Skip to content
Part 8 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Tana buɗe baki sai cewa tayi, “Ai duk kuma halin da kika samu kanki, laifinki ya fi na shi yawa.” Saurin dubanta na yi kyawawan idanuwanta ta watso min, “Ke yanzu kamar wacce ta fito daga dawa, kin yi karatu dai dai gwargwado, wanda za ki laƙanci rayuwa, amma bai maki amfani ba, Aurenku kin san yanda aka yi shi, gari ba zai waye ba ki yi wanka da kwalliyar ki me ban sha’awa, ki je falon ki jira shi. Yana fitowa ki gaishe shi, Ah ah sai ki wani ƙunshe a ɗaka in ba shi ya ce maki ba ke ba za ki ce masa ba. Kina ta fama da uban lulluɓi, Sai ki gaya min ta inda za ki ja hankalinsa gare ki.

Taɓe baki na yi, “Ai ko sai dai mu shekara a haka, sai ka ce wata ƴar iska ni ce ma zan riƙa neman shi? Ina ce idan ya ja ni jikin shi shi ne zan saba da shi, Manzon Allah ma ya ce kunya bata zuwa sai da alheri, nauyin shi nake ji, Musamman idan na tuna shi ɗin fa mijin yayata ne, sai in kasa sakewa.

“To idan mijin yayarki ne haramun ne naku auren da shi? Ina ce koyi ne da fiyayyen halitta yin hakan, Sayyidina Usman Allah ya yarda da shi yar manzon Allah Rukayya, wacce take mata ce ga sayyidina Usman da ta rasu, Sai manzon Allah ya ƙara ba shi Ummu Khulsum, Ita ma Allah ya amshi ranta. Sai manzon Allah ya ce bamu da wata yar ya Usman da mun kara ba ka.”

Na gyaɗa kai, “Haka ne.” Ta ci gaba, “Ba wai za ki riƙa kai kanki bane wajen shi nake nufi, za ki yi amfani da waccan dangantakar taku ki riƙa ba shi girma kina nuna ke fa har yanzu kina ganin ke ƙanwar shi ce, Yaya Ahmad sama da ƙasa, ya zo zai fita ki zo, “Za ka Fita ya Ahmad? Babu abinda za’a yi maka, Ki yi masa girki idan ya dawo ki tare shi, Sannu da zuwa Ya Ahmad ga abinci na yi maka, Ki rika tsala kwalliyarki tuni za ki ɗauke hankalin sa, Shi da kanshi zai nemi canza mu’amalar taku. ni ina ce ma mace komai ƙanƙantarta da kissar ta ake haihuwarta, Kina da ƙirar da ba shi ba, duk namijin da ya zauna da ke ba zai iya kauda kai matuƙar shi ɗin lafiyayye ne? Ki dubi kanki Ina aka rage ki? Sura me ɗaukar hankali Allah ya maki.

Ban ƙaryata ta ba dan ba ita ce farkon wadda ta yabi kyan surata ba. Dan Gwoggo Rakiya ma idan ina tafiya ta dinga min faɗa kenan, Wai wace irin tafiyar karuwai Nake yi, Ina tafe Ina kaɗa jiki, mafari kenan na zaɓi zama da hijab ko yaushe.

Na ce, “Ni da a tunanina ya gama wulaƙancin shi ya sallameni ba shi kenan ba.” Wani kallo ta bi ni da shi galala, girgiza kai tayi. “Wai ma shekarunki nawa ne Shuhaina?” Na ce’ “Yanzun na shiga ta sha takwas.” Ajiyar zuciya ta ja “A sanin da nayi ke ɗin ba ƴar fari ba ce, ballantana in ce sokoncin ƴar fari ke damun ki, Allah ya ba ki mijin nuna ma sa’a za ki wasa da damarki, ga shi inda suke burgeni akwai riƙe addini, na sani miskilayen maza, musamman waɗanda suke ganin sun haɗu ta fannin kyawun halitta uwa uba ga aljihunsu suna jin ya cika, ga wayewa ta ilimi, to fa sai ka sa Juriya da haƙuri me yawa. Amma ina me tabbatar maki da yar jamia a ka ɗauko masa da sai ya raina kansa, Tsaf za ta yi maganinsa. Amma ko ke ɗin kika bani haɗin kai za ki sha mamaki sai ya gane ba shi da wayo.”

