Skip to content
Part 5 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Tun bayan da Abbas ya taya Asma’u kimtsa jikinta take kwance a yalwataccen ƙirjinsa tamkar ƙaramar yarinya, cike da so gami da tausayin ta ya kai bakinsa a masarrafan sautinta, sassauta murya ya yi sannan ya ce “Ba zan hana ki kuka ba Asmy, amma don Allah ki yi kaɗan saboda bana son asarar tsadaddin hawayenki”, tamkar zai maida ta a ciki ya ƙarashe maganar, don burinsa bai wuce yi mata abin da zata dena kukan da take yi cikin shaƙaƙƙiyar murya ba.

Ita kuwa maimakon salonsa ya yi tasiri a kanta, sai ma ya ƙara mata tsanarsa, saboda ba ƙaramar wahala ta sha a hannunsa ba, kuma hakan ya samo asali ne da rashin son kasancewa tare da shi, domin ta daɗe da saudakar da ruhinta ga Alhaji Nas, gangar jikin ne take yaƙin neman ƴancin mallaka mashi, wanda kuma Abbas ya samu galaba a kanta.
Idanunta a rufe ta yunƙura da nufin raba jikinta da nashi, wani irin zugi ne ta ji ya game mata illahirin jiki, “Wai Allah” ta faɗa cikin muryar kuka tare da komawa ta kwanta, cike da kulawa Abbas ya cigaba da shafar bayanta gami da faɗin “Ki yi kwanciyarki a nan har safe”. Maganganu masu tausasa zuciya ya cigaba da faɗa mata a kunne, take kuwa suka yi tasiri a ranta, domin zuciya ta fara haska mata a ƙirjin Nas take kwance ba Abbas ba, aikuwa cikin ƙanƙanen lokaci jikinta ya yi sanyin da ta sakar ma Abbas shi ba tare da ta sani ba. Shi kuwa abin nema ya samu, riritawa ta musamman ya cigaba yi mata har bacci mai nauyin ya ɗauke ta.

Ƙanƙame ta Abbas ya yi, lokaci ɗaya kuma ya lumshe idanu, a ranshi ya cigaba da yi ma Allah godiya bisa ga cikar muradinsa, domin a yau ya ji abin da sauran mazaje suke ji a ranar da suka fara tarawa da iyalansu. Ya ɗauki daƙiƙu masu tsayi kafin ya kwantar da ita a kan fillown dake gabansa, daga kwancen da yake ya miƙa hannu a kan stool ɗin gefensa ya ɗauki waya, haska fuskar Asma’u da ta fara kumbura saboda kuka ya yi, bakinsa ɗauke da dariya ya ɗan ja bakinta da ta tsuke kafin ya ce “Asma’u rigima”, kafe kyakkyawar fuskarta ya yi da idanu, take ƙaunar da yake mata ta ƙara samun mazauni na musamman a cikin zuciyarsa bisa ga tuna yadda ya same ta da cikakken mutuncinta na ƴa mace, duk da dama yana da yaƙinin haka, domin Asma’unsa ba daga baya ba wurin kamun kai.

“Ina son ki Asma’u”, ya faɗa tare da sumbatar ɗan ƙaramin bakinta, addu’a ya shafe mata jiki da ita, daga bisani ya shigar da ita a jikinsa ya lumshe idanu, bacci mai daɗin gaske ne shi ma ya tafi da shi.

Haka zuciyarsa ta kwana cike da farinciki, inda Asma’u kuma ta kasance mai baƙincikin wargaje mata shiri da ya yi.

