Skip to content
Part 9 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

“Wato titsiye ni zaki yi ko?”, bakin Asma’u dauke da dariya ta jefo ma Khadijah wannan tambaya, kai Khadijah ta girgiza “A’a waace ni, kawai dai dan in san irin shawarar da zan baki wadda zata fisshe ki ne.”

‘Dan rausaya kai Asma’u ta yi “Auho!”. Shiru na wucin gadi ta yi tana nazarin hujjar da zata ba Khadijah wadda za ta gamsar da ita, sai dai tsabar nagartar Abbas ta hana ta samun wannan hujja, domin dai-dai gwargwado yana kamanta koyi da Manzon Allah SallaLlahu alaihi wa sallam a wurin kyautata ma iyalinsa, sai dai duk da haka yana da ajizanci irin na ‘dan adam.

“Ko ba ki da hujja ne?”, Khadijah ta sake tambayar ta. “Ni kuwa ke da hujja”, khadijah ta ce “Wace hujja ce?.”

Asma’u ta ce “Toh Mutum a bushe kamar citta mana, kin san dai Abbas ba wani jiki ne da shi ba, kuma kin fi kowa sanin yadda na tsani ramammen namiji”, cike da kwarin guiwa ta ba Khadija wannan amsa da ta samo dakyal, kuma a zahirin gaskiya hujja ce da ke ci mata tuwo a kwarya, mafarin duk sadda ta kalli Abbas ramarsa ke haifar mata da kuna a ranta.

Sosai maganarta ta sa Khadijah dariya hada kwalla, itama Asma’un dariyar ta shiga yi, sai da suka yi mai isar su sannan Khadijah ta ce “Kai Asma’u, wai a bushe kamar citta”, wata dariyar Asma’u ta tuntsure da ita “Toh kamar citta mana, Allah kuwa rashin kibar shi na kona mani rai”, Khadijah ta ce “Ai rashin kiba bai yi ba, amma daga wannan ban ga abin ‘ki a jikin Abbas ba, dan baya da makusa, kuma a ganina in zai samu kyakkyawar kulawa a wurinki zai yi ‘kiba.”

Baki Asma’u ta tabe, lokaci daya kuma ta karkace kai “Ke wannan kowace kulawa zai samu ba zai yi kiba ba”, Khadijah ta ce “Bai samu ba dai, kuma idan kina tantama ki gwada nuna mashi so ki ga ikon Allah”, hade fuska Asma’u ta yi dan abin da ba zata iya ne ba “Aikuwa sai dai ya mutu a bushe. Ni fa bana kallon Abbas ma a matsayin miji bare har in iya kula da shi.”

Khadija ta fahimci da gaske Asma’u ta ke kin Abbas, mafarin ta fito mata da gaskiyar shawarar da take son ba ta, inda ta nuna mata illar dake cikin jifar gafiyar ɓaidun da take shirin yi, don bata da tabbas din idan ta rabu da Abbas za ta samu wanda ya fi shi. Sannan ta nuna mata ta cire batun halitta a cikin jerin abubuwan da za su sanya ta so Abbas, domin idan ana duba wannan bangaren ita kanta ba za a rasa wani nakasu a halittarta ba, duk da kyawun da take ganin tana da shi, don haka ta rika kallon kyawun halinsa, ba halittarsa ba.

Duk wadannan maganganu da Khadijah ta yi basu samu damar shiga a wurin Asma’u ba, mafarin itama ta kauda wasa a cikin maganar ta ce “Khadijah ba ki fahimci irin tsanar da na yi ma Abbas ba ne shi ya sa kike son manna mani shi a zuciya”, hannun Khadijah rike da haba ta ce “Toh fahimtar da ni.”

