Skip to content

Cikin Baure 3

Part 3 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Zuciyata kamar zata faso ƙirjina ta fito na kwanta tare da lulluɓe kaf jikina a lokacin da na ji shigowar Abbas a tsakar gida, cike da tsanar sa dake ta addabar raina na ce “Zaka gane shayi ruwa ne tunda har ka yi gigin aurena”, sai da na haɗe gululun da ya tokare mani zuciya sannan na faɗa duniyar tunanin Nas, inda na ke jin da shi ne zai shigo a zaune zai same ni cikin lulluɓi kamar kowace amarya, kuma da hannayensa masu daraja zai yayen mayafin, inda ni kuma zan tarbe shi da ƙayataccen murmushin da zai tabbatar da na yi farincikin kasancewa da shi a wannan dare.

Sautin muryar Abbas da na tsinkayo a falo ne ya katse mani tunani, inda na ji yana faɗin “Godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mani ranar da zan kasance cikin iyalina”. Yadda ya ƙarashe maganar cikin farinciki ne ya sa ni yin magana a ƙasan raina, inda ni ma na ce “Tabbas yau za ka kwana cikin iyalinka, sai dai kwana ne mai cike da baƙinciki, don ba zaka mori komai daga gare ni ba”, domin na ɗauri niyyar fara lasa mashi gubar ƙiyayyar da nake mashi tun a daren yau, bisa ga tozarcin da ya yi mani.

Kamar daga sama na ji sallamarsa a bedroom, hakan kuma na nuna da sanɗo ya shigo kamar munafiki, ni kuwa dama ko Nas da nake mutuwar so ne ba zan amsa sallamar a fili ba, bare kuma Abbas da na tsana, domin shi ne ya yi mani kutse lokacin da nake ƙoƙarin tallata soyayyata ga Nas.

“Ya Salam! Waye ya bar mani amarya a duhu?”, ya faɗa cikin murya mai sanyi tare da kunna fitilar ɗakin, don tun bayan fitar su Khadija na kashe ta.

Daga cikin lulluɓin da nake na yi ƙwafa bisa ga faɗin amaryarsa da ya yi.

Ina jin sadda ya tako har har bakin gadon, na san yadda yake mararin wannan rana dole ya taɓa ni, hakan ya sa na yi tanadin rashin kunyar da zan yi mashi.

Zama ya yi a gefena tare da ambatar sunana cikin taushin murya, shiru na yi kamar mai bacci, cikin wani irin salo ya ɗan ja mayafin ta ƙafafuna har kaina ya fito, leƙo da fuskarsa ya yi a saitin tawa ya ce “Ko kin yi bacci ne?”, wata irin faɗuwa gabana ya yi, don tunda nake namiji bai taɓa kusantowa gare ni kamar yadda Abbas ya yi ba, wannan faɗuwar gaba da kuma fusatar dake raina ce suka haɗa hannu wurin sa ni wurga mashi mugun kallo, jikinsa a sanyaye ya koma ya zauna. A fusace na tashi zaune da nufin zabga mashi rashin mutunci, sai dai ina saka idanuna cikin nashi na kasa magana saboda kwarjinin da ya yi mani.

A hankali na lumshe idanuna tare da fashewa da kukan kasancewarsa a gabana ba Nas ba, cike da damuwa ya riƙo hannayena “Asma’u kuka kuma; me ya faru?”, fizge hannun na yi gami da goge hawaye kamar ƙaramar yarinya, shi kuwa take ya kiɗime, don na daɗe da sanin fushina babbar barazana ce ga farincikinsa.

Neman ba’asin kukan ya shiga yi, ba tare da na ɓoye mashi ba na ce “Me ya sa ka tozarta mani ƙawaye?”, amma a baɗini kukana ba na abin da ya yi ma ƙawayena ne ba.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin “Wannan ne musabbabin kukan Asmy?”, a ƙufule na kalle shi, don alamu sun nuna bai ɗauki laifin da girma ba, cike da kulawa ya matso dab da ni tare da share mani hawaye da hannayensa, lokaci ɗaya kuma ya ce “Allah ya huci zuciyar Gimbiya Asma’u, tsabar kishin ki da nake ne ya hana ni shigowa da abokaina, ta wani ɓangaren kuma ina son martaba maki ƙawaye ne. Ki sani, darajar ‘ya’ya mata ta wuce a shigo musu da game garin maza a cikinsu, don haka ki gafarce ni”, hannayensa a kunne ya cigaba da lallashina, na so na bijire ma lallashin, amma iya kalaminsa ya sa bakina mutuwa murus!.