Da gari ya waye kuwa, yana dawowa daga sallar Asuba kitchen ya nufa, ruwa wanka ya haɗa mata a electric kettel sannan ya dawo ɗakin, kai tsaye bedroom ya nufa, inda ya same ta a kan abin sallah tana azkar, zama ya yi gefenta duk da wurin ba wata yalwa gare shi ba, kasantuwar ɗakin ƙarami ne. Danna power wayarsa dake hannunsa ya yi, kai tsaye facebok ya shiga, take kuwa ya ci karo da love letter challenge ɗin da ake yi a Group ɗin Home of Solace. Asma’u kuwa tamkar ba mutum a gefenta, dan tun da ya shigo ɗakin ƙafafunsa kaɗai ta kalla, shi ma dan ta gabanta ya wuce da ba zata kalle su ba, tunawa ta yi da yadda ya rikice mata a daren jiya, mai makon hakan ya faranta ranta, don kowace mace tana son ta ga mijinta ya gigice a kanta, wani irin haushinsa ne ya cigaba da bayyana a fuskarta, musamman da ta lura da yadda yake kallon waya yana kwasar dariya, “Allah ka raba ni da wannan mutumin”, ta faɗa a ranta, don a ɓangarenta babu wani abin birgewa a tattare da Abbas.

Shi kuwa bayan ya gama dariyar ne ya ƙara matsowa kusa da ita, fuskarsa ɗauke da tsantsar nishaɗi ya ce “Madam ki shafa hakanan, sai mu gaisa ko”, hannunsa a kan cinyarta ya ƙarashe maganar. Yar! Asma’u ta ji a jikinta, kallon sa ta yi, aikuwa ya kashe mata ido, sosai ya bata dariya, amma fa ta ganin gazawarsa a kan son ya birge ta. Dariyar shi ma ya yi gami da ruƙo hannunta wanda ke riƙe da charbi “Ina kwana Asmy”, ba tare da ta kalle shi ba ta ce “An tashi lafiya”, ya ce “Ƙalau, ya jikin”, a taƙaice ta ce “Da sauƙi.”

Ya daɗe da fahimtar bata son yana liƙe mata, mafarin suna gama gaisawa ya miƙe, amma ba don ranshi ya so ba, kitchen ya koma, inda ya taras har ruwan sun tafasa, fitowa ya yi ya zuba ruwa a babban bokiti, sannan ya koma kitchen ɗin ya juye ruwan, a yadda ya ƙimanta sirka ruwan ya san zafinsu ba zai cutar da Asma’u ba, ɗaukar bokitin ya yi ya kai banɗaki, ƙasan ransa kuma yana ta jin haushin rashin gina banɗaki a bedroom ɗinsa, da yanzu asirinsa da na matarsa rufe zasu yi ta hidimarsu a can. “Allah ka ƙara mani arziki mai yawa na halak, wanda zan gina ƙaton gidan da zamu yi yalwatacciyar rayuwa ni da iyalina”, da wannan addu’ar a bakinsa ya koma ɗakin, tsaye ya samu Asma’u ta cije laɓe, wanda ke nuna tafiya na mata wahala, da sauri ya ƙaraso inda take “Sannu”, ya furta cikin tausayawa, idanunta a rumtse ta ce “Sannun ƙaniya”, don duk sadda ta ji zafi, sai tsanarsa ta ƙaru a ranta, cewa ya yi “Ga ruwa can na haɗa maki, mu je ki ƙara gasa jikinki”. Tuni Asma’u ta san muhimmancin ruwan ɗumi, don duk abin da ta san zai amfani lafiyar mace tana amfani da shi daidai gwargwado, saboda ta yi ma kanta tsarin rayuwa da Nas wadda ba zai ga gazawarta ba, sai dai kuma ƙaddara ta rushe mata wannan tsarin, tunda ta haɗa ta da Abbas, “Toh” kawai ta ce tare da ɗaga ƙafar da ƙyal, aikuwa bata ankare ba sai ji ta yi Abbas ya yi sama da ita, ta kuma ji daɗin ɗaukar, domin ba zata iya kai kanta ba, bai dire ta ko ina ba sai ƙuƙutaccen banɗakin wanda filin wankan ba wani mai yalwa bane, cikin sigar zaulaya ya ce “In gasa maki ko?”, hararar shi ta yi,
dariya ya yi sannan ya fito banɗakin.