A tsakaninsu ba boye-boye, dan haka Asma’u ta bude mata sirrin cikinta, cewar akwai wanda ta dade da mallaka ma kaunarshi yalwatacce mazauni a cikin zuciyarta, wanda har ta kai Abbas ya kasa samun inda zai ra’ba ya ji dadi a cikinta. Cike da son sanin ko waye Khadijah ta tambaye ta “Waye wannan mai sa’ar haka da ki ka yo dakon son shi har gidan aurenki?”, take wannan tambaya ta fama ma Asma’u ciwon son Alhaji Nas, zuciyarta dake ta harba sakon kaunarshi izuwa sassan jikinta ta dafe tare da lumshe idanu “Wani kyakkyawan Alhaji ne, wanda sai anan gaba zaki san cikakken sunanshi”, guntuwar dariyar takaici Khadija ta yi “Allah ya sa dai shi ma yana irin wannan haukan a kanki, dan na ga kin yi nisan da sai wani ikon Allah za ki iya jiyo kira”. Nan fa daya! Domin Nas bai san da zaman wata Asma’u ba a duniyar nan ta Maliki yaumiddini. Sai dai a nata bangaren wannan ba wani abin damuwa bane kasantuwarta mace, in dai ta samu Abbas ya rabu da ita, toh gata can ta yi salon da zata kai kanta gare shi, wanda kuma tuni ta gama wannan tsarin.

“Ai ya fi ni shiga yanayi ma, ke dai ki taya ni da addu’a Allah ya raba ni da wannan makalematan”, kwafa Khadija ta yi “Uhm! Allah ya shirye ki dai, ni dai shawarata gareki ita ce ki rike mijinki gam!, Dan muddin ki ka yi sakaci a kansa toh nadama ce zata biyo baya”, Asma’u ta ce “A ganinki ba”, Khadijah ta ce “Kwarai, shawara ya rage ma mai shiga rijiya, ko ki bi mijinki ki zauna lafiya, ko kuma ki bi son zuciyarki ki yi nadama.”

“Uhm! Ni a bar maganar ma”, Asma’u ta fada, dan ta lura kamar Khadija ta yi fushi, Khadijah ta ce “An bari.” Wayarta dake kan hannun kujera ta dauka tare da danna manhajar Dakandamiya Hikaya dake jere a cikin Apps din wayar, zuciyarta cike da farincikin samun abin da ta je nema ta ce “Yes sun d’ora”, tambayar ta Asma’u ta yi “Me?” bayan ta dawo kusa da ita, idanun Khadija na kan screen din wayar ta ce “Sabon update na audion littafin KO RUWA NA GAMA BA KI”, da yake Asma’u ta san littafin ta tambaye ta “Yaushe aka maida shi audio?”, Khadijah ta ce “Kwanan nan kuwa, manhajar BAKANDAMIYA ke da wannan aikin, kin san yanzu su ne gatan marubuta”, Cike da mamaki Asma’u ta ɗan ja magana “Toooh!”, lokaci daya kuma ta baza masarrafan sautinta ga audion da Khadija ta yi playing. Shiru ne ya ratsa falon kamar ba kowa a cikinsa sai wannan sauti, gabadayansu sun maida dukkan nutsuwarsu ga wayar suna sauraron irin muguwar sakayyar da Habeeb ya yi ma Jummai, duk kuwa da sadaukarwar mutuncinta na ‘ya mace da ta yi mashi.

“Namiji d’an babansa”, Khadijah ta fada bayan ta nisa, d’orawa Asma’u ta yi da fadin “Ai hada mamansa ma, yanzu duk soyayyar da ke tsakaninsu ta kare a jin haushin juna”, Khadijah ta ce “Toh ai sun biye ma son zuciyarsu ne, yanzu idan ba kaddara da rudin shaidan ba me zai kai budurwa mika ma saurayi kanta?”, Asma’u ta ce “Wallahi kuwa, ai ga shi nan ya barta da ciki, wanda kuma shi ne tozarci mafi muni a gareta da kuma mahaifanta”, Khadijah da ta san addu’a ce kadai mafita ta ce “Allah dai ya tsare mu da bakar kaddara”, Asma’u ta ce “Amiin.” Domin a wannan karshen zamanin wayo da dubarar mutum ba sa fidda shi madamar bai koma ga Allah ba tare da kiyaye dokokinshi. Cigaba da sauraron audion suka yi har Abbas ya dawo ba tare da sun sani ba. Sallamar da ya yi a bakin kofar dakin ce ta ankarar da su, amsawa suka yi, Asma’u ta dube shi lokacin da ya dage labulen dakin, Khadijah kuma kanta na kan wayar tana kokarin rage sautinta.