Wardrobe ɗi na ta ce, Tana son ganin kayan aurena. Na buɗe na ciro, Ina buɗe akwatunan tana kallo ganin dunkunan simple style ɗin kawai na yi amfani da su, amma duk daukacin fitted ɗin ban taɓa ba, Cikin wani takaicin ta dube ni, “Su ma duk dan kar ya ga Jikin naki kika ƙi saka su? Ɗaga mata kai nayi kwafa tayi Ta duba in da kayan make-up suke Su ma wa’annan ba’a taɓa ba? Zunɓuro mata baki nayi ta buɗe kit ta ɗauko daga Haɗaɗɗun sarƙa da ƴan kunnaye zuwa abin hannu da agogo da zobuna, ta ce, “Su ma wa’annan duk a banza?” Na ce, “To wai ni ina ma nake zuwa? Hararata tayi “Yar kauye kawai” Na ce “Ah ah daina ce ma garinmu ƙauye.” Ta ce “Dole in ce masa daga kin bada su a wajena” Dan murmushi na yi “Ni kuwa idan aka bar ni zan ce duk local Government ɗin Nigeria bayan Malumfashi suke.” Yar dariya tayi faɗi kike a wajen ki ba?

“Dama wajena mana daga ban da sama da ita.” Na kai hannu na yanki Apple da ƴar wuƙar da ke hannuna, na kai baki na fara taunawa. English wears ta fara Warewa, Ta riƙe kunnena har sai da nayi ƙara.

Na ce, “Wai ke kin manta bani da lafiya? ta saki kunnen dan haka ma ta tsaya a jan kunnen da ranƙwashi zan maki, Allah kar kiji batun wasa matuƙar maigidan yana nan wa’annan sune kayanki, Cin abincin ma zan ce dear ya ɗaga ƙafa har sai kun ƙare amarci, ko ya riƙa ai ko direba yana amsar masa.

Kallonta na yi, “Ke ba ki ga ruwa ba za ki kama shuka, Wannan kayan idan na sa a ina zasu maƙale min?” Ta ce, “Koma ina ne, masu neman wuta ma suka sanya ballantana ke in kin sa ka aljanna ki ke nema. Ta fara jera kayan kwalliya kan dressing mirrow. Tana yi tana mita.

“Bahaushe ya ce In kana da kyau ka kara da wanka. Kin wani kimshe su auren da aka ce yana neman yi idan bai maki sallamar da kike nema ba ciwon zuciya ya wuce da ke karara kishi ya bayyana a fuskata ko lura da hakan da ta yi sai tayi saurin cewa,

“Ba ki san yana neman wata tsaleliyar yarinya a Maiduguri ba? Kar ki so ganinta wata fara mai matsakaicin tsawo tana da dan jiki haka kadan amma ta fi a kasan ta maana daga mazaunan ta, tana da kafadu waanda suka taimaka ma brest din ta tsayawa cak ko da suke manya, tana da fuska me kyau da lallausan gashin kai.”

Dan tsaki na ja ina tura baki da na gane waskewa tayi ta wayance da siffanta ‘kirata bata san na riga na ji maganar su da Abdullahi ba da alama subutar baki ta yi.

“Ina turarukan da na kawo maki? Na nuna mata lokar da na ajiye su ta bude ta dauko ledar ta shiga min bayanin su Ba wai dan kamshi kawai ba har da gyaran jiki, ta jawo bunner ta jona bayan ta zuba wani turare sai da ya dau zafi ta cire. Sa ta cikin zanen ki turirin na shiga gaban ki.”

Da karfi na ce, “Wai ke kin manta ba ni da lafiya ne? Ta ce “Yi hakuri ba wai ina nufin yau za’a yi abin ba kawai tsumaki zan yi” Na amsa na yi yadda ta ce ta jika wani sassake kafin in tafi sai kin shanye shi ganin kallon da nake mata ya sa ta ce, “Da kin san in da aka hado kayan nan da ba ki masu gani gani ba na musamman ne da aka hado min na gyaran amare.”

Ba mu ankara ba sai gani muka yi lokacin sallar magrib ya yi. Sai da ta fara alwalar kafin na yi da na idar na shiga wanka na fito na samu ta Ajiye min riga da wando Irin na mutanen India da gyalen su Kwalliya na yi sosai ina kamshi Sannan na sa kayan kalar su pink ne rigar ta kama ni ta fidda surata da nake jin nauyi a rika dubana a haka. na yane jikina sa gyalen su ta ja ni zuwa falo.

Tana zuba mana abincin da ta yi ina barci, tana gaya min irin kyan da na yi ni dai cikin dar_dar nake zaune dan na san mai wurin ya kusa dawowa. Gyaran muryarsa da muka ji yasa na soma mutsu mutsun neman gyalena wanda Khausar ta take na kuma san tana sane. Cikin faran faran suka gaisa, ya ce, “In zo kenan in kai amaryar mu gida.”

Ta ce, “Ah ah ka huta kawai, direba zai zo dama 8:pm muka yi da shi.” Zungurin da take min yasa na ce, “Sannu da zuwa” Fuskarsa ce ta sauya, ya dan hade fuska ya shige. Dai dai nan wayarta ta shiga ringing ta daga tana cewa, za ta fito yanzu. Ta mike ta hada kayan abincin.