Waje ya tsaya har ta gama. A yadda ya ga ta ɗangyaso ta fito ne ya ƙara tabbatar mashi da sirrin dake cikin ruwan ɗumi, wannan karon hannunta ya kama suka koma ciki. Doguwar riga mai ɗan nauyi ya fiddo mata a wardrob ta sanya, kwantawa ta yi a gefen godo, shi kuma ya lulluɓa mata bargo, a saitin kunnenta ya raɗa mata “Yi baccinki ki huta, yau ni zan yi komai”, yana rufe baki ya sumbace ta a kumci.

Ina ma Asma’u tana ƙaunar Abbas, da ta kwashi romon demkraɗiyyar ƙaunarsa, toh Nas ya yi mata kutsen da sai ta jingina Abbas da shi sannan ta ji daɗin kulawar da Abbas ɗin ke bata.

Kamar yadda Abbas ya ce shi zai yi aikin gidan haka aka yi, shara da wanke-wanke ya fara, yana gamawa ya haɗa musu breakfast, Tea da bread ne da wainar ƙwai, don duk da Abbas ba wasu kuɗi gare shi ba, amma ana cin abinci mai kyau a gidansa. Tada Asma’u ya yi daga bacci suka yi breakfast ɗin, suna gamawa ya raɓa gefenta kan gado ya kwanta.

Bai tashi ba sai wurin ƙarfe shabiyu, Kitchen ya nufa ya dafa cuscus, dan shi ya fi sauƙi, akwai ragowar miyar jiya, wadda ba wani daɗin kirki ta yi ba. Tada Asma’u ya yi, inda ya ji jikinta da zazzaɓi.

Lallaɓata ya yi ta sake gasa jikinta gami da yin alwalar azuhur, shi ma alwalar ya yi ya nufi masallaci, ana gama sallah ya wuce pharmacy ya siyo mata magunguna masu kyau, don ji yake tamkar a jikinsa zazzaɓin yake. Kwance ya same ta falo a kan doguwar kujera, cike da kulawa ya russuna gabanta, lokaci ɗaya kuma ya taɓa wuyanta “Sannu” ya faɗa cikin sigar tausayawa, don jikinta kamar murfin tukunyar dake kan wuta.

Ba tare da ta buɗe idanu ba ta cira kai, don ta san takaicin tsanarsa ne zai cika mata zuciya idan ta haɗa idanu da shi.

“Tashi ki sha maganin”, ya sake faɗa yana duban ta, shiru ta yi kamar ba da ita yake ba, sai da ya sake cewa “Kin ji”, sannan ta ɗan motsa gami da buɗe idanu. Aje maganin ya yi a ƙasan carpet sannan ya miƙe , ɗago kafaɗunta ya yi ta tashi zaune. Fita ya sake yi ya zubo masu cuscus da kuma ruwa a Jug, gefenta ya zauna a kan kujera ya riƙa bata a baki, lokaci ɗaya shi ma yana ci, ba laifi ta ɗan ci, kasantuwar cuscus mutuminta ne, maida plate ɗin ya yi a kitchen sannan ya dawo ya bata magungunan ta sha.

Gani ya yi ta jingina bayanta da kujera ta lumshe idanu, ba tare da ya yi mata magana ba ya saɓe ta suka nufi bedroom, sun kwanta kenan wayarsa ta ɗauki ruri, yana dubawa ya ga ƙanwarsa ce Abeeda, ɗaga kiran ya yi, bayan ya amsa sallamar da ta yi mashi ne ya ce “Ya aka yi?”, daga can ta ce “Wai kun je unguwa ne, an zo gidan a rufe?”, idanunsa a kan Asma’u ya ce “A’a muna nan, Asma’u ce bata jin daɗi”, yana ji daga can Abeeda ta yi magana “Umma wai suna nan”, a nan ya fahimci mahaifiyarsu na kusa da Abeedar.

Tambayar ta ya yi “A buɗe gidan ne?”, amsa ta ba shi “A’a ku bar shi”, ɗan cira kai ya yi “Okay”, sannan ya aje wayar kan stool, don Abeeda ta riga shi tsinke kiran.

