ma banda ina ganin ya kama aje da ba inda za ki, naso in zo in taho da ke aiki ya yi min yawa, amma ki gaida su Mama ki fada masu ina nan zuwa gaishesu.”

Na ce “To”  Ina nan tsaye bayan labulai ina kallon shi  sai da ya shiga motarsa  na dawo na kammala shirina tuni su Tonny sun sanya min kaya a boot, dan haka jakar hannuna kawai na dauka. Malam Isa dama ni yake jira nayo ma Baba Kulu sallama ta biyo ni tana ta min addu’ar sauka lafiya. Ma’aikatan gidan sun taru gaban motar na raba masu kudade muka dau hanya.   Mun yi nisa da tafiya na mika mishi plate din CD na waazin Sheik Giro Argungu yasa mana.

Ya ce “Oga ba dama yana ta gargadin in yi tuki a hankali, bayan na san shi din gwanin gudu a mota ne, shi ne na ce Yallabai  madam dai  yake ji.” Dan murmushi na yi na ce Malam Isa ba dama.” Ya ce, “Allah kuwa Haj. “

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 18Canjin Bazata 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×