“An dawo kenan?” Asma’u ta tambaye shi”, “Eh” ya ce yana kokarin zama kan hannun kujerar da ke bakin ƙofa. Sannu suka yi mashi, bayan ya amsa ya mika masu manyan ledojin da ke hannunsa, karba Asma’u ta yi, tare da kara yi mashi sannu kamar abin arziki, ya kuma ji dadin haka sosai, saboda bai son duniya ta shaida rashin matsayinsa a wurinta.

Mikewa ya yi “Zo Asmy”, sannan ya juya ya fita, sai da ta murguda baki sannan ta mike, tafkar mata baya Khadijah ta yi dan ta ga sadda ta murguda bakin, fita ta yi daga dakin tana dariya. Dab da soro ta iske shi tsaye “Gani”, ta faɗa a takaice, idanunsa cikin nata ya ce “Komawa zan yi, kuma kila ni da dawowa sai yamma insha Allah, saboda muna da aikin blocks sosai”, haka Asma’u take so dama, dan haka ta yi murmushin jin dadi. Fada mata ya yi idan Khadija ta tashi tafiya ta dauki abin da ta ga ya dace a cikin kudinsa ta bata, “Ok” ta ce tare da yi mashi Allah kiyaye da zai tafi, kasan ranta kuma tana jin ina ma idan ya tafi kada ya dawo har abada.

Kitchen ta biya ta dauko plates biyu da cups gami da spoons sannan ta shiga daki, rashewa ta yi kasa, hannunta na kan manyan Purples din ledojin ta dubi Khadija “Madam shido mu yi ci wannan”, dan langabar da kai Khadijah ta yi tana duban ta “Mu yi sallah mana”, kasantuwar an fara kiran azuhur, yamutse fuska Asma’u ta yi “Yunwa fa nake ji”, Khadijah ta ce “Toh ki ci mana”, girza kai ta yi “A’a mu yi sallar dai.”

Sallar suka gabatar, ba tare da sun matsa daga kan sallayar ba Asma’u ta jawo plates din. Alalar da ta bukata ce ya siyo musu, sai kuma farin dambun shinkafa da kuma farfesun ‘yan ciki, bangare daya kuma ga zundumemen lemun Exotic. Juye dambun ta yi a plate daya, Khadijah kuma ta juye farfesun a dayan plate din wanda kamshinsa ya game dakin, alalen kuma suka aza ta a kan dambun. Tun kafin su fara ci Khadija ta dubi abincin, lokaci daya kuma ta dubi Asma’u, “Yanzu wanda ke maki wannan gatan ne bakya so ko?”, dan ko shakka babu Abbas ya kashe kudade masu yawa kafin ya hada masu wannan abincin.

A gaggauce Asma’u ta hade lomar bakinta gami da hade rai “Zaki fara ko?”, Khadijah ta ce “Eh”, Asma’u ta ce “Bari mu gama to, sai in aro maki Loudspeaker yadda za ki ji dadin wa’azin”, guntun tsaki Khadijah ta ja tare da yin kwafa, cikin ranta kuma tana mamakin dolanci irin na Asma’u.

Dariya Asma’u ta yi suka cigaba da cin abincin. Ko da gamawar su suka dasa sauraron audion Ko RUWA NA GAMA BA KI. A nan Asma’u ta bukaci Khadijah ta bata link din audion. A take ta tura mata hikaya.bakandamiya.com a Whatsapp. Ta kuma fada mata a can za su bata option din maido shi a home screen dinta.

Wurin karfe uku ne suka fito tsakar gida. A nan kuma Khadijah ta shiga hidimar yi ma Asma’u share-share, tana gamawa kuma ta dasa da wanke-wanke, inda Asma’u ta taya ta da dauraya. Cikin kankanen lokaci komai na gidan ya yi tsaf, sabanin yadda Khadijah ta iske shi duk ya yi kura.

Da yamma likis ne kuma Khadijar ta fara shirin tafiya. Kudi da turare Asma’u ta dora mata a bisa jakarta da ke kan hannun kujera “Ga wannan kin sha ruwa a hanya”, fasa sanya hijabinta ta yi ta dubi Asma’u “A’a kin manta lemu zan sha”, Asma’u na dariya ta ce “Da zobo ma”, kai ta girgiza tana dariya “A’ah toh nagode. Ina laifin turaren ma”, ta karasa maganar lokacin da ta dauke dari biyar din ta aje a kan kujera. Matsa mata Asma’u ta yi a kan dole sai ta karba, ba dan ta so ba ta karba tare da yi mata godiya.