Koda ganin haka sai ya miƙe tare da kama hannuna cikin kulawa “Mu je falo ki ƙara sanyaya zuciyarki da lemu”, da tsokana ya ƙarashe maganar yana kallo na, zare hannuna na yi gami da faɗin “Ni bana sha”, idanu ya ɗan zaro yana dariya “Ki rufa mani asiri don Allah, idan baki ƙoshi ba ta ya za ki taya ni sauke gajiyar da na ɗauko?”, gani na yi yana shirin saɓa ta, ba arziki na diro daga kan gadon, hannunsa cikin nawa muka fita ɗan madaidaicin falona mai ɗauke da kujeru guda huɗu, a saman bangon kuma ƙaramar tv ce manne tana kallon ƙofar bedroom ɗina.

A kan ɗan tsakatsakiyar carpet ɗin dake shimfiɗe a ƙasa ya taimaka mani na zauna, fita ya yi daga falon, ko minti biyu ba’a yi ba sai ga shi ya dawo da dabban tray na unbreakable, a sama kuma plates ne guda biyu da cups gami da wuƙa, zamansa ke da wuya ya jawo manyan ledoji guda uku da tunda na zauna ƙamshin abin da ke cikinsu ke shiga ta ƙofofin hancina.

Manyan kaji ne guda biyu, ɗaya Peppe chicken, ɗaya kuma gasassa, ɓangare ɗaya kuma balango ne da shi ma ya ji gashin da sai da yawuna ya tsinke. A leda ta biyu kuma FarmFresh (Strawberry) Yourghout ne da kuma lemun Exotic, ita kuma ta ukun Fruits ne da suka haɗa da Apple, Banana da kuma Inabi, haƙiƙa ina da maitar duka abubuwan da ya fiddo, sai dai anya kuwa zan iya ci?.

Ina cikin tababa ne na ji ya sauko mani da mayafina a ƙasan kafaɗata, lokaci ɗaya kuma ya gutsuri peppe cicken ya miƙo mani a baki “Buɗa bakin na ciyar da ke rabin raina”, kallon sa na yi maimakon karɓa, sosai na ga zallar ƙauna ta a tattare da shi, domin ƙwayar idanunsa har wani ƙanƙancewa take saboda iya sarrafa ta wurin kallo na.

“Ina ma Nas ne ke mani wannan kallon”, abin da kawai na ji zuciyata ta faɗa, wata irin ƙuna na ji ta taso mani a rai, ba don na so ba na karɓi naman. Da kansa ya riƙa yagar kazar da balangon yana cika mani baki, ni kuwa tamkar magani nake jin naman, hakan ya sa ina taunawa ina kuka.

Abbas bai tambaye ni dalilin kukan ba tunda bai hana ni cin naman ba, sai dai jikinsa a sanyaye ya riƙa ba ni har sai da na ce na ƙoshi.

Murmushi mai sauti ya yi tare da faɗin “Toh a rama ma kura aniyarta”, da hanzari na tsagaita kukan tare da duban shi ina son sanin manufar maganarsa, ido ya kashe mani tare da ɗan langaɓar da kai “Ina nufin nima ki bani kazar amarcin”.

Ƙasa na yi da kaina ina wasa da hannuna, ganin haka sai bai sake magana ba. Yourghout ya tsiyaya mani a cup na ɗan sha, fruits ɗin kuwa ban ci komai ba duk da yadda nake son Apple.

Da kansa ya ɗan ci kazar da fruits ɗin, bayan ya gama ne ya matsar da komai gefe, irin zaman nan na harɗe kafafu ya yi muna fuskantar juna, gyaran murya na ji ya yi wanda ke nuna magana mai muhimmanci zai yi, ni kuwa tuni na ƙara tattaro nutsuwata na miƙa mashi, sai dai fa idanuna na ƙasa.

“Asma’u”, ya ambaci sunana cike da kulawa, shiru na yi kamar ba da ni yake ba, sake cewa ya yi “Ni kam ban ji daɗin da kunya ta hana mani amarya sakewa a irin wannan lokacin ba”, ɗago kaina na yi na dube shi a karkace, a raina na ce “Kai a suwa da zan ji kunyar ka”, a zahiri kuma sai dai na ɗan motsa baki tare da maida kaina ƙasa.

Ƙara matsowa ya yi har guiyawunmu suna taɓa juna, sassauta murya ya yi, lokaci ɗaya kuma ya ce “Asma’u! Kunya adon mace ne, ba zan ji komai ba don kin bayyana ta ayau”, ɗan saurarawa ya yi sannan ya ɗora da “Aahmm! Asma’u! Kawai ina son faɗa maki irin son da nake maki ne, ina fatan idan kika ji kema zaki faɗa mani irin son da kike mani”.