Fita ya yi gami da buɗe gidan, duk da baya son wani ya shigo ya matsa ma matarshi, yana dawowa ya zauna a falo, karatun Al-ƙur’ani mai girma ya kunna yana sauraro, Asma’u kuma baccinta ta sha son ranta.

A wannan wuni kuwa ta ga zallar kulawa a wurin Abbas, domin wuni ta yi zungur a jikinsa yana ririta ta, sai dai har a ranta ba gode bare nagode, sai ma kallon wahalalle mai ɗauke da cutar son maso wani da ta riƙa yi mashi.

Cikin ikon Allah kuma magungunan da ta sha sun karɓe ta, sosai ta samu sauƙi, don a daren Abbas sai da ya so kasancewa tare da ita amma tsana da tsoro suka hana ta bashi haƙƙinsa, shi ma ko da ya ga ta ƙiya sai bai matsa mata ba.

Yana daga cikin halin Abbas na kirki idan ya yi alƙawali baya saɓawa, bugu da ƙari kuma baya ɗaukar dogon lokaci wurin cika alƙawarin in dai ya samu dama, shi ya sa duk wanda ke da alaƙa da shi yake ƙaunar shi.

Wayar da ya yi ma Asma’u alƙawari ne ya yi mata albishir suna tsaka da cin abin rana, kasantuwar ta samu sauƙi har ta fara girki.

Take fuskar Asma’u ta cika da yalwa, domin waya na ɗaya daga cikin manyan burikanta. Tambayar ta ya yi “Tare zamu je ki zaɓa ko?”, kai ta ɗaga alamar “Eh” tana ƴar dariya, cewa ya yi “A’a, ke da ba kya lafiya?”, ɗan marairaice fuska ta yi “Na ji sauƙi fa”, ya ce “Da gaske?”, ta ce “Eh mana”, ya ce “Toh bari mu je bedroom ki tabbatar mani”, ido ta ɗan zaro dan ta fahimci inda ya dosa, dariya ya yi gami da faɗin “Ko sai mun siyo wayar zaki bani tukuici?”, ƴar harara ta wurga mashi tana dariyar da ya kasa gane yaƙe ce, don har cikin ranta ba abin da zai yi wanda zai birge ta.

Gab da Magarib ne ya ce ta je gidansu ta gaishe da mahaifiyarshi, idan ya dawo bayan isha’i sai su je siyo wayar, ba don Asma’u na son fita ba, da ba inda zata je. Hijabinta ta sanya, suka fita tare.

Kai tsaye gidansu Abbas da ke farkon layin baya suka nufa, inda Abbas ke tura mashin, ita kuma tana ƙasa, tunda suka fito Asma’u bata ce komai ba, sai dai shi ke ta zuba kamar kanyar da ba daɗi, suna zuwa ƙofar gidansu Abbas ta ja tunga a ƙarƙashin bishiyar dirimin da ke dab da shiga gidan, kafe mashin ɗin ya yi shi ma a ƙarƙashin bishiyar sannan ya ce “Mu je ko”, gaba ta yi a soron gidan mai ɗan duhu, hannun ta ya ruƙo, sannan ya yi magana ƙasa-ƙasa “Ki saki fuska fa, kada Umma ta ce na yi ma ɗiyarta wani abu”, don ya lura da yadda ta haɗe rai da suka zo ƙofar gidan, ƴar dariya maganarshi ta bata, da sallama suka shiga, A tsakar gidan mai ɗauke da ɗaukuna uku a suka sai rijiya da banɗaki suka iske Ummansu Abbas, sai Zainab, wannan ƴar gayun da ke birge Asma’u, da kuma Abeeda a kan ƙatuwar tabarma suna hira.

Har ƙasa Asma’u ta durƙusa ta gaida mahaifiyar Abbas, amma fa ba don girmamawa na kasancewar ta suruka ba, kawai dai haka ta saba gaida manya tun tana ƙarama.