Hijabi Asma’u ta ɗauko ta yi mata rakiya har kofar gida. A nan Khadijah ta yi mata maganar ciki, wadda dama ita ce silar zuwanta gidan. Irin nasihar likita da ƴan group ɗinsu ta yi mata, cewar ta gode ma Allah da ya bata cikin, wani na can ya sadaukar da komai nashi amma bai samu ba.

Asma’u na son su rabu lafiya, dan haka ta kwantar da kai har Khadijah ta gama nasiharta kaf. Godiya ta yi mata, sannan suka rabu ba dan son rayukansu ba.

Kasa komawa gida Asma’u ta yi, don ji take kamar Khadijah ta tafi da dukkan nutsuwarta. Jawo ƙofar gidan ta yi da ƙarfi ta datse, sannan ta nufi gidan Aunty Zee domin samun wata nutsuwar a can.

Isarta ƙofar gidan ta yi dai-dai da shigowar Abbas a layin. Faɗuwa gabanta ya yi, wadda ta nasabtu da fitowarta ba tare da ya sanin ba. Danne faɗuwar gabanta ta yi, dan bata son ya ga shakkarsa a tare da ita.

Shi kuwa bai wani damu ba, dalilin kyautata mata zaton ba zata fito ba tare da dalili ba. “Gidan ba daɗi ko?”, ya tambaye ta bayan ya tsaya dab da ita, kai ta ɗaga kamar zata yi kukan baƙincikin dawowar shi, cikin sigar lallashi ya ce “Ayya! Sorry, tunda na dawo ai shikenan ko?”, kasa magana ta yi saboda takaicin da ya zo mata wuya, ko da ganin haka sai ya ƙara sassauta murya tare da ce mata ta hau mashin ɗin su ƙarasa gida, a ƙufule ta ce “Bar ni na ƙarasa da ƙafata”, tana rufe baki ta yi gaba, shi kuma ya bi bayanta a kan mashin ɗin.

Ko da isarsu gida ya same ta a falo tana duba waya, rungumo ta ya yi ta baya, lokaci ɗaya kuma ya cusa kanshi a wuyanta, “Kin ga ko ban dawo ba, bai kamata ki shiga gidan mutane dab da magrib ba”, cikin son ƙwace kanta ta ce “Toh laifi ne dan na shiga?”, girgiza kai ya yi “A’a ba laifi bane, amma ki sani baƙon magrib tafe yake da shaiɗan, don bai barin masu gidan da shi kanshi baƙon su yi sallah a kan lokaci, ga shi kuma magrib ƙurarren lokaci ne da ita.”

Shiru Asma’u ta yi tana nazarin maganarsa, bata wani ɗauki dogon lokaci ba ta gazgata maganarsa.

Tabbas baƙon magrib baya barin sallah a kan lokaci, don haka duk lokacin da mutum ya ji yana son zuwa wani gida a daidai lokacin sallah, toh ya sani shaiɗan ne ke zuga shi, dan haka sai mu kiyaye

Ko da Abbas ya lura da gamsuwarta, sai ya yi mata albishir ɗin iznin zuwa gidan Aunty Zee ba tare da tambayar shi ba, amma da sharaɗin banda zuwa dab da magrib, ko kuma magrib ɗin ta yi mata a can, godiya ta yi mashi, sannan ta zare jikinta daga nashi ta nufi bedroom.

Alwala shi ma ya fito ya yi, daga nan kuma ya tafi masallaci saboda an fara kiran sallah, bai kuma dawo gidan ba sai bayan isha’i, tare da tuwon da ya karɓo a gidansu.
Ko kaɗan Asma’u bata ci wannan tuwo ba, saboda duk ba daɗi a jikinta, bai kuma matsa mata ba, sai ma ya fita ya siyo mata fura. Da kansa ya dama mata, sannan ya lallaɓa ta kamar wata ƴar yarinya ta sha furar da magani, sannan ta kwanta.

Batun haƙƙinsa na aure kuwa fiye da sati biyu bai samu ba saboda wannan laulayin da take, faɗin kuma irin damuwar da ya shiga ma ɓarnar baki ne, kawai dai yana ta aiwatar da lamurransa ne, amma ta ciki na ciki. A daren da ya kasa jurewa ne ya nemi haƙƙinsa lokacin da ya gyara mata kanta da ya sauka daga kan pillow. Kashe fitilar wayar ya yi tare da yi mata abin da ya tabbatar mata da buƙatar haƙƙinsa yake lokacin da ta falka.