Tunda na shigo gidan ban ji maganar da ta sanya ni dariya har ƙasan raina ba sai wannan, sai dai sautin dariyar bai fito ba, amma fuskata ta nuna lokacin da na kalle shi, “Ashe kuwa zaka mutu in dai sai ka ji kalar son da na ke maka”, na ƙarashe maganar a raina ina kallon ƙwayar idanunsa.

Shi kuwa tuni ya fara zayyana mani yadda yake so a, inda ya ce “Asma’u ina son ki, son da ban san ya zan fasalta maki shi ba, amma a taƙaice dai so ne irin wanda ake cewa idan ba ke ba sai rijiya”.

A zuci na ce “Ashe kuwa ga ka can cikin rijiya gaba dubu, domin ni bana son ka, kuma ban shirya rayuwa da kai ba”

A zahiri kuwa murmushin mugunta na yi, sai dai shi so ya rufe mashi ido har ya kasa gane na mugunta ne. Dafa mani cinya ya yi da hannunsa na hagu, kuma har cikin raina na ji wannan dafawar, har ban san lokacin da na ce “Na’am” lokacin da ya ce “Asma’u” ba.

Kallon sa na yi lokacin da yake faɗin “Insha Allah zan faranta ranki gwargwadon iyawata, zan sanya ki zama mace ta nunawa a cikin mata, ina son ki, ina ƙaunarki da dukkan ziciyata”.

Haka ya ƙaraci surutansa da na ke jin su a matsayin shirme, bayan ya gama ne ya tambaye ni kalar son da nake mashi, ban wani wahal da shari’a ba na ce “Ni a aikace zan gwada maka matsayinka a wurina”.

“Da gaske?”, ya tambaye ni yana dariyar jin daɗi, na ce “Sosai ma”, gira ya ɗage tare da faɗin “Wow, to taso mu yi wanka da Sallah sai ki fara gwada mani”, miƙewa ya yi tare da kama hannuna na miƙe nima.

Bedroom na koma na cire kayan jikina, zane na ɗaura tare da zura hijabi na fito, inda shi kuma tuni ya kauda ragowar abin da muka ci zuwa kitchen.

Ina tsaye a ƙofar ɗaki ne na ji ya rungumo ni ta baya “In kai maki ruwan ki fara wankan ko?”

Zare mashi hannu na yi na ce “Eh”, a taƙaice, don raɓar jikina da yake ba ƙaramar ƙona raina take ba.

Akwai wata ƙatuwar roba baƙa a saƙon dake tsakanin windon falona da kuma bangon kitchen, nan ya shiga ya ɗebo ruwa a bokiti ya kai mani banɗaki.

Ina shiga na facaccala wanka na fito. Zaune na same shi a kan rijiyar dake dab da shiga banɗakin, miƙewa ya yi tare da ba ni butar da ke gefensa cike da ruwa “Ki yi alwala, idan na shigo sai mu yi sallah”.

Ƴar harara na wurga mashi wadda bai lura da ita ba, don tuni na yanke shawarar ba zan yi wannan sallar da ake yi ba, saboda bana buƙatar albarkar da zamu roƙa a cikinta. Cikin dakiya akan ƙaryar da zan shirga na ce “Ai period nake”.

Labarin zuciya a tambayi fuska, tun kafin Abbas ya furta “Inna li Llahi..” na ga damuwa kwance a fuskarshi a cikin hasken fitilar da ya garwaye tsakar gidan.

Ni kuwa na ji daɗin haka, don dama neman hanyar da zan fara ƙuntata mashi nake, idanunmu haɗe da juna ya tambaye ni a sanyaye “Tun yaushe kika fara?”

Ba tare da na yi nazarin kwanakin al’adata na dab da zuwa ba na ce “Yau kwana uku”. Sake tambaya ta ya yi “Toh yaushe zaki gama?”, a taƙaice na ce “Jibi”, ido ya lumshe gami da buɗewa sannan ya ce “Okay”, aje butar ya yi sannan ya jawo ni a jikinsa lokacin da nake shirin tafiya, cikin kasalalliyar murya ya ce “Ban so haka ba Asmy, amma ba komai, kwana biyu ba yawa ai”.

Murmushin yaƙe na yi sannan na zare jikina na nufi cikin ɗaki. Kai tsaye wardrob ɗina mai guda uku na buɗe, wata doguwar riga mai kauri na sanya, gami da kashe fitilar ɗakin na kwanta, ina jiyo lokacin da ya shiga banɗaki yana wanka, dariyar mugunta na yi don na san na gama watse mashi shirinsa na yau.

Alhaji Nas ɗin dai da zuciyata ke bugawa da sunansa na fara tunani. Har a cikin raina nake jiyo yadda rayuwar zata kasance idan shi ne angon a wannan daren, hakan ne ya yi sanadiyyar mantar da ni wani Abbas can da ke wanka.