Cike da fara’a mahaifiyar Abbas ta amsa gaisuwar gami da faɗin “Ya ƙarfin jikin”, a taƙaice Asma’u ta ce “Da sauƙi”, daidaita zamanta ta yi kan tabarmar, Zainab da ke kusa da ita ta ce “Amarya ashe ba lafiya?”, Ƴar dariya Asma’u ta yi “Wallahi kuwa”, Maimakon Zainab ta jajanta mata sai ta shiga tsokanarta “Amarya ko dai an shiga layinmu” Asma’u bata fahimci me take nufi ba, Abeeda da yake ba laifi ta girmi Asma’u ta ce “Kai Aunty Zee, gaban suruka take fa”, dariya su duka suka yi, Abbas da tunda ya shigo yake tsaye ya ce ma Abeeda “Faɗa mata dai”, kasantuwar akwai abotar makaranta a tsakanin Zainab da Abbas, course mate ɗinta ne a FCE Katsina.

Sosai ganin Zainab ya sa Asma’u sakin jiki, Abbas na lura da haka ya ce tafiya zai yi, wurin mahaifiyarsu da ke girki a wani fili dake tsakanin ɗakin babansu da banɗaki, ƴar magana suka yi sannan ya tafi.

Asma’u ta sha hira sosai da Zainab, dan Abeeda da mamansu Abbas tashi suka yi suka cigaba da ayyukan gida.

Bayan Isha’i ne Abbas ya dawo, a ɗakin Innarsu ya taras da Asma’u na sallah, inda sauran yaran gidan ke cin tuwo a tsakar ɗakin, zama ya yi kan hannun kujera har Asma’u ta gama sallar, shirin tafiya suka yi, Innarsu dake a tsakar gida ta ce “Ku tsaya a sanya muku tuwon, dan Asma’u taƙi ci”, faɗa mata ya yi akwai inda zasu je.

Cewa ta yi “Unguwa yanzu da daddare, ba’a bari sai gobe?”, dariya ya yi “A’a Umma, yanzu zamu dai”, a dawo lafiya ta yi musu, suka tafi.

Kai tsaye wani babban shagon siyar da wayoyi ƙirar Infinix suka nufa, bayan ya faka mashin ɗin a gefen da mutane suka aje nasu ne ya ambaci “Asma’u”, idanun Asma’u na kan ƙayataccen shagon da ke ɗauke da haske kamar rana ta amsa “Na’am”, Abbas ya lura da sam hankalinta na kan shagon, cewa ya yi “Dube ni nan”, bayan ta kalle shi ya ce “Kin ƙagara mu shiga ko?”, zuciyar Asma’u cike da farinciki ta ɗaga kai “Ok” ya faɗa yana dariya. Cigaba da magana ya yi “Idan mun shiga zaki zaɓi kalar da kike so, amma kada ki ɗauki wayar da ta wuce dubu talatin.”

Mamaki bayyane a fuskar Asma’u ta kafe shi da idanu, bata taɓa tunanin Abbas zai iya sai mata wayar dubu goma ba, saboda kallon faƙiri da take mashi, amma shi ne zai siya mata ta dubu talatin “Ashe dama yana da kuɗi?”, ta tambayi kanta, kamar ya ji tambayar ya ce “Kin ga dai ba wasu kuɗi gare ni ba, kawai dai cikin rufin asirin Allah muke, dan haka kada ki ɗauki wayar da tafi ƙarfina”, murna bata bar Asma’u ta yi magana ba, sai dai ta ɗaga kai kawai, “Okay” ya ce, sannan ya kama hannunta suka shiga cikin shagon. Daga cikin matasa ukun da ke kula da shagon akwai wanda suka san juna shi da Abbas, dan haka Abbas ya nufi wurinsa, bayan ya sallami wani mutum da ya siya ma matarsa wayar dubu saba’in ne ya juyo wurinsu Abbas, gaisuwar yaushe gamo suka yi da Abbas, Asma’u kuma tuni murna ta fara komawa ciki, don har ta raina wayar dubu talatin ɗin bisa ga jin wanda aka sallama ya siya ma matarshi ta dubu saba’in.