Cike da tsanar shi ta janye mashi hannu da ke zagaye da ita, lokaci ɗaya kuma ta matsa gaba. Shima matsawa ya yi gami da sake zagaye ta da hannunsa, sai dai bai ankare ba ya ji ta maido mashi hannushi a jikinshi, murya can ciki ya ce “Asma’u miye haka?”, amsa ta bashi da “Kai zan tambaya, kamar baka san bani da lafiya ba?”, ɗan sauke numfashi ya yi tare da lumshe idanu “Na san baki da lafiya mana, amma ai kin ji sauƙin da zaki iya bani haƙƙina da na daɗe ban karɓa ba ko?”, yana rufe baki ya maida hannunsa a jikinta, burinsa kawai ya samu dama akanta.

Zaune ta tashi tare da kunna fitilar waya “Dan Allah ka rabu da ni na yi bacci”, daga kwancen ya ce “Haba Asma’u, ki taimaka mani kada na cutu dan Allah, haƙƙina nake so, kuma kema na san kina da buƙatar irinsa a wurina”.

Baki ta taɓe gami da faɗin “Uhm! Ni kam bana buƙata, dan haka ka rabu da ni”. Baƙincikin da ya turnuƙe shi baya misaltuwa, zaune ya tashi yana haɗa ta Allah, amma ta kwanta tare da juya mashi baya. Dafe goshi ya yi da duka hannayensa, shi kaɗai ya san irin azabar da yake ji a jikinshi, wata irin ajiyar zuciya ya riƙa saukewa, wadda ita bata san yana yi ba.

Washegari haka ya tashi jiki ba kwari, duk yadda ya so ya danne wannan mugunta da ta yi mashi a cikin dare amma ya kasa, kamar zai yi kuka ya zo gefen gado ya zauna, dan ita har karfe tara bata tashi ba, duk da kuwa ba bacci take ba, hannunta ya riko “Asmy laifin me na yi maki da ki ke yi mani horon da ba zan iya jurewa ba?”, zare hannunta ta yi tare da tashi zaune, kare ma marainiyar fuskarhi kallo ta yi, a ranta ta ce “Tsololon banza”, a zahiri kuma cewa ta yi “Yanzu kai har akwai abin da zaka nema a wurina tare da ka san bani da lafiya?”, kai ya daga “Eh mana, haƙƙina na aure”, ta ce “Toh wannan rashin tausayi ne”, da mamaki ya ce “Rashin tausyi?”, ta ce “Eh, ka barni in ji da wahalar cikin da ka dora mani mana.”

Kallo mai cike da mamaki ya rika yi mata, daga bisani ya ce “Toh shikenan, amma kada ki manta Allah ne ya daura maki ba ni ba, sannan ki nemi gafarar Shi a kan cutarwar da kika yi mani a daren jiya”, yana rufe baki ya tashi, da mugun kallo ta raka shi har ya fice daga dakin, komawa ta yi ta kwanta, bakinta na fadin “Banza kawai”.

Shi kuwa gidansu ya nufa, inda ya taras da Ummansu ita kaɗai a daki, sauran yaran suna islamiyya, zama ya yi a kujera suka gaisa, daga nan kuma ya dafe goshi ya yi shiru.

Cike da rashin jin daɗin yanayinshi ta ce “Ya aka yi ne Malam Abashe?”, dauke hannunsa ya yi daga goshin ya ce “Bana jin dadi ne Ummah”, ta ce “Kuma ka fito?”, ta yi mashi wannan tambayar ne dan ta bugi cikinshi, kuma ta samu sa’ar jin abin da take so, dan cewa ya yi “Wajen ta fi daɗi Ummah”, ta ce “Koh?”, shiru ya yi, ta ce “Toh Allah ya sawaƙe”, ya ce “Amiin.

Maganar zuwan Abeeda gidan ta yi mashi, cewar sai ta dawo daga Islamiyar zata je ta yi ma Asma’u aikin gidan, da mamaki sai cewa ya yi “A’a ta barshi, gidan ba wani datti sosai”, Ummansu ta ce “Duk da haka dai, in dai ba so kake gidan ya yi dattin da za’a wahala idan an tashi share shi ba.” Ƴar hira suka taba sama-sama, daga bisani ya tashi ya tafi.