Na ce, “Dama kin bar su” Ta ce, “Ke da ba ki jin dadi.” Sai da ta kai su Kitchen ta dawo sai ta rataya jakarta tare muka fito, bayan tayi sallama da Ahmad. Da ta shiga motar ta dan rage glass.

“Ki kara hakuri duk wanda ki ka ji ya ce ya yi shi bai ci ribar shi ba to kadan ya yi. in sha Allah komai zai zo iyaka. Na gyada kai.

“Haka ne, na gode kwarai ubangiji ya saka da alheri Allah ya bar kauna sai yaushe?” “Jibi zan biyo ai kafin in wuce.” Daga nan kuma sai Allah ya sake sadamu direba ya ja suka tafi.” Na koma falo na same shi News yake kallo yana cin wani abu da ban tantance ko meye ba. ban san yana kallona ba sai da na murda kofar dakina zan shiga ya ce, “Ya jikin? Kamar me rada, ban waiwaya ba na ce “Da sauki”. Na shiga na canza kayan jikina nayi addu’o’ina na kwanta.

Da safe na tashi garas, na yi wa Allah godiya. Wanka na yi na yi kwalliya da atamfa Holland dinkin fitted ne da ya zauna a jikina. Na kishingida kan kujera kwaya daya da ke dakin, ban sha’awar cin komai dan bakina ba dadi, karatun Al-kur’ani cikin suratu kahfi na ji ya kunna daga falon idona a lumshe nake bin karatun, murda kofar da aka yi yasa ni daga kai, ganin shi yasa ni saurin gyara zama na shiga gaishe shi, kamar kullun ya amsa, ya ce, “Ya jiki?. Na ce Da sauki “Abdullahi na falo ya zo gaishe ki “To” na ce,

Na lalubi hijab dina na zura sai na bi bayan sa Abdullahi tsokana ta ya fara yi “Ka ga mara lafiyar ta samu.” Dan murmushi na yi “Alhamdulillahi” Na yi masa godiyar dawainiyar da ya yi da ni. Bai amsa ba sai dai ya yi murmushi suka fita da Ahmad. Ahmad Ashe wai fitar nan da ya yi sokoto ya nufa Sai Tonny ke gaya min kamar in yi kuka sai na ga to dan me in dai yi hakurin In sha Allah ina sa ran ganin sakamakonsa ko ba yanzu ba.

Khausar ta zo mun yi sallama inda na bata abinda na sa Tonny ya sawo min na ce ta kai wa mamanta. mun rabu cikin begen juna ta bar ni cikin kewar alherinta me yawa a gare ni.

Na ci gaba da amfani da magungunan da ta kawo min dan na yi imani ba za ta cutar da ni ba. Sai da Ahmad ya yi mako guda ya dawo bai amsa sannu da zuwan da na yi masa ba, abin sosai ya bata min rai da na dawo daki na kalli kaina tsaf sanye nake cikin riga da siket na material sai na kawo doguwar hijabi na baka na sanya, na zare hijabin Na zauna bakin gado tare da tagumi hannu bi biyu. Ta waya nayi wa Khausar murnar aurenta da aka ɗaura, har take faɗa min ina ta ma angonki tsiyar me yasa bai taho min da ke ba, ya ke gaya min daga sokoto ya ke. Ni dai uhum kawai na iya cewa.

Washegarin dawowarsa, na tashi da wata matsananciyar yunwar da na riƙa ji kamar an kwashe min ƴan ciki, a daddafe na kai ƙarfe takwas kan sallayata, kasa haƙuri na yi in yi wanka, Sai kawai na zare zanen da na ɗaura saman rigar barcina da zan yi sallah, na zare hijab ɗin Na fito haka, ba tare da tunanin rigar barcin tawa guntuwa ce zuwa gwiwa, Hannunta na shimi ne kalarta baka me kama jiki. Na isa kitchen na jona kettle, Maimakon jira sai na fasa ƙwai na soya, Kamar in zauna kitchen ɗin in ci Sai kuma na ga gara in tafi ɗakina kar Ahmad ya fito sai a sannan ma na tuna da shi, A faranti me faɗi na shirya komai, Ina fitowa muka yi kacibis, mugun gamo in ji hausawa.

Ya yi kyau kwarai cikin shigar suit ƙamshin shi ya mamaye wurin, sosai ya burge ni, a kallon da na samu yi masa sau ɗaya, na sunkuyar da kaina. Sai a sannan na tuna yadda na fito ƙafafuwana har rawa suke, kamar zan kifar da farantin dan tsananin ruɗewa, muryata na sarƙewa, nayi ƙoƙarin gaishe shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 7Canjin Bazata 9 >>

1 thought on “Canjin Bazata 8”

  1. Ah to! Gaskiya dai ya kamata mata su gyara, don bazai yiwu kina nan kullum jiya iyau ba kuma kice wai dole sai shi namijin ne zai zo ya neme ki, mazan yanzu ba irin na da ba ne.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×