Sai da na ji motsin sa a falo ne na dawo daga tunanina mai matar mani da jiki “Ɗan wahala”, na furta lokacin da ya shigo bedroom ɗin. Bana ganin shi saboda na ba shi baya, amma kunnena na haska mani duk inda ya nufa a bedroom ɗin. Wadrobe ya buɗe ya fiddo kaya ya sa, daga nan kuma ya nufi mirror ya yi wanka da turaren da na san tsanar sa ce ta sa na tsani turaren.

Kan gadon ya hau, ba tare da ɓata lokaci ba ya maido ni a jikinsa, cikin muryar da bata fita ya ce “Asma’u duk da period ɗin mu kasance a haka, na san zamu samu nutsuwa”.

Duk yadda Abbas ya taɓa ni sai na ji a jikina, sai dai dole in yi yaƙi da haka tunda ba shi na yi nufin mallaka ma ruhi da gangar jikina ba.

Matsawa na yi gaba na ce “Ka bari dai na gama period ɗin”, matsowa ya yi “Haba dai, ai ba abin da zan maki, kawai dai ki taimake ni..”, sai kuma ya yi shiru.

“In taimake ka in maka me?”, na faɗa ina zare hannunsa dake zagaye da ni”, amsa ya ba ni “Ki yi mani komai ma Asmy”.

A taƙaice dai duk yadda Abbas ya so na kwanta kusa da shi amma na ƙiya, haka ya koma gefe yana faɗin “Anya ma kina so na?”, shiru na yi kamar ba da ni yake ba.

Haka ya gaji da surutansa ya yi shiru, na yi imani da Allah da ƙunci ya kwana, kamar yadda nima na kwana da ƙuncin tunanin Nas.

Washegari da misalin ƙarfe huɗu da rabi na Asuba na tashi da nufin yin sallah, domin duk rintsi Sallar Asuba bata wuce ni, a falo na samu Abbas akan sallaya yana jan carbi, tambayata ya yi “Me zaki yi a waje?”

Na ce “Sallah”, da mamaki ya dube ni “Sallah, ko period ɗin ya ɗauke ne cikin dare?”, daburcewa na yi tare da faɗin “Wai, a’a banɗaki zan shiga”, kai ya jinjina “Okay”.

Fita na yi na shiga ban ɗakin, tunanin yadda zan yi sallah ba tare da Abbas ya sani ba na shiga yi, don muddin bai je masallaci ba toh ina tsaka mai wuya.

Buƙata ta na biya gami da yin alwala kamar yadda na samu shawara daga zuciyata. Fitowa na yi na koma ɗaki na kwanta, cikin ikon Allah Abbas ya ce mani masallaci zai je. Aikuwa yana fita na sauko na yi sallata a gurguje na koma na kwanta. Bacci mai nauyin gaske ya ne ɗauke ni, har Abbas ya dawo ya kwanta a bayana ban sani ba, sai da falka da ƙarfe bakwai na gan shi kamar kaska a jikina.

Batu na gaskiya daga jiya zuwa wayewar gari ni kaɗai na san yadda nake ji a gidan, Abbas na da duk wata kamala da mace zata so shi, sai dai ni kawai bana ra’ayinshi, shi ya sa nake jin kamar zuciyata zata buga,saboda Nas ne zaɓin raina ba shi ba.

Kuma duk hanyar da zan bi don kada zamanmu ya ɗore sai na bi, don haka ne ma na fara sha ma danginsa mur tun daga jiya har kawo yau da suke ta zarya ganin Amarya.

Na san idan danginsa suka fara ƙi na, toh kuwa ba inda zamanmu zai kai. Ta ɓangarensa kuma hana shi kaina kaɗai zai iya raba ni da shi, bare kuma akwai wasu hanyoyin. Don haka yana ji yana gani na gagare shi taɓawa saboda ƙaryar period, na san kafin kwana biyun da na ce mashi zan yi na samu wani matakin ɗauka.

Shi kuwa duk ya damu, sosai ya ke nuna mani zaƙuwarsa a kaina, sai dai fa na matuƙar tausaya mashi da kuma kaina, a ranar da na ce mashi zan gama period ɗin, a ranar ne asalin period ɗina ya dawo.

“Toh ya zan yi ma?”, na tambayi kaina bayan na fito daga banɗaki, domin zan iya sallar ƙarya, amma Abbas na gani zai ce na samu tsarki, kuma dole ya bijiro da buƙatarsa wadda sai dai ya mutu, don ba zan biya mashi ita ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Cikin Baure 2Cikin Baure 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×