Tunda kuma ya bar unguwar bai sake waiwayar ta ba, Asma’u kuwa haka take so. Nafeesa na zuwa ta wartsake suka yi da hirarasu ta ƴan gida ɗaya. Tuwon-ruwan da Aunty ta bada a kawo mata shi ta wuni ci, Nafeesar kuma ta girka taliya da manja ta ci, bayan sun gama kwaɗayinsu sun dawo daki ne Nafisa ta dauki wayar Asmas’u ta jujjuya kana ta ce “Abbas na ji da ke Aunty Asma’u, muma Allah ya bamu miji mai kula irinsa”, saboda Nafeesa babu ƙaryar rayuwa a ranta, ta yadda cewa ita talaka ce, kuma bata ƙallafa ma ranta sai ta samu abin da ya fi ƙarfinta ba.

Harararta Asma’u ta yi “Uhm! Gulma kawai, Abbas ɗin har wani mijin a zo a gani ne da kike fatan samun irinsa?”,

Nafeesa ba ta taɓa zaton fitowar irin wannan magana daga bakin Asma’u ba, cewa ta yi “Aikuwa Abbas mutum ne Aunty Asma’u”, harararta Asma’u ta yi “A wurinku ba.”

Abinda Nafeesa ta ɗauka ƙila faɗan mata da miji ne sukayi, fara zayyano mata Alkhairorin Abbas ta yi, a fusace ta miƙa hannu “Ba ni wayata, kuma a chanja labari”, miƙa mata wayar Nafeesa ta yi tana ƴar dariya, tunda Asma’u ta karɓa kuma bata sake magana ba.

Nafeesa na ganin haka ta miƙe “Bari in je gidansu Abbas ma”, baki Asma’u ta yamutse, “Sai kin dawo.”

A taƙaice ta ce “Toh”, sannan ta ɗauki mayafinta ta fito, tana zura takalma ta nufi gidansu Abbas, Sosai kuma a gidan aka tarbe ta. Hira suka sha saboda dama akwai sanayya a tsakaninsu. Da ta tashi tafiya kuma Ummansu Abbas ta bata dari biyu, tare da curry mai yawa ta kai ma Aunty.

Bayan fitarta Abeeda ta ce ma Ummansu “Wannan ta fi waccan wayau”, wuƙa Ummnsu ta soka ma zancen ta ce “Ke ni bani son gulma”, yar dariya Abeeda ta yi “Umma ke dai bakya son laifinta”, Ummansu ta ce “Eh, ko da wani abu?”, dariya sosai Abeeda ta yi “A’a babu Ummanmu, Allah ya barki da surukar nan taki” ta ce “Amiin dai.”

Nafeesa na shiga gidan Asma’u Abbas ya dawo, fuskarsa cike da annuri suka gaisa, ita kuma Asma’u ta hakimce ko motsawa bata yi ba, tambayarta ya yi “Madam ya jikin?”, kamar an tilasta mata magana ta ce “Da sauki”, bedroom ya shiga ya dan zauna, a tsammanisa zata shigo, amma shiru, fitowa ya yi ya taras tana toshe hanci, lokaci daya kuma tana fadin “Dan Allah ki sa wannan currin a jaka, amai zai sanya ni”, da hanzari ya dubi Nafeesa, “Taimaka mata ki sa shi a jaka dan Allah”, duk da ya ji ba dadi saboda ya gane na gidansu ne, kawai sai zuciya ta ruwaita mashi ta yi haka ne dan ta bata mashi rai, sai dai basarwa ya yi ya fice tsakar gida.

Nafeesa kuwa da ma shirin tafiya take, ta fito kenan Abbas ya fito daga kitchen “Ba dai tafiya ba?”, ta ce “Aikuwa”, ya ce “Bari in kai ki to”, cike da jin dadi ta ce “Aikuwa nagode”, daki ya koma ya kira Asma’u, tana zuwa ya tambaye ta me zata ba Nafeesa, nan ta sanar da shi ta kawo masu tuwon ruwa, dubu daya ya bata ya ce ta ba Nafeesar.