Tuni ta yi zurfi cikin tunanin da Nas ne ma ƙila iPhone zai siya mata, taɓo ta Abbas ya yi “Ku gaisa mana”, fuskarta da ƴar fara’a suka gaisa, daga bisani kuma aka bata zaɓi cikin wayoyin da suke Under Fourty-K, duka wayoyin ba wadda bata da kyau, amma Infinix Smart 5A ce tafi tafiya da ita, dan haka ta nuna ta, Ana fiddota Abbas ya ce “Masha Allah, kin iya zaɓe”, domin wayar ba laifi, ita kanta a take ta dena raina ƙoƙarin Abbas, saboda wayar ta tafi da tunaninta.

Zuciyar Abbas cike da farincinkin faranta ran matarsa ya tambaye ta “Ta yi maki ko?”, kai ta ɗaga tana dariya “Sosai ta yi”, maida dubansa ya yi ga abokin nasa “Toh mu yi ciniki”. Kuɗi kaɗan Abbas ya ƙara a saman dubu talatin aka bar masu wayar, saboda baya ga sanayya, kuma customer ɗinsu ne.

Murna wurin Asma’u ba’a cewa komai, dan kasa cin tuwon da Abbas ya karɓo a gidansu bayan sun koma gida ta yi.

Karɓe wayar Abbas ya yi, don tunda ta zauna ƙasan carpet take ta jujjuya ta, chrge ya maƙala ta, sannan ya dawo gabanta da plate ɗin tuwon. Da kansa ya riƙa cusa mata shi, dan murna ta tafi da yunwar.

A wannan dare kuwa kwanan farinciki suka yi, ita tana murnar waya, shi kuma yana murnar ta bashi haɗin kai cikin sauƙin da bai zata ba.

Da Asuba bayan ya dawo masallaci ne ya zauna falo, cikin abin da bai fi minti biyar ba sai ga Asma’u ta fito, saɓanin can baya da sai ya yi zaman awa kafin ya ganta, ɓoye mamakinsa ya yi suka gaisa, daga bisani ya ɗauki wayar da tun cikin dare ya cire ta daga chrge ya kunna “Bari in saita maki ita” ya faɗa yana kallon wayar, “Toh” Asma’u ta faɗa, tare da ɗan kwantowa a jikinsa ba tare da ta sani ba tana kallon wayar.

Tun ba’a je ko ina ba waya ta rage tazarar nisan dake tsakanin Abbas da Asma’u. Sosai hakan ya sa shi nishaɗi, shige mata shi ma ya yi har ya gama saita mata komai na wayar, miƙa mata ya yi “Toh ga shi, Allah ya tsare”, karɓa ta yi “Amiin ya Allah, nagode sosai” murmushi ya yi “Toh Madallah Asmy!”

WhatsApp shi ne farkon inda ta shiga saboda bata taɓa yinsa ba. A nan ta ga contacts ɗin duk ƙawayenta ne, Sallama ta yi ma Khadija, Abbas na gani ya kama dariya “Anjima zan yi maki sub, sai ki ji daɗin chat ɗin”, sosai hakan ya yi mata daɗi.

Gari na ƙarasa wayewa ta shiga kitchen domin haɗa musu breakfast, sai dai duk abin da take hankalinta na kan waya har ta haɗa breakfast ɗin, zalƙi bai bari ta yi kalacin kirki ba. Wurin ƙarfe tara Abbas ya fita, da nufin siyo cefane.

Maimakon ta shiga gyaran gida kafin ya dawo, sai kawai ta ɗauki waya ta buɗe data..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Cikin Baure 4Cikin Baure 6 >>

3 thoughts on “Cikin Baure 5”

    1. Anan cikin app din, ka duba gefen hagu ta sama akwai menu, wasu zane uku kanana. Sai ka latsa, idan ka yi register kuma ka yi login sai ka zabi ‘subscribe.’ Zai kai ka Subscription Packages page namu, ka zabi subscription da kake so sai ka bi process din har karshe, za ka ga an baka bank acc no, sai ka biya ka turo mana da receipt ta wannan WhatsApp no: 09072304845

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×