Tana fitowa ta damka ma Nafeesa kudi, aikuwa taki karba, aka kaɗa ta dambu taliya amma ta ƙiya saboda tausayin Abbas da kawai ta ji ya kama ta, Asma’u kuwa ta ji haushin ƙin karɓar kuɗin.

Har soro Asma’u ta raka ta tana tambayar ta “Sai yaushe?”, ta ce “Sai kin haihu”, dariya Asma’u ta yi “Ashe ma”, Abbas ma dariya ya rika yi.

Har gida ya kai Nafeesa, ya kuma shiga suka gaisa da Aunty tare da yi mata godiyar tuwon ruwa. A masallacin kusa da gidan ya yi sallar magrib da Isha’i. Da zai fita unguwar kuma ya biya wurin da ake sayar da Naman kai ya siyo ma Asma’u. Da yake ba kunya a idonta sai ga shi ta ci mai isarta.

Cikin dare kuwa da ƙarfi da yaji ya karbi hakkinsa, kuka ta rika yi mashi kamar ranta zai fita, dan ji ta rika yi kamar a daren farko, lallashinta ya shiga yi haɗe da faɗin “Asma’u so kike na kauce hanya?”, a fusace ta ce “Ka kauce mana, kai ne da zunubi ba ni ba”, dariya ya yi son ranshi. tunda kuma ya samu bukatarshi ta biya sai ya fara yin nisa da ita, saboda in dai suna tare a wuri daya toh bai da nutsuwa. Ba tun yau ba kuma ta fi bukatar haka.

Ta ɓangaren zuciyarta kuma tana nan cike da tunanin Nas, kullum ta kan ware mashi lokaci na musamman wanda take tunaninsa. Watarana kuwa sun je unguwa, daidai traffic light mota irin ta Nas ta tsaya a gefensu, wata irin faɗuwar gaba ce ta samu kanta a ciki “Wannan kamar Nas?”, ta kuma jefo ma kanta tambaya. Zuge glass din motar da ya yi ne ya ya kore mata tantamar da ke ranta, cigaba da faɗuwa gabanta ya yi, har ta rasa gane ina take.

“Maigida barka da wuni” da Abbas ya ce ma Nas ɗin ce ta dawo da ita hayyacinta, duba ta kai ga yalwatacciyar fuskar Nas ɗin lokacin da ya dubi Abbas ya ce “Barka dai Malam Abbas, ya iyali?”, wani irin kyau na musamman ta ga ya ƙara mata a cikin blue ɗin shaddarsa, take ta ji wani mahaukacin son shi ya ta so mata, ka sa ɗauke idanunta ta yi a kansa har ya ja motarshi lokacin da aka ba su hanya, wanda har ta kai ga Abbas ya ja mashin ɗinsa sun ta fi ba tare da ta sani ba.

Abbas kuwa tambayar ta ya yi “Asmy mutumin can a unguwarku ya ke ko?”, shiru ya ji ta yi, sake magana ya yi “Kin ji Asmy???”


INA MAI BA MASOYAN WANNAN LITTAFIN HAKURIN JINKIRIN POSTING DA AKE SAMU. INA SO KU SANI WANNAN LITTAFI YANZU NAKE TYPING ƊINSHI, KUMA A GASKIYA INA DA NAWAR RUBUTU, SANNAN TA WANI ƁANGAREN RASHIN COMMENTS ƊINKU NA SARE MANI GUIWA, A CIKIN JERIN ƊARURUWAN MUTANEN DA KE BUƊA SHAFIN, BAI FI MUTUM UKU KO HUDU KE COMMENTS BA, SU KAM INA MATUƘAR GODIYA A GARE SU MASU COMMENTS, AMMA SAURAN BAN SAN ME ZAN CE MAKU BA.

DAN HAKA INA KIRA GA MASOYAN WANNAN LITTAFI DA SU BUƊE ACCOUNT A BAKANDAMIYA KUMA SU RIKA COMMENTS, HAKAN NE ZAI ƘARA MANI ƘWARIN GYUIWAR CIGABA DA KAWO MAKU SHI A KAN LOKACI, DAN FATANA SHI NE IN GAMA LITTAFINNAN KAFIN AZUMI DA YARDAR ALLAH. INA YI MA KOWA FATAN ALKHAIRI.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Cikin Baure 8Cikin Baure 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×